Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Shin ya kamata Shaidun Jehobah su yi amfani da shafuffukan sada zumunta na neman aure ne?

Jehobah yana so mutane biyu da suka yi aure su zauna lafiya kuma su riƙa ƙaunar juna har abada. (Mat. 19:4-6) Idan kana so ka yi aure, ta yaya za ka sami abokiyar aure tagari? Jehobah ne Mahaliccinmu kuma ya san abin da muke bukatar mu yi don mu sami zaman lafiya a aurenmu. Saboda haka, idan ka bi ƙa’idodinsa, za ka yi farin ciki. Ga wasu daga cikin ƙa’idodin.

Na farko, muna bukatar mu fahimci cewa “zuciyar mutum ta fi kome ruɗu, cike take kuma da mugunta ƙwarai.” (Irm. 17:9) Sa’ad da mutum ya sami wadda yake so ya aura, sukan so juna sosai. Idan ba su mai da hankali ba, yadda suke son juna zai iya sa su kasa yanke shawarar da ta dace. Idan saurayi da budurwa sun yi aure domin abin da zuciyarsu ta gaya musu kawai, za su iya yin baƙin ciki daga baya. (K. Mag. 28:26) Shi ya sa ba zai dace saurayi da budurwa su yi wa juna alkawarin aure tun ba su san halin juna da kyau ba.

Littafin Karin Magana 22:3 ta ce: “Mai hankali yakan ga hatsari, ya kauce, amma marar tunani yakan sa kai, ya sha wahala.” Wane haɗari ne yake tattare da yin amfani da dandalin sada zumunta don neman aure? Abin baƙin ciki shi ne, wasu sun haɗu da wanda ba su taɓa sani ba a dandalin sada zumunta kuma suka soma soyayya. Amma daga baya sun gano cewa mutumin yana ruɗin su ne kawai. Ban da haka, wasu suna buɗe shafuffuka a dandalin sada zumunta musamman don su damfari mutane. A wasu lokuta, ’yan damfarar sukan ce su Shaidun Jehobah ne.

Ga wani haɗari kuma da ke tattare da neman abokin aure ta dandalin sada zumunta. Wasu shafuffukan sada zumunta sukan yi amfani da wata fasaha don su haɗa saurayi da budurwa da suke ganin sun dace da juna. Amma babu tabbaci cewa wannan fasahar tana aiki. Wauta ce mutum ya dogara ga fasahar da ’yan Adam suka ƙera, yayin da yake so ya ɗauki mataki mai muhimmanci kamar yin aure. Babu wata fasaha da za ta kai ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki amfani.​—K. Mag. 1:7; 3:5-7.

Littafin Karin Magana 14:15 ta ce: “Marar tunani yakan gaskata kome, amma mai hankali yakan yi tunani kafin ya fara wani abu.” Kafin mutum ya yanke shawarar yin aure, yana bukatar ya san wadda zai aura da kyau. Amma zai yi wuya mutum ya yi hakan idan ta dandalin sada zumunta ne suka haɗu. Ko da kuna ganin bayanai game da juna ko kuma kuna aika wa juna saƙo a kai a kai, ba za ku iya sanin junanku da kyau ba. Wasu da suke ganin sun sami rabin ransu sun yi baƙin ciki sosai bayan da suka haɗu da mutumin ido da ido.

Wani marubucin zabura ya ce: “Ba na sha’ani da mutanen banza, ba ruwana da munafukai.” (Zab. 26:4) Mutane da yawa suna ganin ba laifi ba ne su yi ƙarya a shafuffukansu na sada zumunta domin mutane su so su. Suna iya ɓoye ainihin halinsu sa’ad da suke dandalin sada zumunta. Zai dace mu yi tunani a kan amsoshin tambayoyin nan: Ko da mutum ya ce shi Mashaidin Jehobah ne, shin shi Mashaidi ne da ya yi baftisma? Yana da dangantaka mai kyau da Jehobah? Yana da suna mai kyau a ikilisiya? Shin yana taka dokokin Jehobah? Shi abokin banza ne? (1 Kor. 15:33; 2 Tim. 2:20, 21) Shin yana da izinin yin aure bisa ga ƙa’idar Littafi Mai Tsarki? Kana bukatar ka san amsoshin tambayoyin nan, amma idan ba ka nemi taimako daga ’yan’uwan da suka san mutumin ba, zai yi maka wuya ka san shi da kyau. (K. Mag. 15:22) Bawan Jehobah ba zai ma yi tunanin auran wanda da ba ya bauta wa Jehobah ba.​—2 Kor. 6:14; 1 Kor. 7:39.

Saboda haɗarin da ke tattare da neman abokiyar aure ta shafuffukan sada zumunta, akwai hanyoyi mafi kyau da mutum zai iya samun aboki ko abokiyar aure tagari. Ta yaya za ka iya haɗuwa da mace tagari da za ka aura? A duk lokacin da bayin Jehobah suka taru kamar a Majami’ar Mulki ko taron da’ira ko taron yanki da dai sauransu, za su iya haɗuwa da waɗanda za su iya aura kuma su ɗan gane halin juna.

Yayin da kuke cuɗanya da juna, za ku san ko maƙasudanku da halayenku sun jitu

Idan ba zai yiwu a taru saboda wani yanayi ba, alal misali domin annobar korona, muna yin taro ta na’ura, kuma Shaidun Jehobah da ba su yi aure ba za su iya haɗuwa da juna. Za ka ga yadda suke ayyuka a taro da kuma yadda suke kalami. (1 Tim. 6:11, 12) Ƙari ga haka, za ku iya yin hira tare da sauran ’yan’uwa bayan taro a ɗakin hira na kwamfuta (breakout room). Ta yin cuɗanya ta na’ura tare da ’yan’uwanka, za ka iya ganin yadda mutumin yake sha’ani da wasu, kuma ka gane ainihin halin mutumin. (1 Bit. 3:4) Da shigewar lokaci, za ku san juna sosai kuma za ku iya gane ko maƙasudanku da halayenku sun jitu.

Idan marasa aure sun bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki yayin da suke neman abokin aure, za su iya jin daɗin aurensu. Yanayinsu zai yi daidai da abin da Karin Magana 18:22 ta faɗa, cewa: “Mai samun mata [ko miji nagari], ya sami abu mai kyau, alamar samun farin jini daga wurin Yahweh ne.”