Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 26

Ka Taimaka wa Mutane Su Zama Almajiran Yesu

Ka Taimaka wa Mutane Su Zama Almajiran Yesu

“Allah . . . shi ne yake sa ku yi niyya ku kuma yi aiki bisa ga kyakkyawan nufinsa.”​—FILIB. 2:13.

WAƘA TA 64 Mu Riƙa Yin Wa’azi da Farin Ciki

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Mene ne Jehobah ya yi maka?

ME YA taimaka maka ka zama Mashaidin Jehobah? Da farko, ka ji “shelar labarin nan mai daɗi,” mai yiwuwa daga wurin iyayenka ko abokin aikinka ko abokin makarantarka ko kuma sa’ad da Shaidun Jehobah suke wa’azi gida-gida. (Mar. 13:10) Sai wani Mashaidi ya ɗauki lokaci sosai ya yi nazari da kai. Yayin da ake nazari da kai, ka gano cewa Jehobah yana ƙaunar ka kuma kai ma ka ƙaunace shi. Jehobah ya kawo ka cikin gaskiya kuma yanzu da ka zama almajirin Yesu Kristi, kana da begen yin rayuwa har abada. (Yoh. 6:44) Hakika, kana godiya ga Jehobah da ya tura wani bawansa ya koya maka gaskiya kuma Jehobah ya amince da kai a matsayin bawansa.

2. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

2 Yanzu da muka san gaskiya, muna da damar taimaka wa mutane su ma su soma bauta ma Jehobah. Yana iya mana sauƙi mu yi wa mutane wa’azi, amma zai iya mana wuya mu tambaye mutane ko za su so mu yi nazari da su, ko kuma zai iya mana wuya mu gudanar da nazarin. Yadda kake ji ke nan? Idan haka ne, shawarwarin da ke wannan talifin za su iya taimaka maka. Za mu tattauna abin da yake sa mu koyar da mutane don su zama almajiran Yesu. Ƙari ga haka, za mu tattauna yadda za mu shawo kan matsalolin da za su iya hana mu yin nazari da mutane. Da farko, bari mu tattauna dalilin da ya sa muke bukatar mu yi wa mutane wa’azi da kuma koyar da su.

YESU YA UMURCE MU MU YI WA’AZI KUMA MU KOYAR DA MUTANE

3. Me ya sa muke yin wa’azi?

3 A lokacin da Yesu yake duniya, ya umurci mabiyansa su yi wani aiki da ke da sassa biyu. Da farko, ya gaya musu cewa su yi wa’azin bisharar Mulkin Allah, kuma ya gaya musu yadda za su yi hakan. (Mat. 10:7; Luk. 8:1) Alal misali, Yesu ya gaya wa almajiransa abin da za su yi idan mutane suka saurare su, da kuma abin da za su yi idan mutane ba su saurare su ba. (Luk. 9:2-5) Sa’ad da Yesu ya ce mabiyansa za su yi wa’azi “domin shaida ga dukan al’umma,” yana yin annabci ne cewa mabiyansa za su yi wa’azi ga mutane da yawa, a wurare da yawa. (Mat. 24:14; A. M. 1:8) Yesu ya umurci mabiyansa su yi wa mutane wa’azi game da Mulkin Allah kuma su gaya musu abin da Mulkin zai yi, ko da mutanen sun saurare su ko a’a.

4. Kamar yadda Matiyu 28:18-20 suka nuna, me muke bukatar mu yi ban da yin wa’azin Mulkin Allah?

4 Mene ne abu na biyu da Yesu ya umurci mabiyansa su yi? Ya gaya wa mabiyansa su koya wa mutane su bi umurninsa. Wasu za su iya cewa wannan umurnin ya shafi Kiristoci na farko ne kawai, amma hakan gaskiya ne? A’a, domin Yesu ya ce za a yi wannan aiki mai muhimmanci “har ƙarshen zamani.” (Karanta Matiyu 28:18-20.) Da alama Yesu ya ba da wannan umurnin ga almajiransa ne a lokacin da ya haɗu da fiye da 500 daga cikin su. (1 Kor. 15:6) Kuma a cikin wahayin da Yesu ya ba Yohanna, Yesu ya nuna cewa yana so dukan almajiransa su koya wa mutane game da Jehobah.​—R. Yar. 22:17.

