Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Dogara ga Jehobah a Koyaushe!

Ka Dogara ga Jehobah a Koyaushe!

“Ku al’ummai, ku dogara gareshi kowane loto.”—ZAB. 62:8.

1-3. Me ya sa Bulus ya kasance da tabbaci cewa zai iya dogara ga Jehobah? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

KIRISTOCI da ke Roma sun fuskanci mawuyacin lokaci a ƙarni na farko. A shekara ta 64 bayan haihuwar Yesu, an zarge su da saka gobara a birnin da kuma yin gāba da sauran ’yan Adam. Saboda haka, an tsananta musu matuƙa. Da a ce kana raye a matsayinka na Kirista a lokacin, wataƙila da an kama ka kuma an wulaƙanta ka. Wataƙila, da an jefa wasu ’yan’uwanka Kiristoci wa dabbobin masu haushi don su ragargaza su ko kuma a rataye su da rai a kan gungume kuma a ƙona su don a sami haske da dare.

2 A wannan lokacin matuƙar zalunci ne aka jefa manzo Bulus a cikin kurkuku a karo na biyu. Shin wasu Kiristoci za su taimaka masa ne? Wataƙila wannan al’amarin ya dami Bulus, don a wasiƙarsa zuwa ga Timotawus, ya ce: “Kāriyar kaina ta fari da na yi ba wanda ya komo bayana, amma dukansu suka yashe ni: kada a lissafta wannan a kansu.” Duk da haka, Bulus ya ambata cewa ya sami taimako. Ya ce: “Amma Ubangiji ya tsaya wurina, ya kuwa ƙarfafa ni.” Hakika, Ubangiji Yesu ya taimaka wa Bulus. Amma, ta yaya wannan taimakon ya amfane shi? Bulus ya ba da amsar: An “cece ni . . . daga bakin zaki.”—2 Tim. 4:16, 17. *

3 Babu shakka, tunawa da wannan abin da ya faru ya ƙarfafa Bulus kuma ya taimaka masa ya tabbata cewa Jehobah zai taimaka masa ya jure gwajin da yake fuskanta a lokacin da kuma waɗanda zai fuskanta daga baya. Shi ya sa ya ce: ‘Ubangiji zai fishe ni daga kowane mummunan aiki.’ (2 Tim. 4:18) Hakika, daga abin da ya faru, Bulus ya san cewa ko da ’yan Adam ba su taimake shi ba, Jehobah da kuma Yesu ba za su fasa taimaka masa ba.

ABUBUWAN DA ZA SU SA MU DOGARA GA JEHOBAH

4, 5. (a) Wane ne zai iya taimaka maka a kowane lokacin da kake da bukata? (b) Ta yaya za ka ƙarfafa dangantakarka da Jehobah?

4 Ka taɓa samun kanka a cikin wani mawuyacin hali? Wataƙila rashin aiki ne ko matsi a makaranta, ko rashin lafiya, ko wata matsala mai tsanani. Wataƙila ka nemi taimako daga wurin mutane amma sun kasa taimaka maka. Hakika, ba dukan matsaloli ba ne ’yan Adam za su iya magancewa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka dogara ga Ubangiji.” A irin wannan yanayin, bin wannan shawarar yana da amfani kuwa? (Mis. 3:5, 6) Ƙwarai kuwa! Labaran Littafi Mai Tsarki da yawa sun nuna cewa Allah yana taimakon bayinsa da gaske.

5 Saboda haka, a maimakon ka riƙa fushi don ’yan Adam sun kasa taimaka maka, ka mai da irin waɗannan yanayin dama na dogara ga Jehobah kamar yadda manzo Bulus ya yi, kuma ka ga yadda Jehobah zai kula da kai. Hakan zai sa ka ƙara amincewa da shi kuma dangantakarka da shi za ta yi danƙo sosai.

