Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 27

Me Ya Sa Ya Kamata Mu Ji Tsoron Jehobah?

Me Ya Sa Ya Kamata Mu Ji Tsoron Jehobah?

“Yahweh abokin masu tsoronsa ne.”​—ZAB. 25:14.

WAƘA TA 8 Jehobah Ne Mafakarmu

ABIN DA ZA A TATTAUNA a

1-2. Bisa ga Zabura 25:​14, me muke bukatar mu yi idan muna so mu zama abokan Jehobah?

 IDAN kana so ka ci gaba da zama aminin wani, waɗanne halaye ne kake ganin kake bukata? Ba mamaki za ka ce kana bukatar ka kasance mutum mai ƙauna da kuma halin taimako. Da wuya ka ce kana bukatar ka ji tsoron abokinka. Amma kamar yadda nassin da aka ɗauko jigon wannan talifin ya ce, idan mutum yana so ya zama aminin Jehobah, dole ya ji “tsoronsa.”​—Karanta Zabura 25:14.

2 Ko mun daɗe muna bauta wa Jehobah ko ba mu daɗe ba, dukanmu muna bukatar mu ci gaba da jin tsoron sa. Amma me ake nufi da jin tsoron Allah? Ta yaya za mu koyi zama masu jin tsoron Jehobah? Me za mu iya koya game da jin tsoron Allah daga wurin Obadiya, da Yehoyida Babban Firist da kuma Sarki Yowash?

ME AKE NUFI DA JIN TSORON ALLAH?

3. Ka bayyana yadda jin tsoro zai iya amfanar mu.

3 Mukan ji tsoro idan muka ga cewa muna cikin haɗari. Irin wannan tsoron zai iya taimaka mana mu yi abin da zai ceci ranmu. Idan muna a wani wuri mai tsawo, tsoro zai sa ba za mu yi tafiya a gefen da za mu yi saurin faɗuwa ba. Kuma idan muna a wani wuri mai haɗari, tsoro zai sa mu gudu mu bar wurin. Idan kuma muna tsoron kar mu yi abin da zai ɓata zumunci da ke tsakaninmu da wani, ba za mu yi, ko mu faɗi abin da zai ɓata masa rai ba.

4. Wane irin tsoron Jehobah ne Shaiɗan yake so mu dinga ji?

4 Shaiɗan yana so mutane su dinga yin fargaba idan suka yi tunanin Jehobah. Yana so mu gaskata cewa Jehobah mai zafin rai ne, cewa a kullum, neman dalilin hukunta mu yake yi, kuma ba za mu taɓa iya faranta masa rai ba. (Ayu. 4:​18, 19) Shaiɗan yana so mu riƙa jin irin wannan tsoron har ma mu daina bauta wa Jehobah. Amma bai kamata mu ji tsoron Jehobah haka ba. A maimako, mu koyi yadda za mu girmama shi, kuma mu guji yin abin da zai ɓata masa rai.

5. Me ake nufi da tsoron Allah?

5 Mutumin da yake tsoron Allah da gaske, zai ƙaunaci Allah kuma ba zai so ya yi abin da zai ɓata ma Allah rai ba. Yesu ya kasance da irin wannan “tsoron Allah.” (Ibran. 5:7) Bai yi fargaban Jehobah ba. (Isha. 11:​2, 3) A maimakon haka, ya ƙaunaci Jehobah sosai kuma ya so yin nufinsa. (Yoh. 14:​21, 31) Mu ma muna daraja Jehobah sosai, domin shi Allah ne mai ƙauna, mai hikima, mai adalci da kuma iko. Mun kuma san cewa da yake Jehobah yana ƙaunar mu sosai, yakan so ya ga mun bi abin da ya ce. Idan ba mu bi abin da ya gaya mana ba, yakan yi baƙin ciki, amma idan muka yi abin da ya ce, yakan yi farin ciki.​—Zab. 78:41; K. Mag. 27:11.

