Ka Yi Godiya ga Jehobah Kuma Ka Sami Albarka
“Ku yi godiya ga Ubangiji; gama nagari ne shi.”—ZAB. 106:1.
1. Me ya sa ya dace mu gode wa Jehobah?
GODIYA ta tabbata ga Jehobah, Mai ba da “kowace kyakkyawar baiwa da kowace cikakkiyar kyauta.” (Yaƙ. 1:17) Shi ne makiyayinmu kuma yana ƙaunarmu sosai, shi ya sa yake tanadar mana da dukan abubuwan da muke bukata. (Zab. 23:1-3) Shi ne “mafakanmu . . . da ƙarfinmu,” musamman ma a mawuyacin lokaci! (Zab. 46:1) Babu shakka, muna da dalilai da yawa na amincewa da abin da marubucin zabura ya rubuta cewa: “Ku yi godiya ga Ubangiji; gama nagari ne shi: Gama jinƙansa ya tabbata har abada.”—Zab. 106:1.
Jigonmu na shekara ta 2015: “Ku yi godiya ga Jehobah domin nagari ne shi.”
2, 3. (a) Me ya sa bai kamata mu yi watsi da abubuwan da Jehobah yake ba mu ba? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu bincika a wannan talifin?
2 Me ya sa yake da muhimmanci mu tattauna batun nan na yin godiya? Kamar yadda aka annabta, a zamanin ƙarshe mutane za su zama marasa godiya. (2 Tim. 3:2) Mutane da yawa ba sa gode wa Allah saboda abubuwa masu kyau da yake musu. Da yake muna rayuwa a duniyar da take ƙarfafa mutane su riƙa son abin duniya, miliyoyin mutane suna ƙoƙari su mallaki abubuwa da yawa maimakon su yi hamdala da abin da suke da shi. Wannan halin zai iya shafan mu ma. Kamar Isra’ilawa na dā, mu ma za mu iya yin watsi da abubuwan da Jehobah yake ba mu da kuma dangantakarmu da shi kuma mu daina yin godiya.—Zab. 106:7, 11-13.
3 Har ila, ka yi la’akari da abin da zai iya faruwa a lokacin da muke fuskantar gwaji mai tsanani. A waɗannan lokatan za mu iya yin sanyin gwiwa har mu manta da abubuwa masu kyau da Jehobah yake ba mu. (Zab. 116:3) Saboda haka, ta yaya za mu riƙa nuna godiya kuma mu ci gaba da yin hakan? Mene ne zai taimaka mana mu kasance da ra’ayi mai kyau a lokacin da muke fuskantar gwaji mai tsanani? Bari mu bincika su.
ABUBUWAN DA JEHOBAH YA YI SUNA DA YAWA
4. Ta yaya za mu ci gaba da yin godiya?
4 Idan muna son mu ci gaba da yin godiya, wajibi ne mu riƙa yin bimbini a kan abubuwa masu kyau da Jehobah ya yi mana da kuma yadda yake ƙaunarmu. Abin da marubucin zabura ya yi ke nan kuma bayan hakan, ya fahimci cewa Jehobah ya yi abubuwa masu ban al’ajabi da yawa.—Karanta Zabura 40:5; 107:43.
5. Wane darasi ne za mu koya daga manzo Bulus game da nuna godiya?
5 Za mu iya koyan darasi daga manzo Bulus game da yin godiya. Babu shakka, Bulus ya yi bimbini a kan abubuwan da Jehobah ya yi masa, kuma ya riƙa gode wa Allah. Ƙari ga haka, Bulus ya san cewa shi “mai-saɓo ne dā, mai-tsanani, mai-ɓatanci.” Duk da haka, ya riƙa gode wa Allah da Kristi don sun nuna masa jin ƙai kuma suka ba shi aiki. (Karanta 1 Timotawus 1:12-14.) Bulus ya ɗauki ’yan’uwansa Kirista da mutunci kuma ya gode wa Jehobah don halayensu masu kyau da kuma hidimar da suka yi da aminci. (Filib. 1:3-5, 7; 1 Tas. 1:2, 3) A lokacin da Bulus ya fuskanci yanayi mai wuya, ya gode wa Jehobah saboda taimakon da ya samu daga ’yan’uwansa. (A. M. 28:15; 2 Kor. 7:5-7) Ya ƙarfafa Kiristoci cewa: “Ku zama masu-godiya . . . , kuna kuwa gargaɗi tare da zabura da waƙoƙin yabo da waƙoƙi masu-ruhaniya, kuna rairawa da godiya cikin zukatanku ga Allah.”—Kol. 3:15-17.
