Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 25

Dattawa, Ku Yi Koyi da Gideyon

Dattawa, Ku Yi Koyi da Gideyon

“Ba ni da zarafi in yi zance a kan Gideyon.”​—IBRAN. 11:32.

WAƘA TA 124 Mu Kasance da Aminci

ABIN DA ZA A TATTAUNA a

1. Bisa ga 1 Bitrus 5:​2, wane aiki na musamman ne Allah ya ba wa dattawa?

 JEHOBAH ya ba wa dattawa hakkin kula da tumakinsa masu daraja. Waɗannan ꞌyanꞌuwa masu aminci ba sa wasa da hakkin da Jehobah ya ba su na yi wa ꞌyanꞌuwansu hidima. Kuma suna aiki sosai don su zama “makiyaya masu kirki.” (Irm. 23:4; karanta 1 Bitrus 5:2.) Muna godiya da Allah ya ba mu irin ꞌyanꞌuwan nan a ikilisiyoyinmu!

2. Waɗanne matsaloli ne wasu dattawa suke fuskanta?

2 Dattawa sukan fuskanci matsaloli da yawa yayin da suke yin aikinsu. A gaskiya, kula da ikilisiya ba ƙaramin aiki ba ne. Wani dattijo a ƙasar Amirka mai suna Tony, ya gano cewa ba dukan ayyukan da ake ba shi ne zai iya yin su ba. Ya ce: “Da annobar korona ta soma, na shiga yin ayyuka da dama don in shirya yadda za mu riƙa yin taro da kuma waꞌazi a ikilisiyarmu. Amma komen aiki da na yi, sai in ga cewa da saura. A-kwana-a-tashi, na zo ba na samun lokacin karanta Littafi Mai Tsarki, da yin nazari, da kuma yin adduꞌa.” Wani dattijo a ƙasar Kosovo mai suna Ilir shi ma ya fuskanci wata matsala. Da aka soma yaƙi a inda yake, bai yi masa sauƙi ya bi abin da ƙungiyarmu ta ce ba. Ya ce: “Ya yi min wuya in zama da ƙarfin zuciya a lokacin da reshen ofishinmu ya ce in je in taimaki ꞌyanꞌuwa da ke wani yanki mai haɗari sosai. Tsoro ya kama ni, kuma na ga kamar abin da aka ce in yi ba zai yiwu ba.” Wani ɗanꞌuwa a Asiya da ke waꞌazi a ƙasar waje ya ga cewa ba ya yi masa sauƙi ya yi dukan abubuwa da yake bukatar ya yi kowace rana. Sunansa Tim. Ɗanꞌuwan ya ce: “Wani lokaci nakan ji na gaji.” Me zai taimaka wa dattawa idan suna fuskantar irin matsalolin nan?

3. Ta yaya dukanmu za mu amfana idan muka bincika labarin Gideyon?

3 Dattawa za su amfana sosai idan suka bi halin Gideyon. (Ibran. 6:12; 11:32) Ya kāre mutanen Allah, kuma ya kula da su. (Alƙa. 2:16; 1 Tar. 17:6) Dattawa su ma an ba su hakkin kula da mutanen Allah a wannan lokaci mai wuya sosai. (A. M. 20:28; 2 Tim. 3:1) Za su iya koyan darasi daga yadda Gideyon ya nuna halin tawaliꞌu da biyayya da sanin kasawarsa da kuma jimiri. Ko da mu ba dattawa ba ne, labarinsa zai sa mu ƙara nuna godiya don aikin da dattawa suke yi, kuma mu goyi bayan ꞌyanꞌuwan nan masu aminci da suke aiki tuƙuru wajen kula da mu.​—Ibran. 13:17.

IDAN KANA BUKATAR NUNA HALIN TAWALIꞌU DA SANIN KASAWARKA

4. Ta yaya Gideyon ya nuna cewa shi mai tawaliꞌu ne kuma ya san kasawarsa?

4 Gideyon mutum ne mai tawaliꞌu wanda ya san kasawarsa. b Midiyanawa suna da ƙarfin gaske. Da malaꞌikan Jehobah ya gaya wa Gideyon cewa shi aka zaɓa ya ceci Israꞌilawa daga hannunsu, Gideyon ya ce: “Dangina marar ƙarfi ne a cikin zuriyar Manasse, ni ne kuma mafi ƙanƙanta a cikin gidanmu.” (Alƙa. 6:15) A tunaninsa, ba zai iya yin aikin ba, amma Jehobah ya san cewa zai iya. Da taimakon Jehobah, Gideyon ya kuwa cika aikin nan da aka ba shi.

