Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 27

WAƘA TA 73 Ka Ba Mu Ƙarfin Zuciya

Ka Yi Karfin Zuciya Kamar Zadok

Ka Yi Karfin Zuciya Kamar Zadok

“Zadok wanda yake jarumi, saurayi.”1 TAR. 12:28, Mai Makamantu[n] Ayoyi.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga yadda labarin Zadok zai taimaka mana mu zama masu ƙarfin zuciya.

1-2. Wane ne Zadok? (1 Tarihi 12:22, 26-28)

 KA YI tunanin abin da ya faru ranar da mutane fiye da 340,000 daga dukan ƙasar Israꞌila suka taru don su naɗa Dauda sarki. Sun yi kwanaki uku a kan tuddan da ke kusa da Hebron, suna ta hira da dariya, kuma suna rera waƙoƙin yabo ga Jehobah. (1 Tar. 12:39) Zai yi wuya a san cewa wani matashi mai suna Zadok yana cikin wannan ɗimbin jamaꞌa. Amma Jehobah ya lura cewa Zadok yana wurin, kuma yana so mu ma mu san da haka. (Karanta 1 Tarihi 12:22, 26-28.) Wane ne Zadok?

2 Zadok wani firist ne da yake aiki tare da Babban Firist mai suna Abiyatar, kuma Allah ya ba shi hikima sosai da baiwar sanin nufinsa. (2 Sam. 15:27) Mutane suna zuwa neman shawara a wurinsa. Kuma shi jarumi ne, wato yana da ƙarfin zuciya. Wannan halin da yake da shi ne za mu yi magana a kai a talifin nan.

3. (a) Me ya sa bayin Allah suke bukatar ƙarfi zuciya? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

3 A waɗannan kwanaki na ƙarshe, Shaiɗan yana iya ƙoƙarinsa ya ɓata dangantakarmu da Jehobah. (1 Bit. 5:8) Muna jiran lokacin da Jehobah zai halaka Shaiɗan da miyagun mutane. Amma kafin nan, muna bukatar ƙarfin zuciya. (Zab. 31:24) Don haka bari mu tattauna hanyoyi uku da za mu yi ƙarfin zuciya kamar Zadok.

MU GOYI BAYAN MULKIN ALLAH

4. Me ya sa muke bukatar ƙarfin zuciya a yau don mu iya goyi bayan Mulkin Allah? (Ka kuma duba hoton.)

4 Mu bayin Allah muna goyon bayan Mulkinsa da dukan zuciyarmu. Amma yin haka bai da sauƙi, muna bukatar ƙarfin zuciya. (Mat. 6:33) Alal misali, a wannan muguwar duniya, sai da ƙarfin zuciya ne za mu iya bin ƙaꞌidodin Jehobah kuma mu yi waꞌazin Mulkinsa. (1 Tas. 2:2) Ƙari ga haka, siyasa da dai sauransu, suna raba kan mutane sosai a yau. Ƙarfin zuciya ne zai taimaka mana kar mu goyi bayan wani ɓangare. (Yoh. 18:36) Akwai bayin Jehobah da yawa a wannan zamanin namu da suka rasa dukiyarsu, wasu an zalunce su, wasu kuma an kulle su, don sun ƙi su shiga harkar siyasa ko aikin soja.

Me za ka yi idan wasu suna goyon bayan wani ɓangare a harkar siyasa? (Ka duba sakin layi na 4)


5. Me ya sa Zadok ya bukaci ƙarfin zuciya don ya goyi bayan Dauda?

5 Da Zadok ya je Hebron inda za a naɗa Dauda sarki, ba yin biki ne kawai yake a ransa ba. Domin ya je da kayan yaƙinsa kuma yana a shirye don yaƙi. (1 Tar. 12:38) A shirye yake ya bi Dauda su yaƙi magabtan Allah idan da bukata. Da yake Zadok firist ne, wataƙila bai saba zuwa yaƙi ba, amma shi mai ƙarfin zuciya ne sosai.

6. Ta yaya misalin Dauda ya taimaka wa Zadok ya zama mai ƙarfin zuciya? (Zabura 138:3)

6 A ina ne wannan firist ya koyi ƙarfin zuciya? Amsar ita ce, Zadok ya san mutane da yawa waɗanda suke da ƙarfin zuciya. Ba mamaki halinsu ne ya bi. Alal misali, yadda Dauda ya ‘bi da Israꞌila a yaƙi’ da ƙarfin zuciya, ya sa dukan Israꞌilawa sun goyi bayansa da zuciya ɗaya. (1 Tar. 11:1, 2) Dauda ya dogara ga Jehobah. A kullum yakan roƙi Jehobah ya taimake shi ya iya yaƙan maƙiyansa. (Zab. 28:7; karanta Zabura 138:3.) Ƙari ga haka, akwai wasu maza masu ƙarfin zuciya da Zadok ya yi koyi da su. Alal misali, akwai Yehoyida da ɗansa wanda ya iya yaƙi sosai, mai suna Benaya, da kuma shugabannin kabilu guda 22 da suka goyi bayan Dauda. (1 Tar. 11:22-25; 12:26-28) Dukansu sun ƙuduri cewa, za su mai da Dauda sarkinsu kuma su kāre shi.

