TALIFIN NAZARI NA 23
WAƘA TA 28 Yadda Za Mu Zama Abokan Jehobah
Jehobah Yana Gayyatarmu Mu Zo Tentinsa
“Wurin zamana [ko tentina] zai kasance a tsakiyarsu. Zan zama Allahnsu, su kuma su zama mutanena.”—EZEK. 37:27.
ABIN DA ZA MU KOYA
Za mu koyi abin da kasancewa a cikin tentin Jehobah yake nufi, da kuma yadda Jehobah yake kula da waɗanda ya gayyata.
1-2. Wane gata ne Jehobah ya ba wa bayinsa masu aminci?
IDAN aka tambaye ka, mene ne matsayin Jehobah a gare ka? Me za ka ce? Kana iya cewa Jehobah ‘Ubana ne, Allahna, da kuma Abokina.’ Akwai wasu kalmomi ma da za ka iya amfani da su, ban da waɗannan. Amma za ka kwatanta Jehobah da wani da ya gayyace ka zuwa gidansa?
2 Sarki Dauda ya kwatanta Jehobah da mai karɓan baƙi, kuma ya ce bayinsa masu aminci kamar baƙi ne a tentinsa. Ya ce: “Yahweh, wa ya isa ya zauna a Tentinka? Wa ya isa ya yi sujada a Sihiyona, Tudunka Mai Tsarki?” (Zab. 15:1) Abin da Dauda ya faɗa ya koya mana cewa za mu iya shiga tentin Jehobah, wato, mu zama aminansa. Wannan ba ƙaramin gata ba ne.
JEHOBAH YANA SO MU SHIGO TENTINSA
3. Wane ne ya fara shiga tentin Jehobah, kuma yaya shi da Jehobah suka ji?
3 Jehobah ne kaɗai yake rayuwa kafin ya halicci kome-da-kome. Daga baya, ya halicci Ɗansa na fari, wato Yesu. A lokacin ne ya gayyace shi ya shigo tentinsa. Yin hakan ya sa Jehobah farin ciki sosai. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah ya ji daɗin kasancewa da Ɗansa. Kuma Yesu, wanda shi ne ya fara shiga tentinsa ya ce: “Koyaushe ina farin ciki a gabansa.”—K. Mag. 8:30.
4. Su waye ne kuma suka sami gatan shiga tentin Jehobah?
4 Daga baya kuma, Jehobah ya halicci malaꞌiku kuma su ma ya gayyace su su shigo tentinsa. Littafi Mai Tsarki ya kira malaꞌikun “ꞌyaꞌyan Allah,” kuma ya ce suna farin cikin kasancewa tare da shi. (Ayu. 38:7; Dan. 7:10) A lokacin, waɗanda suke sama ne kaɗai suke tentin Jehobah, kuma an yi shekaru da dama ana haka. Daga baya, ya halicci mutane, kuma ya gayyace su su zo tentinsa. Wasu da suka sami wannan babban gatan su ne Anuhu, da Nuhu, da Ibrahim da kuma Ayuba. Littafi Mai Tsarki ya kuma nuna cewa sun yi ma Jehobah biyayya, shi ya sa suka zama aminansa.—Far. 5:24; 6:9; Ayu. 29:4; Isha. 41:8.
5. Me muka koya daga annabcin da ke Ezekiyel 37:26, 27?
5 Har wa yau, Jehobah yana gayyatar aminansa su zo tentinsa. (Karanta Ezekiyel 37:26, 27.) Alal misali, annabcin da Ezekiyel ya yi ya nuna cewa Allah yana so bayinsa masu aminci su kusace shi sosai. Ya yi alkawari cewa zai “yi yarjejeniyar salama da su.” Annabcin nan yana magana ne game da lokacin da waɗanda za su je sama da waɗanda za su yi rayuwa a duniya, za su kasance cikin tentin Jehobah, kuma dukansu za su zama “garke ɗaya.” (Yoh. 10:16) Annabcin nan yana cikawa a yau!
JEHOBAH YANA KULA DA MU KO DA A INA MUKE
6. Me za mu yi don mu shiga tentin Jehobah, kuma a ina za a iya samun tentinsa?
6 A zamanin dā, tenti wuri ne da mutane suke hutawa kuma suke samun kāriya daga iska mai ƙarfi, da rana, da dai sauransu. Idan wani ya gayyaci mutum zuwa tentinsa, mutumin ya san cewa za a kula da shi sosai. Mu ma idan muka yi alkawarin bauta wa Jehobah, mun shiga tentinsa ke nan. (Zab. 61:4) Jehobah yana kula da mu ta wurin ba mu abubuwa da yawa da za su ƙarfafa dangantakarmu da shi. Kuma muna jin daɗin kasancewa tare da ꞌyanꞌuwanmu waɗanda su ma sun shigo tentinsa. Dukanmu za mu iya shiga tentin Jehobah, ko da a ina ne muke zama. Ko ka je wata ƙasa, idan ka halarci taronmu, za ka haɗu da ꞌyanꞌuwa da su ma suna jin daɗin kasancewa a cikin tentin Jehobah. Hakika, ko da a ina muke, za mu iya shiga tentin Jehobah.—R. Yar. 21:3.
