Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Dattawa, Mene ne Ra’ayinku Game da Horar da Wasu?

Dattawa, Mene ne Ra’ayinku Game da Horar da Wasu?

Kome da lokacinsa.” —M. WA. 3:1, New World Translation.

1, 2. Mene ne masu kula da da’ira suka lura da shi a ikilisiyoyi da dama?

WANI mai kula da da’ira ya kusan kammala taron da yake yi da rukunin dattawa. Sa’ad da ya kalle su, ya yi la’akari cewa suna aiki da ƙwazo duk da cewa wasu daga cikin su tsarar mahaifinsa ne. Ya yaba musu ƙwarai. Amma akwai abin da ya dame shi, saboda haka sai ya tambaye su, “’Yan’uwa, a waɗanne hanyoyi ne kuka horar da wasu don su yi hidima a cikin ikilisiya?” A nan ne suka tuna cewa a ziyarar da ya yi kafin wannan lokacin, ya ƙarfafa su su riƙa mai da hankali wajen horar da wasu. Sai ɗaya daga cikin dattawan ya ce, “Hakika, ba mu yi ƙoƙari ba.” Sauran dattawan suka kaɗa kai don abin da ya faɗa gaskiya ne.

2 Idan kai dattijo ne, babu shakka za ka iya fahimtar yanayin dattawan da ke wannan taron. Masu kula da da’ira a faɗin duniya sun lura cewa a ikilisiyoyi da yawa, ana bukata a yi aiki tuƙuru wajen horar da ’yan’uwa maza, matasa da manya don su taimaka wajen kula da garken. Wannan ba ƙaramin aiki ba ne. Me ya sa?

3. (a) Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa horar da wasu yana da muhimmanci, kuma me ya sa ya dace dukanmu mu ɗauki wannan batun da muhimmanci? (Ka duba ƙarin bayani.) (b) Me ya sa wasu dattawa suke gani cewa horar da wasu yana da wuya?

3 Da yake kai dattijo ne, ka san cewa horar da ’yan’uwa yana da muhimmanci. * Ƙari ga haka, ka san cewa idan har za a cim ma burin inganta ibadar ’yan’uwa a cikin ikilisiya kuma a kafa sababbin ikilisiyoyi, wajibi ne a horar da ƙarin ’yan’uwa maza don su yi hidima. (Karanta Ishaya 60:22.) Ban da haka, Kalmar Allah ta ƙarfafa ka ka ‘koyar da waɗansu.’ (Karanta 2 Timotawus 2:2.) Duk da haka, kamar dattawan da aka ambata a farkon wannan talifin, yin hakan zai iya kasance da wuya a gare ka. Idan ka yi la’akari da hidimomin da kake yi don ka biya bukatun iyalinka, da cika farillan aikinka da na ikilisiya, da kuma wasu abubuwan da suke bukata a mai da musu hankali, za ka iya tunani cewa samun lokacin horar da wasu a cikin ikilisiya zai yi wuya. Saboda haka, bari mu tattauna abin da ya sa yake da muhimmanci dattawa su nemi lokaci don horar da wasu.

HORARWA TANA DA MUHIMMANCI

4. Wane abu ne zai iya sa wasu dattawa su yi jinkirin horar da ’yan’uwa maza?

4 Wane dalili ɗaya ne yake sa wasu dattawa su kasa keɓe lokaci don horar da wasu? Wataƙila, wasu suna tunani cewa: ‘Horarwa yana da amfani, amma ba aikin gaggawa ba ne kamar wasu ayyuka a cikin ikilisiya da suke bukata a mai da wa hankali nan da nan. Ko da ban horar da wasu yanzu ba, ’yan’uwa za su ci gaba da samun ƙarfafa a cikin ikilisiya.’ Gaskiya ne cewa kana bukatar ka yi wasu ayyuka da dama yanzu, amma idan ka ci gaba da yin jinkiri wajen horar da ’yan’uwa maza, hakan zai iya saka ikilisiya cikin hadari.

5, 6. Wane darasi ne za mu iya koya daga kwatancin direba da yadda yake kula da injin motarsa, kuma ta yaya hakan ya shafi horar da wasu a cikin ikilisiya?

5 Ka yi la’akari da wannan misali: Direba ya san cewa yana bukata ya riƙa canja man injin motarsa a kai a kai don motar ta kasance da inganci. Amma zai iya ɗauka cewa hakan ba shi da muhimmanci kamar zuba man fetur, don idan bai sha mai ba, motar za ta tsaya cik. Saboda haka, zai iya tunani cewa: ‘Idan ban sami damar canja man inji ba, hakan ba zai hana motar tafiya na ɗan lokaci ba.’ Shin wannan tunanin yana da kyau ne? Idan direba ba ya canja man inji a lokacin da ya dace, nan ba da daɗewa ba motar za ta lalace. Idan hakan ya faru, zai ɓata lokaci kuma zai kashe kuɗi sosai wajen gyara motar. Shin wane darasi ne muka koya?