7. (a) Labaran su waye ne a zamaninmu za su iya taimaka mana mu zama masu ƙarfin zuciya? (b) Me ka koya daga labarin Ɗanꞌuwa Nsilu da aka nuna a bidiyon?

7 Idan muka yi tunanin yadda wasu suka yi ƙarfin zuciya don su goyi bayan Jehobah da Mulkinsa, hakan zai motsa mu mu yi ƙarfin zuciya. Alal misali, lokacin da Sarkinmu, Yesu Kristi, yake duniya, ya ƙi ya shiga harkokin siyasa. (Mat. 4:8-11; Yoh. 6:14, 15) A kowane lokaci, ya dogara ga Jehobah ya ba shi ƙarfin zuciya. Ban da Yesu ma, akwai ꞌyanꞌuwa matasa da yawa a zamaninmu da suka ƙi shiga harkokin siyasa, ko aikin soja. Zai yi kyau ka karanta labaran wasu daga cikinsu a jw.org. a

KU TAIMAKI ꞌYANꞌUWANKU

8. A wane lokaci ne dattawa za su bukaci ƙarfin zuciya don su taimaka ma ꞌyanꞌuwansu?

8 Bayin Jehobah suna son taimaka wa juna. (2 Kor. 8:4) Amma a wasu lokuta, yin hakan yana bukatar ƙarfin zuciya. Idan aka soma yaƙi, dattawa sun san cewa ꞌyanꞌuwa za su bukaci abubuwa da yawa. Alal misali, za su bukaci ƙarfafawa, da abubuwan biyan bukata, da kuma abubuwan da za su taimaka musu su ci-gaba da yin kusa da Jehobah. Da yake suna ƙaunar ꞌyanꞌuwan nan sosai, sukan tanada musu abubuwan nan duk da cewa yin hakan zai sa rayukansu cikin haɗari. (Yoh. 15:12, 13) Ta wannan hanyar, suna yin ƙarfin zuciya kamar Zadok.

9. Bisa ga 2 Samaꞌila 15:27-29, mene ne Dauda ya ce wa Zadok ya yi? (Ka kuma duba hoton.)

9 Akwai lokacin da ake so a kashe Dauda. Hakan ya faru ne saꞌad da Absalom ya ce lallai sai ya ƙwace sarauta daga hannun babansa Dauda. (2 Sam. 15:12, 13) Nan-da-nan sai Dauda ya ce wa bayinsa: “Ku tashi mu gudu! Idan ba haka ba, babu wanda zai tsira daga hannun Absalom.” (2 Sam. 15:14) Da suke barin Urushalima, Dauda ya ga cewa akwai bukatar wani daga cikinsu ya kasance a wurin, don ya riƙa gaya masa ƙulle-ƙullen da Absalom yake yi. Shi ya sa ya ce wa Zadok da wasu Firistoci su koma Urushalima. (Karanta 2 Samaꞌila 15:27-29.) Amma abin da Dauda yake so su yi yana da haɗari sosai. Don haka, suna bukatar su yi hattara. Absalom mugun mutum ne mai son zuciya da har ya ci amanar mahaifinsa. Don haka, ka yi tunanin abin da zai yi ma Zadok da sauran firistocin idan ya kama su suna leƙen asirinsa don su taimaki Dauda.

Dauda ya ce wa Zadok ya je ya yi wani abu da ke da haɗari sosai (Ka duba sakin layi na 9)


10. Ta yaya Zadok da waɗanda suke tare da shi suka kāre Dauda?

10 Sai Dauda ya shirya yadda Zadok da wani aminin Dauda mai suna Hushai za su cika wannan aikin. (2 Sam. 15:32-37) Hushai ya bi abin da Dauda ya ce, kuma hakan ya sa Absalom ya yarda da shi. Da ya ji cewa za a kai wa Dauda hari, sai ya ba Absalom shawarar da za ta sa su ɗan dakata don Dauda ya samu ya gudu. Bayan haka, sai Hushai ya gaya wa Zadok da Abiyatar abin da Absalom yake shirin yi. (2 Sam. 17:8-16) Sai su ma suka aika a sanar da Dauda. (2 Sam. 17:17) Da taimakon Jehobah, Zadok da sauran firistocin sun taka rawar gani wajen kāre Dauda.—2 Sam. 17:21, 22.

