TALIFIN NAZARI NA 29
Yadda Za Ka Yi Shiri don Kunci Mai Girma
“Ku zauna da shiri.”—MAT. 24:44.
WAƘA TA 150 Mu Bi Allah Don Mu Sami Ceto
ABIN DA ZA A TATTAUNA a
1. Me ya sa yin shiri kafin balaꞌi ya faru yake da muhimmanci?
ZAMA da shiri yakan ceci ran mutum. Misali, idan aka yi balaꞌi, mutane da suka yi shiri tun kamin ya faru za su fi samunsa da sauƙi su tsira kuma su taimaka ma wasu. Wata ƙungiyar ba da agaji a Turai ta ce: “Yin shiri sosai yana ceton rayuka.”
2. Me ya sa muke bukatar mu yi shiri don ƙunci mai girma? (Matiyu 24:44)
2 Za a soma “azaba mai zafi,” wato ƙunci mai girma farat ɗaya, kamar yadda balaꞌi yake zuwa farat ɗaya. (Mat. 24:21) Bambancin kawai shi ne, ba zai zo mana ba zato ba, don mun san yana zuwa. Wajen shekaru 2,000 da suka shige, Yesu ya ce wa mabiyansa su yi shiri don babbar ranar nan. (Karanta Matiyu 24:44.) Idan ranar ta same mu a shirye, za mu iya jimre abubuwa da za su faru kuma mu taimaki ꞌyanꞌuwanmu su jimre.—Luk. 21:36.
3. Ta yaya halin jimiri da tausayi da kuma ƙauna za su taimaka mana mu yi shiri don ƙunci mai girma?
3 Ga wasu halaye uku da za su taimaka mana mu yi shiri don ƙunci mai girma. Misali, me za mu yi idan aka ce mu yi waꞌazin hukunci kuma mutane suka yi gāba da mu? (R. Yar. 16:21) A wannan lokacin, za mu bukaci jimiri don mu iya yin abin da Jehobah ya ce da tabbacin cewa zai kāre mu. Idan kuma ꞌyanꞌuwanmu suka yi hasarar abubuwan da suka mallaka kuma fa? Me za mu yi? (Hab. 3:17, 18) Za mu bukaci halin tausayi. Shi ne zai motsa mu mu taimaka musu da abubuwan da suke bukata. Me za mu yi idan ƙasashen duniya suka haɗa kai kuma suka kawo mana hari, har hakan ya sa mu dole mu kasance a wani wuri tare da ꞌyanꞌuwanmu na tsawon lokaci? (Ezek. 38:10-12) In ba ma ƙaunar su sosai, zai yi mana wuya mu zauna lafiya da juna.
4. Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa muna bukatar mu zama masu jimiri da tausayi da kuma ƙauna?
4 Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu mu ci gaba da zama masu jimiri, da tausayi da kuma ƙauna. Luka 21:19 ta ce: “Idan kuka jimre, za ku tsira.” Kolosiyawa 3:12 ta ce: “Ku ɗauki hali na jin tausayin juna.” 1 Tasalonikawa 4:9, 10 kuma sun ce: “Ku da kanku Allah ya koya muku cewa ku ƙaunaci juna. . . . Sai dai muna ƙarfafa ku, ꞌyanꞌuwa, ku ƙara yin haka ƙwarai da gaske.” ꞌYanꞌuwa da aka ambata a waɗannan ayoyin sun riga sun nuna cewa su masu jimiri, da tausayi, da kuma ƙauna ne. Duk da haka, suna bukatar su ci gaba da nuna waɗannan halayen. Abin da mu ma muke bukatar mu yi ke nan. Me zai taimaka mana? Za mu bincika yadda Kiristoci a ƙarni na farko suka nuna kowanne cikin halayen nan. Saꞌan nan, za mu ga yadda za mu bi halinsu. Yin hakan zai sa mu zauna da shiri don ƙunci mai girma.