YADDA ZA MU KOYI JIN TSORON ALLAH

6. Ka bayyana wata hanya da za mu iya koyan jin tsoron Jehobah. (Zabura 34:11)

6 Ba a haifan mutum da tsoron Allah. Don haka, dole ne dukanmu mu koyi yadda za mu ji tsoron Jehobah. (Karanta Zabura 34:11.) Wata hanya da ake koyan jin tsoron Allah ita ce ta yin lura da halittunsa. Idan muna lura da abubuwan da ya halitta, za mu ga hikimarsa da ikonsa da kuma ƙaunar da yake da ita a gare mu. Hakan zai sa mu ƙara daraja shi kuma mu ƙaunace shi. (Rom. 1:20) Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Adrienne ta ce: “Idan na kalli halittun Jehobah kuma na ga irin hikimar da ya nuna a yadda ya halicce su, abin yakan ba ni mamaki, kuma yakan tabbatar min da cewa ya fi ni sanin abin da ya dace da ni.” Wannan zurfin tunani da ta yi ya sa ta kammala da cewa: “A gaskiya, ba zan so in yi duk wani abin da zai ɓata dangantakata da Jehobah, Allahn da ya ba ni rai ba.” Kai ma ka nemi zarafi wannan makon, don ka yi tunani a kan wani abin da Jehobah ya halitta. Yin hakan zai sa ka ƙara girmama Jehobah, kuma ka ƙaunace shi.​—Zab. 111:​2, 3.

7. Ta yaya yin adduꞌa zai sa mu zama masu tsoron Jehobah?

7 Wata hanya kuma da za mu iya koyan jin tsoron Allah ita ce ta yin adduꞌa a-kai-a-kai. Idan muna yin adduꞌa sosai, hakan zai sa mu ƙara kusantar Jehobah. A duk lokacin da muka roƙe shi ya ba mu ƙarfin jimre wata matsala, za mu tuna cewa shi mai iko duka ne. Idan muka gode ma Jehobah don Ɗansa da ya bayar ya cece mu, hakan zai tuna mana irin ƙaunar da yake mana. Kuma duk lokacin da muka roƙi Jehobah ya ba mu hikimar magance wata matsala, za mu tuna cewa shi mai hikima ne sosai. Irin adduꞌoꞌin nan suna sa mu ƙara girmama Jehobah, kuma sukan sa mu ƙara ƙudura cewa ba za mu yi abin da zai ɓata dangantakarmu da shi ba.

8. Me zai taimaka mana mu ci gaba da jin tsoron Jehobah?

8 Wani abin da zai taimaka mana mu ci gaba da jin tsoron Allah shi ne, yin nazarin Littafi Mai Tsarki da niyyar koyan darasi daga wurin mutanen da suka yi abubuwa masu kyau da kuma waɗanda suka yi marasa kyau. Bari mu tattauna labarin bayin Allah masu aminci guda biyu, wato Obadiya mai kula da gidan Sarki Ahab, da kuma Yehoyida Babban Firist. Bayan haka, za mu ɗauki darasi daga labarin Sarki Yowash na ƙasar Yahuda, wanda ya ƙaunaci Jehobah da farko amma daga baya ya bijire masa.

KA ZAMA MAI ƘARFIN ZUCIYA KAMAR OBADIYA

9. Mene ne tsoron Jehobah ya sa Obadiya ya yi? (1 Sarakuna 18:​3, 12)

9 Da aka fara ba da labarin Obadiya b a Littafi Mai Tsarki, an ce: “Obadiya kuwa mai tsoron Yahweh ne sosai.” (Karanta 1 Sarakuna 18:​3, 12.) Mene ne tsoron Allah ya sa Obadiya ya yi? Tsoron Allah ya sa ya zama amintaccen mutum mai yin gaskiya. Shi ya sa sarki ya naɗa shi ya zama mai kula da gidansa gabaki ɗaya. (Ka kuma duba Nehemiya 7:2.) Tsoron Allah ya kuma sa Obadiya ya zama mai ƙarfin zuciya sosai, kuma hakan ya taimaka masa ba kaɗan ba. A zamanin mugun sarkin nan Ahab ne Obadiya ya yi rayuwarsa. Sarki Ahab kuwa “ya aikata mugunta a idon Yahweh fiye da kowane mutumin da ya taɓa mulki kafin shi.” (1 Sar. 16:30) Matar Ahab kuma mai suna Jezebel, Baal take bauta wa. Ta tsani Jehobah sosai har ta yi ƙoƙarin sa a daina bauta masa a kabilu goma da suke arewacin Israꞌila. Ta kashe annabawan Jehobah da yawa. (1 Sar. 18:4) A gaskiya, abubuwa ba sauƙi a lokacin da Obadiya ya bauta wa Jehobah.

