Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Ci Gaba da ‘Yin Tsaro!’

Ka Ci Gaba da ‘Yin Tsaro!’

Ku yi tsaro fa, gama ba ku san rana ko sa’a ba.”—MAT. 25:13.

1, 2. (a) Mene ne Yesu ya bayyana game da kwanaki na ƙarshe? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu amsa?

 KA YI la’akari da lokacin da Yesu yake zaune bisa Dutsen Zaitun kuma yana hangen haikali da ke Urushalima daga wurin. A lokacin ne Yesu ya yi wani annabci mai ƙayatarwa game da abin da zai faru a nan gaba yayin da Bitrus da Andarawus da Yaƙub da Yohanna suke sauraronsa. Ya gaya musu abubuwa da yawa game da kwanaki na ƙarshe na wannan mugun zamani, wato a lokacin da zai yi sarauta a Mulkin Allah. Yesu ya gaya musu cewa a wannan lokaci mai muhimmanci, bawansa “mai-aminci, mai-hikima” zai kula da mabiyansa ta wajen tanadar musu da abubuwan da za su ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah.—Mat. 24:45-47.

2 Bayan ya ambata hakan, sai ya ci gaba da yin annabcin ta wajen faɗa musu wata almara game da budurwai goma. (Karanta Matta 25:1-13.) Bari mu tattauna waɗannan tambayoyi uku da ke gaba: (1) Wane darasi ne ainihi almarar take koya mana? (2) Ta yaya amintattun shafaffu suka yi amfani da darasin almarar, kuma mene ne sakamakon? (3) Ta yaya kowannenmu zai amfana daga almarar Yesu a yau?

WANE DARASI NE ALMARAR TAKE KOYA MANA?

3. A dā, ta yaya aka bayyana almarar budurwai goma a littattafanmu, mene ne sakamakon?

3 A talifin da ya gabata, mun tattauna cewa a waɗannan shekarun, bawan nan mai aminci ya fi mai da hankali ga darussan da labaran Littafi Mai Tsarki suke koya mana maimakon ma’anarsu a alamance. A dā, mun bayyana a littattafanmu cewa fitilu da mai da kwalaban man da kuma wasu abubuwa da Yesu ya ambata a almarar budurwai goma suna da ma’ana ta alama. Shin yana iya yiwuwa ne cewa irin wannan bayanin ya sa ba mu koyi ainihin darasin da ke almarar ba? Amsar wannan tambayar tana da muhimmanci.

4. A almarar Yesu, ta yaya za mu san ko wane ne (a) angon? (b) budurwoyin?

4 Bari mu bincika ainihin darasin almarar Yesu. Da farko, ka yi la’akari da waɗanda Yesu ya ambata a cikin almarar. Wane ne angon? Hakika, Yesu ne. Mun san hakan don akwai lokacin da Yesu ya ce shi ango ne. (Luk. 5:34, 35) Su wane ne budurwoyin? A cikin almarar, Yesu ya ce budurwoyin za su kasance da shiri da fitilunsu a kunne a lokacin zuwan angon. Ka tuna cewa Yesu ya ba da irin wannan shawara ga “ƙaramin garke,” wato mabiyansa shafaffu sa’ad da ya ce: “Ku kasance da ɗamara a gindi, fitilunku suna ci; ku da kanku kuma ku zama kamar mutane masu-duban hanyar ubangijinsu, sa’anda za ya komo daga bikin angonci.” (Luk. 12:32, 35, 36) Ƙari ga haka, Allah ya hure manzo Bulus da manzo Bitrus su kwatanta shafaffu na Kristi da budurwai masu tsabta ko ɗa’a. (2 Kor. 11:2; R. Yoh. 14:4) A bayyane yake cewa almarar Yesu da ke Matta 25:1-13 shawara ce da kuma kashedi ga mabiyansa shafaffu.

5. Ta yaya Yesu ya nuna lokacin da wannan almarar take cika?

5 Bayan haka, ya kamata mu yi la’akari da lokaci. Shin wane lokaci ne almarar Yesu ta cika? Sa’ad da Yesu ya kusan gama yin bayani game da almarar, ya taimaka mana mu san lokacin, ya ce: ‘Angon ya zo.’ (Mat. 25:10) Kamar yadda aka tattauna a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Yuli, 2013, an ambata ‘zuwan’ Yesu sau takwas a annabcin Yesu da aka rubuta a Matta surori na 24 da 25 kuma an yi amfani da wata kalmar Helenanci a duk wuraren da aka ambata. A duk inda Yesu ya ambata wannan kalmar, yana magana game da lokacin ƙunci mai girma sa’ad da zai zo ya yi shari’a kuma ya hukunta wannan mugun zamani. Babu shakka, wannan almarar tana cika ne a kwanaki na ƙarshe, amma zai gama cika ne a lokacin ƙunci mai girma.