MUNA BUKATAR MU DOGARA GA ALLAH

6. Me ya sa yake da wuya mu dogara da Jehobah, musamman ma sa’ad da muke fuskantar wata matsala mai tsanani?

6 Sa’ad da kake fuskantar wata matsala mai tsanani, za ka iya yin addu’a game da ita kuma ka kasance da kwanciyar hankali don ka san cewa ka yi iya ƙoƙarinka ka magance matsalar. (Karanta Zabura 62:8; 1 Bitrus 5:7.) Idan kana so ka kasance da dangantaka ta kud da kud da Jehobah, wajibi ne ka riƙa dogara da shi a koyaushe. Duk da haka, ba da gaskiya cewa Jehobah zai biya bukatarka yana da wuya a wani lokaci. Me ya sa? Wani dalilin shi ne ba kowane lokaci ba ne Jehobah yake amsa addu’o’inmu nan take.—Zab. 13:1, 2; 74:10; 89:46; 90:13; Hab. 1:2.

7. Me ya sa ba a kowane lokaci ba ne Jehobah yake amsa addu’o’inmu nan take ba?

7 Me ya sa Jehobah ba ya amsa dukan addu’o’inmu nan take? Jehobah ya kwatanta dangantakarmu da shi kamar na ’ya’ya da mahaifinsu. (Zab. 103:13) Yaro ya san cewa ba kowane abu ne ya tambaya mahaifinsa yake ba shi nan take ba. Zai iya yin sha’awar wani abu yanzu, amma daga baya ya ce ba ya so. A wani sa’i kuma, lokaci bai yi ba da zai samu wasu abubuwa da yake so. Har ila wasu kuma ba za su amfani yaron da kuma wasu ba. Ƙari ga haka, idan mahaifin yana ba wa yaron duk wani abin da yake so, zai mai da kansa kamar bawa a gaban ɗansa. Hakazalika, Jehobah yana ƙaunarmu, saboda haka zai iya bari lokaci ya wuce kafin ya amsa wasu addu’o’inmu. A matsayinsa na Mahalicci da Ubangiji mai ƙauna, ya san cewa idan ya biya dukan bukatunmu a lokacin da muke so, hakan zai ɓata dangantakarmu da shi.—Gwada hakan da Ishaya 29:16; 45:9.

8. Wani alkawari ne Jehobah ya yi mana game da kasawarmu?

8 Wani dalili kuma shi ne cewa Jehobah ya san kasawarmu. (Zab. 103:14) Saboda haka, ba ya barin mu mu jimre wani yanayi da gwanintarmu. A maimakon haka, yana tanadar mana da taimako a matsayinsa na Uba. Ko da yake a wani lokaci muna iya ɗauka cewa ba za mu iya ci gaba da jimrewa ba. Amma Jehobah ya yi mana alkawari cewa ba zai taɓa barin bayinsa su fuskanci matsalolin da suka fi ƙarfinsu ba. Hakika, zai tanadar da “hanyar tsira.” (Karanta 1 Korintiyawa 10:13.) Saboda haka, mun tabbata cewa Jehobah ya san irin yanayin da za mu iya jimrewa.

9. Mene ne ya kamata mu yi idan Jehobah bai amsa addu’armu nan da nan ba?

9 Idan muka yi addu’a kuma ba mu sami amsar addu’armu nan da nan ba, mu dogara ga Jehobah. Ya san daidai lokacin da ya kamata ya biya bukatarmu. Kada mu manta cewa shi ma yana haƙuri kuma yana marmarin taimaka mana. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ubangiji fa za ya yi sauraro, domin shi yi maku alheri, za ya fa ɗaukaka, domin shi yi maku jinƙai: gama Ubangiji Allah mai-shari’a ne; masu-albarka ne dukan waɗanda ke sauraronsa.”—Isha. 30:18.

“BAKIN ZAKI”

10-12. (a) Ta yaya Kirista da yake kula da memban iyalinsa da yake rashin lafiya zai iya samun kansa a tsaka mai wuya? (b) Ta yaya dogara da Jehobah a mawuyacin yanayi zai shafi dangantarka da shi? Ka yi bayani.

10 Sa’ad da muke cikin tsaka mai wuya, za ka iya ji kamar yadda Bulus ya taɓa ji, wato kamar kana kusa da ko kuma a cikin “bakin zaki.” A irin wannan yanayin, dogara da Jehobah yana da wuya, amma kuma yana da muhimmanci mu yi hakan. Alal misali, a ce kana kula da wani a cikin iyali da yake rashin lafiya mai tsanani. Wataƙila ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka yanke shawarwari masu kyau kuma ka kasance da ƙarfin zuciya. * Idan ka yi iya ƙoƙarinka, za ka sami kwanciyar hankali domin ka san cewa Jehobah yana sane da yanayinka kuma zai tanadar maka da abin da kake bukata don ka jimre.—Zab. 32:8.