7. Me ya sa muka ce bayin Allah da suka mutu ma suna cikin tentin Jehobah? (Ka kuma duba hoton.)
7 Shin, za mu iya cewa bayin Allah da suka mutu ma suna cikin tentin Jehobah? Ƙwarai kuwa! Me ya sa muka ce hakan? Domin a gun Jehobah, kamar suna raye ne. Yesu ya ce: “Musa ya kuma nuna a fili cewa waɗanda suka mutu za su tashi. A labarin ƙaramin itacen da ya ci wuta, ya yi magana a kan Ubangiji cewa, ‘Shi ne Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku, da kuma Allah na Yakub’. Shi ba Allah na matattu ba ne, amma na masu rai. Wannan ya nuna cewa a gare shi kowa mai rai ne.”—Luk. 20:37, 38.
YADDA MUKE AMFANA DA KUMA HAKKINMU
8. Ta yaya kasancewa cikin tentin Jehobah yake amfanar mu?
8 Kamar yadda mutum zai iya samun kāriya da hutu idan ya shiga tenti, haka ma tentin Jehobah yana kāre bayinsa daga duk wani abin da zai ɓata dangantakarsu da shi, kuma yana ba su bege. Idan mun ci-gaba da kusantar Jehobah, Shaiɗan ba zai iya yi mana illa da za ta dawwama ba. (Zab. 31:23; 1 Yoh. 3:8) A sabuwar duniya, Jehobah zai ci-gaba da kāre bayinsa daga duk wani abin da zai ɓata dangantakarsu da shi, kuma zai kawar da mutuwa.—R. Yar. 21:4.
9. Mene ne Jehobah yake so waɗanda suke a tentinsa su yi?
9 Hakika, kasancewa cikin tentin Jehobah babban gata ne, domin hakan ya ba mu damar zama aminansa har abada. Mene ne ya kamata mu yi don mu ci-gaba da zama cikin tentin Jehobah? Idan wani ya gayyace ka zuwa gidansa, ba za ka so ka yi wani abu da zai ɓata masa rai ba. Alal misali, idan ba zai so ka shiga ɗakinsa da takalma ba, ba za ka yi hakan ba. Haka ma, idan muna so mu ci-gaba da kasancewa cikin tentin Jehobah, dole ne mu yi abin da yake so. Kuma ƙaunar da muke yi wa Jehobah zai sa mu yi duk abin da za mu iya yi don mu “faranta masa rai.” (Kol. 1:10) Ko da yake Jehobah amininmu ne, ya kamata mu tuna cewa shi Allahnmu ne da kuma Ubanmu, wanda ya cancanci mu girmama shi. (Zab. 25:14) Hakan yana da muhimmanci sosai. Saboda haka, mu ci-gaba da girmama shi kowane lokaci. Idan muna girmama Jehobah, za mu ji tsoron yin abin da zai ɓata masa rai, kuma za mu ci-gaba da bauta masa “cikin sauƙin kai.”—Mik. 6:8.
JEHOBAH BAI NUNA BAMBANCI BA SAꞌAD DA YAKE SHAꞌANI DA ISRAꞌILAWA
10-11. Wane misali ne ya nuna cewa Jehobah ba ya nuna bambanci?
10 Jehobah ba ya nuna bambanci saꞌad da yake shaꞌani da baƙinsa. (Rom. 2:11) Idan muka dubi yadda ya bi da Israꞌilawa a Dajin Sinai, za mu ga cewa Jehobah ba mai nuna bambanci ba ne.
11 Bayan da Jehobah ya ꞌyantar da Israꞌilawa daga ƙasar Masar, ya naɗa firistoci su yi hidama a tentin saɗuwa. Ya kuma ba Lawiyawa hakkin yin wasu ayyuka a tentin. Amma, Jehobah ya kula da waɗanda suke hidima a tentin, da waɗanda suke zama kusa da tentin fiye da sauran jamaꞌar ne? Aꞌa. Jehobah ba ya nuna bambanci.