BIMBINI DA ADDU’A ZA SU SA MU ZAMA MASU GODIYA
6. Waɗanne abubuwa ne musamman suka sa kake gode wa Jehobah?
6 Ta yaya za mu bi misalin Bulus game da nuna godiya? Kamar manzo Bulus, ya dace mu riƙa yin bimbini a kan abubuwan da Jehobah ya yi mana. (Zab. 116:12) Mene ne za ka ce idan aka tambaye ka, ‘Wace albarka ce za ka yi godiya a kai?’ Za ka ambaci abotarka da Allah kuwa? Ko za ka ambaci yadda aka yafe maka zunubanka don ka ba da gaskiya ga hadayar fansar Kristi? Shin za ka ambata sunayen ’yan’uwa da suka taimake ka lokacin da kake fuskantar matsaloli? Abokin aurenka da kuma yaranka fa? Idan ka yi bimbini a kan albarkar da kake samu daga Ubanmu mai ƙauna, Jehobah, za ka yi farin ciki kuma hakan zai motsa ka ka riƙa gode wa Allah kowace rana.—Karanta Zabura 92:1, 2.
7. (a) Me ya sa ya kamata mu riƙa gode wa Allah a addu’armu? (b) Ta yaya za ka amfana idan kana gode wa Allah a addu’arka?
7 Idan muna bimbini a kan albarkar da muke samu daga Jehobah, za mu kasance a shirye mu riƙa yin addu’a da godiya. (Zab. 95:2; 100:4, 5) Wasu sun ɗauka cewa lokacin bukata ne kawai ya dace mutum ya yi addu’a. Amma mu mun san cewa Jehobah yana farin ciki idan muka yi masa godiya don abin da muke da shi. Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da addu’o’i da yawa da mutane kamar su Hannatu da Hezekiya suka yi don nuna godiya. (1 Sam. 2:1-10; Isha. 38:9-20) Ya kamata mu bi misalin waɗannan bayin Allah masu aminci da suka yi godiya. Hakika, zai dace mu riƙa yin addu’a ga Jehobah don mu gode masa saboda abubuwan da yake yi mana. (1 Tas. 5:17, 18) Za ka amfana sosai idan ka yi hakan. Ƙari ga haka, za ka yi farin ciki kuma za ka so Jehobah sosai. Ƙari ga haka, za ka daɗa ƙarfafa dangantakarka da shi.—Yaƙ. 4:8.
8. Me zai sa mu daina nuna godiya ga dukan abubuwan da Jehobah ya yi mana?
8 Me ya sa yake da muhimmanci mu mai da hankali don kada mu daina nuna godiya ga Jehobah don alherinsa? Domin an haife mu da wannan hali na rashin godiya. Alal misali: An saka iyayenmu na farko, Adamu da Hawwa’u a gonar Adnin. An biya duka bukatunsu kuma suna da gatan yin rayuwa cikin salama har abada. (Far. 1:28) Duk da haka, ba su nuna godiya ga abubuwan da Jehobah ya yi musu ba. Maimakon haka, sun yi hadama kuma a sakamakon haka, suka yi biyu babu. (Far. 3:6, 7, 17-19) Da yake muna zama a cikin mutane marasa godiya, hakan zai iya sa mu daina godiya ga Jehobah don abubuwan da ya yi mana. Ƙari ga haka, hakan zai iya sa mu yi watsi da dangantakarmu da Jehobah. Ban da haka ma, ba za mu ɗauki gatan kasancewa cikin ’yan’uwanmu da ke faɗin duniya da muhimmanci ba. Za mu iya sa abin duniya da zai shuɗe ba da daɗewa ba ya janye hankalinmu. (1 Yoh. 2:15-17) Amma za mu guji wannan mummunan yanayi idan muka yi bimbini a kan abubuwan da Jehobah ya yi mana kuma mu gode masa don gatan da ya ba mu na bauta masa.—Karanta Zabura 27:4.
