Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shirya Al’ummai don Koyarwar Jehobah

Shirya Al’ummai don Koyarwar Jehobah

Muƙaddas, . . . ya ba da gaskiya, yana mamaki da [koyarwar Ubangiji, Littafi Mai Tsarki].’ —A. M. 13:12.

1-3. Waɗanne ƙalubale ne almajiran Yesu suka fuskanta a yin wa’azin bishara ga “dukan al’ummai”?

BA ƘARAMIN aiki ba ne Yesu Kristi ya ba wa mabiyansa. Ya umurce su cewa: “Ku tafi, . . . ku almajirtar da dukan al’ummai.” Yayin da almajiran Yesu suke wa’azin “bishara . . . ta mulki,” da shigewar lokaci, bisharar za ta kai “iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai.”—Mat. 24:14; 28:19.

2 Babu shakka, almajiran Yesu suna ƙaunar Yesu kuma suna son bisharar. Duk da haka, wataƙila sun yi tunanin yadda za su iya cika umurnin da aka ba su. Me ya sa? Don ba su da yawa kuma an kashe Yesu da suke wa’azi cewa shi Ɗan Allah ne. Ƙari ga haka, mutane suna musu kallon “marasa karatu” da kuma “talakawa.” (A. M. 4:13) Koyarwarsu dabam ne da na manyan malaman Yahudawa masu ilimin al’adu na dā. Daɗin daɗawa, mutanen Isra’ila ba sa ɗaukan almajiran Yesu da mutunci. Shin ta yaya za su iya yin wa’azin bishara a dukan masarautar Roma?

3 Yesu ya gaya wa almajiransa cewa za a ƙi jininsu kuma za a tsananta musu. Ƙari ga haka, za a kashe wasu daga cikinsu. (Luk. 21:16, 17) Ban da haka ma, ’yan’uwansu za su ci amanarsu kuma za su yi fama da annabawan ƙarya da yaɗuwar mugunta. (Mat. 24:10-12) Ko da mutane a ko’ina za su saurare wa’azinsu, ta yaya za su iya yaɗa bishara “zuwa iyakar duniya”? (A. M. 1:8) Hakika, wannan ba ƙaramin aiki ba ne!

4. Wane sakamako ne almajiran Yesu a ƙarni na farko suka samu a wa’azi?

4 Almajiran Yesu sun san cewa aikin ba mai sauƙi ba ne, amma sun yi wa’azin bishara a Urushalima da Samariya har zuwa iyakar duniya a zamanin. Ko da yake sun fuskanci mawuyacin hali, amma a cikin shekara 30, an yi wa’azin bishara ga “dukan halitta da ke ƙarƙashin sama.” Ƙari ga haka, bishara ta yaɗu “cikin dukan duniya kuma tana ba da amfani.” (Kol. 1:6, 23) Alal misali, muƙaddashin Roma mai suna Sergius Paulus da ke Tsibirin Ƙubrus, ‘ya ba da gaskiya, yana mamaki da [koyarwar Ubangiji, LMT]’ saboda abubuwan da manzo Bulus ya faɗa da kuma yi.—Karanta Ayyukan Manzanni 13:6-12.

5. (a) Mene ne Yesu ya tabbatar wa almajiransa? (b) Mene ne wani littafin tarihi ya faɗa game da yanayin ƙarni na farko?

5 Almajiran Yesu sun san cewa ba za su iya cim ma aikin da ƙarfinsu ba. Yesu ya yi musu alkawari cewa zai kasance tare da su kuma cewa ruhu mai tsarki zai taimake su. (Mat. 28:20) Bugu da ƙari, yanayin lokacin ya taimaka wa almajiran Yesu su ji daɗin wa’azin bishara. Littafin nan Evangelism in the Early Church ya ce: “Wataƙila babu lokaci a tarihin duniya da ya fi dace wa addinin Kirista kamar ƙarni na farko . . . A ƙarni na biyu Kiristoci . . . sun soma da’awa cewa ikon Allah ne ya sa duniya ta karɓi Addinin Kirista.”

