Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
Mene ne Zabura 12:7 take nufi?
Idan muka dubi Zabura ta 12 gabaki-ɗayanta, za mu ga cewa aya 7 tana magana game da mutane ne.
A Zabura 12:1-4 Dauda ya bayyana cewa “masu faɗin gaskiya sun ɓace daga cikin ꞌyan Adam.” Saꞌan nan a ayoyi 5-7 ya ce:
“Yahweh ya ce, ‘Tsanantawar matalauta, na gani,
nishi mai zafi na masu bukata, na ji.
To, yanzu zan tashi
zan kiyaye su bisa ga bukatarsu!’
Maganar Yahweh zallar gaskiya ce,
Maganarsa kamar zallar azurfa ce, azurfar da aka tace da wuta har sau bakwai.
Ya Yahweh, bari ka kiyaye mu,
daga waɗannan mugaye ka tsare mu, ka tsare mu har abada.”
Aya ta 5 tana magana a kan abin da Allah zai yi wa “matalauta” da ake tsananta musu ne. Ta ce Allah zai cece su.
Aya ta 6 kuma ta ƙara da cewa, “Maganar Yahweh zallar gaskiya ce, Maganarsa kamar zallar azurfa ce.” Kuma dukanmu mun yarda da hakan.—Zab. 18:30; 119:140.
Amma wasu juyin Littafi Mai Tsarki sun fassara Zabura 12:7 da cewa, “Ka tsare su.”
Da yake an ambaci “Maganar Yahweh” a aya ta 6, wasu sun ɗauka cewa maganar Allah ce aya 7 ta ce za a “tsare.” Kuma mun san cewa duk da ƙoƙarin da maƙiyan Allah suka yi don su ga cewa an kawar da Littafi Mai Tsarki, Allah ya tsare shi.—Isha. 40:8; 1 Bit. 1:25.
Amma kuma, Jehobah yana tsare waɗanda aka ambata a aya ta 5, wato waɗanda ake tsananta musu, kuma zai cece su.—Ayu. 36:15; Zab. 6:4; 31:1, 2; 54:7; 145:20.
Yanzu tambayar ita ce, mene ne aya 7 take nufi? Mutane ne Jehobah zai tsare ko maganarsa?
Idan muka bincika Zabura 12 sosai, za mu ga cewa ana magana ne game da mutane.
A Zabura 12:1, 2 Dauda ya yi zancen mutanen kirki da ake yi musu ƙarya. Saꞌan nan aya ta 3 ta ce Allah ya hukunta maƙaryata. Abin da aka rubuta a Zabura sura 12 ya tabbatar mana da cewa Jehobah zai taimaka wa mutanensa, domin maganarsa zallar gaskiya ce.
Don haka, waɗanda aya 7 ta ce za a kiyaye “su,” mutane ne wato waɗanda mugaye suke tsananta musu.
To me ya sa wasu juyin Littafi Mai Tsarki suka ce, “ka tsare su” a aya ta 7? Domin haka yake a ainihin Nassosin Ibrananci da aka kofa. Amma, a wanda aka fassara zuwa Hellenanci tun zamanin dā (Greek Septuagint), abin da aka ce shi ne, “Zai kiyaye mu” da kuma, “Zai tsare mu.” Wannan ya nuna cewa bayin Allah da ake tsananta musu ne ake magana a kai. Za a tsare su daga hannun mugaye. (Zab. 12:7, 8) Ƙari ga haka, a Nassosin Ibrananci da aka fassara zuwa yaren Aramaic, Aya 7 ta ce: “Kai, ya Ubangiji, za ka tsare masu adalci, za ka kiyaye su daga wannan muguwar tsara har abada.” Hakan ya ba mu ƙarin tabbaci cewa mutane ne ake nufi a Zabura 12:7 ba maganar Allah ba.
Shi ya sa wannan ayar tana sa bayin Allah su kasance da bege cewa zai taimake su.