Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Yadda Dattawa Suke Horar da Wasu don Su Kware

Yadda Dattawa Suke Horar da Wasu don Su Kware

“Abubuwan da ka ji daga gare ni . . . sai ka danƙa ma mutane masu-aminci.”—2 TIM. 2:2.

1. (a) Mene ne bayin Allah suka sani game da horarwa tun da daɗewa, kuma ta yaya hakan yake da amfani a yau? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

TUN da daɗewa, bayin Allah sun san cewa horar da mutane yana sa a sami ci gaba. Alal misali, uban iyali Ibrahim ya tsara mazajen gidansa, ‘horarrun mutane’ don su ceci Lutu kuma sun yi nasara. (Far. 14:14-16) A zamanin Sarki Dauda, an tsara mawaƙa kuma an ‘koya masu su yi waƙa ga Ubangiji.’ (1 Laba. 25:7) A yau, muna yaƙi da Shaiɗan da mabiyansa don mu kāre dangantakarmu da Jehobah. (Afis. 6:11-13) Ƙari ga haka, muna aiki da ƙwazo don mu ɗaukaka Jehobah ta wurin sanar da mutane game da sunansa. (Ibran. 13:15, 16) Saboda haka, idan muna so mu yi nasara kamar bayin Allah na dā, muna bukatar horarwa. Jehobah ya danƙa wa dattawan ikilisiya hakkin horar da wasu. (2 Tim. 2:2) Ta yaya dattawa da suka ƙware suke horar da ’yan’uwa maza don su ƙware kuma su kula da ’yan’uwa a ikilisiya?

KA ƘARFAFA ƊAN’UWAN YA SO JEHOBAH DA ZUCIYA ƊAYA

2. Kafin dattijo ya koya wa ɗan’uwa wasu abubuwa, mene ne ya kamata ya yi, kuma me ya sa?

2 Za a iya kwatanta dattijo da manomi. Kafin manomi ya soma shuki, wataƙila zai bukaci ya saka taki a gonar don ta ba da amfani. Hakazalika, kafin ka koya wa ɗan’uwa da bai ƙware ba wasu abubuwa, za ka iya tattauna wasu darussa daga Littafi Mai Tsarki da shi. Ta hakan, za ka taimaka masa ya amince da horarwa da za ka yi masa.—1 Tim. 4:6.

3. (a) Ta yaya za ka iya yin amfani da furucin Yesu da ke Markus 12:29, 30 sa’ad da kake tattaunawa da wanda kake horarwa? (b) Ta yaya addu’a da dattijo ya yi zai shafi wanda yake horarwa?

3 Idan kana so ka san yadda gaskiyar ta shafi halinsa da ayyukansa, za ka iya yi masa wannan tambayar, ‘Ta yaya ba da kanka ga Jehobah ya shafi rayuwarka?’ Wannan tambayar za ta iya sa ku yi taɗi sosai game da bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya. (Karanta Markus 12:29, 30.) Bayan irin wannan tattaunawar, za ka iya yin addu’a ga Jehobah cewa ya ba wa ɗan’uwan ruhu mai tsarki don ya ƙware. Idan ɗan’uwan ya ji kana wannan addu’ar daga zuciyarka, hakan zai ƙarfafa shi.

4. (a) Ka ba da misalai daga Littafi Mai Tsarki da za su taimaka wa ɗan’uwa ya ƙarfafa dangantakarsa da Jehobah. (b) Wane maƙasudi ne ya kamata dattawa su kasance da shi sa’ad da suke horar da wasu?

