Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TARIHI

Mun Gano Wata Sana’a Mai Albarka Sosai

Mun Gano Wata Sana’a Mai Albarka Sosai

A LOKACIN da nake shekara biyar, sai na soma koyan yin rawa, haka ma yake da Gwen. Amma ba mu wayi juna ba a lokacin. Da muke girma, mun kuɗiri niyya mu zama fitattun masu rawan ballet. Sa’ad da muka kusan zama shahararru a wannan sana’ar, sai muka yi watsi da ita. Me ya sa?

David: An haife ni a shekara ta 1945, a wani yankin Shropshire da ke ƙasar Ingila. Babana yana da gona a karkara inda ake zaman lafiya. Bayan na dawo daga makaranta, nakan ciyar da kaji, na kwashe ƙwansu, kuma in kula da shanu da tumaki. A lokacin hutu, ina taya mahaifina girbi, a wani lokaci ina amfani da ɗaya daga cikin taraktocinmu.

Amma, wani abu ya soma raba hankalina. Mahaifina ya lura cewa tun da nake yaro, ina sha’awar yin rawa a duk inda na ji ana kiɗa. Da na kai shekara biyar, sai mahaifina ya gaya wa mamata ta kai ni makarantar horar da masu rawa don in koyi wata irin rawar da ake kira tap dancing. Da malamina ya ga cewa ina da baiwar yin rawa sai ya horar da ni a yin rawar ballet. Da na kai shekara 15, an ba ni sukolashif zuwa wata makaranta da ake kira Royal Ballet School da ke birnin Landan. A nan ne na haɗu da Gwen, sai aka haɗa mu yin rawa tare.

Gwen: An haife ni a birnin Landan a shekara ta 1944. Na yi imani da Allah sa’ad da nake ƙarama. Ina karanta Littafi Mai Tsarki amma ba na fahimtar abin da ke ciki. Kafin wannan lokaci, sa’ad da nake shekara biyar na soma zuwa wani aji da ake horar da masu rawa. Bayan shekara shida sai aka yi wata gasar rawa a faɗin ƙasar Biritaniya kuma na ci gasar, hakan ya ba ni damar shiga The Royal Ballet School, sashen ɗalibai masu somawa. Makarantar tana cikin wani babban gini mai kyau da ake kira White Lodge a Richmond Park da ke bayan garin Landan. A wurin ne na yi makaranta kuma ƙwararrun malamai ne suka horar da ni a rawar Ballet. A lokacin da nake shekara 16, sai na shiga sashen manyan ɗalibai na makarantar da ke cikin birnin Landan kuma a wurin ne na haɗu da David. Cikin ’yan watanni, sai muka soma rawar ballet tare da wasu masu rawa a wani gidan wasa da ake kira Royal Opera House da ke Covent Garden, a Landan.

Sana’armu ta rawan ballet ta sa mu tafiye-tafiye zuwa ƙasashe dabam-dabam

David: Kamar yadda Gwen ta faɗa, sana’armu ta sa mun yi rawa a sanannun gidajen rawa kamar su Royal Opera House da London Festival Ballet (da yanzu ake kira English National Ballet). Ɗaya daga cikin masu tsara rawar ya kafa wani babban kamfani a Wuppertal, a ƙasar Jamus kuma ya zaɓe mu mu riƙa yin rawa. A lokacin da muke wannan sana’ar mun yi rawa sosai a filayen wasa dabam-dabam a faɗin duniya. Muna rawa tare da wasu shahararrun masu rawa kamar su Margot Fonteyn da Rudolf Nureyev. Irin wannan rayuwar gasa takan sa mutum ya riƙa yawan tunani game da kansa kuma abin da muka sa a gaba shi ne sana’armu ta yin rawa.

Gwen: Na ba da dukan hankalina da kuma ƙarfina ga yin rawa. Ni da David na da burin zama taurari da suka shahara sosai. Ina jin daɗin rattaba hannu a takarda wa mutane da karɓan furanni da kuma yadda masu kallo suke yi mana tafi. Mutane da nake tarayya da su suna yawan shaye-shaye da kuma yin lalata; na dogara ga layu sosai kamar sauran ’yan wasa.

RAYUWARMU TA CANJA GABA ƊAYA

Ranar aurenmu

David: Bayan da na yi shekaru da yawa ina yin rawa, sai na gaji da yawan tafiye-tafiye. Da yake na yi girma a karkara, sai na soma sha’awar yin rayuwa a karkara. Saboda haka, a shekara ta 1967, na daina yin rawa kuma na koma aikin noma a wata babbar gona kusa da inda iyayena suke. Mai gonar ya ba ni hayar wani ƙaramin gida. Sai na yi wa Gwen waya kuma na ce mata ta aure ni. Ta sami ƙarin matsayi a rawa kuma tana samun ci gaba sosai, wannan yanayin ya sa tsai da shawarar yin aure bai kasance mata da sauƙi ba. Amma ta yarda mu yi aure kuma muka soma yin rayuwa a karkara duk da cewa ba ta taɓa yin irin wannan rayuwa ba.