LOKACIN DA MUKE FUSKANTAR GWAJI
9. Me ya sa ya kamata mu yi bimbini a kan abubuwan da Jehobah ya yi mana sa’ad da muke fuskantar mugun yanayi?
9 Yin godiya a koyaushe zai taimaka mana mu jimre da gwaji mai tsanani. Wani mugun yanayi kamar cin amanar abokin aure ko ciwo mai tsanani ko mutuwar wani da muke ƙauna ko kuma wani bala’i zai iya sa mu sanyin gwiwa. A irin wannan yanayi, za mu iya samun ƙarfafa idan muka yi bimbini a kan abubuwan
da Jehobah ya yi mana. Bari mu tattauna abin da ya faru da wasu mutane.10. Ta yaya Irina ta amfana daga yin bimbini a kan abubuwan da Jehobah ya yi mata?
10 Wata majagaba mai suna Irina * tana zama a Amirka. Mijinta dattijo ne amma ya ci amanarta kuma ya bar ta da yara. Mene ne ya taimaka wa Irina ta ci gaba da bauta wa Jehobah da aminci? Ta ce: “Na gode wa Jehobah don yadda yake kula da ni. Da yake ina godiya ga dukan abubuwan da Jehobah yake yi mini kowace rana, na fahimta cewa gata ne Jehobah, wato Ubanmu na sama ya san ni kuma ya so ni. Na san cewa ba zai taɓa yasar da ni ba.” Ko da yake Irina ta fuskanci matsaloli sosai, farin cikin da take yi kullum da kuma yadda ta jimre sun zama abin koyi ga ’yan’uwa.
11. Mene ne ya taimaka wa Kyung-sook ta jimre da mugun cutar da take da shi?
11 Wata ’yar’uwa mai suna Kyung-sook da ke nahiyar Asiya, ta yi hidimar majagaba tare da mijinta fiye da shekaru 20. Farat ɗaya, sai likita ya gaya mata cewa cutar daji ya riga ya ci jikinta kuma a cikin wata uku zuwa shida za ta mutu. Ko da yake ita da mijinta sun fuskanci matsaloli da yawa, suna gani cewa suna da koshin lafiya. Ta ce: Wannan cutar ta girgiza ni sosai, na ji kamar na yi hasarar kome kuma hakan ya sa na tsorata ba kaɗan ba.” Me ya taimaka wa Kyung-sook ta jimre? Ta ce: “Kowane dare kafin in yi barci na kan hau saman gidanmu kuma in yi addu’a da babbar murya game da abubuwa guda biyar da Jehobah ya yi mini a ranar. Hakan yana sa ni in wartsake kuma ya motsa ni in nuna cewa ina ƙaunar Jehobah.” Ta yaya Kyung-sook ta amfana daga addu’o’in da take yi a kowane dare? Ta ce: “Na fahimta cewa Jehobah yana taimaka mana a lokacin wahala kuma albarkar da muke samu sun fi matsalolin da muke fuskanta.”
12. Ta yaya Jason ya sami ƙarfafa sa’ad da matarsa ta rasu?
12 Wani Ɗan’uwa mai suna Jason da ke hidima a wani ofisoshin Shaidun Jehobah a Afirka, ya yi sama da shekara 30 yana hidima ta cikakken lokaci. Ya ce: “Matata ta rasu shekaru bakwai da suka shige kuma hakan ya sa ni baƙin ciki sosai. Yin tunani a kan abin da ta fuskanta sa’ad da take fama da cutar daji yana sa ni sanyin gwiwa.” Mene ne ya taimaka wa Jason ya jimre? Ya ce: “Akwai wani lokaci da na tuna wani abin farin ciki da muka yi sa’ad da nake tare da matata, sai na yi addu’a ga Jehobah don in gode masa saboda hakan. Na sami ƙarfafa kuma sai na soma gode wa Jehobah a kai a kai don hakan. Yin godiya ya taimaka mini in kasance da ra’ayi mai kyau. Ko da yake ina baƙin ciki har ila, amma na gode wa Jehobah don aurena da kuma gatan bauta masa tare da wadda take ƙaunarsa. Hakan ya sa na kasance da ra’ayi mai kyau.”