6. Bisa ga mahallin, mene ne ainihin darasin almarar?

6 Mene ne ainihin darasin almarar Yesu? Ka yi la’akari da mahallin. A lokacin, Yesu ya gama magana game da ‘bawan nan mai aminci mai hikima.’ Wannan bawan yana wakiltar wani ƙaramin rukuni da suka ƙunshi shafaffu maza da za su ja-goranci mabiyan Kristi a kwanaki na ƙarshe. Daga baya, Yesu ya yi amfani da almarar wajen ba wa duka mabiyansa shafaffu a kwanaki na ƙarshe shawara cewa su ci gaba da ‘yin tsaro’ don kada su rasa gatansu na zuwa sama. (Mat. 25:13) Bari mu bincika almarar da kuma yadda shafaffu suka bi shawarar da ta ƙunsa.

TA YAYA SHAFAFFU SUKA YI AMFANI DA DARASIN ALMARAR?

7, 8. (a) Waɗanne halaye biyu ne suka taimaka wa budurwai masu hikima su kasance a shirye? (b) Ta yaya shafaffu suka kasance a shirye?

7 Sa’ad da yake faɗin almarar, ya nanata cewa budurwai masu hikima ba kamar marasa azancin ba don sun yi shirin zuwan angon. Me ya sa? Saboda waɗannan halaye guda biyu: Shiri da kuma tsaro. Wajibi ne budurwoyin su kasance a faɗake da dare don zuwan angon, kuma su tabbata cewa fitilunsu suna kunne. Budurwai masu hikima ba kamar marasa azancin ba don sun shirya da kyau, sun je da mai a cikin fitilunsu da kuma saura a cikin kwalabansu. Shin amintattun shafaffu sun kasance a shirye kamar waɗannan budurwai masu hikima?

8 Ƙwarai kuwa! A waɗannan kwanaki na ƙarshe, shafaffu Kiristoci sun bi misalin waɗannan budurwai masu hikima don suna a shirye su yi aikinsu da aminci har ƙarshen wannan zamani. Sun yi lissafin irin sadaukarwar da za su yi kuma suka ga cewa idan suna so su bauta wa Jehobah da aminci, wajibi ne su yi watsi da abin duniya. Sun kuɗiri niyya su bauta wa Jehobah da aminci domin suna ƙaunarsa da kuma Ɗansa, ba domin cewa ƙarshen wannan zamanin ya kusa ba. Sun kasance da aminci kuma suka ƙi bin halin mutanen wannan muguwar duniya da ya haɗa da cika son abin duniya da lalata da son zuciya. Shafaffu sun ci gaba da ba da haske kamar budurwai masu hikima da suke a shirye da fitilunsu, sun sa rai cewa Angon zai zo duk da cewa ana gani kamar yana jinkiri.—Filib. 2:15.

9. (a) Wane kashedi ne Yesu ya ba da game da yin gyangyaɗi? (b) Mene ne shafaffu suka yi sa’ad da aka ce: “Ga ango”? (Ka duba ƙarin bayani.)

9 Yin tsaro ne hali na biyu da ya taimaka wa budurwai su kasance a shirye. Shin zai yiwu wasu shafaffu Kiristoci su yi barci a daren da ya kamata su yi tsaro suna jiran zuwan angon? Hakika. Yesu ya ce budurwai goma sun “yi rurrumi, suka yi barci” a lokacin da kamar angon yana jinkiri. Yesu ya san cewa kasawa yana iya sa mutumin da yake son ya yi tsaro sanyin gwiwa. Shafaffu masu aminci sun bi wannan shawara kuma suka yi aiki tuƙuru don su kasance a faɗake kuma su yi tsaro. A cikin almarar, dukan budurwai sun amsa kiran da aka yi a tsakar dare cewa: “Ga ango!” Amma waɗanda suka yi tsaro ne kawai suka jimre har zuwa ƙarshe. (Mat. 25:5, 6; 26:41) Amintattu shafaffu a yau kuma fa? A waɗannan kwanaki na ƙarshe, sun ga tabbacin kuma sun amince cewa “angon” yana nan tafe. Sun jimre kuma sun kasance a shirye don zuwan Angon. a Amma yadda Yesu ya kammala almarar ya nuna cewa yana magana game da ainihin wani lokaci ne. Ta yaya muka sani?

