TALIFIN NAZARI NA 28
Ku Ci Gaba da Barin Tsoron Allah Ya Amfane Ku
“Mai yin tafiyarsa cikin gaskiya, mai tsoron Yahweh ne.”—K. MAG. 14:2.
WAƘA TA 122 Mu Tsaya Daram, Babu Tsoro!
ABIN DA ZA A TATTAUNA a
1-2. Kamar Lutu, wace matsala ce Kiristoci suke fuskanta a yau?
IDAN muka ga halaye marasa kyau da mutane suke da su a yau, yana sa mu ji kamar yadda Lutu ya ji. Lutu “ya damu ƙwarai game da irin mugayen ayyuka na mutanen Sodom marasa bin doka,” domin ya san cewa Ubanmu na sama ya tsani mugayen halaye. (2 Bit. 2:7, 8) Da yake Lutu yana tsoron Allah kuma yana ƙaunar sa sosai, ya tsani halayen mugayen mutane a zamaninsa. Mu ma a yau, muna rayuwa ne tare da mutanen da ba sa daraja ƙaꞌidodin Allah game da ɗabiꞌa. Duk da haka, za mu iya kasancewa da halaye masu kyau idan muka ci gaba da ƙaunar Allah kuma muna jin tsoron sa.—K. Mag. 14:2.
2 Saboda haka, Jehobah ya ba mu abin da zai taimaka mana ta wurin shawarwarin da ke littafin Karin Magana. Dukan Kiristoci, maza da mata, manya da ƙanana, za su amfana sosai idan suka bi shawarwari masu kyau da ke cikin littafin Karin Magana.
TSORON ALLAH KĀRIYA CE GARE MU
3. Bisa ga Karin Magana 17:3, me ya sa muke bukatar mu kāre zuciyarmu? (Ka kuma duba hoton.)
3 Yana da muhimmanci mu kāre zuciyarmu, domin Jehobah yana gwada zuciyarmu. Hakan yana nufin cewa idan ya kalle mu, yana ganin fiye da abin da mutane suke gani, kuma ya san ainihin tunanin zuciyarmu. (Karanta Karin Magana 17:3.) Idan tunanin abin da ya ce muka sa a zuciyarmu, hakan zai taimaka mana mu rayu har abada kuma zai sa ya ƙaunace mu. (Yoh. 4:14) Idan muka yi hakan, halaye marasa kyau da ƙararrayin Shaiɗan da na mugayen mutane a duniyar nan, ba za su samu wurin zama a zuciyarmu ba. (1 Yoh. 5:18, 19) Yayin da muke ƙara kusantar Jehobah, za mu ci gaba da ƙaunar sa kuma za mu ƙara daraja shi. Da yake ba ma so mu ɓata wa Ubanmu rai, ko tunanin yin zunubi ma ba za mu so yin sa ba. Idan muka shiga yanayin da zai sa mu yi zunubi, za mu tambayi kanmu cewa, ‘Don me zan yi abin da zai ɓata ran Wanda yake ƙauna ta sosai?’—1 Yoh. 4:9, 10.
4. Ta yaya tsoron Jehobah ya kāre wata ꞌyarꞌuwa daga faɗa wa jaraba?
4 Wata ꞌyarꞌuwa a ƙasar Kuroshiya mai suna Marta ta ce: “Yana min wuya in dinga tunanin abubuwa masu kyau kuma in guji shaꞌawar abubuwa marasa kyau. Amma jin tsoron Jehobah ya kāre ni.” b Ta yaya tsoron Allah ya kāre ꞌyarꞌuwarmu? Marta ta ce ta yi tunani a kan mugun sakamako da yin lalata zai jawo mata. Mu ma zai yi kyau mu yi hakan. Sakamako mafi muni shi ne, za mu sa Jehobah baƙin ciki sosai kuma mu rasa damar yi masa sujada har abada.—Far. 6:5, 6.
5. Wane darasi ka koya daga labarin Leo?
5 Idan muna tsoron Jehobah da gaske, za mu kiyayi yin abokantaka da waɗanda ba su da hali mai kyau. Wani ɗanꞌuwa mai suna Leo a ƙasar Kwango ya ga muhimmancin yin hakan. Shekaru huɗu bayan da ya yi baftisma, sai ya fara bin abokan banza. Ya zata cewa ba zunubi yake yi ba tun da ba ya bin su yin abubuwan da Jehobah ba ya so. Amma ba da jimawa ba, sai abokan nan nasa suka rinjaye shi ya sha giya fiye da kima kuma ya yi lalata. A lokacin ne ya soma tunanin abubuwa da iyayensa suka koya masa game da Jehobah, da kuma yadda ya rasa farin cikin da a dā yake yi. Hakan ya sa ya dawo hankalinsa. Da taimakon dattawa, ɗanꞌuwan ya komo ga Jehobah kuma yanzu yana farin ciki. Shi dattijo ne a ikilisiya kuma yana hidimar majagaba na musamman.