Gwen: Hakika, ya yi mini wuya in saba da rayuwa a karkara. Tatsar nono da kuma ciyar da aladu da kaji a kowane yanayi ba irin rayuwar da na saba da ita ba. David ya soma wani kwas na watanni tara a wata makarantar horar da manoma don sanin yadda ake noman zamani, hakan ya sa na kaɗaita har sai lokacin da ya dawo gida da dare. A wannan lokacin, mun haifi Gilly ’yarmu na fari. David ya ba ni shawara na koyi tuƙa mota, kuma wata rana da na ziyarci wani gari kusa da mu, sai na haɗu da Gael. Na waye ta tun lokacin da ta yi aiki a wani shago.

Rayuwa a karkara jim kaɗan bayan aure

Gael ta gayyace ni zuwa gidanta don mu sha shayi. Muka nuna wa juna hotunan aurenmu, kuma a cikin albam ɗin ta, na ga hoton da aka ɗauka kusa da wani wuri da ake kira Majami’ar Mulki. Sai na tambaye ta wane irin coci ne wannan. Na yi farin ciki sosai, da ta gaya mini cewa ita da mijinta Shaidun Jehobah ne. Na tuna cewa wata gwaggona Mashaidiya ce. Mahaifina ya ƙi jininta sosai, kuma yakan zubar da littattafanta a cikin kwandon shara. A lokacin, na rasa abin da ya sa mahaifina mai fara’a ba ya shiri wannan mace mai kirki.

Yanzu ne na sami zarafin sanin yadda imanin gwaggona ya bambanta da koyarwar coci. Gael ta nuna mini ainihin abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa. Na yi mamaki da na san cewa koyarwa da yawa kamar su Allah-Uku-Cikin Ɗaya da rashin mutuwar kurwa ba koyarwar Littafi Mai Tsarki ba ne. (M. Wa. 9:5, 10; Yoh. 14:28; 17:3) A lokacin ne na soma ganin sunan Allah, wato Jehobah, a cikin Littafi Mai Tsarki.—Fit. 6:3.

David: Gwen ta gaya mini abin da take koya. Sai na tuna cewa sa’ad da nake yaro, mahaifina ya gaya mini cewa in riƙa karanta Littafi Mai Tsarki. Saboda haka, ni da Gwen muka amince Gael da mijinta, Derrick su yi nazarin Littafi Mai Tsarki da mu. Bayan wata shida, sai muka ƙaura zuwa garin Oswestry a yankin Shropshire domin an ba mu damar hayar wata ƙaramar gona. Da muke wurin, Deirdre, wata Mashaidiya da ke yankin ta ci gaba da nazarin Littafi Mai Tsarki da mu da haƙuri. Da farko, ba ma samun ci gaba sosai, domin kula da dabbobin ba ya ba mu dama sosai. Duk da haka, abin da muke koya yana shigan zuciyarmu.

Gwen: Ya kasance mini da wuya sosai na shawo kan camfi. Littafi Mai Tsarki ya taimaka mini na fahimci yadda Jehobah yake ɗaukan waɗanda suke ‘sujada ga . . . allan sa’a.’ (Ishaya 65:11, Littafi Mai Tsarki) Ya ɗauki lokaci kafin in kawar da guru da layu da nake amfani da su, amma yin addu’a ya taimaka min sosai. Na koya cewa “dukan wanda za ya ɗaukaka kansa za ya ƙasƙanta; dukan wanda ya ƙasƙantar da kansa kuwa za ya ɗaukaka.” Hakan ya sa in san irin mutane da Jehobah yake so su bauta masa. (Mat. 23:12) Ina son in bauta wa Allah da ya ba da Ɗansa fansa a madadinmu saboda yadda yake ƙaunarmu. A wannan lokacin, na haifi ’yarmu ta biyu, kuma sanin cewa za mu iya yin rayuwa har abada a cikin aljanna a duniya ya burge ni ƙwarai.

David: A lokacin da na fahimci cikar annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki, kamar waɗanda suke cikin Matta sura 24 da kuma littafin Daniyel, sai na tabbata cewa wannan shi ne addini na gaskiya. Na fahimci cewa babu kome a wannan zamanin da yake da muhimmanci kamar kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah. Saboda haka, da shigewar lokaci sai na daina kasancewa da dogon buri. Na fahimci cewa ya kamata in ɗauki matata da ’ya’yanmu da mutunci sosai. Na koya daga Filibiyawa 2:4 cewa bai kamata na riƙa son zuciya da burin kasancewa da babbar gona ba. Maimakon haka, ya kamata na sa bauta wa Jehobah a kan gaba a rayuwata. Na daina shan taba. Amma tsara ayyukanmu don mu riƙa halartan taro da ke da nisan mil shida a ranar Asabar da yamma ba shi da sauƙi domin a wannan lokacin ne muke tatsar nono. Da taimakon Gwen ba mu taɓa fasa halartan taro ba, kuma a kowace ranar Lahadi da safe bayan mun tatse nono, mukan fita wa’azi da yaranmu.