MASU HIKIMA SUN SAMI LADA AMMA AN HUKUNTA MARASA AZANCI

10. Wace tambaya ce tattaunawa tsakanin budurwai masu hikima da marasa azanci ta tayar?

10 Sa’ad da Yesu ya kusan gama almarar, ya ce budurwai marasa azancin sun roƙi masu hikima su ɗan ba su mai don su kunna fitilunsu amma abin mamaki, budurwai masu hikima sun ƙi su taimaka. (Karanta Matta 25:8, 9.) Hakan zai iya ta da wannan tambayar: “Yaya za a yi bayin Jehobah amintattu su ƙi taimaka wa mabukata, kuma a wane lokaci ne suka yi hakan?” Za mu sami amsar idan muka san lokacin da almarar take cika. Mu tuna cewa mun sami ƙarin haske cewa Yesu, Angon, zai zo a lokacin da ƙunci mai girma yana gab da ƙarewa don ya zartar da hukunci. Saboda haka, zai iya zama cewa tattaunawa tsakanin budurwai marasa azancin da masu hikima yana nuni ga abin da zai faru gab da ƙarshen ƙunci mai girma ne. Me ya sa muka ce haka? Don a lokacin za a buga wa shafaffu hatimi na ƙarshe.

11. (a) Mene ne zai faru gab da somawar ƙunci mai girma? (b) Mene ne budurwai masu hikima suke nufi sa’ad da suka gaya wa marasa azancin su je wurin masu sayar da mai?

11 Saboda haka, kafin a soma ƙunci mai girma, za a buga wa dukan amintattun shafaffu da suke duniya hatimi na ƙarshe. (R. Yoh. 7:1-4) Daga wannan lokacin suna da tabbaci cewa za su je sama. Amma ka yi la’akari da shekarun da za su wuce kafin a soma ƙunci mai girma. Mene ne zai faru da shafaffu da suka daina kasancewa a faɗake, wato waɗanda suka yi rashin aminci? Za su rasa gatan zuwa sama. Hakika, ba za a buga musu hatimi na ƙarshe kafin a soma ƙunci mai girma ba. A lokacin, za a shafe waɗansu amintattu don su sauya su. Sa’ad da aka soma ƙunci mai girma, waɗannan shafaffu da suka yi rashin aminci za su yi mamaki sosai don za a halaka Babila Babba suna ji suna gani. A wannan lokacin ne za su ankara cewa ba su shirya don zuwan Angon ba. A sakamakon haka, za su karaya kuma su soma neman taimako, amma mene ne zai faru? Yesu ya ba da amsar a cikin almarar. Budurwai masu hikima sun ƙi ba wa budurwai marasa azanci mansu, amma sun ce musu su je su sami masu sayar da mai. Ka tuna cewa a “tsakiyar dare” ne. Shin za su iya samun masu sayar da mai a wannan lokacin? A’a. Sun riga sun makara.

12. (a) A lokacin ƙunci mai girma, shafaffu za su iya taimaka wa waɗanda aka shafe amma suka yi rashin aminci kafin buga hatimi na ƙarshe? Me ya sa? (b) Yaya waɗanda suka zama kamar budurwai marasa azanci za su ƙarasa?

12 Hakazalika, a lokacin ƙunci mai girma, shafaffu masu aminci ba za su iya taimaka wa waɗanda suka yi rashin aminci ba. Ba za su iya su taimaka wa marasa aminci ba don sun riga sun makara. Yesu ya bayyana abin da ya faru sa’ad da budurwai marasa hikima suka je neman mai da tsakar daren. Ya ce: “Ango ya zo; waɗanda suna nan a shirye suka shiga tare da shi wurin anganci: aka rufe ƙofa.” Idan Kristi ya zo gab da ƙarshen ƙunci mai girma, zai tattara amintattun shafaffu zuwa sama. (Mat. 24:31; 25:10; Yoh. 14:1-3; 1 Tas. 4:17) Hakika, za a rufe kofa ga marasa aminci waɗanda suka zama kamar budurwai marasa azanci. Za su iya yin roƙo cewa: “Ubangiji, Ubangiji, ka buɗe mana.” Amma za a ba su irin amsar da aka ba wa waɗanda aka kwatanta da akuya a lokacin shari’a: “Hakika, ina ce muku, ban san ku ba.” Abin baƙin ciki!—Mat. 7:21-23; 25:11, 12.

13. (a) Me ya sa bai kamata mu ɗauka cewa mabiyan Kristi shafaffu da yawa za su yi rashin aminci ba? (b) Me ya sa kashedin da Yesu ya bayar ya nuna cewa ya amince da shafaffu? (Ka duba hoton da ke shafi na 12.)

