Idan Aka Sare Bishiya Tana Iya Sake Tohuwa Kuwa?
CEDAR wato, bishiyar al’ul ta ƙasar Lebanon, bishiya ce mai girma sosai da kuma ban sha’awa. Akasin haka, bishiyar zaitun ba ta girma sosai kuma ba ta kai bishiyar al’ul kyau ba. Amma an san bishiyar zaitun da dauriya a yanayi dabam-dabam. Wasu suna kai wajen shekara 1,000. Bishiyar zaitun tana da jijiyoyi masu shiga ƙasa sosai kuma hakan yakan sa ta sake tohuwa bayan an datse bishiyar. Muddin jijiyoyin ba su mutu ba, za su sake tohuwa.
Uban iyali Ayuba ya tabbata cewa idan ya mutu, zai sake rayuwa. (Ayu. 14:13-15) Ya yi amfani da bishiya, wataƙila bishiyar zaitun wajen nuna tabbaci da yake da shi cewa Allah zai ta da shi bayan ya mutu. Ayuba ya ce: ‘Ana sa zuciya gareshi [itace] ya sake tohuwa.’ ‘Gama icen da an datse . . . zai sake tohuwa.’ Idan aka yi ruwan sama bayan fāri mai tsawo, kututturen bishiyar zaitun zai iya sake tohuwa kuma ya yi rassa. —Ayu. 14:7-9.
Kamar yadda manomi yana marmarin ganin tohuwar bishiyar zaitun da aka datse, Jehobah yana marmarin ta da bayinsa da kuma mutane da yawa da suka mutu don su sake rayuwa. (Mat. 22:31, 32; Yoh. 5:28, 29; A. M. 24:15) Babu shakka, za mu yi farin cikin marabtar waɗanda suka mutu don su sake jin daɗin rayuwa, ko ba haka ba?