6 Dattawa suna da ayyuka da dama da ya kamata su yi cikin gaggawa; kuma idan ba su yi waɗannan ayyukan ba, hakan zai hana ruwa gudu a cikin ikilisiya. Kamar yadda direba yake zuba man fetur a motarsa kowane lokaci, wajibi ne dattawa su mai da hankali ga “mafifitan al’amura.” (Filib. 1:10) Amma, wasu dattawa suna yawan mai da hankali ga waɗannan bukatu na gaggawa kuma su yi watsi da horar da wasu. Za a iya kwatanta wannan horarwa da canja man inji. Idan dattawa suka ci gaba da yin watsi da horar da ’yan’uwa maza, nan ba da daɗewa ba ikilisiya ba za ta kasance da isashen ’yan’uwa da suka ƙware ba.

7. Yaya ya kamata mu ɗauki dattawa da suke ba da lokacinsu don horar da wasu?

7 Saboda haka, ya kamata mu daina tunani cewa horarwa bai da muhimmanci sosai. Dattawa masu hangen nesa da suke horar da ’yan’uwa maza da ba su ƙware ba suna nuna hikima kuma suna taimaka wa ikilisiya sosai. (Karanta 1 Bitrus 4:10.) Ta yaya ikilisiya take amfana?

HORAR DA ’YAN’UWA MAZA JARI NE

8. (a) Waɗanne halaye da kuma tunani ne za su sa dattawa su horar da ’yan’uwa maza? (b) Wane aiki na gaggawa ne dattawa da suke hidima a wurare da ake bukatar masu shela suke da shi? (Ka duba akwatin nan “Aiki na Gaggawa.”)

8 Wajibi ne dattawa, har da waɗanda suka ƙware sosai, su kasance da tawali’u kuma su fahimta cewa tsufa zai hana su yin ayyukan da ya kamata su yi a cikin ikilisiya da sannu a hankali. (Mi. 6:8) Ƙari ga haka, ya kamata su yi la’akari cewa wani yanayi zai iya hana su yin hidima a cikin ikilisiya saboda ‘sa’a da tsautsayi.’ (M. Wa. 9:11, 12, Littafi Mai Tsarki; Yaƙ. 4:13, 14) Da yake dattawa masu hangen nesa suna ƙaunar tumakin Jehobah, suna koya wa ’yan’uwa maza da ke tasowa wasu abubuwa da suka koya a hidimarsu.—Karanta Zabura 71:17, 18.

9. Wane abu da zai faru a nan gaba ne ya nuna cewa horar da ’yan’uwa maza tana da muhimmanci?

9 Ta wace hanya ce kuma dattawa da suke horar da wasu suke taimaka wa ’yan’uwa? Suna kāre ikilisiya. Ta yaya? Ƙoƙarin da suke yi yana sa a sami ƙarin ’yan’uwa maza da suke shirye su taimaka wa ’yan’uwa a ikilisiya su kasance da bangaskiya da kuma haɗin kai a yanzu da kuma a nan gaba, musamman ma a lokacin ƙunci mai girma. (Ezek. 38:10-12; Mi. 5:5, 6) Saboda haka, dattawa, don Allah muna roƙon ku ku riƙa horar da ’yan’uwa maza yayin da kuke hidima, somawa daga yau.

10. Mene ne dattijo yake bukata ya yi don ya sami lokacin horar da ’yan’uwa maza?

10 Ko da yake mun san cewa kula da muhimman batutuwa a cikin ikilisiya wataƙila ba zai iya sa ka sami lokaci ba. Saboda haka, kana bukata ka tsara ayyukanka don ka sami lokacin horar da wasu. (M. Wa. 3:1) Yin hakan jari ne.

KA SHIRYA DAN’UWAN DA KAKE HORARWA

11. (a) Mene ne shawarwarin dattawa daga ƙasashe dabam-dabam suka nuna? (b) Bisa ga Misalai 15:22, me ya sa bin shawarwarin wasu dattawa zai kasance da amfani?