5. A waɗanne yanayoyi ne zai iya yi wa dattijo wuya ya nuna sauƙin kai da tawaliꞌu?

5 Dattawa suna iya ƙoƙarinsu su nuna halin sauƙin kai da kuma tawaliꞌu a kome da suke yi. (Mik. 6:8; A. M. 20:​18, 19) Ba sa takama da baiwarsu ko abubuwan da suka cim ma. Kuma ba sa ganin cewa ba su da amfani don kurakuren da suka taɓa yi. Amma akwai wasu matsalolin da dattijo zai iya fuskanta. Alal misali, zai iya karɓan ayyuka da yawa ya ce zai yi, ƙarshenta abin ya gagare shi. Ko kuma wataƙila ya yi masa wuya ya nuna sauƙin kai idan aka kushe shi ko aka yabe shi don wani aikin da ya yi. Ta yaya misalin Gideyon zai taimaka wa dattawa a irin wannan yanayin?

Kamar Gideyon, dattijon da ya san kasawarsa yakan nemi taimako, misali idan yana so ya shirya yadda za a yi waꞌazi da amalanke (Ka duba sakin layi na 6)

6. Ta yaya dattawa za su nuna cewa sun san kasawarsu kamar Gideyon? (Ka kuma duba hoton.)

6 Ka nemi taimako. Wanda ya san kasawarsa, ya san cewa ba kome ne zai iya yi ba. Gideyon ya nuna cewa ya san kasawarsa ta yadda ya ce a taimaka masa. (Alƙa. 6:​27, 35; 7:24) Abin da dattawa masu hikima suke yi ke nan. Tony da muka ambata ɗazu ya ce: “Saboda yadda aka raine ni, duk aikin da aka ba ni karɓa nake yi, har ya fi ƙarfina. Sai na sa muka yi nazarin talifin da ya yi magana a kan sanin kasawarmu a ibada ta iyalinmu. Kuma na nemi shawarar matata. Mun kuma kalli bidiyon nan mai jigo, Ku Koyar da Wasu, Ku Amince da Su Kuma Ku Ba Su Aiki Kamar Yadda Yesu Ya Yi.” Da haka, Tony ya soma kiran wasu ꞌyanꞌuwa su taimaka masa da aikinsa. Wane amfani hakan ya kawo? Tony ya ce: “Yanzu ana kula da ayyukan ikilisiyar da kyau, kuma ina samun lokacin yin abubuwan da za su sa in ƙara kusantar Jehobah.”

7. Ta yaya dattawa za su bi halin Gideyon idan aka kushe su? (Yakub 3:13)

7 Kada ka yi fushi idan aka kushe ka. Ba ya ma dattawa sauƙi su nuna tawaliꞌu idan aka kushe su. Amma har ila misalin Gideyon zai iya taimaka musu. Da yake ya san cewa yana da kasawa, bai yi fushi ba da mutanen Ifrayim suka kushe shi. (Alƙa. 8:​1-3) Ya amsa musu a hankali. Yadda ya saurare su ya nuna cewa shi mai tawaliꞌu ne, kuma ya yi maganar da za ta kwantar musu da hankali. Dattawa masu hikima suna bin halin Gideyon. Sukan saurari mutum da kyau, kuma idan aka kushe su, sukan faɗi alheri. (Karanta Yakub 3:13.) Ta yin hakan, suna ƙara sa ikilisiya ta zauna lafiya.