13 Shin Yesu yana nufin cewa shafaffu da yawa za su yi rashin aminci kuma a sauya su ne? A’a. Ka tuna cewa ya gama yi wa “bawan nan mai aminci mai hikima” kashedi cewa kada ya zama mugun bawa. Ba wai yana zaton cewa hakan zai faru ba. Hakazalika, wannan almarar tana ɗauke da muhimmin kashedi. Kamar yadda budurwai guda biyar ba su da azanci amma biyar suna da hikima, kowane shafaffe yana da damar kasancewa da shiri kuma ya yi tsaro ko kuma ya yi sakaci da kuma rashin aminci. Allah ya hure Bulus ya yi irin wannan furucin sa’ad da yake wa ’yan’uwansa shafaffu magana. (Karanta Ibraniyawa 6:4-9; gwada Kubawar Shari’a 30:19.) Ka lura cewa Bulus ya yi magana kai tsaye, amma ya kasance da tabbaci cewa ’yan’uwansa maza da mata za su sami ladan “abubuwa mafi kyau” a nan gaba. Hakazalika, Yesu ya ba da kashedin a almararsa da tabbaci. Kristi ya san cewa kowane bawansa shafaffe zai iya kasancewa da aminci kuma ya sami ladarsa mai daraja!

TA YAYA “WAƊANSU TUMAKI” NA KRISTI ZA SU AMFANA?

14. Me ya sa “waɗansu tumaki” ma za su iya amfana daga almarar budurwai goma?

14 Da yake Yesu ya yi wannan almarar budurwai don amintattun shafaffunsa ne, shin hak an yana nufin cewa babu darasin da “waɗansu tumaki” na Kristi za su koya? (Yoh. 10:16) A’a. Kada mu manta cewa darasin shi ne: “Ku yi tsaro.” Shin hakan ya shafi shafaffu ne kawai? Yesu ya taɓa cewa: ‘Abin da ni ke ce maku, ina faɗa wa duka; Ku yi tsaro.’ (Mar. 13:37) Yesu ya bukaci duka mabiyansa su yi shiri don yin ibada cikin aminci kuma su bi ƙa’idodinsa game da yin tsaro. Saboda haka, duka Kiristoci za su iya bin kyakkyawan misali da shafaffu suka kafa da kuma saka ibada kan gaba. Kowannenmu zai iya tuna cewa budurwai marasa azanci sun roƙi masu hikima su ɗan ba su mansu. Wannan roƙo kamar ihu bayan hari ne kuma darasin da muka koya shi ne wani ba zai iya kasancewa da aminci ko kuma bauta wa Jehobah a madadinmu ba, kuma wani ba zai iya yin tsaro a madadinmu ba. Kowannenmu zai ba da lissafin kansa ga Alƙali mai adalci da Jehobah ya naɗa. Wajibi ne mu kasance da shiri. Hakika, zai zo nan ba da daɗewa ba!

Roƙon man fitila ya koya mana cewa wani ba zai iya yin tsaro ko kuma kasance da aminci a madadinmu ba

15. Me ya sa dukan Kiristoci na gaskiya suke farin ciki saboda auren Kristi da amaryarsa?

15 Duka Kiristoci za su iya amfana daga abin da ya faru a almarar Yesu. Babu shakka, dukan mu muna farin ciki game da auren da Yesu ya ambata a cikin almararsa. Shafaffu za su kasance a sama kuma bayan yaƙin Armageddon za su zama amaryar Kristi. (R. Yoh. 19:7-9) A lokacin, kowa da ke zama a duniya zai amfana daga auren da za a yi a sama. Me ya sa? Don auren zai tabbatar da gwamnati da za ta magance dukan matsalolin ’yan Adam. Ko da muna da begen zuwa sama ko kuma na zama a aljanna a duniya, bari mu yi ƙudiri cewa za mu koyi darasi daga almarar Yesu na budurwai goma. Mu kasance da shiri ta wajen yin hattara kuma mu ci gaba da yin tsaro. Idan muka yi hakan, za mu gāji abubuwa masu kyau da Jehobah yake shirya mana a nan gaba!

a A cikin almarar, akwai rata tsakanin lokacin da aka yi kira cewa “Ga ango!” (aya ta 6) da kuma ainihin lokacin da angon ya zo (aya ta 10). A waɗannan kwanaki na ƙarshe, shafaffu masu yin tsaro sun fahimci alamar zuwan Yesu. Ta hakan, sun san cewa ya iso, wato yana sarauta. Suna fuskantar ƙalubalen jimrewa har sai ya zo a lokacin ƙunci mai girma.