11 A kwanan baya, an tambayi wasu dattawa da suka yi nasara a horar da ’yan’uwa maza matakan da suka ɗauka don su cim ma hakan. * Ko da yake yanayin ’yan’uwan ya bambanta sosai, amma shawarwarin da suka bayar kusan iri ɗaya ne. Mene ne hakan ya nuna? Ya nuna cewa horarwa bisa Littafi Mai Tsarki yana da amfani a ‘ko’ina a cikin kowace ikilisiya,’ kamar yadda yake a zamanin manzo Bulus. (1 Kor. 4:17) Saboda haka, za mu tattauna shawarwarin da waɗannan dattawan suka bayar a wannan talifin da kuma a na gaba.—Mis. 15:22.

12. Wane yanayi ne dattijo yake bukata ya nema, kuma me ya sa?

12 Dattijo yana bukata ya nemi yanayin da ya dace don ya horar da ɗan’uwa. Mai lambu yana bukata ya nome lambun kafin ya soma watsa iri, hakazalika, dattijo yana bukata ya shirya ko kuma ƙarfafa ɗan’uwan da yake so ya horar kafin ya koya masa yadda ake yin wasu ayyuka. Shin ta yaya dattijo zai nemi yanayin da ya dace don horar da wasu? Ta wajen bin tsarin da wani annabi na zamanin dā ya bi. Wane tsari ke nan?

13-15. (a) Wane aiki ne aka sa annabi Sama’ila ya yi? (b) Yaya Sama’ila ya yi aikinsa? (Ka duba hoton da ke shafi na 3.) (c) Me ya sa ya kamata dattawa a yau su yi la’akari da tsarin da Sama’ila ya bi?

13 Sama da shekaru 3,000 da suka shige, Jehobah ya gaya wa annabi Sama’ila sa’ad da ya tsufa cewa: “Gobe war haka zan aike maka wani mutum daga cikin ƙasar Banyamin, za ka shafe shi da mai kuma shi zama shugaban jama’ata Isra’ila.” (1 Sam. 9:15, 16) Sama’ila ya san cewa nan ba da daɗewa ba, zai daina ja-gorar al’ummar Isra’ila don Jehobah ya umurce shi ya shafe wani da zai maye gurbinsa. Babu shakka, Sama’ila ya yi tunani a kan yadda zai shirya wannan mutumin don ya cika aikinsa. Wani tunani ya zo masa sai ya tsara yadda zai cim ma shirinsa.

14 Washe gari, sa’ad da Sama’ila ya ga Saul, sai Jehobah ya gaya wa annabi Sama’ila cewa: “Ga mutumin.” Sai Sama’ila ya soma aiwatar da shirinsa. Ya gayyaci Saul zuwa cin abinci a wani ɗaki. Sama’ila ya ba wa Saul da baransa wurin zama mafi kyau da nama mai kyau kuma ya ce: “Ka ci; gama an ajiye maka ita kan ayananniyar sa’a.” Bayan haka, Sama’ila da Saul suka tafi gidan Sama’ila, suna taɗi yayin da suke tafiya. Da yake Sama’ila yana so ya yi amfani da wannan yanayi da abinci mai daɗi da kuma ɗan yawon da suka yi, sai ya gayyaci Saul zuwa bene, wato gidan sama. A wannan yammar da ake iska mai sanyi, Sama’ila ya riƙa tattaunawa da “Saul a bisa bene,” har suka yi barci. Washe gari, Sama’ila ya shafe Saul, ya yi masa sumba kuma ya ƙara ba shi umurni. Bayan ya shirya Saul don abubuwan da za su faru, sai suka yi ban kwana.—1 Sam. 9:17-27; 10:1.

15 Hakika, naɗa mutum ya zama sarkin al’umma ba ɗaya ba ne da horar da wani ɗan’uwa ya zama dattijo ko kuma bawa mai hidima a cikin ikilisiya. Duk da haka, dattawa a yau za su iya koyan darussa da dama daga abin da Sama’ila ya yi. Bari mu tattauna biyu daga cikinsu.

MASU KOYARWA DA SON RAI, ABOKAI NA ƘWARAI

16. (a) Yaya Sama’ila ya ji sa’ad da Isra’ilawa suka ce suna so a naɗa musu sarki? (b) Mene ne ra’ayin Sama’ila sa’ad da Jehobah ya ce masa ya naɗa Saul sarki?

16 Ka horar da ɗan’uwan da son rai, kada ka yi jinkiri. Sa’ad da Sama’ila ya ji cewa Isra’ilawa suna so a naɗa musu sarki, bai ji daɗi ba don ya ɗauka cewa ba sa son sa. (1 Sam. 8:4-8) Saboda haka, ya yi jinkirin yin abin da mutanen suke so. Amma, sau uku Jehobah ya gaya masa ya saurare su. (1 Sam. 8:7, 9, 22) Duk da haka, Sama’ila bai riƙe mutumin da zai ɗauki matsayinsa a zuciya ba. Annabin ya yi biyayya ga Jehobah sa’ad da ya gaya masa ya naɗa Saul sarki, kuma ya yi hakan da zuciya ɗaya ba kawai don ya bi umurni ba.