8. Me ya kamata dattawa su yi idan aka yaba musu? Ka ba da misali.

8 Ka miƙa yabo ga Jehobah. Da aka yabi Gideyon don nasarar da ya yi a kan mutanen Midiyan, ya miƙa yabon ga Jehobah. (Alƙa. 8:​22, 23) Ta yaya dattawa za su bi halin Gideyon? Idan aka yabe su don wani abin da suka yi, zai dace su miƙa yabon ga Jehobah. (1 Kor. 4:​6, 7) Misali, idan aka yabi dattijo don yadda yake koyarwa, zai iya cewa abin da ya koyar daga Kalmar Allah ne, kuma koyawar da muke samu daga ƙungiyar Jehobah ce take taimaka wa dukanmu. Wani lokaci, zai dace dattawa su yi tunani ko suna yin abubuwa don su jawo hankalin mutane gare su. Ga misalin wani dattijo mai suna Timothy. A lokacin da aka naɗa shi dattijo, ya so yin jawabi ga jamaꞌa sosai. Ya ce: “Nakan kirkiro dogayen gabatarwa da kuma misalai da suke jan hankalin mutane sosai. Hakan yakan sa a yaba min. Amma matsalar ita ce, duk hankalin mutane ya koma kaina maimakon su mai da hankali ga Jehobah da kuma Kalmarsa.” A-kwana-a-tashi, Timothy ya ga cewa yana bukatar ya canja yadda yake koyarwa don mutane su daina mai da hankali gare shi. (K. Mag. 27:21) Wane amfani hakan ya kawo? Ya ce: “Mutane da yawa sun yi ta gaya min yadda jawabina ya taimaka musu su iya jimre wata matsala da suke fuskanta kuma su kusaci Jehobah. Abin da suka gaya min ya faranta mini rai fiye da duk yabon da nake samu a dā.”

IDAN YANA MAKA WUYA KA YI BIYAYYA KO KA YI ƘARFIN ZUCIYA

Gideyon ya yi biyayya kuma ya rage yawan sojojinsa, ya zaɓi maza 300 da suka nuna halin tsaro (Ka duba sakin layi na 9)

9. Me ya sa yin biyayya da yin ƙarfin zuciya bai yi wa Gideyon sauƙi ba? (Ka duba hoton da ke shafin farko.)

9 Da Gideyon ya zama alƙali, ya bukaci halin biyayya da kuma ƙarfin zuciya sosai. Domin an ba shi aiki mai wuya, wato cewa ya rushe bagadin Baal na babansa. (Alƙa. 6:​25, 26) Daga baya, da Gideyon ya tattara sojojinsa, sai aka gaya masa ya rage yawan sojojin har sau biyu. (Alƙa. 7:​2-7) A ƙarshe, an umurce shi ya kai wa maƙiyansa hari da tsakar dare.​—Alƙa. 7:​9-11.

10. Mene ne zai iya sa ya yi wa dattijo wuya ya yi biyayya?

10 Ya kamata dattawa su zama masu “sauƙin kai,” wato masu saurin yin biyayya. (Yak. 3:17) Dattijon da yake da sauƙin kai yakan yi biyayya da umurnin da ƙungiyar Jehobah ta bayar da kuma wanda ya karanta daga Littafi Mai Tsarki. Ta haka, yana kafa misali mai kyau ma sauran ꞌyanꞌuwa. Duk da haka, a wasu lokuta zai iya masa wuya ya yi biyayya. Alal misali, zai iya masa wuya idan ana ba shi umurnai da yawa ko ana canja umurnan a-kai-a-kai. A wasu lokuta ma, zai iya yin shakkar ko umurnin da aka ba shi ya dace. Ƙari ga haka, za a iya ce ya yi aikin da zai sa hukumomi su kama shi ko su tsare shi. Ta yaya dattawa za su yi biyayya kamar Gideyon a yanayoyin nan?

11. Me zai taimaka wa dattawa su iya yin biyayya?

11 Ka saurari umurnin da aka ba ka da kyau kuma ka yi daidai abin da aka ce. Allah ya gaya wa Gideyon yadda zai rushe bagadin babansa, da inda zai gina bagadi, da kuma dabbar da zai yi hadaya da ita. Gideyon bai yi shakkar umurnin da Jehobah ya ba shi ba. Amma ya yi daidai yadda Jehobah ya gaya masa ya yi. A yau, akan ba wa dattawa umurni ta wasiƙu da sanarwa da wasu hanyoyi don su kāre mu kuma su taimaka mana mu ci gaba da kusantar Jehobah. Muna ƙaunar dattawanmu domin suna yin daidai abin da ƙungiyarmu ta gaya musu. Kuma hakan yana sa kowa a ikilisiya ya amfana.​—Zab. 119:112.

