Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Taimaka wa ’Yan’uwan Kristi da Aminci

Taimaka wa ’Yan’uwan Kristi da Aminci

Da yake kun yi wannan ga guda ɗaya a cikin waɗannan ’yan’uwana . . . mafiya ƙanƙanta, ni kuka yi wa.’—MAT. 25:40.

1, 2. (a) Waɗanne kwatance-kwatance ne Yesu ya tattauna da abokansa na kud da kud? (Ka duba hoton da ke shafi nan.) (b) Mene ne muke bukata mu sani game da kwatancin tumaki da awaki?

 YESU yana hira da abokansa na kud da kud, wato Bitrus da Andarawus da Yaƙub da kuma Yohanna. Sun kasa kunne sa’ad da yake yin kwatance-kwatancen bawan nan mai aminci mai hikima da na budurwai goma da kuma na talanti. A wannan lokacin ne Yesu ya ba da kwatanci na ƙarshe. Ya kwatanta lokacin da “Ɗan mutum” zai yi wa “dukan al’ummai” shari’a. Babu shakka, wannan kwatancin ya burge almajiransa! Sa’ad da Yesu yake ba da kwatancin, ya yi magana game da rukuni biyu, wato na tumaki da na awaki. Ya kuma ambaci wani rukuni na uku mai muhimmanci, kuma ya ce waɗanda suke rukunin sun ƙunshi ‘’yan’uwan’ “Sarkin.”—Karanta Matta 25:31-46.

2 Wannan kwatancin yana ƙayatar da bayin Jehobah tun ba yau ba, kuma hakan ba abin mamaki ba ne don a cikin kwatancin, Yesu ya nuna cewa batu ne na rai da mutuwa. Ya bayyana dalilin da ya sa wasu za su sami rai na har abada, yayin da wasu za su fuskanci halaka na dindindin. Idan muna so mu rayu, wajibi ne mu fahimci wannan kwatanci kuma mu bi umurnin da Yesu ya bayar a ciki. Saboda haka, ya kamata mu yi waɗannan tambayoyin: Ta yaya Jehobah ya sa muka sami ƙarin haske game da wannan kwatanci da sannu-sannu? Me ya sa mun amince cewa kwatancin yana nanata muhimmancin wa’azin bishara? Wane ne aka ba wa umurnin yin wa’azi? Kuma me ya sa yake da muhimmanci mu kasance da aminci ga “Sarkin” da kuma ‘’yan’uwansa’?

YADDA MUKA SAMI ƘARIN HASKE

3, 4. (a) Waɗanne muhimman abubuwa ne muke bukata mu fahimta game da kwatancin tumaki da awaki? (b) Ta yaya aka bayyana kwatancin a Zion’s Watch Tower a shekara ta 1881?

3 Idan muna so mu fahimci kwatancin tumaki da awaki da kyau, wajibi ne mu mai da hankali ga muhimman abubuwa guda uku a ciki: Su wane ne Sarkin da ’yan’uwan sarkin da tumakin da kuma awakin suke wakilta? A wane lokaci ne za a yi shari’ar, kuma wane dalili ne zai sa a yi wa mutane shari’a a matsayin tumaki ko kuma awaki?

4 A shekara ta 1881, Zion’s Watch Tower (Hasumiyar Tsaro) ta bayyana cewa “Ɗan mutum” ko kuma “Sarkin,” shi ne Yesu. Yaya Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka fahimci furucin nan “’yan’uwana” da aka ambata a ayar? A lokacin, sun ɗauka cewa sun ƙunshi waɗanda za su yi sarauta tare da Kristi, da kuma dukan ’yan Adam bayan an mai da su kamilai a duniya. Sun ɗauka cewa za a ware tumakin daga awakin a lokacin Sarautar Kristi na Shekara Dubu. Ƙari ga haka, sun gaskata cewa za a ware mutane a matsayin tumaki ne don sun yi koyi da ƙaunar Allah a dukan al’amuransu.

5. Ta yaya muka sami ƙarin haske a shekara 1920 zuwa 1929?

5 A shekara ta 1920 zuwa 1929, Jehobah ya taimaka wa bayinsa su sami ƙarin haske game da wannan kwatancin. Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Oktoba, 1923, ta bayyana cewa “Ɗan mutum” shi ne Yesu. Amma an bayyana a ciki cewa ’yan’uwan Kristi su ne waɗanda za su yi sarauta tare da shi a sama kawai kuma an kwatanta tumakin a matsayin waɗanda suke da begen yin rayuwa a duniya sa’ad da Kristi ya soma sarauta. Wane lokaci ne za a ware tumaki daga awaki? Talifin ya ce ’yan’uwan Kristi za su yi sarauta tare da shi a sama a lokacin sarautarsa na shekara dubu, tun da haka ne, rukunin da ke duniya ba za su iya taimaka musu ko kuma wulaƙanta su ba. Saboda haka, za a ware tumaki daga awaki ne kafin Kristi ya soma sarauta na shekara dubu. Talifin ya kammala da cewa dalilin da ya sa za a yi wa wasu shari’a a matsayin tumaki shi ne don sun amince da Yesu a matsayin Ubangiji kuma sun sa rai cewa Mulkin zai kyautata rayuwar ’yan Adam.