4 Zai dace ka tattauna wasu labaran Littafi Mai Tsarki da za su taimaka masa ya san muhimmancin kasancewa mai taimaka wa mutane, mai riƙe amana kuma mai tawali’u. (1 Sar. 19:19-21; Neh. 7:2; 13:13; A. M. 18:24-26) Kamar yadda taki zai sa ƙasa ya ba da amfani, waɗannan halayen za su taimaka wa ɗan’uwan ya inganta ibadarsa ga Jehobah. Wani dattijo daga Faransa mai suna Jean-Claude ya ce: “Maƙasudina shi ne in taimaka wa ɗan’uwan da nake horarwa ya kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah. Nakan nemi zarafi mu karanta wani nassi tare don ‘buɗe idanun’ ɗan’uwan ya fahimci abubuwa masu ban ‘al’ajabi’ da ke cikin Kalmar Allah.” (Zab. 119:18) Ta yaya za ka iya ƙarfafa ɗan’uwan da kake horarwa?

KA AMBACI WASU MAƘASUDAI WA ƊAN’UWAN KUMA KA BA DA HUJJA

5. (a) Me ya sa yake da muhimmanci dattijo ya tambayi ɗan’uwa game da maƙasudan da ya kafa? (b) Me ya sa ya kamata dattawa su soma horar da ’yan’uwa maza tun suna matasa? (Ka duba ƙarin bayani.)

5 Ka tambayi ɗan’uwan, ‘Waɗanne maƙasudai ne kake so ka cim ma a bautar Jehobah?’ Idan bai kafa maƙasudai ba, ka taimaka masa ya kafa ɗaya da zai iya cim ma. Ka gaya masa yadda ka taɓa kafa wani maƙasudi, kuma ka bayyana masa irin farin cikin da ka yi sa’ad da ka cim ma maƙasudin. Yin hakan bai da wuya kuma yana da amfani sosai. Wani dattijo da kuma majagaba a Afirka ya ce: “Lokacin da nake yaro, wani dattijo ya yi mini wasu tambayoyi masu kyau game da maƙasudaina. Waɗannan tambayoyin sun sa na soma tunani sosai game da hidimata.” Dattawa da suka ƙware sun ce yana da muhimmanci a soma horar da ’yan’uwa maza tun suna ƙanana, wato sa’ad da suke wajen shekaru 13-15, ta wajen ba su aikin da za su iya yi a cikin ikilisiya. Irin wannan horarwa za ta sa su mai da hankali ga maƙasudai a bautar Jehobah a lokacin da suke fuskantar abubuwa masu raba hankali da yawa, wato a shekarunsu na sha shida zuwa sha tara.—Karanta Zabura 71:5, 17. *

6. Wane abu mai muhimmanci ne Yesu ya yi sa’ad da yake horar da wasu?

6 Za ka taimaka wa ɗan’uwa da kake horarwa ya kasance da marmarin yin hidima a cikin ikilisiya idan ka ba shi aiki kuma ka gaya masa dalilin da ya sa ya kamata ya yi aikin. Idan ka yi hakan, kana koyi da Yesu, wanda shi ne Babban Malami. Alal misali, kafin ya ba wa almajiransa umurni su yi wa’azin bishara, ya gaya musu dalilin da ya sa ya kamata su bi umurnin, ya ce: “An mallaka mini dukkan iko a Sama da ƙasa.” Bayan haka ne ya ce musu: “Ku je ku almajirtar da dukkan al’ummai.” (Mat. 28:18, 19, Littafi Mai Tsarki) Ta yaya za ka bi misalin Yesu sa’ad da kake horar da wani ɗan’uwa?

7, 8. (a) Ta yaya dattawa za su bi misalin Yesu sa’ad da suke horar da ’yan’uwa? (b) Me ya sa yaba wa ɗan’uwan da ake horarwa yake da muhimmanci? (c) Waɗanne shawarwari ne za su taimaka wa dattawa wajen horar da wasu? (Ka duba akwatin nan “ Yadda Za A Horar da Wasu.”)