10. Ta yaya Obadiya ya nuna cewa shi mai ƙarfin zuciya ne sosai?

10 Ta yaya Obadiya ya nuna cewa shi mai ƙarfin zuciya ne sosai? Da Jezebel ta tashi neman annabawan Allah za ta kashe su, Obadiya ya ɓoye annabawa 100, ya sa su ‘hamsin-hamsin a kogo biyu, ya yi ta ba su abinci da ruwa.’ (1 Sar. 18:​13, 14) Da a ce Jezebel ta ji abin da Obadiya ya yi, da ta kashe shi. Ba mamaki Obadiya ya ji tsoro, don ba wanda yake so ya mutu. Amma Obadiya ya fi ƙaunar Jehobah da bayinsa, fiye da ransa.

Duk da cewa gwamnati ta hana aikinmu a ƙasarsu, wani ɗanꞌuwa ya yi ƙarfin zuciya yana raba ma ꞌyanꞌuwa littattafanmu (Ka duba sakin layi na 11) d

11. Ta yaya bayin Jehobah a zamaninmu suke bin halin Obadiya? (Ka kuma duba hoton.)

11 A yau, akwai mutane da yawa da suke zama a ƙasashen da gwamnati ta hana aikinmu. Suna daraja waɗanda suke mulki, amma kamar Obadiya, sun ƙi su daina bauta ma Jehobah. (Mat. 22:21) Sun nuna cewa suna tsoron Allah ta yadda suke yi masa biyayya fiye da mutum. (A. M. 5:29) Suna hakan ta wurin ci gaba da yin waꞌazi da kuma yin taro a ɓoye. (Mat. 10:​16, 28) Kuma suna yin iya ƙoƙarinsu wajen samar wa ꞌyanꞌuwansu abubuwa da za su sa su ci gaba da yin kusa da Jehobah. Alal misali, akwai wani ɗanꞌuwa mai suna Henri daga wata ƙasa a Afirka inda gwamnati ta taɓa hana aikinmu. A lokacin, Ɗanꞌuwa Henri ya yarda a dinga aikan sa yana kai wa ꞌyanꞌuwa littattafanmu. Ya ce: “Ni mai kunya ne sosai. Don haka, na tabbata yadda nake girmama Jehobah a zuciyata shi ne ya sa na iya yin ƙarfin zuciya har na yi aikin nan.” Kai ma za ka iya yin ƙarfin zuciya kamar Henri? Tabbas za ka iya, idan kana tsoron Jehobah.

KA ZAMA MAI AMINCI KAMAR YEHOYIDA BABBAN FIRIST

12. Ta yaya Yehoyida Babban Firist da matarsa suka nuna aminci sosai ga Jehobah?

12 Yehoyida Babban Firist ya ji tsoron Jehobah. Wannan tsoron ya sa ya zama mai aminci kuma ya goyi bayan bautar Jehobah. Ya nuna wannan halin a lokacin da Ataliya ꞌyar Jezebel ta kwace sarauta a ƙasar Yahuda. Ataliya abin tsoro ce kam. Ita muguwa ce kuma tana son yin sarauta sosai, da har ta yi ƙoƙarin kashe dukan jikokinta da za su gāji mulkin! (2 Tar. 22:​10, 11) Amma ɗaya cikinsu ya tsira. Sunansa Yowash, kuma Yehosheba matar Yehoyida ce ta ceto shi. Ita da maigidanta sun ɓoye yaron kuma sun yi ta kula da shi. Wannan abin da suka yi ne ya sa aka sami ɗan zuriyar Dauda da ya zama sarki a lokacin. Yehoyida ya riƙe amincinsa ga Jehobah kuma bai ji tsoron Ataliya ba.​—K. Mag. 29:25.