6. Ta yaya muka sami ƙarin haske a shekara ta 1995?

6 Saboda wannan ƙarin haske da aka samu, bayin Jehobah sun ɗauka cewa za a yi wa mutane shari’a a matsayin tumaki ko kuma awaki a kwanaki na ƙarshe ne, kuma za a yi hakan ne bisa ga halin da suka nuna sa’ad da aka yi musu wa’azin bishara. Amma a shekara ta 1995, an sami ƙarin haske. A wasu talifofi biyu na Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Oktoba, 1995, an tattauna cewa akwai kamanni tsakanin kalmomin da Yesu ya ambata a Matta 24:29-31 (karanta) da kuma na Matta 25:31, 32. (Karanta.) a A talifin farko na mujallar, an bayyana cewa za a yi shari’a bisa tumaki da awaki ne a nan gaba. Yaushe ke nan? Bayan an soma “babbar tsanani” da aka ambata a Matta 24:29, 30 kuma Ɗan mutum ya “zo cikin darajarsa.” . . . Sa’an nan, a ƙarshen zamani, Yesu za ya yi shari’a kuma ya zartar da hukunci.

7. Wane bayani mai ƙayatarwa ne muka samu yanzu?

7 A yau, mun sami bayani mai ƙayatarwa game da kwatancin tumaki da awaki. Game da waɗanda aka ambata a cikin kwatancin, Yesu shi ne “Ɗan mutum,” wato Sarkin. ‘’Yan’uwan’ Sarkin su ne shafaffu maza da mata da za su yi sarauta tare da Kristi a sama. (Rom. 8:16, 17) Mutane daga dukan al’ummai ne “tumaki” da “awaki.” Ba a shafe waɗannan da ruhu mai tsarki ba. Wane lokaci ne za a yi shari’ar? Za a yi shari’ar gab da ƙarshen ƙunci mai girma da ke nan tafe. Wane dalili ne zai sa a yi wa mutane shari’a a matsayin tumaki ko kuma awaki? Hakan ya dangana ne ga yadda suka bi da ’yan’uwan Kristi shafaffu da suka rage a duniya. Da yake ƙarshen wannan zamanin ya kusa sosai, muna farin ciki cewa Jehobah ya sa mun sami ƙarin haske game da wannan kwatancin da kuma sauran kwatance-kwatancen da ke Matta surori 24 da 25 da sannu-sannu, ko ba haka ba?

TA YAYA KWATANCIN YA NUNA MUHIMMANCIN WA’AZIN BISHARA?

8, 9. Me ya sa aka ce tumakin suna da “adalci”?

8 Yesu bai ambata wa’azin bishara kai tsaye a kwatancin tumaki da awaki ba. Shin me ya sa za mu iya cewa ya nanata muhimmancin wa’azin bishara?

9 Ɗa farko, ka lura cewa Yesu ya yi amfani da wannan kwatancin don mu koyi darasi. Hakan ya nuna cewa tumaki da awaki da ya ambata ba na zahiri ba ne. Hakazalika, ba ya nufin cewa wajibi ne duk wanda aka ware a matsayin tunkiya ya ciyar da ɗaya daga cikin ’yan’uwansa ko kuma ya samar masa da tufafi ko ya kula da shi ko kuma ya kai masa ziyara sa’ad da yake cikin kurkuku. A maimakon haka, yana nuna yadda tumakin, wato mutane daga al’ummai za su bi da ’yan’uwansa ne. Ya ce tumakin suna da “adalci” don sun amince cewa Yesu yana da rukunin ’yan’uwa shafaffu da suka rage a duniya. Ƙari ga haka, suna taimaka wa shafaffun a waɗannan miyagun kwanaki na ƙarshe.—Mat. 10:40-42; 25:40, 46; 2 Tim. 3:1-5.

