Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
Bayan haifuwar Yesu, me ya sa Yusufu da Maryamu suka ci gaba da zama a Baiꞌtalami maimakon su koma Nazaret?
Littafi Mai Tsarki bai faɗi dalilin ba. Amma ya gaya mana wasu abubuwa da wataƙila su ne suka sa suka zaɓi su ci gaba da zama a Baiꞌtalami ko kuma Betelehem.
Wani malaꞌika ya gaya wa Maryamu cewa za ta yi ciki kuma za ta haifi ɗa. Saꞌad da malaꞌikan ya idar da wannan saƙon, Yusufu da Maryamu suna zama a Nazaret, wani gari a Galili. (Luk. 1:26-31; 2:4) Daga baya, saꞌad da suka dawo daga Masar, sun koma Nazaret. Yesu ya yi girma a wurin kuma ya zama Baꞌnazaret. (Mat. 2:19-23) Shi ya sa mukan tuna da Nazaret a duk lokacin da muka ambaci sunan Yusufu da Yesu da Maryamu.
Maryamu tana da wata dangi mai suna Alisabatu da take zama a Yahudiya. Alisabatu ce matar firist mai suna Zakariya, kuma daga baya ta zama mamar Yohanna mai Baftisma. (Luk. 1:5, 9, 13, 36) Maryamu ta ziyarci Alisabatu kuma ta zauna da ita na tsawon watanni uku a Yahudiya. Bayan haka, Maryamu ta koma Nazaret. (Luk. 1:39, 40, 56) Don haka, Maryamu ta san wasu yankunan Yahudiya.
Daga baya, Yusufu ya bi umurnin da aka bayar cewa mutane su “koma garuruwansu domin a ƙirga su.” Don haka, Yusufu ya yi tafiya daga Nazaret zuwa Baiꞌtalami, “wato garin da aka haifi sarki Dawuda,” kuma an annabta cewa a garin ne za a haifi Almasihu. (Luk. 2:3, 4; 1 Sam. 17:15; 20:6; Mik. 5:2) Bayan Maryamu ta haifi Yesu a Baiꞌtalami, Yusufu bai sa ta yi dogon tafiya zuwa Nazaret da jaririnta ba. Sun zauna a Baiꞌtalami, wanda daga wurin zuwa Urushalima wajen kilomita tara ne. Don haka, zai yi musu sauƙi su je Urushalima kuma su yi hadaya kamar yadda Dokar Jehobah ta ce su yi.—L. Fir. 12:2, 6-8; Luk. 2:22-24.
Kafin wannan lokacin, malaꞌikan Ubangiji ya gaya wa Maryamu cewa Yesu zai karɓi “kujerar mulkin kakansa Dawuda” kuma zai yi mulki. Don haka, wataƙila Yusufu da Maryamu sun yi tunani cewa yana da muhimmanci da aka haifi Yesu a Baiꞌtalami, wato birnin Dauda. (Luk. 1:32, 33; 2:11, 17) Kuma mai yiwuwa sun yi tunani cewa zai dace su ci gaba da zama a wurin, har sai Jehobah ya gaya musu abin da yake so su yi.
Ba mu san shekaru nawa ne suka yi a Baiꞌtalami kafin masu ilimin taurari suka ziyarce su ba. Mun dai san cewa a lokacin, sun soma zama a wani gida kuma Yesu ya zama ‘ɗan yaro’ ba jariri kuma ba. (Mat. 2:11) Da alama cewa maimakon su koma Nazaret, sun yanke shawarar zama a Baiꞌtalami.
Hiridus ya ba da umurni cewa “a kakkashe dukan ꞌyan yara maza waɗanda suke cikin Betelehem . . . daga masu shekara biyu zuwa ƙasa.” (Mat. 2:16) Wani malaꞌika ya gargaɗi Yusufu game da wannan umurnin. Don haka, Yusufu da Maryamu sun gudu zuwa Masar tare da ɗansu Yesu, kuma sun zauna a wurin har sai da Hiridus ya mutu. Daga baya, sai Yusufu ya ƙaurar da iyalinsa zuwa Nazaret. Me ya sa ba su koma Baiꞌtalami ba? A lokacin, yaron Hiridus mai suna Arkilayus ne yake mulki kuma shi mugu ne. Ƙari ga haka, malaꞌika ya gargaɗi Yusufu game da haɗari da ke tattare da komawa Baiꞌtalami. Don haka, shi da iyalinsa sun koma Nazaret inda zai iya renon yaronsa hankali kwance don ya bauta ma Jehobah.—Mat. 2:19-22; 13:55; Luk. 2:39, 52.
Da alama Yusufu ya mutu kafin Yesu ya mutu kuma ya buɗe wa mutane hanyar zuwa sama. Don haka, a nan duniya ne za a tā da Yusufu. Mutane da yawa za su haɗu da shi. Lokacin, za a iya tambayar sa dalilin da ya sa shi da Maryamu suka ci gaba da zama a Baiꞌtalami bayan haifuwar Yesu.