13. Ta yaya Yehoyida ya sake nuna cewa shi mai aminci ne a lokacin da Yowash ya kai shekara bakwai?

13 Da Yowash ya kai shekara bakwai, Yehoyida ya sake nuna amincinsa ga Jehobah. Ta yaya ya yi hakan? Ya yi wata dabara don ya sa a naɗa Yowash sarki. Idan ya yi nasara, hakan zai tabbata, amma idan bai yi nasara ba, zai iya rasa ransa. Jehobah ya albarkace shi kuma ya yi nasara. Shugabannin Yahuda da Lawiyawa sun taimaka wa Yehoyida ya naɗa Yowash sarki kuma ya kashe Ataliya. (2 Tar. 23:​1-5, 11, 12, 15; 24:1) Sai Yehoyida “ya sa Sarki Yowash da mutanen su yi yarjejeniya da Yahweh cewa za su kasance mutanen Yahweh.” (2 Sar. 11:17) Yehoyida ya kuma ‘sa masu gadi a ƙofofin shiga Gidan Yahweh, su dinga koran mutane masu ƙazanta.’​—2 Tar. 23:19.

14. Ta yaya aka girmama Yehoyida don ya girmama Jehobah?

14 Tun dama Jehobah ya ce: “Nakan girmama waɗanda suke girmama ni.” Kuma haka ya yi. Ya saka wa Yehoyida da alheri. (1 Sam. 2:30) Misali, ya sa an rubuta labarin wannan Babban Firist don mu ɗauki darasi. (Rom. 15:4) Kuma da Yehoyida ya rasu, an girmama shi sosai ta yadda aka “binne shi a Birnin Dawuda inda ake binne sarakuna, gama ya yi aiki mai kyau domin mutanen Israꞌila kuma domin Allah da Gidansa.”​—2 Tar. 24:​15, 16.

Kamar Yehoyida Babban Firist, bari tsoron Allah ya sa mu taimaka wa ꞌyanꞌuwanmu a kowane lokaci (Ka duba sakin layi na 15) e

15. Waɗanne darussa muka koya daga labarin Yehoyida? (Ka kuma duba hoton.)

15 Labarin Yehoyida zai iya taimaka mana mu ma mu zama masu tsoron Allah. Dattawa za su iya yin koyi da Yehoyida ta wurin neman yadda za su kāre ꞌyanꞌuwa a ikilisiya a ko da yaushe. (A. M. 20:28) Tsofaffi kuma, wannan labarin ya koya musu cewa idan suka ji tsoron Jehobah kuma suka riƙe aminci, Jehobah zai iya yin amfani da su don ya cika nufinsa. Kuma Jehobah ba zai taɓa manta da su ba. Matasa kuma, zai dace su tuna da yadda Jehobah ya sa aka girmama Yehoyida, kuma hakan ya sa su girmama ꞌyanꞌuwa tsofaffi, musamman waɗanda suka daɗe suna bauta ma Jehobah da aminci. (K. Mag. 16:31) A ƙarshe, za mu iya ɗaukan darasi daga wurin shugabanni da Lawiyawa da suka goyi bayan Yehoyida. Kamarsu, mu ma mu goyi bayan waɗanda suke mana ja-goranci a yau, ta wurin bin abin da suke gaya mana.​—Ibran. 13:17.

KADA MU ZAMA KAMAR YOWASH

16. Me ya nuna cewa Sarki Yowash ba ya tsoron Allah da gaske?

16 Yehoyida ya taimaka wa Yowash ya zama mutumin kirki. (2 Sar. 12:2) Don haka da sarki Yowash yake ƙarami, ya so yin abin da zai faranta wa Jehobah rai. Amma bayan rasuwar Yehoyida, sai Yowash ya bi shawarar dattawan Israꞌila da ba sa ƙaunar Jehobah. A ƙarshenta, sun rinjaye shi har shi da mutanensa “suka koma suna bauta wa gumakan Ashera da sauran gumaka.” (2 Tar. 24:​4, 17, 18) Abin ya ɓata wa Jehobah rai sosai har ya yi ta “aika musu da annabawa su ja musu kunne, duk da haka mutanen suka ƙi ji.” Har ma sun ƙi jin annabi Zakariya ɗan Yehoyida. c Zakariya kuwa firist ne a lokacin, kuma shi ɗan ꞌyarꞌuwar mahaifin Yowash ne. Har Sarki Yowash ya sa an kashe Zakariya, wanda iyayensa ne suka ceci ran shi Yowash.​—2 Tar. 22:11; 24:​19-22.