10. Ta yaya tumakin suke yi wa ’yan’uwan Kristi alheri?

10 Na biyu, ka yi la’akari da yanayin da Yesu ya yi wannan maganar. Yana tattauna alamar zuwansa da kuma ƙarshen zamani ne. (Mat. 24:3) Sa’ad da Yesu ya soma wannan jawabin, ya ambata cewa alamar za ta ƙunshi wani fasali na musamman, wato za a yi wa’azin bisharar Mulki har “iyakar duniya.” (Mat. 24:14) Kafin ya ba da kwatancin tumaki da awaki, ya ba da kwatancin talanti. Kamar yadda aka ambata a talifin da ya gabata, Yesu ya ba da wannan kwatancin don ya nanata wa almajiransa shafaffu, wato ‘’yan’uwansa’ cewa wajibi ne su yi wa’azin bishara da ƙwazo. Amma yin wa’azin bishara ga “dukan al’ummai” kafin ƙarshen zamani ba ƙaramin aiki ba ne, kuma shafaffun da suka rage a duniya kaɗan ne kawai. Kwatancin tumaki da awaki ya nuna cewa za a taimaka wa shafaffu a wannan aikin. Saboda haka, hanya ɗaya ta musamman da waɗanda aka ware a matsayin tumaki suke wa ’yan’uwan Kristi alheri ita ce ta taimaka musu a yin wa’azin bishara. Mene ne wannan taimakon ya ƙunsa? Shin ba da taimakon kuɗi da kayayyaki da kuma ƙarfafa ne kawai, ko kuma akwai wani abin da ake bukata?

SU WANE NE YA KAMATA SU YI WA’AZI?

11. Wace tambaya ce wasu za su iya yi, kuma me ya sa?

11 A yau, a cikin almajiran Yesu miliyan takwas, yawancin ba shafaffu ba ne. Ba sa cikin waɗanda suka karɓi talanti da Yesu ya ba wa mabiyansa shafaffu. (Mat. 25:14-18) Saboda haka, wasu za su iya yin wannan tambayar, ‘Shin umurnin yin wa’azin bishara ya shafi waɗanda ba shafaffu ba kuwa?’ Hakika. Ga wasu dalilai da ya sa muka ce hakan.

12. Wane darasi ne muka koya daga kalmomin Yesu da ke Matta 28:19, 20?

12 Yesu ya umurci dukan almajiransa su yi wa’azi. Bayan Yesu ya tashi daga mutuwa, ya gaya wa mabiyansa cewa su almajirtar da mutane kuma su koya musu yadda za su kiyaye “dukan iyakar abin” da ya umurta. Wannan umurnin ya haɗa da yin wa’azin bishara. (Karanta Matta 28:19, 20.) Saboda haka, wajibi ne dukan  almajiran Kristi su yi wa’azi, ko da suna da begen zuwa sama ko na zama a aljanna a duniya.—A. M. 10:42.

13. Mene ne wahayin da aka saukar wa Yohanna ya nuna, kuma me ya sa?

13 Littafin Ru’ya ta Yohanna ya nuna cewa shafaffu da waɗanda ba shafaffu ba za su yi wa’azin bishara. Yesu ya saukar wa manzo Yohanna wahayin ‘amaryar,’ wato shafaffun mutane guda 144,000 da za su yi sarauta da Kristi a sama, suna gaya wa mutane su “ɗiba ruwa na rai kyauta.” (R. Yoh. 14:1, 3; 22:17) Wannan ruwan yana wakiltar abubuwan da Jehobah ya tanadar ta fansar Kristi don kawo ƙarshen zunubi da mutuwa. (Mat. 20:28; Yoh. 3:16; 1 Yoh. 4:9, 10) Fansar tana da muhimmanci sosai a wa’azin bishara da muke yi, kuma shafaffu ne ke kan gaba a koya wa mutane yadda za su amfana daga fansar. (1 Kor. 1:23) Amma Yohanna ya ga wasu da ba sa cikin shafaffu, wato amaryar. Su ma an umurce su su riƙa gaya wa mutane su “zo.” Suna bin wannan umurnin kuma suna gayyatar mutane su zo su ɗiba ruwa na rai. Wannan rukuni na biyun su ne waɗanda suke da begen yin rayuwa a aljanna a duniya. Saboda haka, wannan wahayin ya nuna dalla-dalla cewa dukan waɗanda suka amsa wannan kiran cewa “zo” suna da hakkin yi wa mutane wa’azin bishara.