Danginmu ba su yi farin ciki da muka soma bauta wa Jehobah ba. Mahaifin matata ya share shekara shida bai yi mata magana ba. Iyayena sun yi ƙoƙari su hana mu yin tarayya da Shaidun Jehobah.

Gwen: Jehobah ya taimaka mana mu jimre waɗannan ƙalubale. Da shigewar lokaci, ’yan’uwa da ke ikilisiyar Oswestry suka zama kamar sabuwar iyalinmu, sun taimaka mana sosai a lokacin da muke fuskantar gwaji. (Luk. 18:29, 30) Mun ba da kanmu ga Jehobah kuma mun yi baftisma a shekara ta 1972. Na soma hidimar majagaba domin ina son in taimaka wa mutane da yawa su san Jehobah.

SABUWAR HIDIMA MAI ALBARKA

David: Rayuwa ba ta kasance mana da sauƙi ba a shekarun da muka yi aikin gona. Duk da haka, mun yi ƙoƙari mu kafa wa yaranmu misali mai kyau a bautar Jehobah. Da shigewar lokaci, gwamnati ta daina taimaka wa manoma, saboda haka muka sayar da gonarmu. Da yake ba mu da gida ko aiki kuma muna tare da ’yarmu ta uku yar shekara ɗaya, mun roƙi Jehobah ya taimake mu kuma ya yi mana ja-gora. Mun tsai da shawara mu yi amfani da baiwa da muke da shi na yin rawa, sai muka buɗe gidan horar da masu rawa don mu biya bukatun iyalinmu. Da yake mun ƙuduri niyya mu sa ibada kan gaba, Jehobah ya albarkace mu. Mun yi farin ciki sosai don dukan yaranmu uku sun soma hidimar majagaba sa’ad da suka gama makaranta. Da yake Gwen majagaba ce, tana taimaka wa yaran kullum.

Bayan yaranmu Gilly da Denise suka yi aure, sai muka rufe gidan horar da masu rawa. Mun rubuta wa ofishin Shaidun Jehobah da ke ƙasar wasiƙa don a tura mu inda za mu iya taimakawa. Sun ce mu je hidima a garuruwa da ke kudu maso gabashin Ingila. Da yake Debbie ’yar autarmu ce kawai ta rage, sai na soma hidimar majagaba kamar matata. Bayan shekara biyar sai aka ce mu je mu taimaka wa wasu ikilisiyoyi da ke arewacin ƙasar. Bayan da Debbie ta yi aure, mun yi shekara goma muna yin hidima a matsayin masu aikin gine-gine a Zimbabwe da Moldova da Hungary da kuma Côte d’Ivoire. Sai muka koma Ingila don mu taimaka da aikin gini da ake yi Bethel da ke Landan. Da yake ina da masaniya game da noma, an ce in yi aiki a gonar da ke Bethel a lokacin. A yanzu, muna hidimar majagaba a arewa maso gabashin Ingila.

Mun yi farin ciki sosai sa’ad da muke aikin gine-gine a ƙasashe dabam-dabam

Gwen: Sana’armu ta farko, wato yin rawan ballet, sana’a ce mai ƙayatarwa amma ba ta sa farin ciki na gaske. Ba da kai wajen bauta wa Jehobah ita ce sana’armu ta biyu kuma ita ce mafi muhimmanci, ba za mu fasa yinta ba. Ta sa mu farin ciki na gaske kuma za ta kasance har abada. Har ila mu abokan wasa ne, amma maimakon mu riƙa yin rawa tare, muna yin wa’azi tare. Taimaka wa mutane da yawa su koyi abubuwa da za su sa su sami rai na har abada yana sa mu farin ciki matuƙa. Waɗannan “wasiƙu” na yabo sun fi sunan da mutum zai yi a wannan duniya. (2 Kor. 3:1, 2) Da a ce ba mu soma bauta wa Jehobah ba, da kawai abubuwan da za mu kasance da su su ne tarihinmu da tsofaffin hotuna da kuma takardun tsarin wasanni da muka yi a dā.

David: Yi wa Jehobah hidima ya taimaka mana sosai a rayuwa. Na san ya taimaka mini na kyautata halina a matsayin maigida da kuma mahaifi. Littafi Mai Tsarki ya ce Maryamu (Yayar Musa) da Sarki Dauda da wasu sun nuna farin cikinsu ta wajen yin rawa. Muna marmarin yin rawa tare da mutane da yawa a sabuwar duniya da Jehobah zai kawo.—Fit. 15:20; 2 Sam. 6:14.