KA ƘARA ZAMA MAI JIMIRI
5. Mene ne Kiristoci na farko suka yi don su iya jimre matsalolinsu?
5 Kiristoci na farko sun bukaci halin jimiri. (Ibran. 10:36) Domin ban da matsalolin da kowa yake fuskanta a lokacin, sun yi fama da ƙarin matsaloli. Shugabannin addinin Yahudawa da kuma Romawa da suke mulki a lokacin, sun tsananta musu. Ban da haka, sun fuskanci tsanantawa a cikin iyalinsu. (Mat. 10:21) A cikin ikilisiya ma, akwai lokutan da suka sha gwagwarmaya da ꞌyan ridda waɗanda suke kawo tasu koyarwa don su raɓa kan ikilisiya. (A. M. 20:29, 30) Duk da haka, waɗannan ꞌyanꞌuwan sun jimre. (R. Yar. 2:3) Me ya taimaka musu? Sun yi ta tunani a kan bayin Allah da su ma suka jimre matsaloli, kamar Ayuba. (Yak. 5:10, 11) Sun roƙi Allah ya ƙarfafa su. (A. M. 4:29-31) Kuma sun mai da hankali ga ladar da za su samu.—A. M. 5:41.
6. Me ka koya daga abin da Merita ta yi don ta iya jimre tsanantawa?
6 Mu ma za mu iya jimrewa idan muna nazari game da waɗanda suka nuna halin jimiri a Littafi Mai Tsarki da kuma littattafanmu, kuma muna yin tunani mai zurfi a kan labarinsu. Abin da ya taimaka ma wata ꞌyarꞌuwa mai suna Merita a ƙasar Albaniya ta jimre tsanantawar da iyalinta suka yi mata ke nan. Ta ce: “Da na bincika labarin Ayuba, abin ya tsotsa zuciyata sosai. Ba ƙaramin wahala ya sha ba, kuma a lokacin bai ma san wa yake jawo masa matsalolin ba. Duk da haka ya ce: ‘Har in mutu, ba zan daina tsare mutuncina [amincina] ba.’ (Ayu. 27:5) Da na yi tunani, sai na ga cewa matsalolina ba su kai kome ba idan aka kwatanta su da na Ayuba. Bai san wa yake jawo masa matsalolin ba, amma ni na san wa yake jawo min nawa matsalolin.”
7. Ko da ba ma fama da babbar matsala a yanzu, me ya kamata mu koyi yi?
7 Wani abu kuma da zai sa mu ƙara zama masu jimiri shi ne, idan muna adduꞌa kullum muna gaya wa Jehobah abubuwa da muke fuskanta. (Filib. 4:6; 1 Tas. 5:17) Wataƙila ba ka fuskantar wata babbar matsala yanzu, amma idan wani abu ya ɓata maka rai, ko ka riƙice, ko abubuwa sun yi maka yawa, kana roƙon Jehobah ya taimaka maka? Idan ka saba roƙon Jehobah ya taimake ka da ƙananan matsalolin da kake fuskanta yanzu, za ka yi saurin neman taimakonsa idan babbar matsala ta same ka a nan gaba. Idan kana hakan, ba za ka yi shakkar cewa Jehobah ya san lokaci, da kuma hanyar da ta fi dacewa ya taimaka maka ba.—Zab. 27:1, 3.
8. Ta yaya labarin ꞌyarꞌuwa Mira ya nuna cewa idan muna jimre matsalolinmu a yau, za mu iya jimre na gaba? (Yakub 1:2-4) (Ka kuma duba hoton.)
8 Idan muna jimre matsalolin da muke fuskanta a yau, za mu iya jimre waɗanda za mu fuskanta a lokacin ƙunci mai girma. (Rom. 5:3) Me ya sa? Domin ꞌyanꞌuwa da yawa sun ce duk lokacin da suka jimre wata matsala, yana ba su ƙarfin jimre wadda za ta taso a gaba. Yadda Jehobah ya taimaka musu suka iya jimrewa yana ƙara sa su gaskanta cewa Jehobah yana tare da su kuma yana so ya taimake su. Wannan bangaskiyar ce ta taimaka musu suka jimre matsalar da ta sake taso musu. (Karanta Yakub 1:2-4.) Wata majagaba mai suna Mira daga ƙasar Albaniya, ita ma ta shaida cewa yadda ta jimre matsaloli a dā ya ba ta ƙarfin jimre na yanzu. Ta ce a gaskiya wani lokaci takan ji kamar matsalolinta sun fi na kowa. Amma da ta tuna hanyoyi da dama da Jehobah ya taimake ta cikin shekaru 20 da suka shige, sai ta ce wa kanta: “Ki ci gaba da riƙe amincinki. Jehobah ya riga ya taimaka miki ki jimre abubuwa da yawa a rayuwa. Don haka kada ki gaji, ki ci gaba da bauta masa.” Kai ma za ka amfana idan ka yi tunani a kan yadda Jehobah ya taimaka maka ka jimre matsalolinka. Tabbas duk lokacin da ka jimre wata matsala, Jehobah yana gani kuma zai ba ka lada. (Mat. 5:10-12) Za ka ga cewa kafin ƙunci mai girma, ka riga ka koyi halin jimiri, kuma za ka ƙudura cewa za ka ci gaba da jimrewa.