14. Mene ne bin “shari’ar Kristi” ya ƙunsa?

14 Wajibi ne dukan waɗanda suke bin “shari’ar Kristi” su yi wa’azi. (Gal. 6:2) Jehobah ya bukaci dukan waɗanda suke bauta masa su bi tsarin doka iri ɗaya. Alal misali, ya gaya wa Isra’ilawa cewa: “Doka ce ɗaya ga haifaffen gida, da baƙo wanda ke sauke a wurinku.” (Fit. 12:49; Lev. 24:22) Ko da yake Kiristoci ba sa bin dokar da aka ba da ta hannun Musa. Amma dukanmu muna bin “shari’ar Kristi” ko da mu shafaffu ne ko a’a. Wannan shari’ar ta ƙunshi dukan abubuwan da Yesu ya umurta. Ya umurci mabiyansa su riƙa ƙaunar Allah da mutane. (Yoh. 13:35; Yaƙ. 2:8) Wata hanya ta musamman da za mu nuna cewa muna ƙaunar Allah da Kristi da kuma maƙwabtanmu ita ce ta yin wa’azin bishara ta Mulki.—Yoh. 15:10; A. M. 1:8.

15. Me ya sa za mu iya cewa umurnin da Yesu ya bayar ya shafi dukan mabiyansa?

15 Abin da Yesu ya faɗa wa mutane ƙalilan zai iya shafan mutane da yawa. Alal misali, almajirai 11 ne kawai suke tare da Yesu a lokacin da ya yi alkawari da mabiyansa cewa za su yi sarauta tare da shi, amma alkawarin ya shafi dukan shafaffu 144,000. (Luk. 22:29, 30; R. Yoh. 5:10; 7:4-8) Hakazalika, Yesu ya ba da umurnin yin wa’azi ga mabiyansa ƙalilan ne, wato waɗanda ya bayyana a garesu bayan ya tashi daga mutuwa. (A. M. 10:40-42; 1 Kor. 15:6) Amma dukan amintattun almajiransa na ƙarni na farko sun fahimci cewa umurnin ya shafe su, duk da cewa ba sa wurin a lokacin da Yesu yake ba da umurnin. (A. M. 8:4; 1 Bit. 1:8) Haka ma yake a yau, alal misali, a cikin mutane miliyan takwas da ke wa’azin bishara ta Mulki a yau, babu wanda ya ji Yesu sa’ad da yake ba da umurnin. Amma dukanmu mun fahimci cewa wajibi ne mu ba da gaskiya ga Kristi kuma mu yi wa’azin bishara.—Yaƙ. 2:18.

KASANCEWA DA AMINCI YANA DA MUHIMMANCI YANZU

16-18. Ta yaya waɗanda suke so su kasance cikin tumaki za su iya taimaka wa ’yan’uwan Kristi, kuma me ya sa yake da muhimmanci su yi hakan yanzu?

16 Shaiɗan yana yaƙi da ’yan’uwan Kristi shafaffu da suka rage a duniya, kuma zai ci gaba da tsananta musu don lokacinsa “kaɗan ya rage.” (R. Yoh. 12:9, 12, 17) Shafaffu suna ja-gorar wa’azin bishara mafi girma a tarihi duk da tsanani da suke fuskanta. Babu shakka, Yesu yana tare da su kuma yana ja-gorarsu.—Mat. 28:20.

17 Tumakin, wato mabiyan Yesu da za su gāji duniya suna ƙaruwa kuma suna taimaka wa ’yan’uwan Kristi a wa’azin bishara da kuma a wasu hanyoyi. Alal misali, suna ba da gudummawar kuɗi kuma suna taimakawa a gina Majami’un Mulki, Majami’un Taro da kuma ofisoshin Shaidun Jehobah a faɗin duniya. Ƙari ga haka, suna bin umurnan waɗanda bawan nan mai aminci ya naɗa don su yi ja-gora.—Mat. 24:45-47; Ibran. 13:17.

Waɗanda suke kamar tumaki suna taimaka wa ’yan’uwan Kristi a hanyoyi dabam-dabam (Ka duba sakin layi na 17)

18 Nan ba da daɗewa ba, mala’iku za su sake “iskoki huɗu na duniya,” wato ƙunci mai girma. Hakan zai faru bayan an buga wa sauran ’yan’uwan Kristi da suka rage a duniya hatimi na ƙarshe. (R. Yoh. 7:1-3) Kafin a soma yaƙin Armageddon, shafaffu za su je sama. (Mat. 13:41-43) Saboda haka, yanzu ne ya kamata mu taimaka wa ’yan’uwan Kristi da aminci idan muna so a yi mana shari’a a matsayin tumaki.

a Za ka sami cikakken bayani game da wannan kwatancin a waɗannan talifofin, “Ina Yadda Zaka Tsaya A Gaban Kursiyin Shari’a?” da kuma “Wane Gaba Ke Ga Tumaki Da Awaki?” da ke Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Nuwamba, 1995.