6. Mene ne za mu tattauna (a) a wannan talifin? (b) a talifi na gaba?

6 Shin Jehobah ne ya canja yanayin abubuwa a ƙarni na farko don a yaɗa bishara? Littafi Mai Tsarki bai bayyana ba. Abin da muka sani shi ne Jehobah yana son a yi wa’azin bishara, amma Shaiɗan bai so hakan ba. A wannan talifin, za mu tattauna wasu abubuwan da suka sa wa’azin bishara ya sami ci gaba sosai a ƙarni na farko fiye da wasu lokatai. A talifi na gaba kuma, za mu bincika abubuwan da suka taimaka wajen yaɗa bishara har iyakar duniya a zamaninmu.

WATAƘILA KWANCIYAR HANKALI A ROMA YA TAIMAKA

7. Yaya yanayi yake a ƙarni na farko a Daular Roma? Me ya sa yanayin lokacin ya bambanta da na wasu lokatai?

7 Sarautar Roma ta amfani Kiristoci a wasu hanyoyi. Alal misali, a zamanin, mulkin Roma ya zartar da zaman lafiya a dukan masarautar. Ko da yake, a wasu lokatai, an yi “yaƙe-yaƙe da jitajitarsu” kamar yadda Yesu ya annabta. (Mat. 24:6, LMT) Rundunar Roma ta halaka Urushalima a shekara ta 70 daga zamanin Yesu, kuma an yi faɗace-faɗace a iyakokin masarautar. Amma, wajen shekaru 200 daga lokacin da Yesu yake duniya, a yawancin lokaci, an yi zaman lafiya a daular Roma. Wani littafin bincike ya ce: “Ba a taɓa samun kwanciyar hankali gama gari kuma na lokaci mai tsawo kamar haka ba, kuma ba a sake samun lokacin da mutane suka yi zaman lafiya da juna kamar haka ba.”

8. Ta yaya yanayin kwanciyar hankali ya amfani Kiristoci na farko?

8 Wani ɗan tauhidi mai suna Origen ya ce: “Da a ce akwai mulkoki da yawa, da hakan ya hana yaɗuwar koyarwar Yesu . . . don da mutane a ko’ina sun shiga soja don su kāre ƙasarsu. . . . Ƙari ga haka, in da a ce yanayin ƙasashen duniya bai kasance cikin lumana kuma ba a yi kwanciyar hankali a zamanin Yesu ba, da wannan addinin da ke wa’azin salama, wanda mabiyansa ba sa kai wa magabtansu hari bai sami ci gaba ba.” An tsananta wa masu wa’azin bishara a daular Roma, amma sun yi zaman lafiya da mutane kuma sun amfana daga kwanciyar hankali da aka yi a lokacin.—Karanta Romawa 12:18-21.

YADDA CI GABA DA AKA SAMU A SUFURI YA TAIMAKA

9, 10. Me ya sa sufuri ya kasance da sauƙi wa almajiran Yesu a Daular Roma?

9 Kiristoci sun yi amfani da hanyoyin da aka tsara a Daular Roma sosai. Da yake Roma tana da burin kāre da kuma nuna iko a kan dukan mazauna daular, ta tsara rundunar sojoji mai iko da kuma inganci kuma ta sa ƙwararrun masu gyaran hanya sun tsara hanyoyi masu kyau don rundunar sojojin su riƙa zagaya Daular da sauƙi. Waɗannan hanyoyin suna da tsawon kilomita 80,000 kuma sun shiga kusan kowane lardin da ke Masarautar. Ƙari ga haka, hanyoyin sun bi ta kurmi da hamada da kuma tsaunuka.

10 Ban da waɗannan hanyoyin, Romawa sun yi amfani da jiragen ruwa kuma sun bi koguna da mashigan kogi da kuma teku. Hanyoyin ruwan sun kai kimanin 900 kuma idan aka haɗa tsawon hanyoyin, ya kai wajen kilomita 27,000. Ƙari ga haka, suna da ɗarurruwan tashoshin jirgin ruwa. Saboda haka, Kiristoci sun yi tafiye-tafiye sosai a masarautar. Ko da yake sun fuskanci matsaloli, amma manzo Bulus da kuma wasu Kiristoci sun yi tafiya zuwa wurare dabam-dabam a daular ba tare da fasfo ko biza ba. A lokacin, ba masu kula da shige da fice kuma ba a bincike sa’ad da ake ƙetare iyaka. Ana hukunta masu aikata laifi sosai saboda haka, ba a yawan fashi. Ƙari ga haka, da yake sojojin ruwa na Roma suna zagaya ko’ina, ba a haɗuwa da mafasan teku. Ko da yake, Bulus ya sha yin hatsari a teku, amma Littafi Mai Tsarki bai ambata cewa mafasa sun taɓa tare shi ba.—2 Kor. 11:25, 26.