5. Bisa ga abin da ke 1 Korintiyawa 3:6-9, da me Bulus ya kwatanta yin wa’azi da kuma koyarwa?

5 Manzo Bulus ya kwatanta aikin almajirtarwa da yin noma don ya nuna cewa ba shuka iri ne kaɗai muke bukatar mu yi ba. Ya tuna wa Kiristocin da suke Korinti cewa: “Ni na shuka, Afollos ya yi ban ruwa, . . . ku kuwa gona ce ta Allah.” (Karanta 1 Korintiyawa 3:6-9.) Mu ma’aikata ne a ‘gonar Allah.’ Don haka, a duk lokacin da muka yi wa’azi, kamar mun yi shuki ne, idan muka koyar da mutane kuma, kamar mun yi ban ruwa ne. (Yoh. 4:35) Amma mun san cewa Allah ne yake sa shukin ya yi girma, wato shi yake jawo mutane gare shi.

6. Me muke bukatar mu taimaka wa ɗalibanmu su yi?

6 Muna neman waɗanda “suke da zuciya ta samun rai na har abada.” (A. M. 13:48, New World Translation) Kafin mu taimaka wa irin mutanen nan su zama almajiran Yesu, wajibi ne mu taimaka musu (1) su fahimta, (2) su amince, kuma (3) su bi abubuwan da suke koya daga Littafi Mai Tsarki. (Yoh. 17:3; Kol. 2:6, 7; 1 Tas. 2:13) Kowa a ikilisiya zai iya taimaka wa ɗalibai ta wajen marabtar su da kuma nuna musu ƙauna a duk lokacin da suka halarci taro. (Yoh. 13:35) Wanda yake nazari da ɗalibi ma yana bukatar ya yi amfani da lokacinsa da kuzarinsa ya taimaka wa ɗalibin ya yi watsi da imani ko kuma halaye marasa kyau da ya shaƙu da su. (2 Kor. 10:4, 5) Zai iya ɗaukan watanni kafin ka taimaka wa mutum ya yi canje-canjen nan kuma ya cancanci yin baftisma. Amma ƙoƙarin da muka yi ba zai bi ruwa ba.

ƘAUNA CE TAKE SA MU ALMAJIRTAR DA MUTANE

7. Me ya sa muke yi wa mutane wa’azi da kuma koyar da su?

7 Me ya sa muke wa’azi da kuma koyar da mutane su zama mabiyan Yesu? Dalili na farko shi ne, muna ƙaunar Jehobah. Idan ka yi iya ƙoƙarinka don ka bi umurnin Yesu game da yin wa’azi da kuma koyar da mutane, za ka nuna cewa kana ƙaunar Allah. (1 Yoh. 5:3) Babu shakka, yadda kake ƙaunar Allah ne ya sa kake yin wa’azi. Shin yi wa mutane wa’azi yana yi maka sauƙi? Wataƙila ba ya yi maka sauƙi. Ka ji tsoro a ranar da ka fara yin wa’azi? Babu shakka! Amma ka san cewa aikin da Yesu yake so ka yi ke nan, don haka, ka bi umurninsa. Mai yiwuwa da shigewar lokaci yin wa’azi ya soma yi maka sauƙi. Amma ya kake ji idan ya zo ga batun yin nazari da mutane? Kana jin tsoro a duk lokacin da ka yi tunanin yin hakan? Wataƙila. Amma idan ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka daina jin tsoro kuma ka tambaye mutane ko za su so ka yi nazari da su, Jehobah zai ba ka ƙarfin zuciya na yin hakan.