12. Ta yaya Jehobah ya nuna cewa ba ya nuna bambanci a shaꞌaninsa da Israꞌilawa? (Fitowa 40:38) (Ka kuma duba hoton.)
12 Kowane Baꞌisraꞌile ne zai iya zama aminin Jehobah ko da ba ya hidima a tentin, ko ba ya zama kusa da tentin. Alal misali, Jehobah ya tabbatar da cewa, dukan jamaꞌar Israꞌila suna iya ganin ƙunshin girgijen da yakan kasance a bisa tentin da rana, da kuma wuta da yakan kasance cikin girgijen da dare. (Karanta Fitowa 40:38.) Idan girgijen ya soma tafiya, waɗanda suke nesa da tentin ma sukan gani, su tattara kayansu, su warware tentinsu kuma su kama tafiya tare da sauran jamaꞌar. (L. Ƙid. 9:15-23) Ƙari ga haka, idan aka busa kakaki biyu na azurfa don a yi shelar tashi daga zango, kowa yakan ji kuma ya kama hanya. (L. Ƙid. 10:2) Hakan yana nufin cewa waɗanda suke kusa da tentin ba su fi waɗanda suke nesa da tentin kusa da Jehobah ba. Don haka, kowane Baꞌisraꞌile zai iya shiga tentin Jehobah kuma ya kasance da tabbaci cewa Jehobah zai kāre shi, kuma ya yi masa ja-gora. A yau ma, ko da a ina ne muke zama, muna da tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunarmu, yana kula da mu, kuma zai kāre mu.
MISALAI DA SUKA NUNA CEWA JEHOBAH BA YA NUNA BAMBANCI A YAU
13. A yau, ta yaya Jehobah yake nuna wa bayinsa cewa ba ya nuna bambanci?
13 Wasu yanꞌuwa suna zama kusa da hedkwatarmu ko kuma reshen ofishinmu. Wasu ma a wuraren nan suke hidima. Hakan yana ba su damar yin ayyuka da yawa a wurin, kuma sukan yi cuɗanya da ꞌyanꞌuwa da ke ja-goranci. Wasu kuma suna yin hidima ta cikakken lokaci, kamar mai kula da daꞌira da dai sauransu. Amma yawancin bayin Jehobah ba sa kusa da hedkwata ko reshen ofishinmu, kuma ba sa irin wannan hidimar. Idan kana cikinsu, ka kasance da tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunar dukan bayinsa kuma ya amince su zauna a tentinsa. Ya san kowannenmu sosai kuma yana kula da mu. (1 Bit. 5:7) Jehobah yana ba wa dukan bayinsa abubuwan da suke bukata don su ƙara yin kusa da shi. Yana musu ja-goranci kuma yana kāre su.
14. Mene ne kuma Jehobah ya ba mu da ya nuna cewa ba ya nuna bambanci?
14 Wata hanya kuma da Jehobah ya nuna cewa shi ba mai nuna bambanci ba ne, ita ce ya ba mu Kalmarsa a hanyar da kowa zai iya samu ya karanta. Da yaruka uku ne aka rubuta asalin Littafi Mai Tsarki, wato Ibrananci da yaren Aramaic da kuma Helenanci. Amma, waɗanda sun iya karatun yarukan nan sun fi waɗanda ba su iya ba kusantar Jehobah ne? Sam, ba haka ba ne.—Mat. 11:25.
15. Game da Littafi Mai Tsarki, me ya nuna cewa Jehobah ba ya nuna bambanci? (Ka kuma duba hoton.)
15 Ba masu ilimi ko waɗanda suka iya karanta ainihin yaren da aka rubuta Littafi Mai Tsarki ne kawai Jehobah yake amince da su ba. Ya sa an fassara Littafi Mai Tsarki zuwa dubban yaruka. Kowa a duniya, ko yana da ilimi sosai ko aꞌa, zai iya samun Littafi Mai Tsarki kuma ya karanta shi, ya amfana daga koyarwarsa kuma ya san yadda zai zama aminin Allah.—2 Tim. 3:16, 17.
KA CI-GABA DA KASANCEWA CIKIN TENTIN JEHOBAH
16. Kamar yadda Ayyukan Manzanni 10:34, 35 suka nuna, me ya kamata mu yi don mu ci-gaba da zama a tentin Jehobah?
16 Babban gata ne Jehobah ya ba mu da ya gayyace mu zuwa tentinsa. Babu mai karɓan baƙi kamar Jehobah domin ya fi kowa nuna ƙauna. Ban da haka ma, Jehobah ba ya nuna bambanci ko kaɗan. Yana so dukanmu maza da mata mu yi kusa da shi, ba tare da yin laꞌakari da inda muke zama, ko alꞌadunmu, ko launin fatarmu, ko ƙabilunmu, ko shekarunmu, ko muna da ilimi ko ba mu da shi ba. Amma waɗanda suke yi ma Jehobah biyayya ne kaɗai za su ci-gaba da zama a tentinsa.—Karanta Ayyukan Manzanni 10:34, 35.
17. Me za mu tattauna a talifi na gaba?
17 A Zabura 15:1, Dauda ya ce: “Yahweh, wa ya isa ya zauna a Tentinka? Wa ya isa ya yi sujada a Sihiyona, Tudunka Mai Tsarki?” Kuma Jehobah ya sa Dauda ya rubuta amsar tambayoyin. A talifi na gaba, za mu tattauna wasu abubuwa da wajibi ne mu yi don mu ci-gaba da zama a tentin Jehobah.
WAƘA TA 32 Mu Kasance da Aminci ga Jehobah!