11. Ta yaya za mu yi ƙarfin zuciya kamar Zadok yayin da muke taimaka ma ꞌyanꞌuwanmu?

11 Idan ꞌyanꞌuwanmu suna cikin haɗari kuma aka ce mu taimaka musu, ta yaya za mu nuna ƙarfin zuciya kamar Zadok? (1) Mu bi umurni da aka ba mu. Idan muna cikin haɗari, muna bukatar mu zama masu yin biyayya don bakinmu ya zama ɗaya. Mu bi umurni da muka samu daga reshen ofishinmu. (Ibran. 13:17) Ya kamata dattawa su riƙa bincika umurnai da aka bayar a kan yadda za su yi shiri don lokacin balaꞌi, da abin da ya kamata su yi idan balaꞌi ya auku. (1 Kor. 14:33, 40) (2) Ka yi ƙarfin zuciya, amma ka yi hattara. (K. Mag. 22:3) Kar ka sa ranka cikin haɗari, babu-gaira-babu-dalili. (3) Ka dogara ga Jehobah. Ka tuna cewa Jehobah ba ya so wani abu ya same ka da ꞌyanꞌuwanka. Da taimakonsa, za ka iya taimaka wa ꞌyanꞌuwanka ba tare da wani abu ya same ka ba.

12-13. Me ka koya daga labarin Viktor da Vitalii? (Ka kuma duba hoton.)

12 Ga abin da ya faru da wasu ꞌyanꞌuwa guda biyu, wato Viktor da Vitalii, da suka yi aiki sosai don su samar wa ꞌyanꞌuwa a Yukiren abinci da ruwan sha. Viktor ya ce: “Mun bi koꞌina muna neman abinci, kuma a yawanci lokuta mukan ji harbin bindiga kusa da mu. Akwai lokacin da wani ɗanꞌuwa ya ba da gudummawar kayan abinci da ya ajiye a gidansa. Kuma gudummawarsa ta sa ꞌyanꞌuwa da yawa sun samu abin da za su ci na wasu kwanaki. Da muke loda kayan a mota, sai wani bam da aka jefa ya faɗi kusa da mu, wajen kafa 66 daga inda muke, amma bai tashi ba. Ranar na yi ta roƙon Jehobah ya ba ni ƙarfin zuciya don in iya ci-gaba da taimaka wa ꞌyanꞌuwana.”

13 Ɗanꞌuwa Vitalii ya ce: “Mun bukaci ƙarfin zuciya sosai. A tafiyata ta farko, na yi awa 12 ina tuƙi, kuma da nake hanya ban daina yin adduꞌa ga Jehobah ba.” Ɗanꞌuwa Vitalii ya yi ƙarfin zuciya, amma kuma ya yi hattara. Ya ce: “Na yi ta roƙon Jehobah ya ba ni hikima kuma ya taimake ni kar in wuce gona da iri. Ba na bin hanya sai dai wadda hukumomi suka ce a bi. Ƙari ga haka, ganin yadda ꞌyanꞌuwa suke aiki tare ya ƙarfafa ni. ꞌYanꞌuwa sun ta cire abubuwa da suka tare hanya, da sauke da kuma loda kayan agaji a motar, da kuma samo mana abinci da wurin kwana yayin da muke tafiye-tafiyen.”

Idan ꞌyanꞌuwanka suna cikin haɗari kuma kana bukatar ka taimaka musu, ka yi hakan da ƙarfin zuciya, amma ka yi hattara (Ka duba sakin layi na 12-13)


KA RIƘE AMINCINKA GA JEHOBAH

14. Me zai iya faruwa da mu idan wani da muke ƙauna ya daina bauta ma Jehobah?

14 Wani abin da zai iya sa mu yi sanyin gwiwa sosai shi ne, idan wani a iyalinmu ko wani abokinmu ya daina bauta ma Jehobah. (Zab. 78:40; K. Mag. 17:22) Idan muna ƙaunar mutumin sosai, hakan zai sa ya ƙara mana wuya mu jimre yanayin. Idan ka sami kanka a irin wannan yanayin, labarin Zadok da yadda ya riƙe aminci, zai ƙarfafa ka.

