Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shawarwarin Littafi Mai Tsarki Za Su Taimaka

Shawarwarin Littafi Mai Tsarki Za Su Taimaka

Abin da ke Littafi Mai Tsarki ya taimaka wa miliyoyin mutane a fannonin rayuwa guda huɗu da za a tattauna yanzu.

1. Aure

Mutane suna da raꞌayoyi dabam-dabam game da aure da kuma abin da za a iya yi don a sami zaman lafiya a iyali.

LITTAFI MAI TSARKI YA CE: “Bari kowane ɗayanku ya ƙaunaci matarsa kamar kansa, ita matar kuwa ta girmama mijinta.”—Afisawa 5:33.

MAꞌANA: Allah ne tushen aure, don haka, ya san abin da zai sa maꞌaurata farin ciki. (Markus 10:​6-9) Idan mata da miji sun damu da juna, hakan zai sa su farin ciki. Mijin da yake ƙaunar matarsa zai kula da ita kuma ba zai wulaƙanta ta. Kuma matar da take daraja mijinta za ta yi hakan ta wajen yadda take masa magana da kuma taimaka masa.

LITTAFI MAI TSARKI YANA TAIMAKAWA: Quang da Thi, mata da miji ne daga ƙasar Vietnam, ba su ji daɗin aurensu ba sam. Quang ba ya yawan damuwa da matarsa. Ya ce: “Ban damu da yadda Thi take ji ba kuma ina yawan wulaƙanta ta.” Thi ta so su kashe auren. Ta ce: “Na ga cewa ba zan iya amince da mijina ko in girmama shi ba.”

Daga baya, Quang da Thi sun koyi abin da ke Littafi Mai Tsarki da kuma yadda za su bi abin da ke Afisawa 5:33 a aurensu. Quang ya ce: “Ayar ta taimaka min in zama mai alheri. Ƙari ga haka, ina ƙaunar matata da kuma kula da ita da kyau yanzu. Idan na yi hakan tana daraja ni da kuma nuna min ƙauna.” Thi ta ce, “Idan ina bin abin da ke Afisawa 5:33 kuma ina daraja mijina, hakan yana sa shi ya daɗa ƙaunata, ya kāre ni kuma in sami kwanciyar hankali.”

Don samun ƙarin bayani game da aure, ka karanta Awake! Na 2 2018, mai jigo “12 Secrets of Successful Families” a dandalin jw.org.

2. Yadda Za Ka Yi Maꞌamala da Mutane

Mutane suna yawan wulaƙanta wasu don launin fatarsu ko ƙasarsu ko yadda suke ko addininsu ko kuma raꞌayinsu game da jimaꞌi.

LITTAFI MAI TSARKI YA CE: “Ku ba da girma ga kowa.”—1 Bitrus 2:17.

MAꞌANA: Littafi Mai Tsarki bai ce mu tsane mutanen da launin fatarsu ba ɗaya ba ne da namu, ko waɗanda suka fito daga wata ƙasa ko ꞌyan luwaɗi ba. Maimakon haka, ya ce mu riƙa daraja dukan mutane ko da launin fatarmu ba ɗaya ba ne ko sun fito daga wata ƙasa ko su talakawa ne ko masu arziki. (Ayyukan Manzanni 10:34) Ko da ba ma son abin da wasu suka yi imani da shi, ko yadda suke yin abubuwa, hakan ba zai hana mu daraja su ko nuna musu alheri ba.—Matiyu 7:12.

LITTAFI MAI TSARKI YANA TAIMAKAWA: An gaya wa wani mai suna Daniel cewa mutane daga Asiya matsala ce ga ƙasarsu. Hakan ya sa ya tsane duk wanda ya fito daga Asiya kuma yana yawan zagin su a gaban mutane. Daniel ya ce: “Na ɗauka yin hakan yana nuna cewa ina kishin ƙasarmu ne. Ban taɓa tunani cewa abin da nake yi ba daidai ba ne.”

Daga baya, Daniel ya koyi abin da ke Littafi Mai Tsarki. Daniel ya ce: “Na canja tunanina gabaki ɗaya. Ina ganin mutane yadda Allah yake ganinsu, kuma na san cewa dukanmu ɗaya ne ko da daga ina muka fito.” Daniel ya faɗi yadda yake ji yanzu idan ya haɗu da mutane. Ya ce: “Ba na damuwa da inda suka fito. Yanzu ina ƙaunar mutane ko daga ina ne suka fito, kuma ina da abokai da suka fito daga wurare dabam-dabam a faɗin duniya.”