8. Kamar yadda Markus 6:34 ta nuna, mene ne kuma zai iya taimaka mana mu koyar da mutane?

8 Na biyu, muna yin wa’azi don muna ƙaunar mutane. Akwai lokacin da Yesu da almajiransa sun gaji sosai bayan da suka gama yin wa’azi. Suka je wani wuri domin su huta, amma taron jama’a suka bi su. Tausayi ya sa Yesu ya soma koya wa mutanen “abubuwa da yawa.” (Karanta Markus 6:34.) Ya yi aiki tuƙuru duk da cewa ya gaji. Me ya sa? Yesu ya fahimci yanayin mutanen. Ya taimaka musu don ya ga yadda suke shan wahala kuma ya san cewa suna bukatar bege. Ko da yake a yau mutane da yawa suna yi kamar suna farin ciki, gaskiyar ita ce suna fama da matsaloli da yawa kuma suna bukatar bege. Suna kama da tumakin da suka ɓace kuma ba su da makiyayi. Manzo Bulus ya ce irin mutanen nan ba su da bege kuma ba su san Allah ba. (Afis. 2:12) Suna “ƙofar zuwa halaka.” (Mat. 7:13) Idan muka yi tunanin yadda mutane a yankinmu suke bukatar su sani game da Allah, ƙauna da tausayi za su sa mu taimaka musu. Kuma hanya mafi kyau da za mu iya taimaka musu ita ce yin nazarin Littafi Mai Tsarki da su.

9. Kamar yadda Filibiyawa 2:13 ta nuna, ta yaya Jehobah zai iya taimaka maka?

9 Mai yiwuwa kana jinkirin soma nazari da mutane domin ka san cewa yin shiri da kuma nazari da mutane zai ɗauki lokacinka sosai. Idan haka ne, ka gaya wa Jehobah yadda kake ji. Ka roƙe shi ya ba ka niyyar neman waɗanda za su yarda ka yi nazari da su. (Karanta Filibiyawa 2:13.) Manzo Yohanna ya tabbatar mana cewa Allah zai amsa addu’o’in da suka jitu da nufinsa. (1 Yoh. 5:14, 15) Don haka, ka tabbata cewa Jehobah zai taimaka maka ka kasance da niyyar neman waɗanda za su yarda ka yi nazari da su.

YADDA ZA MU MAGANCE WASU MATSALOLI

10-11. Me zai iya sa mu jinkirin soma yin nazari da mutane?

10 Mun san cewa yana da muhimmanci mu koyar da mutane, amma zai iya yi mana wuya mu yi koyarwa yadda muke so. Bari mu ga wasu daga cikin matsalolin nan, da yadda za mu magance su.

11 Wataƙila ba ma iya yin wa’azi yadda muke so. Alal misali, wasu masu shela suna rashin lafiya ko sun tsufa. Shin, abin da yake faruwa da kai ke nan? Idan haka ne, ka yi tunanin ɗaya daga cikin darussan da annobar korona ta koya mana. Mun gano cewa za mu iya yin amfani da na’ura mu yi nazari da ɗalibanmu. Don haka, za ka iya soma yin nazari da mutum daga gidanka, kuma hakan zai iya fi maka sauƙi. Wani abu kuma shi ne, wasu za su so mu yi nazari da su, amma ba sa samun zarafi a lokacin da muke wa’azi. Wataƙila da sassafe ko kuma da dare ne suke samun zarafi. Za ka iya yin nazari da mutane a wannan lokacin? Da dare ne Yesu ya koyar da Nikodimus don lokacin ne Nikodimus ya fi so.​—Yoh. 3:1, 2.