YADDA YARE YA TAIMAKA

Littafin codex ya sa bincika nassi ya kasance da sauƙi (Ka duba sakin layi na 12)

11. Me ya sa almajiran Yesu suka yi amfani da yaren Girka?

11 Yaren Girka, wato Koine ya sa Kiristoci sun yi sadarwa da kyau kuma sun kasance da haɗin kai a cikin ikilisiyoyi. Nasarar da Alexander the Great ya yi ya sa yaren girka ya zama yare gama gari a daular. Ta hakan, Kiristoci sun yi hulɗa da mutane iri-iri, kuma hakan ya sa bishara ta haɓaka. Ƙari ga haka, Yahudawa da suka zauna a Masar sun fassara littafin Farawa zuwa Malakai cikin yaren Girka. Mutane da yawa sun saba da wannan fassara da ake kira Septuagint, kuma almajiran Kristi sun yi ƙaulinta sa’ad da suke koyarwa. Ƙari ga haka, Kiristoci sun yi amfani da yaren Girka a rubuce-rubucen da suka yi. Yaren Girka yana da tsarin kalmomi mai yawa da kuma ma’ana sosai. Ƙari ga haka, kalmomin sun taimaka sosai wajen bayyana abubuwan da suka shafi ibada.

12. (a) Mene ne codex, kuma me ya sa ya fi naɗaɗɗen littafi inganci? (b) A wane lokaci ne Kiristoci suka yi amfani da littafin codex sosai?

12 Naɗaɗɗen littafi, wato scroll yana da nauyi kuma amfani da shi yana da wuya don yana bukatar warwarewa da naɗewa a kowane lokaci. A yawancin lokaci, a gefe ɗaya ne kawai ke ɗauke da rubutu, shin ta yaya Kiristoci za su karanta nassosi sa’ad da suke wa’azi? Littafin Matta kaɗai zai cika naɗaɗɗen littafi guda. A wannan lokacin ne wani nau’in littafi da ake kira codex ya fito. Wannan nau’in ya kusan kama da tsarin littafi da muke amfani da shi yanzu. Mai amfani da codex zai iya duba wani nassi da yake so ba tare da ɓata lokaci ba. Ko da yake ba a san lokacin da Kiristoci suka soma amfani da codex ba, wani littafin bincike ya ce: “Kiristoci a faɗin duniya sun yi amfani da codex a ƙarni na biyu sosai. Saboda haka, an soma amfani da shi ne kafin shekara ta 100 daga zamanin Yesu.”

YADDA TSARIN DOKOKIN ROMA YA TAIMAKA

13, 14. (a) Ta yaya Bulus ya yi amfani da ’yancinsa na ɗan Roma? (b) Ta yaya tsarin dokar Roma ya amfani Kiristoci?

13 Dokokin Roma sun yi inganci a ko’ina a daular, kuma kasancewa ɗan Roma yana tattare da ’yanci da kuma kāriya da dama. Bulus ya yi amfani da ’yancinsa na ɗan Roma a lokatai da dama. Sa’ad da wani shugaban sojan Roma yake so ya bulale shi a Urushalima, sai manzo Bulus ya tambaye shi: “Ya halatta a gare ka ka yi wa mutumin da ke da ’yancin Roma bulala, ba ko bin ba’asi,” wato ko ba a hukunta shi ba? Amsar ita ce a’a. Sa’ad da Bulus ya bayyana cewa shi haifaffen ɗan Roma ne, sai “waɗanda ke shirin tuhumarsa, suka rabu da shi nan da nan. Shi ma shugaban da ya fahimci Bulus Barome ne sai ya tsorata, ga shi kuwa, ya ɗaure shi.”—A. M. 22:25-29, LMT.