17. Me ya faru da Yowash daga baya?

17 Yowash bai ci gaba da jin tsoron Jehobah ba kuma hakan ya sa bai gama lafiya ba. Dā ma Jehobah ya ce: “Waɗanda suke rena ni za su sha wulaƙanci.” (1 Sam. 2:30) Daga baya sojojin Suriya da ba su da yawa ma, sun ci Yowash da yaƙi, duk da cewa yana tare da sojoji “masu yawan gaske.” Sun kuma bar shi da “rauni mai tsanani sosai.” Bayan yaƙin, sai bayin Yowash suka kashe shi don kisan da ya yi wa Zakariya. Saboda muguntarsa, mutanen ba su ma ga ya cancanta “a binne shi inda ake binne sarakuna ba.”​—2 Tar. 24:​23-25.

18. Bisa ga Irmiya 17:​7, 8, me za mu yi don kar mu zama kamar Yowash?

18 Wane darasi za mu koya daga labarin Yowash? Abin da Yowash ya yi ya nuna cewa shi kamar bishiya ne da jijiyoyinsa ba su riƙe ƙasa ba. Sanda da aka tokare bishiyar da ita ce take taimaka ma bishiyar ta tsaya a tsaye. Yehoyida shi ne kamar wannan sandan da Yowash ya dogara a kai. Da Yehoyida ya rasu kuma Yowash ya saurari ꞌyan ridda, ya faɗi kasa, wato ya daina bauta wa Jehobah. Wannan ya koya mana cewa, bai kamata mu dinga jin tsoron Allah don kawai mun ga ꞌyanꞌuwanmu Kiristoci ko kuma ꞌyan gidanmu suna hakan ba. Idan muna so mu riƙe aminci ga Jehobah, dole mu ci gaba da yin abubuwan da za su sa mu ƙaunace shi kuma mu girmama shi, wato mu dinga yin nazarin Littafi Mai Tsarki a-kai-a-kai, da yin tunani mai zurfi, da kuma yin adduꞌa.​—Karanta Irmiya 17:​7, 8; Kol. 2:​6, 7.

19. Mene ne Jehobah yake so mu yi?

19 Jehobah ba ya gaya mana mu yi abin da ya fi ƙarfinmu. Littafin Mai-Waꞌazi 12:13 ta gaya mana abin da yake so daga gare mu. Ta ce: “Ka ji tsoron Allah, ka kiyaye umarnansa, gama wannan kaɗai shi ne aikin mutum.” Idan muna da tsoron Allah, za mu iya riƙe amincinmu ga Jehobah ko da me zai faru a nan gaba, kamar yadda Obadiya da Yehoyida suka yi. Ba abin da zai ɓata dangantakarmu da Jehobah.

WAƘA TA 3 Ƙarfinmu, Begenmu da Makiyayinmu

a A Littafi Mai Tsarki, kalmar nan ‘tsoro’ tana iya nufin abubuwa dabam-dabam. Wani lokaci tana nufin mutum ya yi fargaba, ya girmama wani ko kuma ya yi mamaki. Wannan talifin zai taimaka mana mu ga yadda za mu zama masu tsoron Allah. Wato irin tsoron da zai sa mu zama da ƙarfin zuciya da kuma aminci, yayin da muke bauta wa Ubanmu na sama.

b Obadiya da aka ambata a nan ba shi ne annabi Obadiya wanda ya rubuta littafin Obadiya ba. Ɗarurruwan shekaru bayan wannan Obadiyan ne aka haifi annabi Obadiya.

c A Matiyu 23:​35, an kira Zakariya ɗan Berekiya. Wasu sun ce mai yiwuwa Yehoyida yana da suna biyu shi ya sa, kamar yadda wasu a Littafi Mai Tsarki suke da suna biyu. (Ga misali a Matiyu 9:9 da Markus 2:14.) Wasu kuma sun ce mai yiwuwa Berekiya kakan Zakariya ne.

d BAYANI A KAN HOTUNA: Ana kwatanta yadda wani ɗanꞌuwa ya raba wa ꞌyanꞌuwa littattafai a lokacin da aka hana aikinmu.

e BAYANI A KAN HOTUNA: Wata ꞌyarꞌuwa matashiya tana koyan yadda za ta yi waꞌazi da waya daga wurin wata ꞌyarꞌuwa da ta manyanta; wani ɗanꞌuwa da ya tsufa yana waꞌazi da ƙarfin zuciya a inda akwai jamaꞌa; wani ɗanꞌuwa da ya ƙware yana koya ma wasu matasa yadda za su kula da Majamiꞌar Mulki.