Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 26

WAƘA TA 8 Jehobah Ne Mafakarmu

Ka Mai da Jehobah Dutsen Buyanka

Ka Mai da Jehobah Dutsen Buyanka

“Babu wani dutsen ɓuya kamar Allahnmu.”1 SAM. 2:2.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga halaye da suka sa aka kira Jehobah dutse, da kuma yadda za mu yi koyi da halayen.

1. Kamar yadda aka nuna a Zabura 18:46, da mene ne Dauda ya kwatanta Jehobah?

 A WASU lokuta, za mu iya fuskantar matsaloli da ba mu yi tsammani ba, kuma hakan zai iya sa mu shiga mawuyacin yanayi ko kuma ya canja rayuwarmu gabaki ɗaya. Amma abin farin cikin shi ne idan muka roƙi Jehobah, zai taimaka mana! A talifin da ya gabata, mun koyi cewa Jehobah Allah ne mai rai kuma a kullum yana a shirye ya taimaka mana. Idan Jehobah ya taimaka mana, hakan yana tabbatar mana da cewa shi “mai rai ne!” (Karanta Zabura 18:46.) Bayan da Dauda ya ce Yahweh mai rai ne, sai ya kwatanta shi da abin da bai da rai. Ya ce da shi, “dutsen ɓuyana!” Me ya sa Dauda ya kwatanta Jehobah da dutse?

2. Me za mu tattauna a wannan talifi?

2 A wannan talifin, za mu ga dalilin da ya sa aka kira Jehobah dutse, da abin da hakan ya koya mana game da shi. Za mu kuma koyi yadda za mu dogara gare shi, don ya zama Dutsen ɓuyanmu. A ƙarshe, za mu ga yadda za mu yi koyi da halayen da suka sa aka kira Jehobah dutse.

ME YA SA AKA KIRA JEHOBAH DUTSE?

3. Me ya sa aka yi ta kwatanta Jehobah da “dutse” a Littafi Mai Tsarki? (Ka duba hoton.)

3 A Littafi Mai Tsarki, an kwatanta Jehobah da dutse don a taimaka mana mu fahimci wasu halayensa. A yawanci lokuta, saꞌad da bayin Allah suke yabon sa ne suke kiran sa dutse. Kuma a Maimaitawar Shariꞌa 32:4 ne aka fara kwatanta Jehobah da dutse. Saꞌad da Hannatu take adduꞌa ta ce: “Babu wani dutsen ɓuya kamar Allahnmu.” (1 Sam. 2:2) Habakkuk ma ya kira Jehobah “Dutse.” (Hab. 1:12) Ƙari ga haka, marubucin Zabura ta 73 ya ce “Allah shi ne pa [ko dutse] na zuciyata.” (Zab. 73:26, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Jehobah da kansa ma ya ce shi dutse ne. (Isha. 44:8) Bari mu tattauna halaye uku da suka sa aka kwatanta Jehobah da dutse, da yadda za mu ɗauki Jehobah a matsayin “Dutsenmu.”M. Sha. 32:31.

Jehobah yana kama da dutsen ɓuya ga bayinsa (Ka duba sakin layi na 3)


4. Me ya sa za mu ce Jehobah wurin ɓuya ne? (Zabura 94:22)

4 Jehobah wurin ɓuya ne. Kamar yadda mutum zai iya ɓoyewa a kogon dutse don ya samu kāriya idan ana ruwa da iska mai ƙarfi, haka ma Jehobah yakan kāre mu idan muka shiga yanayi mai wuya. (Karanta Zabura 94:22.) Yakan kāre mu daga duk wani abin da zai ɓata dangantakarmu da shi. Kuma ya tabbatar mana da cewa matsalolin da muke fuskanta yanzu ba za su iya yi mana lahani da zai dawwama ba. Ban da haka ma, ya yi mana alkawari cewa a nan gaba zai kawar da matsaloli da baƙin ciki da muke fama da su a yanzu.—Ezek. 34:25, 26.

5. Me za mu yi don Jehobah ya kāre mu?

5 Wani abu da za mu yi don Jehobah ya kāre mu shi ne adduꞌa. Idan muka yi adduꞌa, ‘Allah zai ba mu salama’ da za ta tsare zukatanmu da tunaninmu. (Filib. 4:6, 7) Abin da ya faru da wani ɗanꞌuwa mai suna Artem ke nan. An kulle shi a fursun don yana bauta ma Jehobah. Da yake fursun, an yi masa tambayoyi da dama, kuma wanda ya yi masa tambayoyin ya zalunce shi. Artem ya ce: “Nakan ji tsoro idan mutumin ya kira ni yana so ya yi min tambayoyi. . . . Amma nakan roƙi Jehobah ya ba ni hikima da kwanciyar hankali. Don haka, na iya jimre abubuwan da na fuskanta. . . . Jehobah ya taimaka min. Ya zama kamar dutse a gabana, ni kuma na ɓoye a bayansa.”