14 ’Yancin Bulus na ɗan Roma ya shafi yadda aka bi da shi a Filibi. (A. M. 16:35-40) A garin Afisus, marubucin gari ya ambaci kundin tsarin dokar Roma bayan ya kwantar da hankalin wasu ’yan zanga-zanga da suke so su cim ma wani mugun nufi. (A. M. 19:35-41) Sa’ad da Bulus yake Kaisariya, ya yi amfani da ’yancinsa na Ba-rome don ya sami damar bayyana imaninsa a gaban Kaisar. (A. M. 25:8-12) Ta hakan, tsarin dokar Roma ya sa an yi “kariyar bishara da tabbatar da ita” a shari’ance.—Filib. 1:7, LMT.

SAKAMAKON YAƊUWAR YAHUDAWA A ƘASASHE DA YAWA

15. A waɗanne wurare ne Yahudawa suka kasance a ƙarni na farko?

15 Wani abu kuma da ya sa bishara ta ci gaba shi ne yaɗuwar Yahudawa a ƙasashe dabam-dabam a cikin masarautar Roma. Ƙarnuka kafin wannan lokacin, Assuriyawa da kuma Babiloniyawa sun kwashi Yahudawa daga ƙasarsu kuma sun kai su bauta. Saboda haka, a ƙarni na biyar kafin zamanin Yesu, Yahudawa suna zaune a larduna 127 a daular Fasiya. (Esther 9:30) Sa’ad da Yesu yake duniya, Yahudawa suna zaune a Masar da wasu wurare a Afirka ta Arewa, da kuma Girka da Asiya Ƙarama da Mesopotamiya. An ce sama da mutane miliyan 4 cikin miliyan 60 da ke Daular Roma Yahudawa ne. Yahudawa suna bin addininsu a duk inda suka je.—Mat. 23:15.

16, 17. (a) Ta yaya yaɗuwar Yahudawa a ƙasashe dabam-dabam ya taimaka wa waɗanda ba Yahudawa ba? (b) Wane tsarin Yahudawa ne almajiran Yesu suke bi?

16 Mutane da yawa da ba Yahudawa ba sun san Attaura don Yahudawa sun bazu a wurare dabam-dabam. Sun koyi cewa Allah ɗaya ne kuma waɗanda suke bauta masa suna bin tsarin rayuwa da ɗabi’a mai kyau. Ƙari ga haka, akwai annabce-annabce da yawa game da Almasihu a cikin Attaura. (Luk. 24:44) Da yake Yahudawa da Kiristoci sun fahimci cewa Allah ne ya hure Attaura, Bulus ya yi nasara sa’ad da yake wa’azin bishara ga masu kirki da ke cikin su. Bisa al’adar Bulus, yakan shiga cikin majami’ar Yahudawa kuma ya yi amfani da Nassosi don ya tattauna da su.—Karanta Ayyukan Manzanni 17:1, 2.

17 Yahudawa suna da tsari na ibada. Sukan haɗu a majami’a ko kuma a fili don su rera waƙoƙi, su yi addu’a kuma su tattauna Nassosi. Bisa ga wannan tsarin ne Kiristoci suke yin taro a yau.

JEHOBAH NE YA SA HAKAN YA YIWU

18, 19. (a) Mene ne yanayin ƙarni na farko ya sa aka cim ma? (b) Ta yaya abin da muka tattauna ya shafi ra’ayinka game da Jehobah?

18 Hakika, abubuwa da muka ambata sun sa an yi nasara wajen yaɗa bishara. Kwanciyar hankali da aka yi a daular da sauƙin sufuri da haɓakar yaren Girka da tsarin dokokin Roma da kuma yaɗuwar Yahudawa a ƙasashe sun taimaka wa almajiran Yesu wajen yin wa’azin bishara.

19 Shekaru ɗari huɗu kafin zamanin Yesu, wani ɗan falsafar Girka mai suna Plato ya ce: “Zai yi wuya a gane mahaliccin duniya da sararin sama, ko da mun san shi, ba za mu iya gaya dukan mutane game da shi ba.” Amma, Yesu ya ce: “Abin da ba shi yiwuwa ga mutum ya yiwu ga Allah.” (Luk. 18:27) Mahaliccin duniya da sararin sama yana son mutane su biɗe shi kuma su san shi. Ƙari ga haka, Yesu ya ce wa mabiyansa: ‘Ku almajirtar da dukan al’ummai.’ (Mat. 28:19) Da taimakon Jehobah Allah, wannan umurnin zai cika. Talifi na gaba zai bayyana yadda ake cika wannan umurnin a zamaninmu.