12. Waɗanne abubuwa ne suka tabbatar mana cewa za mu iya koyar da mutane?

12 Za mu iya ɗauka cewa ba za mu iya yin nazari da mutane ba. Mai yiwuwa muna ganin sai muna da ilimi ko ƙwarewa sosai kafin mu iya yin nazari da mutane. Idan haka ne kake ji, ga abubuwa uku da za su tabbatar maka cewa za ka iya yin nazari da mutane. Na farko, Jehobah ya san cewa za ka iya koyar da mutane. (2 Kor. 3:5) Na biyu, Yesu, wanda aka ba shi “dukan iko a sama da kuma nan duniya,” ya umurce ka ka koyar da mutane, hakan ya nuna cewa ya san za ka iya yin aikin. (Mat. 28:18) Na uku, Jehobah da kuma ’yan’uwanka za su iya taimaka maka. Yesu ya yi koyarwa bisa ga abin da Ubansa ya koya masa, kuma kai ma za ka iya yin haka. (Yoh. 8:28; 12:49) Ƙari ga haka, za ka iya gaya wa mai kula da rukuninku na wa’azi ko wani majagaba da ya ƙware ko kuma mai shela da ya manyanta ya koya maka yadda za ka soma nazari da mutane. Wata hanya da za ka iya samun ƙarfin gwiwa ita ce ta wurin bin ɗaya daga cikinsu yin nazari da ɗalibansu.

13. Me ya sa zai yi kyau mu kasance a shirye mu canja yadda muke nazari da mutane?

13 Zai iya mana wuya mu koyi sabbin hanyoyi ko kuma abubuwan da muke wa’azi da su. Yadda muke gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki yanzu ya canja. Muna bukatar mu yi shiri sosai kafin mu yi amfani da littafin nan, Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! wajen yin nazari da mutane, kuma muna bukatar mu gudanar da nazarin a hanyar da ta bambanta da na dā. Mun daina karanta sakin layi da yawa, amma muna mai da hankali ga tattaunawa da ɗalibi. Mun fi amfani da bidiyoyi da kuma abubuwa kamar manhajar JW Library® yayin da muke koyarwa. Idan ba ka iya amfani da waɗannan abubuwan ba, ka gaya ma wani ya koya maka. A matsayinmu na ’yan Adam, yana mana wuya mu canja yadda muka saba yin abubuwa. Amma da taimakon Jehobah da kuma ’yan’uwanmu, zai yi mana sauƙi mu yi canji har ma mu ji daɗin yin nazari da mutane. Wani ɗan’uwa ya ce “ɗalibi da malaminsa za su ji daɗin wannan hanyar yin nazari sosai.”

14. Me muke bukatar mu tuna idan mutane a yankinmu ba sa saurarar mu, kuma ta yaya 1 Korintiyawa 3:6, 7 suka ƙarfafa mu?

14 Mai yiwuwa saboda wurin da muke zama, yana mana wuya mu soma nazari da mutane. Wataƙila mutane ba sa so su saurari wa’azin da muke yi ko kuma suna hamayya da mu. Me zai taimaka mana mu kasance da tabbaci cewa daga baya irin mutanen nan za su iya saurarar wa’azinmu? Yanayin mutane yana iya canjawa da sauri a wannan duniyar da ke cike da matsaloli, kuma waɗanda ba sa saurarar wa’azinmu a dā za su iya soma yin hakan. (Mat. 5:3) Wasu da a dā ba sa karɓan littattafanmu sun amince a yi nazari da su daga baya. Mun kuma san cewa Jehobah shi ne Ubangijin girbin. (Mat. 9:38) Yana so mu ci gaba da yin shuki da kuma ban ruwa, amma shi ne zai sa irin ya yi girma. (1 Kor. 3:6, 7) Sanin cewa Jehobah zai yi mana albarka don ƙoƙarin da muka yi ne, ba don sakamakon da muka samu ba, yana da ban ƙarfafa! *

KA JI DAƊIN ALMAJIRTARWA

Yadda yin wa’azi da kuma koyarwa suke taimaka wa mutane (Ka duba sakin layi na 15-17) *

