Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DAGA TARIHINMU

“Lokaci Mai Muhimmanci Sosai”

“Lokaci Mai Muhimmanci Sosai”

A SHEKARA ta 1870, wani ƙaramin rukuni da ke birnin Pittsburgh (Allegheny), Pennsylvania a Amirka sun soma bincika Nassosi. Charles Taze Russell ne ya ja-gorance su, sun yi bincike a kan fansa na Kristi kuma suka gane cewa tana da muhimmanci a cikar nufin Jehobah. Sun yi farin ciki sosai da suka koya cewa fansar ta ba wa mutane, har da waɗanda ba su taɓa jin labarin Yesu ba, damar samun ceto. Hakan ya motsa su su nuna godiya ta yin taron tuna mutuwar Yesu kowace shekara.—1 Kor. 11:23-26.

Ɗan’uwa Russell ya soma wallafa Zion’s Watch Tower, (Hasumiyar Tsaro) da ke bayyana cewa tanadin fansa ya nuna cewa Allah yana ƙaunar ’yan Adam sosai. Hasumiyar Tsaro ta ce lokacin Tuna Mutuwar Kristi lokaci ne “mai muhimmanci sosai” an shawarci masu karanta mujallar su yi taro don tuna mutuwar Yesu a birnin Pittsburgh ko kuma wani wuri a ƙananan rukuni. “Ko da masu bangaskiya biyu ko uku ne suka taru” ko ma ɗaya ne, “Kristi yana tare da su.”

A kowace shekara, mutane da suke zuwa birnin Pittsburgh don Tuna da Mutuwar Yesu suna ta ƙaruwa. Takardar gayyatar ta ce: “Mutane masu fara’a za su sa ka ji daɗin zuwanka.” Hakika, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki da suke yankin sun ba ’yan’uwansu wurin kwana da kuma abinci. A shekara ta 1886 an yi taron kwanaki da yawa bayan taron Tuna Mutuwar Yesu. Hasumiyar Tsaro ta ce mutane su “zo da zuciya ɗaya su nuna ƙaunarsu ga Ubangiji da kuma ’yan’uwansa da kuma koyarwarsa.”

Taswira na zagaya da isharori a taron Tuna Mutuwar Yesu a London Tabernacle

Shekaru da yawa, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki a birnin Pittsburgh sun gudanar da manyan taro don masu ba da gaskiya ga fansa da suka halarci taron Tuna Mutuwar Yesu. Yayin da adadin Ɗaliban Littafi Mai Tsarki yake ƙaruwa, adadi da girman wuraren da ake taron Tuna Mutuwar Yesu a faɗin duniya ma sun ƙaru. Ɗan’uwa Ray Bopp da ke ikilisiyar Chicago ya tuna cewa a shekara ta 1910 zuwa 1919, kafin a zagaya da isharorin tsakanin ɗarurruwan ’yan’uwa da suka halarta, ana sa’o’i da dama domin kusan duka suna ci.

Mene ne isharori da aka yi amfani da su? Ko da yake sun san cewa Yesu ya yi amfani da ruwan inabi a lokacin Jibin Ubangiji, Hasumiyar Tsaro ta ce a yi amfani da ruwan lemun inabi ko kuma na busashen lemun inabi da aka dafa a maimakon ruwan inabi tsantsa don kada a sa waɗanda ba za su iya kame kansu ba cikin jaraba. Amma, ana ba da ruwan inabi ga waɗanda suke gani ya kamata “a yi amfani da ruwan inabi da ya kwana.” Daga baya, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun fahimci cewa ya dace a yi amfani da ruwan inabi zalla don shi ne abin da ya fi dacewa da abin da jinin Yesu yake wakilta.