“Ina godiya cewa Jehobah shi ne Allahna.”
13. Mene ne ya taimaka wa Sheryl ta jimre a lokacin da ta rasa iyayenta da wasu ’yan’uwanta?
13 A lokacin da guguwar Haiyan ta addabi wani sashen ƙasar Filifin a ƙarshen shekara ta 2013, wata yarinya mai suna Sheryl mai shekara sha uku a lokacin ta yi hasarar kusan kome. Ta ce: “Gidanmu ya halaka kuma na yi rashin iyayena da wasu ’yan’uwana.” Mahaifinta da mahaifiyarta da ’yan’uwanta uku sun rasu a sakamakon hakan. Mene ne ya taimaka wa Sheryl ta jimre kuma ta ci gaba da kasancewa da ra’ayi mai kyau? Ba ta daina godiya ga Jehobah ba kuma ta tuna da abubuwan da take mora yanzu. Ta ce: “Kuma na ga duk abubuwa da ’yan’uwa suka yi Filibiyawa 4:6, 7.
don su taimaka da kuma ƙarfafa waɗanda suke bukatar taimako. Na san cewa ’yan’uwa a dukan duniya suna addu’a a madadina.” Ta ƙara cewa: “Ina godiya cewa Jehobah shi ne Allahna. Yana ba mu dukan abubuwan da muke bukata.” Hakika, baƙin ciki ba zai sha kanmu ba idan muka ci gaba da nuna godiya don albarka da muka samu. Yin godiya zai sa mu ci gaba da rayuwa duk da matsaloli.—Afis. 5:20; karanta“ZAN YI MURNA CIKIN UBANGIJI”
14. Wane bege mai ban sha’awa ne muke jira? (Ka duba hoton da ke shafi na 8.)
14 A duk tarihi, mutanen Jehobah suna nuna godiya don albarka da suka samu. Alal misali, bayan da aka ceci Isra’ilawa daga hannun Fir’auna da sojojinsa a Jar Teku, sun rera waƙar yabo da godiya don su nuna farin cikinsu. (Fit. 15:1-21) A yau, albarka da ta fi muhimmanci a gare mu ita ce begenmu na sanin cewa ba da daɗewa ba, azaba da baƙin ciki ba za su ƙara kasancewa ba. (Zab. 37:9-11; Isha. 25:8; 33:24) Ka yi tunanin yadda za mu ji sa’ad da Jehobah ya kawar da dukan magabtanmu kuma ya sa muka shiga cikin sabuwar duniya inda za a yi salama da adalci. Babu shakka, za mu gode wa Jehobah a wannan lokacin!—R. Yoh. 20:1-3; 21:3, 4.
15. Mene ne ka ƙuduri niyyar yi a shekara ta 2015?
15 Muna ɗokin samun albarka mai yawa daga Jehobah a shekara ta 2015. Hakika, za mu fuskanci wasu gwaji. Ko da mene ne za mu fuskanta, mu san cewa Jehobah ba zai taɓa yasar da mu ba. (K. Sha 31:8; Zab. 9:9, 10) Zai ci gaba da yi mana tanadi don mu bauta masa da aminci. Saboda haka, bari mu ƙuduri niyyar kasancewa da ra’ayin annabi Habakkuk, wanda ya ce: “Gama ko itacen ɓaure ba ya yi fure ba, ba kuwa ’ya’ya a cikin kuringar anab ba; wahalar zaitun ta zama banza, gonaki ba su bada abinci ba: ko da tumaki ba su ribbababanya a garkensu ba, ba a iske kuma shanu a dangwalinsu ba; duk da haka zan yi murna cikin Ubangiji; zan yi murna a cikin Allah mai-cetona.” (Hab. 3:17, 18) A wannan shekarar, bari mu riƙa tunawa da albarka da muke mora kuma hakan ya motsa mu mu bi shawara da ke jigonmu na shekara ta 2015: Ku yi godiya ga Jehobah domin nagari ne shi.—Zab. 106:1.
^ sakin layi na 10 An canja wasu sunaye a wannan talifin.