11 Yanayi zai iya sa mu ɗauka cewa Jehobah ba ya taimakonmu. Likitoci za su iya ba ka shawarwari da suka saɓa wa juna. A wani lokaci, ’yan gidanku ko danginku za su iya sa yanayin ya daɗa muni maimakon su taimaka maka. Ka ci gaba da dogara da Jehobah. Kada ka fasa ƙarfafa dangantakarka da shi. (Karanta 1 Sama’ila 30:3, 6.) Daga baya, idan ka yi la’akari da yadda Jehobah ya taimake ka, abotarka da shi zai daɗa inganci.

12 Abin da Linda * ta shaida ke nan bayan ta yi shekaru tana kula da iyayenta sa’ad da suke rashin lafiya kafin su mutu. Ta ce: “Sa’ad da nake fuskantar wannan yanayin, ni da maigidana da ƙanena ba mu san abin da za mu yi ba. Mukan karaya a wani lokaci. Amma yanzu, idan muka tuna da abin da ya faru, mun tabbata cewa Jehobah ya kula da mu. Ya ƙarfafa mu kuma ya tanadar mana da abin da muke bukata, duk da cewa mun ga kamar ba mu da mafita.”

13. Ta yaya wata ’yar’uwa da ta dogara da Jehobah ta jure da matsaloli masu tsanani?

13 Idan muka dogara da Jehobah da dukan zuciyarmu, za mu iya jure da yanayi na baƙin ciki. Wata ’yar’uwa mai suna Rhonda da mijinta ba Mashaidi ba ta shaida hakan. A lokacin da mijin yana so ya kashe aurensu ne aka gano cewa ɗan’uwanta yana da wani mugun ciwo mai karya garkuwar jiki da ake kira lupus. ’Yan watanni bayan haka, matar ɗan’uwanta ta mutu. Sa’ad da ta soma samun sauƙi daga yanayin sai ta soma hidimar majagaba na kullum. Jim kaɗan bayan haka, sai mahaifiyarta ta mutu. Shin me ya taimaka wa Rhonda ta jure? Ta ce: “Ina yin addu’a kullum, ko a batun da bai taka kara ya karya ba. Hakan ya sa na kasance da dangantaka ta kud da kud da Jehobah. Kuma ya sa na soma dogara ga Jehobah, a maimakon in dogara ga kaina ko kuma wasu. Jehobah ya taimaka mini ƙwarai da gaske, don ya biya dukan bukatuna. Saboda haka, ina jin daɗin abotarmu da Jehobah.”

Wasu abubuwa za su iya faruwa da za su gwada dangantakarmu da Jehobah, ko a cikin iyali ma (Ka duba sakin layi na 14-16)

14. Wane tabbaci ne amintaccen bawan Allah da aka yi wa danginsa yankan zumunci zai iya kasancewa da shi?

14 Ka yi la’akari da wani yanayi. A ce an yi wa wani ɗan’uwanka yankan zumunci. Bisa ga abin da ka koya daga Littafi Mai Tsarki, ka san yadda ya kamata a bi da waɗanda aka yi musu yakan zumunci. (1 Kor. 5:11; 2 Yoh. 10) Duk da haka, a wani lokaci za ka iya ɗauka cewa bin umurnin Littafi Mai Tsarki game da yankan zumunci yana da wuya ko kuma ka ɗauka cewa bai dace ba sam. * A wannan lokacin, ya kamata ka dogara da Ubanmu na sama don ya ba ka ƙarfin zuciyar bin wannan shawarar Littafi Mai Tsarki game da yankan zumunci. Zai dace ka ƙarfafa dangantakarka da Jehobah a irin wannan yanayin, ko ba haka ba?