6. Waɗanne mata biyu ne za mu yi magana a kansu?
6 Bari mu bincika littafin Karin Magana sura 9. A wurin, an yi amfani da mata biyu don a kwatanta hikima da wawanci. c Yayin da muke wannan tattaunawar, mu tuna cewa duniyar nan tana ɗaukaka yin lalata da kuma batsa sosai. (Afis. 4:19) Don haka, yana da muhimmanci mu ci gaba da koyan yadda za mu ji tsoron Allah kuma mu kauce wa ayyuka marasa kyau. (K. Mag. 16:6) Hakika, dukanmu maza da mata, za mu amfana sosai in mun bi shawarar da ke surar nan. A surar, mun ji cewa kowace cikin matan nan tana gayyatar “marasa tunani.” Kowace tana cewa: ‘Ku zo gidana ku ci ku sha.’ (K. Mag. 9:1, 5, 6, 13, 16, 17) Amma abin da ke faruwa da waɗanda suka je gidajen mata biyun nan ya bambanta.
KADA KA BI WAWIYAR MACEN
7. Kamar yadda Karin Magana 9:13-18 suka ce, me ke faruwa da waɗanda suka bi wawiyar macen? (Ka kuma duba hoton.)
7 Ku ji gayyatar da macen nan da take wakiltar wawanci take yi. (Karanta Karin Magana 9:13-18.) Ta ɗaga murya tanakira ga marasa tunani tana cewa: “Ku zo nan!” Ku ci ku sha. Me zai faru da masu zuwa gidanta? “Matattu ne suke a wurin.” Wataƙila ku tuna inda aka yi irin wannan kwatancin a littafin Karin Magana. Misali, an ce mu guje wa mace mai zina da kuma “zaƙin baki.” An gaya mana cewa: “Gama gidanta hanyar mutuwa ce.” (K. Mag. 2:11-19) Karin Magana 5:3-10 sun sake jan kunnenmu game da wata “mace mai zina” wadda “ƙafafunta suna gangarowa zuwa kabari ne.”
8. Wane zaɓi ne ya zama dole mu yi?
8 Yanzu dole waɗanda suka ji gayyatar wawiyar macen su zaɓa ko za su je gidanta ko ba za su je ba. Mu ma za mu iya shiga yanayi da za mu bukaci yin irin wannan zaɓi. Me za mu yi idan wani ya zo yana rinjayar mu mu yi lalata ko in muka gamu da batsa?
9-10. Waɗanne dalilai ne suka sa ya dace mu guji halin lalata?
9 Akwai dalilai masu kyau da suka sa ya dace mu guji halin lalata. A kwatancin, an ce wawiyar macen tana cewa: “Ruwan sata yana da zaki.” Me ake nufi da “ruwan sata?” Littafi Mai Tsarki ya ce jimaꞌi da mata da miji suke yi kamar ruwa ne mai kayatarwa. (K. Mag. 5:) Idan namiji da mace suka yi aure, ba laifi ba ne su yi jimaꞌi. Amma ba haka yake da fasikanci ko kuma lalata da mutane suke yi ba. Wataƙila abin da ake nufi “ruwan sata” ke nan. Yawancin lokaci a ɓoye mutane suke yin sa, kamar ɓarayi. Wannan “ruwan sata” zai yi musu zaƙi musamman idan suna ganin ba za a taɓa kama su ba. Amma abin baƙin cikin shi ne, ruɗin kansu suke yi, domin Jehobah yana ganin kome. Ba abin da yake da ɗaci ko kuma muni kamar a ce mun ɓata dangantakarmu da Jehobah. Don haka, ba “zaƙi” ko kaɗan a wannan lamarin. ( 15-181 Kor. 6:9, 10) Amma fa, zancen bai ƙare a nan ba.
10 Lalata tana jawo wa mutum kunya kuma ta sa ya ji ba shi da daraja. Tana jawo yin cikin shege kuma takan raba aure. Shi ya sa hikima ce a gare mu mu guje wa wannan wawiyar matar da duk wani abin da za ta ba mu. Ban da cewa yin lalata zai sa Allah ya yi fushi da mu, da yawa cikin masu yin lalata suna kamuwa da cututtukan da suke sa su mutu da sauri. (K. Mag. 7:23, 26) Sura 9 aya 18 ta kammala da cewa: “Baƙinta kuma suna gangarowa zuwa wurin zaman matattu,” wato kabari. To me ya sa mutane da yawa suke karɓan gayyatarta tun da hakan yana da haɗari sosai?—K. Mag. 9:13-18.