15. Yaya Jehobah yake ji a duk lokacin da mutum ya yarda a yi nazari da shi, kuma ya yi abin da yake koya?

15 Jehobah yana farin ciki a duk lokacin da wani ya karɓi gaskiya kuma shi ma ya soma koyar da mutane. (K. Mag. 23:15, 16) Jehobah yana farin ciki sosai yayin da yake ganin bayinsa suna wa’azi da ƙwazo a yau! Alal misali, duk da annobar da ta ɓarke a shekarar hidima ta 2020, Shaidun Jehobah sun yi nazari da mutane 7,705,765, sun taimaka wa mutane 241,994 su yi baftisma kuma su soma bauta wa Jehobah. Waɗannan sabbin almajiran ma za su yi nazari da wasu kuma su taimaka musu su soma bauta wa Jehobah. (Luk. 6:40) Za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah yana farin ciki a duk lokacin da muka koyar da mutane don su zama mabiyansa.

16. Wane maƙasudi mai kyau ne za ka iya kafawa?

16 Koyar da mutane su soma bauta wa Jehobah yana da wuya, amma da taimakon Jehobah, za mu iya koyar da sabbi su soma ƙaunar Ubanmu na sama. Shin za ka iya kafa maƙasudin soma nazari da wani? Za ka iya yin mamakin abin da zai faru idan kana tambayar duk wanda ka haɗu da shi ko zai yarda ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Ka tabbata cewa Jehobah zai albarkace ka don ƙoƙarin da kake yi.

17. Yaya yin nazari da mutane zai sa mu ji?

17 Yin wa’azi da kuma koyar da gaskiya ga mutane babban gata ne! Wannan aikin yana sa mu farin ciki sosai. Manzo Bulus, wanda ya taimaka wa mutane da yawa a Tasalonika su zama mabiyan Yesu ya ce: “Mene ne abin sa zuciyarmu, da abin farin cikinmu, da kuma hular ladan taƙamarmu a gaban Ubangiji Yesu a ranar dawowarsa, in ba ku ba? Ai, ku ne abin taƙamarmu, da abin farin cikinmu.” (1 Tas. 2:19, 20; A. M. 17:1-4) Yadda bayin Jehobah da yawa a yau suke ji ke nan. Wata ’yar’uwa mai suna Stéphanie, wadda ita da mijinta sun taimaka wa mutane da yawa su yi baftisma ta ce: “Babu abin da ya fi sa farin ciki kamar taimaka wa mutane su soma bauta wa Jehobah.”

WAƘA TA 57 Ku Yi wa Dukan Mutane Wa’azi

^ sakin layi na 5 Jehobah ya ba mu gatan yin wa’azi da kuma koya wa mutane su yi dukan abubuwan da Yesu ya ce su yi. Mene ne yake motsa mu mu koyar da mutane? Waɗanne matsaloli ne za mu iya fuskanta yayin da muke yi wa mutane wa’azi da kuma koyar da su su zama almajiran Yesu? Kuma ta yaya za mu shawo kan matsalolin nan? A wannan talifin, za mu tattauna waɗannan tambayoyin.

^ sakin layi na 14 Don samun ƙarin bayani a kan yadda kowa a cikin ikilisiya zai iya taimakawa, ka duba talifin nan, “Yadda Kowa a Ikilisiya Zai Taimaki Ɗalibi Ya Yi Baftisma” da aka wallafa a Hasumiyar Tsaro ta Maris 2021.

^ sakin layi na 53 BAYANI A KAN HOTUNA: Ga wasu canje-canje da mutum zai iya yi a rayuwarsa domin ana yin nazari da shi: Wani mutum yana ganin rayuwarsa ba ta da amfani kuma bai san Jehobah ba. Sai Shaidun Jehobah suka yi masa wa’azi kuma ya yarda su yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Abin da aka koya masa ya sa shi ya yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma ya yi baftisma. Daga baya shi ma ya soma taimaka wa mutane su zama almajiran Yesu. A ƙarshe, dukansu suna jin daɗin rayuwa a Aljanna.