6. Me ya tabbatar mana da cewa za mu iya dogara ga Jehobah a kowane lokaci? (Ishaya 26:3, 4)

6 Jehobah madogara ne. Kamar yadda ba za a iya matsar da babban dutse ba, haka ma Jehobah yana nan tare da mu har abada. Za mu iya dogara gare shi domin shi “dutsen ɓuyanmu na har abada ne.” (Karanta Ishaya 26:3, 4.) Har abada Jehobah zai ci-gaba da cika alkawuransa, da jin adduꞌoꞌinmu, da kuma taimaka mana idan muna cikin bukata. Ƙari ga haka, za mu iya dogara ga Jehobah domin shi mai aminci ne da ba ya barin bayinsa. (2 Sam. 22:26) Ba zai taɓa manta da ayyuka da muka yi dominsa ba, kuma zai ba mu lada.—Ibran. 6:10; 11:6.

7. Ta yaya za mu amfana idan muka dogara ga Jehobah? (Ka kuma duba hoton.)

7 Ta yaya za mu mai da Jehobah dutsen ɓuyanmu? Ta wurin dogara gare shi da dukan zuciyarmu. Muna da tabbaci cewa idan muka yi masa biyayya ko da hakan ba shi da sauƙi, za mu amfana. (Isha. 48:17, 18) A duk lokacin da muka ga yadda Jehobah ya taimaka mana, za mu ƙara dogara gare shi. Saꞌan nan za mu kasance da tabbaci cewa ko da wace irin matsala ce za ta zo mana, Jehobah zai taimaka mana. A yawancin lokuta idan muka shiga yanayi mai wuya, kuma ba wanda zai taimaka mana, mukan tuna cewa Jehobah ne kaɗai za mu iya dogara gare shi a kowane lokaci. Wani ɗanꞌuwa mai suna Vladimir ya ce: “Tun da na soma bauta ma Jehobah, lokacin da aka kulle ni ne na fi yin kusa da shi. Na ƙara dogara ga Jehobah domin a lokacin an raba ni da kowa, kuma shi kaɗai ne zai iya taimaka min in jimre.”

Idan muka dogara ga Jehobah da dukan zuciyarmu, zai zama Dutsen ɓuyanmu (Ka duba sakin layi na 7)


8. (a) Me ya nuna cewa Jehobah ba ya canjawa? (b) Ta yaya sanin cewa Jehobah ba ya canjawa yake amfanar mu? (Zabura 62:6, 7)

8 Jehobah ba ya taɓa canjawa. Kamar yadda babban dutse ba ya canja kamanninsa, haka ma Jehobah ba ya canjawa. Ba zai taɓa canja halinsa da nufinsa ba. (Mal. 3:6) A lokacin da Adamu da Hauwaꞌu suka yi masa tawaye, Jehobah bai canja nufinsa ga ꞌyan Adam ba. Shi ya sa manzo Bulus ya ce, Jehobah “ba za ya iya yin mūsun kansa ba.” (2 Tim. 2:13) Hakan yana nufin cewa, ko da me zai faru, Jehobah ba zai taɓa canja yadda yake, ko nufinsa, ko ƙaꞌidodinsa ba. Da yake Jehobah ba ya canjawa, mun san cewa zai taimaka mana idan muka shiga yanayi mai wuya, kuma zai cika alkawuran da ya yi mana.—Karanta Zabura 62:6, 7.

9. Me ka koya daga labarin Tatyana?

9 Idan muna tunani mai zurfi a kan halayen Jehobah, da nufinsa ga duniya da kuma ꞌyan Adam, hakan zai taimaka mana mu ƙara dogara gare shi, kuma zai zama dutsen ɓuyanmu. Hakan zai ba mu kwanciyar hankali, kuma zai sa mu riƙe amincinmu idan muna cikin matsala. (Zab. 16:8) Abin da wata ꞌyarꞌuwa mai suna Tatyana ta yi ke nan saꞌad da hukumomi suka hana ta barin gida domin bangaskiyarta. Ta ce: “Na kaɗaita. Da farko, abin bai yi min sauƙi ba sam, kuma na yi baƙin ciki sosai.” Amma sai ta soma tunani mai zurfi a kan Jehobah da nufinsa ga duniya da kuma ꞌyan Adam, kuma ta ga cewa yana da muhimmanci ta jimre tsanantawa da ake mata. Hakan ya kwantar mata da hankali kuma ya ba ta ƙarfin jimrewa. Ta ce: “Da na tuna abin da ya sa abubuwan nan suke faruwa da ni, sai na ga cewa wahalar da nake sha don Jehobah ne. Hakan ya taimaka min in daina mai da hankali a kan wahalar da nake sha.”