KA ZAMA MAI TAUSAYI
9. Ta yaya ꞌyanꞌuwa a ikilisiyar da ke Antakiya na Suriya suka nuna halin tausayi?
9 Ka yi laꞌakari da abin da ya faru a lokacin da aka yi babbar yunwa a Yahudiya. Da ꞌyanꞌuwa a ikilisiyar Antakiya da ke Suriya suka ji cewa ꞌyanꞌuwansu a Yahudiya suna cikin yunwa, sun tausaya musu. Amma ba su tsaya a nan ba, sun ɗauki matakin taimaka musu. Sai “suka yanke shawara cewa su aika wa ꞌyanꞌuwan da suke cikin yankin Yahudiya taimako, kowa daidai ƙarfinsa.” (A. M. 11:27-30) Duk da cewa inda ꞌyanꞌuwa da yunwar ta shafa suke yana nesa da Antakiya, ꞌyanꞌuwan nan sun ce sai sun taimaka musu.—1 Yoh. 3:17, 18.
10. Ta yaya za mu nuna halin tausayi idan balaꞌi ya sami ꞌyanꞌuwanmu? (Ka kuma duba hoton.)
10 Mu ma za mu nuna cewa mu masu tausayi ne idan muka ji cewa balaꞌi ya sami ꞌyanꞌuwanmu. Za mu yi hakan ta wurin ɗaukan mataki nan da nan. Za mu iya tambayar dattawanmu ko akwai aikin da za mu yi don mu taimaka. Mu yi gudummawa don aikinmu na faɗin duniya, ko kuma mu sa ꞌyanꞌuwa da balaꞌin ya shafa a cikin adduꞌa. b (K. Mag. 17:17) Misali, a 2020, an kafa Kwamitin Ba da Agaji fiye da 950 a faɗin duniya, don su kula da ꞌyanꞌuwa da annobar korona ta shafa. ꞌYanꞌuwa da suka yi wannan aikin agajin sun cancanci yabo. Don tausayi, sun yi iya ƙoƙarinsu sun kai wa ꞌyanꞌuwa kayan agaji, kuma sun taimaka musu su ci gaba da bauta wa Jehobah. A wasu wurare ma sun gyara, ko sun sake gina gidajen ꞌyanꞌuwa da wuraren taro.—Ka ga misalin da ke 2 Korintiyawa 8:1-4.
11. Yaya abubuwan da muke yi don tausayi suke sa a ɗaukaka Ubanmu na sama?
11 Idan muka nuna cewa muna tausaya wa ꞌyanꞌuwanmu saꞌad da aka yi balaꞌi, mutane za su lura da hakan. Misali a 2019, wata guguwa mai suna Dorian ta rusa Majamiꞌar Mulki a yankin Bahamas. Da ꞌyanꞌuwa suke sake gina Majamiꞌar Mulkin, sun tambayi wani ɗan kwangila nawa zai yi musu wasu ayyuka. Sai mutumin ya ce: “Zan yi muku aikin kyauta. . . . Da kayan aikin, da leburorin, duk zan kawo. . . . Ina so in yi wa ƙungiyarku wannan gudummawar, domin gaskiya yadda kuke ƙaunar junanku yana burge ni.” Yawancin mutane a yau ba su san Jehobah ba. Amma da yawa a cikinsu suna lura da abin da Shaidun Jehobah suke yi. Abin ban ƙarfafa ne mu san cewa abubuwa da muke yi don muna tausaya wa ꞌyanꞌuwanmu, suna sa mutane su so bauta wa Allahnmu “mai yawan tausayi.”—Afis. 2:4.