12. Ta yaya dattawa za su bi abin da ke Ibraniyawa 13:17 saꞌad da ƙungiyarmu ta canja umurnin da ta ba su?

12 Ka kasance a shirye don ka bi sabbin umurnai. Ka tuna cewa Jehobah ya gaya wa Gideyon ya mayar da kusan dukan sojojinsa gida. (Alƙa. 7:8) Mai yiwuwa Gideyon ya yi tunani cewa: ‘Shin dole ne a yi canjin nan? Wannan canjin zai amfane mu kuwa?’ Duk da haka, Gideyon ya yi biyayya. A yau, dattawa suna yin koyi da Gideyon idan suna bin canjin da ƙungiyarmu ta yi. (Karanta Ibraniyawa 13:17.) Alal misali, a shekara ta 2014 Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ta canja yadda za a riƙa biyan kuɗin da aka gina Majamiꞌun Mulki da shi da Majamiꞌun Manyan Taro. (2 Kor. 8:​12-14) A dā, ƙungiyarmu takan ba wa ikilisiyoyi bashin kuɗi don su gina Majamiꞌar Mulki. Sai daga baya ikilisiyoyin su biya bashin. Amma a yanzu, ƙungiyarmu tana amfani da gudummawar da ikilisiyoyi a duk faɗin duniya suka yi don ta yi gine-ginen nan, ko da gudummawar da ikilisiyar da ake so a gina musu Majamiꞌar Mulki za su yi kaɗan ne. Da Ɗanꞌuwa José ya ji game da wannan canjin, ya yi shakka cewa canjin zai yi amfani. Ya ce: ‘Ba za a iya gina ko guda ɗaya ba. Ba haka ake yin abubuwa a yankinmu ba.’ Mene ne ya taimaka wa José ya goyi bayan umurnin da aka bayar? Ya ce: “Kalmomin da ke Karin Magana 3:​5, 6 sun tuna min muhimmancin dogara ga Jehobah, kuma hakan ya kawo sakamakon mai kyau. Umurnin ya sa mun iya gina Majamiꞌun Mulki da yawa, kuma yanzu muna tallafa wa juna domin kome ya zama daidai.”

Za mu iya yin waꞌazi da ƙarfin zuciya ko a inda aka hana aikinmu (Ka duba sakin layi na 13)

13. (a) Wane tabbaci ne Gideyon yake da shi? (b) Ta yaya dattawa za su yi koyi da hakan? (Ka kuma duba hoton.)

13 Ka yi nufin Jehobah da ƙarfin zuciya. Gideyon ya yi biyayya ga Jehobah duk da cewa yana tsoro kuma aikin da aka ba shi yana da haɗari. (Alƙa. 9:17) Bayan Jehobah ya tabbatar wa Gideyon cewa yana tare da shi, Gideyon ya yarda da gaske cewa Allah zai taimaka masa ya kāre mutanensa. Dattawan da suke zama a wuraren da aka hana aikinmu suna yin koyi da Gideyon. Suna ja-goranci a taro da kuma waꞌazi da ƙarfin zuciya duk da cewa za a iya kama su, ko a yi musu tambayoyi, ko su rasa aikinsu, ko kuma a yi musu dūka. c A lokacin ƙunci mai girma, dattawa za su bukaci ƙarfin zuciya don su iya bin umurnin da za a ba su ko da yin hakan yana da haɗari. Alal misali, za a iya ba mu umurni mu yi waꞌazin saƙon hukunci kuma a gaya mana abin da za mu yi don mu tsira daga harin Gog na Magog.​—Ezek. 38:18; R. Yar. 16:21.

IDAN YANA MAKA WUYA KA JIMRE

14. Me ya sa bai yi ma Gideyon sauƙi ya jimre ba?

14 A matsayinsa na Alƙali, Gideyon yana bukatar ya yi aiki sosai. Saꞌad da Gideyon yake yaƙi da sojojin Midiya da tsakar dare, sojojin sun gudu. Sai Gideyon ya bi su daga Kwarin Jezreel har zuwa Kogin Urdun, wanda mai yiwuwa yana cike da bishiyoyi. (Alƙa. 7:22) Shin Gideyon ya tsaya a Kogin Urdun ne? Aꞌa! Ko da yake ya gaji, shi da mutanensa guda 300 sun tsallake kogin kuma suka ci gaba da bin su. A ƙarshe, sun kama Midiyanawan kuma suka kakkashe su.​—Alƙa. 8:​4-12.

15. Me ya sa a wani lokaci zai iya yi wa dattijo wuya ya jimre?

15 A wasu lokuta, dattijo zai iya gajiya saboda ayyukan da yake yi don ya kula da ikilisiya da iyalinsa. A irin wannan yanayin, ta yaya dattawa za su yi koyi da Gideyon?

