HASUMIYAR TSARO—NA NAZARI Maris 2015

Wannan fitowar tana dauke da talifofin nazari da za a yi daga 4 zuwa 31 ga Mayu, 2015.

TARIHI

Mun Gano Wata Sana’a Mai Albarka Sosai

David Cartwright da Gwen abokan rawar ballet ne a dā amma yanzu su abokan aiki ne a wata sana’a da ta fi albarka.

“Haka nan Ya Gamshe Ka Sarai”

Me ya sa littattafanmu na kwanan nan suke bayyana wasu labaran Littafi Mai Tsarki a hanya mai saukin fahimta?

Ka Ci Gaba da ‘Yin Tsaro!’

Ka karanta wannan karin haske da aka ba da a kan kwatancin Yesu na budurwai goma, an mai da hankali ga darasin da kwatancin yake koya mana.

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

A dā, ana bayyana a littattafanmu cewa wasu labaran Littafi Mai Tsarki suna wakiltar muhimman mutane ko abubuwa, amma a kwanan nan ba a yawan yin hakan. Me ya sa?

Ka Koyi Darasi Daga Kwatancin Talanti

Mun sami karin haske game da kwatancin talanti a wannan talifin.

Taimaka wa ’Yan’uwan Kristi da Aminci

Ta yaya wadanda Kristi ya ware a matsayin tumaki za su taimaka wa ’yan’uwansa da aminci?

Ku Auri “Mai Bin Ubangiji” Kadai, Umurnin Yana da Amfani Har Ila?

Wadanda suka kudura su yi shawarar Allah suna faranta masa rai kuma suna samun albarka.