11. Me ya sa kallon batsa yake da haɗari sosai?
11 Wani abin da ke sa mutane su amince da gayyatarta shi ne batsa. Wasu suna ganin kallon batsa ba ya yi wa mutum lahani. Amma gaskiyar ita ce, kallon batsa yana cutarwa sosai. Yana zub da mutuncin mutum kuma ya sa ba zai dinga ganin mutane da daraja ba. Ban da haka, in mutum ya fara, barin halin nan yana da wuya. Idan mutum ya kalli hoton batsa, da wuya ya manta abin da ya gani. Kallon batsa yana ƙara hura wa mutum muguwar shaꞌawa ne, maimakon ya kashe masa shaꞌawar. (Kol. 3:5; Yak. 1:14, 15) Shi ya sa da yawa daga cikin masu kallon batsa abin yakan kai su ga yin lalata.
12. Ta yaya za mu nuna cewa ba ma son kallon abubuwan da za su sa mu tunanin yin lalata?
12 Me ya kamata mu Kiristoci mu yi idan muka ga batsa babu zato, ko a waya ko talabijin ko kuma a kwamfutarmu? Mu kau da idanunmu nan da nan. Wani abin da zai taimaka mana mu yi hakan shi ne idan muka tuna cewa abokantakarmu da Jehobah ita ce abu mafi daraja da muke da ita. Ko hotunan da mutane suke gani ba batsa ba ne za su iya sa mu tunanin yin lalata. Me ya sa ya dace mu guji kallon su? Domin bai kamata mu yi duk wani abin da zai sa mu tunanin yin lalata ba, komen ƙaƙantarsa. (Mat. 5:28, 29) Wani dattijo a ƙasar Thailand mai suna David ya ce: “Nakan tambayi kaina cewa: ‘Ko da ma wannan abin ba batsa ba ne, Jehobah zai ji daɗi idan na ci gaba da kallon sa?’ Irin wannan tunanin yakan taimake ni in yi abin da ya dace.”
13. Me zai taimaka mana mu yi abin da ya dace?
13 Idan muka zama masu tsoron yin abin da zai ɓata wa Jehobah rai, hakan zai taimaka mana mu yi abin da ya dace. Tsoron Allah “shi ne mafarin hikima.” (K. Mag. 9:10) Kwatancin da aka yi a farko-farkon littafin Karin Magana sura 9 ya nuna gaskiyar wannan maganar. A wurin, an yi zancen ɗayan macen, kuma tana wakiltar “hikima.”
KA AMSHI GAYYATAR “HIKIMA”
14. Wace gayyata ce aka ba mu labarinta a Karin Magana 9:1-6?
14 Karanta Karin Magana 9:1-6. Gayyatar da ke ayoyin nan daga wurin Jehobah ne, Mahaliccinmu da kansa, wanda Shi ne Tushen hikima ta gaske. (K. Mag. 2:6; Rom. 16:27) Gidan da ake gayyatar mu mu je a wannan kwatancin babba ne, mai ginshiƙai bakwai. Wannan ya nuna yawan alherin Jehobah, don yana marabtar kowa da yake so ya saurare shi kuma ya koyi hikima.
15. Wace gayyata ce Jehobah yake mana a yau?
15 Jehobah Allah ne mai alheri sosai, kuma yakan yi mana tanadin abubuwa a yalwace. Kwatancin mace da ke nufin hikima ta gaske a Karin Magana sura 9, ya nuna hakan. A kwatancin, macen nan ta sa an yanka dabbobi domin bikin. Ta shirya ruwan inabinta, kuma ta shirya inda za a zauna a ci a sha. (K. Mag. 9:2) Ƙari ga haka, ayoyi 4 da 5 sun ce macen nan, wato “hikima,” ta yi kira “ga marasa hankali kuma ta ce, ‘Ku zo, ku ci abincina.’” Me ya sa zai dace mu je gidanta? Don Jehobah yana so ꞌyaꞌyansa su yi hikima kuma kar kome ya same su. Ba ya so mu yi kuskure kuma mu sha wuya kafin mu koyi darasi. Shi ya sa yake “ba masu gaskiya a zuci ainihin hikima.” (K. Mag. 2:7) Idan muna tsoron Jehobah da gaske, za mu so yin abin da zai faranta masa rai. Za mu saurari shawararsa, wadda hikima ce, kuma za mu so bin abin da ya gaya mana.—Yak. 1:25.