10. Me za ka yi don Jehobah ya zama Dutsen ɓuyanka?

10 A nan gaba, za mu shiga yanayi mai wuya da ba mu taɓa shiga ba, kuma za mu bukaci taimakon Jehobah sosai. Saboda haka, yana da muhimmanci ka yi abubuwan da za su sa ka ƙara ba da gaskiya ga Jehobah, kuma ka kasance da tabbaci cewa zai taimaka maka ka riƙe amincinka ko da me za ka fuskanta. Waɗanne abubuwa ke nan? Ka karanta labaran bayin Allah a Littafi Mai Tsarki da na zamaninmu. Yayin da kake karatun, ka lura da yadda Jehobah ya taimake su. Kuma ka yi tunani mai zurfi a kan abin da ya faru da su. Hakan zai sa kai ma ka mai da Jehobah Dutsen ɓuyanka.

KA YI KOYI DA HALAYEN JEHOBAH

11. Ta yaya za mu amfana idan muka yi koyi da halayen Jehobah? (Ka kuma duba akwatin nan “ Maƙasudin da Samari Za Su Iya Kafawa.”)

11 Mun ga halaye da suka sa aka kwatanta Jehobah da dutse. Yanzu, bari mu ga yadda za mu yi koyi da shi. Idan muka yi ƙoƙari muka yi hakan, za mu ƙarfafa ꞌyanꞌuwanmu. Alal misali, Yesu ya ba Siman suna, Kefas ko kuma, “Bitrus mai maꞌana ‘dutse.’” (Yoh. 1:42) Me ya sa Yesu ya ba shi suna dutse? Domin Yesu ya san cewa zai ƙarfafa ꞌyanꞌuwa, kuma zai taimaka musu su riƙe aminci. Littafi Mai Tsarki ya kwatanta dattawa da “inuwar babban dutse.” Wato suna kāre ꞌyanꞌuwa a ikilisiya. (Isha. 32:2) Amma idan dukanmu muka yi koyi da halayen Jehobah, za mu ƙarfafa juna.—Afis. 5:1.

12. Ta yaya za mu zama wurin ɓuya ga ꞌyanꞌuwanmu?

12 Ka zama wurin ɓuya. Idan balaꞌi ya shafi ꞌyanꞌuwanmu, ko ana tashin hankali a inda suke, za mu iya ba su wurin kwana. Da yake muna “kwanakin ƙarshe,” abubuwa suna daɗa muni. Don haka ꞌyanꞌuwa za su bukaci taimakonmu sosai. (2 Tim. 3:1) Za mu iya nuna musu ƙauna kuma mu taꞌazantar da su idan da bukata. Hanya ɗaya da za mu iya yin haka ita ce ta wurin marabtar su, da kuma yin faraꞌa idan muka haɗu da su a Majamiꞌar Mulki. Hakan zai sa kowa ya ji daɗin kasancewa a ikilisiya. Mutane da yawa a yau ba sa nuna ƙauna, kuma hakan zai iya sa ꞌyanꞌuwanmu baƙin ciki. Shi ya sa yana da muhimmanci mu yi iya ƙoƙarinmu mu nuna musu ƙauna idan suka zo taro.

13. Ta yaya dattawa za su zama wurin ɓuya ga ꞌyanꞌuwa? (Ka kuma duba hoton.)

13 Dattawa za su iya zama wurin ɓuya ga ꞌyanꞌuwa da suke fama da matsaloli dabam-dabam. Idan aka yi wani balaꞌi ko kuma wani yana rashin lafiya, nan-da-nan dattawa sukan shirya yadda za su taimaka musu. Ban da haka ma, suna yin amfani da Littafi Mai Tsarki don su ƙarfafa mu kuma su ja-gorance mu. Idan ꞌyanꞌuwa suka lura cewa wani dattijo yana da sauƙin kai da tausayi, kuma yakan saurari mutum, za su yi sauri neman taimakonsa. Idan dattijo yana da irin halayen nan, ꞌyanꞌuwa za su ga cewa ya damu da su, kuma ba zai yi musu wuya su bi shawarar da ya ba su daga Littafi Mai Tsarki ba.—1 Tas. 2:7, 8, 11.

Idan ꞌyanꞌuwa suna cikin matsala, dattawa sukan ƙarfafa su (Ka duba sakin layi na 13) a


14. Ta yaya za mu sa ꞌyanꞌuwa su dogara da mu?

14 Ka zama wanda za a iya dogara da shi. Muna so mutane su san cewa za mu iya taimaka musu idan suna cikin matsala. (K. Mag. 17:17) Mene ne za mu yi don ꞌyanꞌuwa su iya dogara da mu? Mu yi iya ƙoƙarinmu mu bi halin Jehobah kowace rana. Alal misali, idan muka yi alkawari, mu cika shi, kuma mu riƙa yin abubuwa a kan lokaci. (Mat. 5:37) Idan mun lura cewa wani yana bukatar taimako, mu taimaka masa. Ƙari ga haka, idan aka ba mu aiki, mu tabbata cewa mun yi shi daidai yadda aka ce.