12. Ta yaya zama masu tausayi yanzu zai taimaka mana mu yi shiri don ƙunci mai girma? (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 13:16, 17)
12 Me ya sa za mu bukaci halin tausayi a lokacin ƙunci mai girma? Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa waɗanda suka ƙi goyon bayan gwamnatocin duniyar nan, za su fuskanci matsaloli a yau da kuma a lokacin ƙunci mai girma. (Karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 13:16, 17.) Ƙila hakan ya sa ꞌyanꞌuwanmu su shiga cikin bukata. Idan Sarkinmu, wato Yesu Kristi ya zo yin hukunci, bari ya same mu muna nuna wa ꞌyanꞌuwanmu halin tausayi kuma ya ce mana mu zo mu gāji mulkin.—Mat. 25:34-40.
KA ƘARA ƘAUNAR ꞌYANꞌUWANKA
13. Kamar yadda Romawa 15:7 ta ce, mene ne Kiristoci na farko suka yi don su ƙara ƙaunar juna?
13 A zamanin dā, kowa ya san cewa Kiristoci suna ƙaunar juna, amma nuna wannan ƙaunar ba ta yi musu sauƙi ba. Wasu ꞌyanꞌuwa a ikilisiyar Roma Yahudawa ne da a dā suna bin Dokar Musa. Wasu kuma ba Yahudawa ba ne, suna da tasu alꞌadun. Wasu bayi ne, wasu kuma ba bayi ba ne. Ƙari ga haka, da alama cewa wasu cikinsu masu arziki ne, har suna da bayin kansu. Me ya taimaka musu su ci gaba da ƙaunar juna duk da cewa yanayinsu ba ɗaya ba ne? Manzo Bulus ya ƙarfafa su cewa su “karɓi juna hannu biyu-biyu.” (Karanta Romawa 15:7.) A Helenanci, kalmar da Bulus ya yi amfani da ita a nan tana nufin mu karɓi mutum da alheri ko kuma mu mai da shi abokinmu. Misali, Bulus ya gaya wa Filimon yadda zai karɓi bawansa da ya komo wurinsa hannu biyu-biyu, ya ce: “Ka karɓe shi daidai yadda za ka karɓe ni.” (Fil. 17) Da Biriskila da Akila suka haɗu da Afolos wanda bai san koyarwar Kristi kamar su ba, su ma sun karɓe shi hannu biyu-biyu ta yadda “suka ɗauke shi,” wato yadda suka jawo shi kusa da su. (A. M. 18:26) Ko da yake yanayin Kiristocin nan ba ɗaya ba ne, ba su bar hakan ya raɓa kansu ba. A maimako, sun karɓi juna hannu biyu-biyu.
14. Ta yaya ꞌYarꞌuwa Anna da maigidanta suka nuna cewa suna ƙaunar ꞌyanꞌuwa?
14 Mu ma za mu nuna cewa muna ƙaunar ꞌyanꞌuwanmu idan muka mai da su abokanmu. Su ma idan suka ga haka, za su ƙaunace mu. (2 Kor. 6:11-13) Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Anna da maigidanta sun shaida hakan. Jim kaɗan bayan da suka isa wata ƙasa a yammacin Afirka a matsayin masu waꞌazi a ƙasar waje, sai aka soma annobar korona. Ga shi ba dama su je taro da ꞌyanꞌuwa a Majamiꞌar Mulki. Ya za su nuna wa ꞌyanꞌuwan cewa suna ƙaunar su? Sun dinga kiran ꞌyanꞌuwan ta bidiyo, kuma suka gaya musu cewa suna so su tattauna da su don su san juna kuma su zama abokai. ꞌYanꞌuwan sun ji daɗin hakan kuma sun dinga kiran maꞌauratan suna aika musu saƙonni. Me ya sa suka yi ƙoƙari don su kusaci ꞌyanꞌuwa da ke ikilisiyar? ꞌYarꞌuwa Anna ta ce: “Ba zan taɓa manta da irin ƙaunar da aka nuna min da iyalina a lokacin daɗi da lokacin wuya ba. Wani babban abin da ke motsa ni in nuna wa ꞌyanꞌuwa ƙauna ke nan.”