15. Me ya sa Adamu ya ƙi bin umurnin Jehobah a lambun Adnin?

15 Ka yi la’akari da Adamu, mutumin da Allah ya soma halitta. Shin ya ɗauka cewa idan ya ƙi bin umurnin Jehobah ba zai mutu ba ne? A’a, don Littafi Mai Tsarki ya ce ba a ‘ruɗi’ Adamu ba. (1 Tim. 2:14) To, me ya sa ya yi rashin biyayya? Adamu ya ci ’ya’yan itacen ne don ya so matarsa fiye da Jehobah. Ya saurare ta maimakon ya saurari Jehobah, Allahnsa.—Far. 3:6, 17.

16. Wane ne ya kamata ka so fiye da kowa, kuma me ya sa?

16 Shin hakan yana nufin bai kamata mu so danginmu sosai ba? A’a. Amma, ya kamata mu so Jehobah fiye da kowa da kome. (Karanta Matta 22:37, 38.) Yin hakan zai amfani danginmu ko da suna bauta wa Jehobah yanzu ko a’a. Saboda haka, ka ci gaba da ƙarfafa dangantakarka da Jehobah kuma ka riƙa dogara da shi. Idan ka damu da yanayin danginka da aka yi masa yakan zumunci, ka yi addu’a a kan batun. * (Rom. 12:12; Filib. 4:6, 7) Ka yi amfani da wannan yanayin don ka ƙarfafa dangantakarka da Jehobah sosai. Hakan zai taimaka maka ka dogara ga Jehobah kuma ka kasance da tabbaci cewa yin biyayya ya fi albarka.

YAYIN DA MUKE SAURARON JEHOBAH

Ka nuna cewa ka dogara da Jehobah ta wajen kasancewa da ƙwazo a wa’azin bishara (Ka duba sakin layi na 17)

17. Ta yaya muke nuna cewa mun dogara ga Jehobah, idan muka kasance da ƙwazo a wa’azin bishara ta Mulki?

17 Me ya sa aka ceci Bulus daga “bakin zaki”? Ya ce: “Domin ta wurina shela ta watsu sarai, dukan Al’ummai kuma su ji.” (2 Tim. 4:17) Yayin da muke yin wa’azin bishara da ƙwazo kamar manzo Bulus, muna da tabbaci cewa Jehobah zai “ƙara” mana sauran abubuwa, wato zai biya bukatunmu. (Mat. 6:33) Jehobah ya ba mu gatan zama ‘abokan aikinsa,’ shi ya sa ya “sanya bishara a hannunmu.” (1 Kor. 3:9; 1 Tas. 2:4) Idan muka kasance da ƙwazo a yin aikin da Allah ya ba mu, hakan zai taimaka mana mu zama masu haƙuri yayin da muke sauraron Allah ya amsa addu’armu.

18. Waɗanne abubuwa ne za mu iya yi don mu ƙara kasancewa da aminci kuma mu ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah?

18 Saboda haka, bari mu yi amfani da zarafin da muke da shi yanzu wajen ƙarfafa dangantakarmu da Allah. Idan muka sami kanmu a cikin wani yanayi da yake sa mu fargaba, mu yi ƙoƙari mu kusaci Jehobah. Bari mu riƙa yin karatu da nazarin Kalmar Allah da kuma yin bimbini a kan abin da muka karanta. Ƙari ga haka, mu riƙa yin addu’a babu fashi, kuma mu kasance da himma a ibadarmu ga Jehobah. Idan muka yi waɗannan abubuwa, muna da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka mana mu jure kowane mawuyacin hali da muke ciki yanzu da kuma wanda za mu fuskanta a nan gaba.

^ sakin layi na 2 “Bakin zaki” da aka ceto Bulus zai iya kasancewa na zahiri ko kuma a alamance.

^ sakin layi na 10 Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Maris, 2014, shafuffuka na 20-24, da ta 15 ga Mayu, 2010, shafuffuka na 17-19 da kuma ta Janairu-Maris, 2010, shafuffuka na 16-18.

^ sakin layi na 12 An canja sunaye.

^ sakin layi na 14 Ka duba talifin nan “Me Ya Sa Yankan Zumunci Tsari Ne Mai Kyau?” a wannan fitowar.

^ sakin layi na 16 Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Janairu 2013, shafuffuka na 15-16, da ta 15 ga Yuni 2013 shafuffuka na 24-28.