Takardar da fensir da aka yi amfani da su don a rubuta adadin waɗanda suka halarci taron Tuna Mutuwar Yesu a kurkuku da ke kasar Nicaragua

Tuna da Mutuwar Yesu yana ba da damar yin bimbini sosai. Amma, a wasu ikilisiyoyi, yanayin yana kama da inda aka yi rasuwa kuma lokacin da aka gama taro, sai kowa ya fita ba tare da ce uffan ba. Littafin nan Jehovah, da aka wallafa a shekara ta 1934 ya ce bai dace a yi taron nan “da baƙin ciki” don mutuwar azaba da Yesu ya yi ba. Amma, zai dace a yi taron da “farin ciki” domin Yesu ya soma sarauta tun shekara ta 1914.

’Yan’uwan sun taru a sansanin aiki da ke Mordvinia a Rasha don su yi taron Tuna Mutuwar Yesu a shekara ta 1957

A shekara ta 1935, an yi canji na musamman da ya shafi yadda za a riƙa yin taron Tuna Mutuwar Yesu daga lokacin, wato an bayyana abin da “taro mai-girma” da aka ambata a Ru’ya ta Yohanna 7:9 yake nufi. Kafin wannan lokacin, bayin Jehobah sun ɗauka cewa “taro mai girma” ya ƙunshi Kiristoci da suka tsai da shawarar bauta wa Jehobah amma ba su da ƙwazo. A yanzu, an san taro mai girma a matsayin masu ibada da aminci, waɗanda suke da begen kasancewa a aljanna a duniya. Ɗan’uwa Russell Poggensee ya bincika kansa sosai bayan wannan bayanin, kuma ya ce: “Jehobah bai bayyana mini cewa ina da begen zuwa sama ta wurin ruhunsa mai tsarki ba.” Ɗan’uwa Poggensee da kuma wasu amintattu kamar shi sun daina cin isharar amma sun ci gaba da halartar taron Tuna Mutuwar Yesu.

A wannan “lokaci mai muhimmanci sosai,” kamfen na musamman na wa’azi ya ba da zarafi wa dukan ’yan’uwa su nuna godiya don fansar. A shekara ta 1932, Bulletin (Hidimarmu ta Mulki) ta ce kada Kiristoci su zama masu cin ishara ba tare da yin wa’azi ba. A shekara ta 1934, Hidimarmu ta Mulki ta ce ana bukatar “majagaba na ɗan lokaci” kuma ta yi tambaya: “Shin za a sami ’yan’uwa 1,000 da za su yi hidimar nan a lokacin Tuna Mutuwar Yesu?” Hidimarmu ta Mulki ta ce game da shafaffu: “Za su yi farin ciki sosai idan suka yi wa’azin Mulki.” Da shigewar lokaci, waɗanda suke da begen zama a duniya ma sun yi hakan kuma sun yi farin ciki.

Sa’ad da yake kurkuku, Harold King ya rubuta waƙoƙi game da taron Tuna Mutuwar Yesu

Daren taron Tuna Mutuwar Yesu, shi ne mafi tsarki ga dukan mutanen Jehobah. Suna yin taron ko a mawuyacin yanayi. A shekara ta 1930, Pearl English da ’yar’uwarta Ora, sun yi tafiya na kilomita 80 don su halarci taron Tuna Mutuwar Yesu. Sa’ad da wani mai wa’azi a ƙasar waje mai suna Harold King yake cikin kurkuku a keɓe a ƙasar Sin, ya rubuta waƙoƙi game da taron Tuna Mutuwar Yesu kuma ya yi isharorin daga wani ’ya’yan itace kamar ɗinya da kuma shinkafa. Daga Gabashin Turai zuwa Amirka ta Tsakiya da Afirka, Kiristoci sun yi ƙarfin zuciya don su yi taron Tuna da Mutuwar Yesu a lokacin yaƙi ko kuma hani. Ko da a ina ne muke ko a wane yanayi, muna ɗaukaka Jehobah Allah da Yesu Kristi a wannan lokaci mai muhimmanci na Tuna da Mutuwar Yesu.