15. Me labarin Vanessa ya koya maka game da ƙaunar dukan ꞌyanꞌuwa? (Ka kuma duba hoton.)
15 Yawancinmu muna a ikilisiyoyi da akwai ꞌyanꞌuwa daga wurare dabam-dabam kuma halinsu ya bambanta. Wani abin da zai taimaka mana mu ƙara ƙaunar su shi ne, mu dinga lura da halayensu masu kyau. A dā, wata ꞌyarꞌuwa mai suna Vanessa a ƙasar New Zealand, ba ta jin daɗin yadda wasu ꞌyanꞌuwa a ikilisiya suke yin abubuwa. Amma sai ta ce maimakon ta share su kawai, za ta ƙara yin cuɗanya da su fiye da dā. Da ta kusace su, sai ta ga abin da ya sa Jehobah yake ƙaunarsu. Ta ce: “Tun lokacin da maigidana ya zama mai kula da daꞌira, mun soma kasancewa tare da ꞌyanꞌuwa masu hali iri-iri kuma ba ya min wuya in zama abokiyarsu. Yanzu ina jin daɗin yadda ake da ꞌyanꞌuwa iri-iri a ikilisiya. Ba mamaki Jehobah ma yana jin daɗin hakan, domin shi ne ya jawo mu kuma ya haɗa mu tare.” Idan muka yi ƙoƙari kuma muka kasance da raꞌayin Jehobah game da ꞌyanꞌuwanmu, hakan zai nuna cewa muna ƙaunarsu da gaske.—2 Kor. 8:24.
16. Me ya sa za mu bukaci ƙaunar ꞌyanꞌuwa sosai a lokacin ƙunci mai girma? (Ka kuma duba hoton.)
16 Za mu bukaci ƙaunar ꞌyanꞌuwa sosai a lokacin ƙunci mai girma. Ta yaya Jehobah zai kāre mu a lokacin? Ku yi laꞌakari da abin da Jehobah ya ce bayinsa su yi a lokacin da aka kai wa birnin Babila hari. Ya ce: “Ku tafi ku shiga ɗakunanku, ku rufe ƙofofinku ku ɓoye kanku, sai fushina ya wuce.” (Isha. 26:20) Mai yiwuwa mu ma haka za a ce mu yi a lokacin ƙunci mai girma. ‘Ɗakunan’ suna iya nufin ikilisiyoyinmu. Jehobah ya yi mana alkawari cewa a lokacin ƙunci mai girma, zai kāre mu idan muka ci gaba da bauta masa tare da ꞌyanꞌuwanmu. Don haka, dole mu yi iya ƙoƙarinmu yanzu mu ƙaunaci ꞌyanꞌuwanmu da dukan zuciyarmu. Mai yiwuwa abin da zai ceci ranmu ke nan!
KA YI SHIRI TUN YANZU
17. Ta yaya yin shiri tun yanzu zai taimaka mana a lokacin ƙunci mai girma?
17 Idan “Babbar Ranar Yahweh” ta zo, abubuwa za su yi ma kowa wuya sosai. (Zaf. 1:14, 15) Mutanen Jehobah ma za su sha wuya. Amma idan muka yi shiri tun yanzu, za mu iya kasancewa da kwanciyar hankali kuma mu taimaki ꞌyanꞌuwanmu. Za mu iya jimre duk wani abin da zai same mu. Idan ꞌyanꞌuwanmu suka shiga cikin wahala, za mu yi iya ƙoƙarinmu mu taimaka musu. Za mu tausaya musu, kuma mu ba su abin da suke bukata. Ƙari ga haka, za mu manne wa ꞌyanꞌuwanmu domin muna ƙaunar su sosai. Bayan ƙuncin, Jehobah zai ba mu rai na har abada a duniya, lokacin kuwa, balaꞌi da matsaloli duk za su zama labari.—Isha. 65:17.
WAƘA TA 144 Mu Riƙa Ɗokin Samun Ladan!
a Nan ba da daɗewa ba, za a soma ƙunci mai girma. Halin tausayi, da jimiri, da kuma ƙauna, za su taimaka mana mu yi shiri don abubuwan da za su faru a lokacin da za a yi wahalar da ba a taɓa irinta ba. Za mu ga yadda Kiristoci na farko suka nuna halayen nan, da yadda mu ma za mu yi hakan, da kuma yadda za mu zauna da shiri don ƙunci mai girma.
b Waɗanda suke so su taimaka da aikin agaji su cika fom da ake kira, Local Design/Construction Volunteer Application (DC-50) ko kuma, Application for Volunteer Program (A-19). Bayan haka, su jira sai an kira su su zo su taimaka da wani aiki.