15. Me ya sa Zadok ya bukaci ƙarfin zuciya don ya ci-gaba da bauta ma Jehobah? (1 Sarakuna 1:5-8)

15 Zadok ya ci-gaba da bauta ma Jehobah da aminci duk da cewa abokinsa Abiyatar ya juya ma Jehobah baya. Hakan ya faru ne saꞌad da Dauda ya tsufa kuma ya kusan mutuwa. A wannan lokacin, ɗansa Adoniya ya yi ƙoƙari ya sa a naɗa shi sarki duk da cewa Sulemanu ne Jehobah ya zaɓa. (1 Tar. 22:9, 10) Abiyatar ya goyi bayan Adoniya. (Karanta 1 Sarakuna 1:5-8.) Abin da Abiyatar ya yi, rashin aminci ne ga Dauda da kuma Jehobah. Ba shakka hakan ya sa Zadok baƙin ciki sosai, domin shi da Abiyatar sun yi fiye da shekaru 40 suna aikin firist tare. (2 Sam. 8:17) Sun kula da “Akwatin Yarjejeniya na Allah” tare. (2 Sam. 15:29) Su biyun sun goyi bayan Dauda da sarautarsa, kuma sun yi abubuwa da dama a bautar Jehobah.—2 Sam. 19:11-14.

16. Mene ne wataƙila ya taimaka wa Zadok ya riƙe amincinsa ga Jehobah?

16 Zadok ya ci-gaba da riƙe amincinsa duk da cewa Abiyatar ya bar Jehobah, kuma Dauda bai taɓa yin shakkar Zadok ba. Shi ya sa da Dauda ya ji abin da Adoniya yake ƙullawa, sai ya zaɓi Zadok da Natan da Benaya, kuma ya ce musu su naɗa Sulemanu sarki. (1 Sar. 1:32-34) Mai yiwuwa wani abin da ya ƙarfafa Zadok ya riƙe amincinsa shi ne, kasancewa da bayin Jehobah masu aminci kamar annabi Natan, domin su ma sun goyi bayan Jehobah da Sarki Dauda. (1 Sar. 1:38, 39) Da Sulemanu ya zama sarki, “sai ya mai da Zadok firist a maimakon Abiyatar.”—1 Sar. 2:35.

17. Idan wani da kake ƙauna ya daina bauta ma Jehobah, ta yaya za ka yi koyi da Zadok?

17 Ta yaya kai ma za ka yi koyi da Zadok? Idan wani da kake ƙauna ya daina bauta ma Jehobah, ka nuna wa Jehobah cewa kai ba za ka bar shi ba. (Yosh. 24:15) Jehobah zai ba ka ƙarfin zuciya don ka iya yin abin da ya dace. Don haka ka roƙe shi ya taimake ka, kuma ka ci-gaba da kusantar ꞌyanꞌuwa masu aminci kamarka. Hakan zai nuna cewa ka dogara ga Jehobah. Jehobah yana farin ciki don yadda kake bauta masa da aminci, don haka zai ba ka lada.—2 Sam. 22:26.

18. Me ka koya daga labarin Marco da matarsa Sidse?

18 Ka lura da abin da ya faru da wani ɗanꞌuwa mai suna Marco da matarsa Sidse. ꞌYan matansu biyu sun daina bauta ma Jehobah saꞌad da suka yi girma. Ɗanꞌuwa Marco ya ce: “Iyaye sukan ƙaunaci yaransu sosai tun daga haihuwa, kuma sukan yi duk wani abin da ya kamata don su kāre su. Don haka, idan yaran suka daina bauta ma Jehobah, abin yakan sa iyayen baƙin ciki ba kaɗan ba.” Ya ci-gaba da cewa: “Amma Jehobah ya taimaka mana mu jimre wannan yanayin. Ya sa mu biyun mun iya ƙarfafa juna. Alal misali, idan ina baƙin ciki, matata ce takan ƙarfafa ni don in iya yin abin da ya dace, kuma idan ita ma tana baƙin ciki, nakan ƙarfafa ta.” ꞌYarꞌuwa Sidse ta ce: “Da a ce Jehobah bai ƙarfafa mu ba, da ba za mu iya jimre wannan abin ba. Na yi ta damuwa ina tunani cewa abin da ya faru laifina ne, amma sai na gaya ma Jehobah yadda nake ji. ꞌYan kwanaki bayan haka, sai ga wata ꞌyarꞌuwa da muka yi shekaru da yawa ba mu haɗu ba ta zo ta same ni, ta riƙe ni a kafaɗa, kuma ta kalle ni ta ce: ‘Sidse, ki tuna cewa ba laifinki ba ne.’ Jehobah ya taimaka min in ci-gaba da bauta masa da farin ciki.”

19. Mene ne ƙudirinka?

19 Jehobah yana so dukan bayinsa su zama masu ƙarfin zuciya kamar Zadok. (2 Tim. 1:7) Amma kuma, yana so mu dogara gare shi ne ba ga kanmu ba. Don haka, idan ka shiga yanayi mai wuya kuma kana bukatar ƙarfin zuciya, ka roƙi Jehobah ya ba ka. Babu shakka in ka yi haka, Jehobah zai ba ka ƙarfin zuciya kamar Zadok.—1 Bit. 5:10.

WAƘA TA 126 Mu Yi Tsaro, Mu Riƙe Aminci, Mu Yi Ƙarfi