15. Idan dattawa suka nuna cewa za a iya dogara da su, ta yaya kowa zai amfana?

15 Idan dattawa sun nuna cewa za a iya dogara da su, kowa a ikilisiya zai iya amfana. Ta yaya? Idan ꞌyanꞌuwa sun san cewa za su iya kiran dattawa a lokacin da suke da bukata, hakan zai sa su rage damuwa. Kuma idan suka ga cewa dattawa suna marmarin taimaka musu, hakan zai tabbatar musu cewa dattawan suna ƙaunar su. Ban da haka ma, idan Littafi Mai Tsarki da littattafanmu ne dattawa suke amfani da su su ba da shawara, ba raꞌayinsu ba, ꞌyanꞌuwa za su yarda da su. Ƙari ga haka, idan dattijo yana riƙe sirri kuma yana cika alkawarinsa, ꞌyanꞌuwa za su dogara da shi.

16. Idan muna yin abin da Jehobah yake so a kullum, ta yaya hakan zai amfane mu da ꞌyanꞌuwanmu?

16 A kullum, ka riƙa yin abin da Jehobah yake so. Idan muna yi ma Jehobah biyayya a duk abubuwan da muke yi kuma muna yanke shawarwari bisa ga Kalmarsa, za mu zama misali mai kyau ga ꞌyanꞌuwanmu. Idan muna nazarin Littafi Mai Tsarki kuma muna yin abubuwan da za su ƙara mana bangaskiya, hakan zai sa mu riƙe amincinmu kuma mu ci-gaba da bin ƙaꞌidodin Jehobah. Ban da haka ma, za mu yi saurin gane koyarwar ƙarya, da raꞌayoyi da ba su jitu da ƙaꞌidodin Jehobah ba, kuma ba za mu bari su shafi tunaninmu ba. (Afis. 4:14; Yak. 1:6-8) Idan muna dogara ga Jehobah da alkawuransa, hankalinmu ba zai tashi sosai ba ko da mun ji mugun labari. (Zab. 112:7, 8) Kuma idan ꞌyanꞌuwanmu suna cikin matsala, za mu iya taimaka musu.—1 Tas. 3:2, 3.

17. Mene ne dattawa za su iya yi don su kwantar ma ꞌyanꞌuwa hankali, kuma su sa su dogara ga Allah?

17 Ya kamata dattawa su zama masu hankali, masu kamun kai, masu natsuwa, da masu tawaliꞌu. Dattawa suna taimaka ma ꞌyanꞌuwa su sami kwanciyar hankali kuma su ƙara dogara ga Jehobah, domin suna “riƙe da tabbatacciyar maganar nan ta Allah daidai.” (Tit. 1:9; 1 Tim. 3:1-3) Ƙari ga haka, ta yadda suke kafa misali mai kyau da ziyarar ƙarfafa da suke kai ma ꞌyanꞌuwa, suna taimaka ma ꞌyanꞌuwa su riƙa zuwa taro a-kai-a-kai, su riƙa fita waꞌazi kuma su riƙa yin nazarin Littafi Mai Tsarki. Kuma idan ꞌyanꞌuwa suka shiga yanayi mai wuya, dattawa sukan ƙarfafa su su dogara ga Jehobah da alkawuran da ya yi mana.

18. Me ya sa muke so mu yabi Jehobah kuma mu ci-gaba da yin kusa da shi? (Ka kuma duba akwatin nan “ Abin da Za Ka Yi don Ka Ƙara Kusantar Jehobah.”)

18 Yanzu da muka tattauna halayen Jehobah masu burgewa, kamar Sarki Dauda, mu ma za mu iya yabon Jehobah kuma mu ce: “Albarka ta tabbata ga Yahweh, dutsen ɓuyana.” (Zab. 144:1) Jehobah Allah ne da za mu iya dogara gare shi har abada. Har iya rayuwarmu, kowannenmu zai iya cewa: “Dutsen ɓuyana ne shi,” domin muna da tabbaci cewa a kullum zai taimaka mana mu ci-gaba da bauta masa.—Zab. 92:14, 15.

WAƘA TA 150 Mu Bi Allah Don Mu Sami Ceto

a BAYANI A KAN HOTUNA: A Majamiꞌar Mulki, wata ꞌyarꞌuwa ta saki jiki tana gaya ma dattawa biyu damuwarta.