17. Ta yaya dattawa a yau suke yin koyi da Sama’ila, kuma ta yaya hakan yake sa su farin ciki?

17 Kamar Sama’ila, dattawa da suka ƙware a yau suna bin waɗanda suke horarwa da hankali. (1 Bit. 5:2) Irin waɗannan dattawa ba sa fargabar horar da ’yan’uwa maza don suna tsoron cewa ’yan’uwan za su karɓe gatansu. Dattawa masu kirki suna ɗaukan ’yan’uwa da suke horarwa kamar “abokan aiki,” ba abokan gāba ba. Suna gani cewa waɗannan ’yan’uwan za su taimaka wa ikilisiya. (2 Kor. 1:24; Ibran. 13:16) Waɗannan dattawa za su yi farin ciki sosai sa’ad da suka lura da yadda ’yan’uwan suke amfani da abubuwan da aka koya musu wajen taimaka wa ikilisiya.—A. M. 20:35.

18, 19. Ta yaya dattijo zai iya shirya ɗan’uwan da yake horarwa, kuma me ya sa ya dace dattijo yin hakan yake da muhimmanci?

18 Ka mai da ɗan’uwan abokinka. A ranar da Sama’ila ya haɗu da Saul, da a ce ya ɗauki santalin mai ya tsiyaye a kan Saul nan da nan kuma ya ce masa ya je ya soma hidima a matsayin sarki, da Saul bai kasance a shirye don aikin da ke gabansa ba. A maimakon haka, Sama’ila ya ɗauki lokaci don ya shirya Saul da sannu a hankali. Bayan sun ci abinci, suka ɗan zagaya, suka tattauna kuma suka huta sosai ne Sama’ila ya ga cewa ya dace ya shafe Saul.

Horarwa tana somawa da ƙulla abota (Ka duba sakin layi na 18, 19)

19 Hakazalika, ya kamata dattijo a yau ya nemi yanayin da ya dace kuma ya ƙulla abota da ɗan’uwan da yake so ya horar. Matakan da dattijo zai ɗauka don ya ƙulla abota da ɗan’uwan da yake horarwa ya dangana ga ƙasa da kuma al’ada. Duk da haka, ko a wace ƙasa kake, idan a matsayinka na dattijo da ke da ayyuka da yawa ka keɓe lokaci don ƙulla abota da ɗan’uwan da kake horarwa, hakan zai sa ya san cewa kana ƙaunarsa. (Karanta Romawa 12:10.) Hakika, ɗan’uwan zai ji daɗi don yadda kake bi da shi.

20, 21. (a) Ta yaya ake sanin dattijon da yake yin nasara a horar da wasu? (b) Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

20 Dattawa, ya kamata ku tuna cewa dattijo da ke nasara shi ne dattijon da ke son horar da ’yan’uwa da kuma ƙaunar wanda yake horarwa. (Gwada hakan da Yohanna 5:20.) Ɗan’uwan da kake horarwa zai yi saurin gane cewa kana ƙaunarsa kuma hakan zai sa ɗan’uwan ya bi umurnin da ka ba shi. Saboda haka, dattawa ku yi ƙoƙari ku ƙulla abota da waɗanda kuke horarwa.—Mis. 17:17; Yoh. 15:15.

21 Bayan dattijo ya shirya zuciyar ɗan’uwan da yake horarwa, sai ya koya masa abubuwan da suka wajaba. Ta yaya dattijon zai yi hakan? Za mu tattauna wannan a talifi na gaba.

^ sakin layi na 3 An wallafa wannan talifin da kuma na gaba musamman don dattawa ne. Duk da haka, ya kamata kowa a cikin ikilisiya ya mai da hankali ga batun. Me ya sa? Hakan zai ƙarfafa dukan maza da suka yi baftisma su san cewa suna bukatar horarwa kafin su yi hidima a cikin ikilisiya. Kuma yayin da ake cim ma hakan, kowa zai amfana.

^ sakin layi na 11 Waɗannan dattawan suna zama a Ostareliya da Bangladesh da Belgium da Brazil da Faransa da French Guiana da Japan da Koriya da Meziko da Namibiya da Nijeriya da Réunion da Rasha da Afirka ta Kudu da kuma Amirka.