Don samun ƙarin bayani, ka karanta Awake! Na 3 2020, mai jigo “Is There a Cure for Prejudice?” a dandalin jw.org.

3. Kuɗi

Mutane da yawa suna ƙoƙari su zama masu arziki don su yi farin ciki kuma su ji daɗin rayuwa a nan gaba.

LITTAFI MAI TSARKI YA CE: “Hikima takan tsare mutum kamar yadda kuɗi yakan yi. Hikima takan kiyaye ran mai ita, wannan ita ce amfanin sani.”—Mai-Wa’azi 7:12.

MAꞌANA: Muna bukatar kuɗi, amma ba shi ne zai sa mu farin ciki ko mu ji daɗin rayuwa a nan gaba ba. (Karin Magana 18:11; 23:​4, 5) A maimakon haka, za mu yi farin ciki da kuma rayuwa mai kyau a nan gaba idan muka bi umurnin da ke Littafi Mai Tsarki.—1 Timoti 6:​17-19.

LITTAFI MAI TSARKI YANA TAIMAKAWA: Wani mutum mai suna Cardo daga Indonesiya ya dukufa neman arziki. Ya ce “Ina da yawancin abubuwan da mutane suke fatan su samu. Ina iya zuwa duk inda na ga dama, kuma in sayi manyan-manyan motoci da gidaje da kuma wasu abubuwa.” Waɗannan dukiyoyin ba su jima ba. Cardo ya ce “An damfare ni, kuma kafin in hankara an kwashe duk kuɗin da na yi shekaru ina tarawa. Na dukufa ina ta neman kuɗi ido rufe, amma a ƙarshe an bar ni da baƙin ciki da kaɗaici da kuma yin da-na-sani.”

Cardo ya soma bin shawarar Littafi Mai Tsarki game da kuɗi. Ya daina mai da hankalinsa wajen tara dukiya amma ya zaɓi ya sauƙaƙa rayuwarsa. Ya ce: “Yanzu ina gani ni mai arziki ne don na ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah. Ina iya barci da kyau yanzu kuma ina farin ciki sosai.”

Don samun ƙarin bayani game da kuɗi, ka karanta talifin nan “Neman Kudi da Ilimi Ne Zai Sa Mu More Rayuwa a Nan Gaba?” a Hasumiyar Tsaro Na 3 2021, a dandalin jw.org/ha.

4. Jimaꞌi

Mutane suna da raꞌayoyi da yawa game da batun yin jimaꞌi.

LITTAFI MAI TSARKI YA CE: “Ku guje wa halin lalata. Kowa ya san yadda zai bi da jikinsa cikin tsarki da mutunci, ba ta muguwar shaꞌawa ba yadda waɗanda ba Yahudawa ba suke yi, waɗanda ba su san Allah ba.”—1 Tasalonikawa 4:​3-5.

MAꞌANA: Littafi Mai Tsarki ya bayyana irin jimaꞌin da bai kamata ba. Furucin nan “halin lalata” ya ƙunshi masu zina da masu karuwanci da jimaꞌi tsakanin mutanen da ba su yi aure ba da masu luwaɗi da kuma masu kwana da dabbobi. (1 Korintiyawa 6:​9, 10) Allah ya ba wa mace da namiji kaɗai da suka yi aure damar yin jimaꞌi.—Karin Magana 5:​18, 19.

LITTAFI MAI TSARKI YANA TAIMAKAWA: Wata mata daga ƙasar Australia mai suna Kylie ta ce: “A lokacin da ban yi aure ba, ina ganin idan na yi jimaꞌi, hakan zai sa a ƙaunace ni kuma in sami kāriya. Amma hakan bai faru ba. Na ji kamar ba wanda yake ƙaunata kuma na shiga damuwa.”

Daga baya, Kylie ta koyi yadda za ta bi koyarwa Littafi Mai Tsarki game da jimaꞌi. Ta ce: “Na ga cewa Allah ya kafa ƙaꞌidodinsa ne don ya kāre mu daga damuwa iri-iri. A yanzu, ina samun kāriya kuma ana ƙaunata domin ina yin abubuwa yadda Jehobah yake so. Bin abin da ke Littafi Mai Tsarki ya taimaka min in guji matsaloli da yawa!”

Don samun ƙarin bayani, ka karanta talifin nan “What Does the Bible Say About Living Together Without Marriage?” a dandalin jw.org.

Mahaliccinmu yana taimaka mana mu san abin da ya dace da wanda bai dace ba. Ba kowane lokaci ne bin ƙaꞌidodinsa yake da sauƙi ba, amma za mu amfana idan muka yi hakan, kuma za mu yi farin ciki na dogon lokaci.