7 Idan ka ba wa ɗan’uwa aiki, ka bayyana masa dalilai daga Littafi Mai Tsarki da suka nuna cewa aikin yana da muhimmanci. Ta hakan, za ka taimaka masa ya riƙa bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki a yadda yake tafiyar da al’amuransa. Alal misali, a ce ka ba wa ɗan’uwa aiki ya share kujeru a Majami’ar Mulki don su kasance da tsabta. Za ka iya tattauna Titus 2:10 kuma ka bayyana masa cewa aikin da yake yi zai zama “ado ga koyarwa ta Allah Mai-cetonmu.” Ƙari ga haka, ka gaya masa yadda aikin zai amfani ’yan’uwa a ikilisiya. Tattauna irin waɗannan batutuwan da ɗan’uwan zai sa ya riƙa yin abubuwa don ya taimaka wa mutane kuma don ya ɗaukaka sunan Allah, ba don cika doka kawai ba. Hakika, zai yi farin ciki sa’ad da ya lura da yadda hidimarsa yana amfanar ’yan’uwa a ikilisiya.

8 Ƙari ga haka, ka tabbata cewa ka yaba wa ɗan’uwan don yana ƙoƙarin bin shawarwarin da ka ba shi. Me ya sa hakan yake da muhimmanci? Yabo zai daɗa sa shi ya kasance da ƙwazo a bautar Jehobah, kamar yadda ban ruwa zai sa abin da aka shuka ya ba da amfani.—Gwada hakan da Matta 3:17.

WANI ƘALUBALE

9. (a) Waɗanne ƙalubale ne dattawa da suke ƙasashen da suka sami ci gaba suke fuskanta? (b) Me ya sa wasu matasa ba su saka ibada kan gaba a rayuwarsu ba?

9 Dattawa a ƙasashen da suka sami ci gaba suna fuskantar ƙalubalen taimaka wa ’yan’uwa maza su yi hidima a ikilisiya. Mun tambayi ƙwararrun dattawa a ƙasashen yamma su gaya mana dalilan da suke gani ya sa wasu ’yan’uwa maza ba sa son yin hidima a ikilisiya. Yawancinsu sun ce sa’ad da waɗannan ’yan’uwan suke girma, ba a taimaka musu su kafa maƙasudai a bautar Jehobah ba. Har ma a wani yanayi, matasan da suke son su kafa maƙasudai da suka shafi ibada ba su sami goyon bayan iyayensu ba, a maimakon haka, iyayen sun ƙarfafa su su shiga jami’a ko kuma su biɗi abin duniya. A sakamako, yaran ba su ɗauki bautar Jehobah da muhimmanci ba.—Mat. 10:24.

10, 11. (a) Ta yaya dattijo zai iya taimaka wa ɗan’uwa da ba ya son yin hidima a cikin ikilisiya ya canja ra’ayinsa da sannu-sannu? (b) Waɗanne nassosi ne dattijo zai iya amfani da su wajen tattaunawa da ɗan’uwan, kuma me ya sa? (Ka duba ƙarin bayani.)

10 Idan ɗan’uwa ba ya son yin hidima a cikin ikilisiya, sai an dāge kuma an bi shi da haƙuri kafin a yi nasara wajen canja ra’ayinsa. Kamar yadda manomi zai gyara amfaninsa da ke karkacewa don ya tsira da kyau, za ka iya taimaka wa wasu ’yan’uwa da sannu-sannu su canja ra’ayinsu don su yi hidima a ikilisiya. Ta yaya za ka yi hakan?

11 Ka zama abokin ɗan’uwan da kake horarwa. Ka sa ya fahimci cewa ana bukatar taimakonsa a cikin ikilisiya. Ka riƙa tattauna wasu nassosi na musamman kuma ka taimaka masa ya yi tunani game da addu’ar da ya yi na bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya. (M. Wa. 5:4; Isha. 6:8; Mat. 6:24, 33; Luk. 9:57-62; 1 Kor. 15:58; 2 Kor. 5:15; 13:5) Za ka iya yi masa wannan tambayar: ‘Wane alkawari ne ka yi wa Jehobah a lokacin da ka yi addu’a cewa za ka ba da kanka don bauta masa?’ Ka motsa zuciyarsa ta yi masa wannan tambayar, ‘Yaya kake gani Jehobah ya ji sa’ad da ka yi baftisma?’ (Mis. 27:11) ‘Yaya Shaiɗan ya ji?’ (1 Bit. 5:8) Tattauna irin waɗannan nassosin zai yi tasiri a rayuwar ɗan’uwan kuma zai motsa shi sosai.—Karanta Ibraniyawa 4:12. *