16. Ta yaya tsoron Allah ya taimaka wa Ɗanꞌuwa Alain ya tsai da shawarar da ta dace, kuma wane sakamako aka samu?
16 Ka lura da yadda tsoron Allah ya taimaka ma wani dattijo mai suna Alain ya tsai da shawarar da ta dace. Shi malami ne. Ya ce: “Abokan aikina da dama suna cewa a nasu raꞌayin, fim da ake nuna batsa hanya ce da ake ilimantar da mutane game da jimaꞌi.” Amma Ɗanꞌuwa Alain bai bari su ruɗe shi ba. Ya ce: “Saboda ina tsoron Allah, na gaya musu gar-da-gar cewa ba zan kalli bidiyoyin ba, kuma na gaya musu dalilin da ya sa.” Ɗanꞌuwa Alain ya yi hakan ne don yana bin shawarar da “hikima” ta ba mu cewa, “Ku yi tafiya a hanyar ganewa.” (K. Mag. 9:6) Abin da ya yi ya burge wasu malaman makarantarsu har sun soma nazarin Littafi Mai Tsarki kuma suna zuwa taro.
17-18. Waɗanne albarku ne waɗanda suka saurari kiran da hikima ta yi suke samu a yau, kuma me za su samu a nan gaba? (Ka kuma duba hoton.)
17 Jehobah ya yi amfani da kwatancin mata biyun nan ne don ya nuna mana abin da za mu yi don mu ji daɗin rayuwa a nan gaba. Waɗanda suke bin wawiyar macen, jin daɗin lalata ne suka sa a gaba. Ba su san cewa abin da suke yi zai shafe su a nan gaba ba. Ƙarshenta mutuwa za su yi.—K. Mag. 9:13, 17, 18.
18 Amma ba haka yake da masu bin macen nan da take wakiltar hikimar Jehobah ba. Suna farin ciki domin suna samun ci da sha, wato suna samun dukan abubuwa da suke bukata don su ci gaba da kusantar Jehobah. (Isha. 65:13) Ga abin da Jehobah ya ce ta bakin annabi Ishaya: “Ku ji ni da kyau, ku ci abinci mai kyau, ku ji wa ranku daɗi da abinci mafi kyau.” (Isha. 55:1, 2) Muna koyan yadda za mu so abin da Jehobah yake so kuma mu ƙi abin da yake ƙi. (Zab. 97:10) Kuma yadda muke gayyatar mutane su ma su zo su amfana daga hikimar Jehobah yana sa mu farin ciki. Kamar dai kira muke yi daga wurare mafi tsayi na birni, muna cewa: “Bari ku da kuke marasa tunani, ku juyo nan!” Mu da waɗanda suka saurare mu za mu amfana a yanzu, kuma za mu amfana har abada, don zai sa mu “rayu” yayin da muke “tafiya a hanyar ganewa.”—K. Mag. 9:3, 4, 6.
19. Bisa ga littafin Mai-Waꞌazi 12:13, 14, mene ne ya kamata ya zama ƙudurinmu? (Ka kuma duba akwatin nan “ Tsoron Allah Yana Amfanar Mu.”)
19 Karanta Mai-Waꞌazi 12:13, 14. Bari tsoron Allah ya ci gaba da kāre zukatanmu kuma ya taimaka mana mu guji halin lalata. Mu kuma ci gaba da kusantar sa a waɗannan miyagun kwanaki na ƙarshe. Tsoron Allah zai sa mu yi iya ƙoƙarinmu wajen gayyatar kowa da kowa su zo, su nemi “hikima,” don su ma su amfana.
WAƘA TA 127 Irin Mutumin da Ya Kamata In Zama
a Dole ne Kiristoci su zama masu tsoron Allah. Wannan tsoron zai kāre zuciyarmu, kuma zai taimaka mana mu guji halin lalata da kuma batsa. A wannan talifin, za mu tattauna Karin Magana sura 9. A wurin an yi kwatanci game da mata biyu, ɗaya tana wakiltar hikima, ɗaya kuma wawanci. Za mu koyi darussa masu muhimmanci a surar nan da za su taimaka mana a yau da kuma a nan gaba.
b An canja sunayen.
c Don ka ga misalin irin wannan kwatancin a Littafi Mai Tsarki, ka duba Romawa 5:14 da Galatiyawa 4:24.