Dattawa masu ƙauna sun ƙarfafa ꞌyanꞌuwa da yawa da suke bukatar taimako (Ka duba sakin layi na 16-17)

16-17. Mene ne ya taimaka wa Gideyon ya jimre, kuma wane tabbaci ne dattawa za su iya kasancewa da shi? (Ishaya 40:​28-31) (Ka kuma duba hoton.)

16 Ka kasance da tabbacin cewa Jehobah zai ƙarfafa ka. Gideyon ya kasance da tabbacin cewa Jehobah zai ƙarfafa shi kuma abin da ya faru ke nan. (Alƙa. 6:​14, 34) Akwai lokacin da Gideyon da mutanensa suke bin sarakunan Midiya da ƙafa, sarakunan kuma suna gudu a kan raƙuma. (Alƙa. 8:​12, 21) Amma da taimakon Jehobah, Israꞌilawan sun kama su kuma suka ci yaƙin. Dattawa ma za su iya dogara ga Jehobah a kowane lokaci, wanda “ba ya gajiya ko ƙarfi ya kāsa masa.” Zai ƙarfafa su a lokacin da suke bukatar hakan.​—Karanta Ishaya 40:​28-31.

17 Ka yi laꞌakari da misalin wani dattijo mai suna Matthew, wanda Memban Kwamitin Hulɗa da Asibitoci ne. Me ya taimaka masa ya jimre? Matthew ya ce: “Na samu ƙarfafa daga wurin Jehobah kamar yadda Filibiyawa 4:13 ta ce. A duk lokacin da na gaji kuma na ji kamar ba zan iya ci gaba da yin aikin ba, nakan yi adduꞌa sosai, ina roƙon Allah ya ba ni ƙarfi don in ci gaba da taimaka wa ꞌyanꞌuwana. A waɗannan lokutan, na ga yadda Jehobah ya ƙarfafa ni, kuma ya taimaka mini in ci gaba da jimrewa.” Kamar Gideyon, dattawanmu suna aiki sosai don su kula da mutanen Jehobah, ko da yake yin hakan bai da sauƙi a wasu lokuta. Amma dattawa suna bukatar su san kasawarsu kuma su san cewa ba dukan abin da suke so su yi ne za su iya yi ba. Don haka, su kasance da tabbacin cewa Jehobah zai ji adduꞌarsu kuma zai ƙarfafa su don su ci gaba da jimrewa.​—Zab. 116:1; Filib. 2:13.

18. A taƙaice, ta yaya dattawa za su yi koyi da Gideyon?

18 Akwai darussa da yawa da dattawa za su iya koya daga wurin Gideyon. Wato, ya kamata dattawa su san kasawarsu kuma kada su karɓi aikin da ya fi ƙarfinsu. Ya kamata su kasance da tawaliꞌu saꞌad da ꞌyanꞌuwa suka kushe su ko kuma suka yabe su. Dole ne su zama masu biyayya da masu ƙarfin zuciya, musamman ma yanzu da ƙarshen zamanin nan yake gabatowa. Kuma ya kamata su kasance da tabbacin cewa ko da mene ne za su fuskanta, Jehobah zai ƙarfafa su. Zai dace mu ci gaba da nuna godiya don waɗannan makiyaya kuma mu riƙa “girmama” su.​—Filib. 2:29.

WAƘA TA 120 Mu Koyi Nuna Sauƙin Kai Kamar Yesu

a A lokacin da Israꞌilawa suke cikin hali mai wuya ne Jehobah ya zaɓi Gideyon ya yi musu ja-goranci kuma ya kāre su. Gideyon ya yi shekaru 40 yana aikin nan da Jehobah ya ba shi da aminci. Amma ya fuskanci wasu matsaloli. Za mu tattauna yadda bin halin Gideyon zai taimaka wa dattawa saꞌad da suke fuskantar matsaloli a yau.

b Za mu nuna cewa mun san kasawarmu idan ba mu da girman kai kuma muka san cewa ba kome ne za mu iya yi ba. Za mu kuma nuna cewa mu masu tawaliꞌu ne idan muna girmama mutane kuma muna ɗaukansu da muhimmanci fiye da kanmu. (Filib. 2:3) Halaye biyun nan kusan ɗaya suke. Mutum mai tawaliꞌu yakan san cewa yana da kasawa.

c Ka duba talifin nan mai jigo, “Ku Ci Gaba da Bauta wa Jehobah Idan An Saka wa Aikinmu Taƙunƙumi” da ke Hasumiyar Tsaro ta Yuli, 2019, shafuffuka na 10-11, sakin layi na 10-13.