’YAN’UWA DA AKE HORARWA, KU KASANCE DA AMINCI

12, 13. (a) Wane hali ne Elisha ya nuna sa’ad da ake horar da shi? (b) Ta yaya Jehobah ya albarkaci Elisha don amincinsa?

12 Ku matasa da ake bukatar taimakonku fa? Wane hali ne zai sa ku yi nasara? Bari mu tattauna wasu abubuwa da suka faru a rayuwar wani da aka horar a dā don mu amsa wannan tambayar.

13 Kusan shekaru 3,000 da suka shige, annabi iliya ya gayyaci Elisha ya zama bawansa. Elisha ya amince ba tare da ɓata lokaci ba kuma ya yi wa wannan dattijon hidima ta wajen yin ƙananan ayyuka. (2 Sar. 3:11) Iliya ya yi wajen shekara shida yana horar da shi. Sa’ad da Iliya ya kusan gama aikinsa a ƙasar Isra’ila, sai ya gaya wa abokin aikinsa, wato Elisha ya daina yi masa hidima. Amma sau uku Elisha ya gaya wa Iliya cewa: “Ba ni barinka.” Ya ƙosa ya ci gaba da zama tare da malaminsa. Ta yaya Jehobah ya albarkace Elisha don amincinsa? Ya ba shi damar shaida yadda aka tafi da Iliya a cikin guguwa.—2 Sar. 2:1-12.

14. (a) Ta yaya waɗanda ake horar da su za su yi koyi da Elisha? (b) Me ya sa yake da muhimmanci ɗan’uwa da ake horarwa ya kasance da aminci?

14 Ta yaya za ka yi koyi da Elisha a yau? Ka riƙa yin ayyukan da aka ba ka kome ƙanƙantarsa. Ka mai da dattijon da yake horar da kai abokinka kuma ka nuna masa cewa kana godiya don yadda yake taimakonka. Idan kana bin umurni, kamar kana gaya masa cewa: “Ba ni barinka.” Mafi muhimmanci, ka kasance da aminci wajen yin aikin da aka ba ka. Me ya sa hakan yake da muhimmanci? Don idan ka nuna cewa kai mai aminci ne kuma kana riƙe amana, dattawa za su amince da kai kuma su ba ka ƙarin aiki a cikin ikilisiya.—Zab. 101:6; karanta 2 Timotawus 2:2.

A DARAJA DATTAWA

15, 16. (a) Ta yaya Elisha ya nuna cewa ya girmama malaminsa? (Ka duba hoton da ke shafi na 9.) (b) Mene ne Elisha ya yi da ya ƙarfafa sauran abokan aikinsa annabawa?

15 Labarin Elisha ya nuna yadda ya kamata ’yan’uwa su girmama dattawa da suka ƙware. Bayan Iliya da Elisha suka ziyarci wasu annabawa a Yariko, sai suka taka da ƙafa zuwa Kogin Urdun. A nan ne “Iliya ya ɗauki alkyabbatasa, ya naɗe, ya bugi ruwa, ya rabu biyu.” Sai suka kama tafiya a ciki “suna zance.” Har zuwa wannan lokacin, Elisha bai ɗauka cewa ya san kome ba. Ya ci gaba da sauraron malaminsa Iliya har sai lokacin da aka ɗauki Iliya a cikin guguwa aka tafi da shi. Sai Elisha ya koma Kogin Urdun ya ɗauki taguwar Iliya ya buga ruwan kogin da shi kuma ya ce: “Ina Ubangiji Allah na Iliya?” Sai ruwan ya sake rabuwa.—2 Sar. 2:8-14.

16 Ka lura cewa mu’ujiza na farko da Iliya ya yi ɗaya ne da na wanda Elisha ya yi. Me ya sa hakan yake da muhimmanci? A bayyane yake cewa Elisha bai ɗauka cewa yana bukata ya bi wani sabon tsari da yake shi ne ke da iko a lokacin ba. A maimakon haka, ya ci gaba da bin gurbin Iliya a hidimarsa kuma ta hakan, ya nuna cewa ya girmama malaminsa. Wannan matakin da ya ɗauka ya ƙarfafa sauran annabawa abokan aikin Elisha. (2 Sar. 2:15) Elisha ya yi shekara 60 yana hidimar annabi kuma Jehobah ya yi amfani da shi wajen yin mu’ujizai da yawa sosai, fiye da na waɗanda Iliya ya yi. Wane darasi ne za ka koya daga wannan a matsayin wanda ake horar da shi?

17. (a) Ta yaya waɗanda ake horar da su za su yi koyi da Elisha? (b) Ta yaya Jehobah zai iya yin amfani da amintattun ’yan’uwan da aka horar?

17 Kada ka ɗauka cewa da zarar an ba ka wani aiki a cikin ikilisiya, kana bukata ka canja tsarin abubuwa ko kuma ka kirkiro wani sabon tsari a yadda ake gudanar da ayyuka. Ka tuna cewa ana yin canji ne don akwai bukata a cikin ikilisiya ko kuma don wata ja-gorar da ƙungiyar Jehobah ta bayar. Saboda haka, kada ka ɗauka cewa ana bukatar canji don kana ganin hakan ya dace. Za ka iya ƙarfafa ’yan’uwanka kuma ka girmama dattawan da suka ƙware ta wajen bin shawarwarinsu da ke bisa Littafi Mai Tsarki, kamar yadda Elisha ya ƙarfafa sauran annabawa ta ayyukansa, da kuma yadda ya girmama Iliya ta bin gurbinsa. (Karanta 1 Korintiyawa 4:17.) Amma, yayin da kake ƙwarewa, za ka iya kasance cikin waɗanda za su aiwatar da canje-canje da za su taimaka wa ’yan’uwa a cikin ikilisiya su ci gaba da bauta wa Jehobah tare da ƙungiyarsa. Hakika, Jehobah zai iya yin amfani da ku amintattun ’yan’uwa da aka horar wajen yin abubuwan da suka fi na waɗanda suka horar da ku, kamar yadda labarin Elisha ya nuna.—Yoh. 14:12.

18. Me ya sa horar da ’yan’uwa maza a cikin ikilisiya yake da muhimmanci sosai a yau?

18 Muna fata cewa shawarwarin da ke wannan talifin da kuma wanda ya gabata zai motsa dattawa da dama su nemi lokaci don horar da wasu. Ƙari ga haka, muna addu’a cewa ’yan’uwa maza da suka cancanta su yi marmarin amincewa da wannan horarwa kuma su yi amfani da ita wajen kula da bayin Jehobah. Yin hakan zai inganta ikilisiyoyi a faɗin duniya kuma zai taimaka wa kowannenmu ya kasance da aminci a nan gaba da za mu fuskanci mawuyacin yanayi.

^ sakin layi na 5 Idan matashi ya soma nuna halin dattako a matsayinsa na Kirista kuma shi mai tawali’u ne, ƙari ga haka, idan ya cancanta bisa ga ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki, dattawa za su iya yin shawara a naɗa shi bawa mai hidima ko da bai kai shekara 20 ba.—1 Tim. 3:8-10, 12; ka duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Yuli, 1989, shafi na 29 a Turanci.

^ sakin layi na 11 Za ka iya yin amfani da darussan da ke cikin Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Afrilu, 2012, shafuffuka na 14-16, sakin layi na 8-13; da kuma darussan da ke cikin littafin nan “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah,” babi na 16, sakin layi na 1-3 wajen tattaunawa da ɗan’uwan.