Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Wane ne Gog na Magog da aka ambata a littafin Ezekiyel?

Mun yi shekaru da dama muna bayyanawa a cikin littattafanmu cewa sunan da aka ba Shaiɗan Iblis sa’ad da aka koro shi daga sama shi ne Gog na Magog. An yi wannan bayanin bisa ga abin da aka faɗa a cikin littafin Ru’ya ta Yohanna cewa Shaiɗan Iblis ne zai yi ja-gora a harin da za a kai wa mutanen Allah a faɗin duniya. (R. Yoh. 12:1-17) Saboda haka, an ɗauka cewa Gog wani suna ne da aka ba wa Shaiɗan.

Amma, wannan bayanin ya ta da wasu tambayoyi masu muhimmanci. Me ya sa? Alal misali, sa’ad da Jehobah ya yi magana game da lokacin da za a yi nasara a kan Gog, ya ce masa: “Zan bāshe ka ga tsuntsaye na kowane iri mai-ƙawan nama da naman jeji domin a cinye ka.” (Ezek. 39:4) Jehobah ya daɗa cewa: “A ranan nan zan ba Gog wurin kushewa a cikin Isra’ila, . . . can za su bizne Gog da dukan tattarmukansa.” (Ezek. 39:11) Amma zai yiwu ne “tsuntsaye . . . da naman jeji” su cinye halittar da ba a gani da ido, wato ruhu? Ta yaya za a ‘binne’ Shaiɗan a duniya? Babu inda aka ce za a cinye Shaiɗan ko kuma za a binne shi. A maimakon haka, Littafi Mai Tsarki ya bayyana filla-filla cewa za a jefa shi cikin rami marar matuƙa na tsawon shekara dubu.—R. Yoh. 20:1, 2.

Littafi Mai Tsarki ya ce bayan shekara dubun, za a fitar da Shaiɗan daga rami mara matuƙa. “Za ya fito kuma garin ya ruɗe al’umman da ke cikin ƙusurwoyi huɗu na duniya, Gog da Magog, shi tattara su zuwa yaƙin.” (R. Yoh. 20:8) Shin, idan Shaiɗan ne Gog, yaya za a ce zai ruɗi Gog? Saboda haka, “Gog” da aka ambata a cikin littattafan Ezekiyel da Ru’ya ta Yohanna ba Shaiɗan ba ne.

Shin, wane ne Gog na Magog? Muna bukata mu bincika Littafi Mai Tsarki don mu gane ko wane ne zai kai hari wa mutanen Allah idan muna son mu sami amsar tambayar nan. Ba harin Gog na Magog ba ne kawai Littafi Mai Tsarki ya ambata, ya kuma ambata harin da “sarkin arewa” da kuma “sarakunan duniya” za su kai. (Ezek. 38:2, 10-13; Dan. 11:40, 44, 45; R. Yoh. 17:14; 19:19) Shin waɗannan hare-haren dabam-dabam ne? Da wuya. Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da sunaye dabam-dabam wajen kwatanta hari guda ne. Me ya sa muka ce hakan? Don Littafi Mai Tsarki ya ce dukan al’ummai za su saka hannu a wannan hari na ƙarshe kuma hakan zai sa a soma yaƙin Armageddon.—R. Yoh. 16:14, 16.

Idan muka bincika duka waɗannan nassosin da suka yi magana a kan hari na ƙarshe da za a kai wa mutanen Allah, za mu ga cewa ba Shaiɗan ne Gog na Magog ba, amma Al’ummai ne da suka haɗa kai. Shin “sarkin arewa” da aka ambata ne zai ja-goranci wannan tarin al’ummai? Ba mu da tabbaci. Amma wannan tunanin ya zo daidai da wannan bayanin da Jehobah ya yi game da Gog: ‘Za ka taso daga wurinka, daga ƙurewar ƙasar arewa, kai, da dangi dayawa tare da kai, dukansu a kan dawakai, jama’a mai-girma, babbar rundunar yaƙi ƙwarai.’—Ezek. 38:6, 15.

Hakazalika, annabi Daniyel wanda suka yi zamani ɗaya da Ezekiyel ya bayyana game da sarkin arewa cewa: “Labari daga gabas da arewa za su dami hankalinsa: za ya fita kuwa da babbar hasala domin shi halaka mutane da yawa, ya washe su sarai. Za ya kafa tents na fādassa tsakanin teku da dutse mai-tsarki mai-daraja; duk da haka za ya ƙare, ba kuwa mai-taimakonsa.” (Dan. 11:44, 45) Wannan bayanin ya zo daidai da abin da littafin Ezekiyel ya ce Gog zai yi.—Ezek. 38:8-12, 16.

Bayan haka, mai zai faru a sakamakon wannan hari na ƙarshe? Littafin Daniyel ya ce: ‘A wannan lokaci fa Michael [Yesu Kristi] za ya tashi tsaye [a Armageddon], shi babban jarumin nan mai-kāriyar ’ya’yan jama’arka [tun daga shekara ta 1914], za a yi kwanakin [ƙunci mai girma] wahala irin da ba a taɓa yi ba tun da aka yi al’umma har loton nan; a loton nan kuwa za a ceci mutanenka, kowane ɗaya wanda aka iske shi a rubuce cikin litafin.’ (Dan. 12:1) An kuma bayyana a littafin Ru’ya ta Yohanna 19:11-21 cewa Yesu zai ɗauki wannan matakin.

Amma, wane ne “Gog da Magog” da aka ambata a Ru’ya ta Yohanna 20:8? A ƙarshen shekara dubun, wato a lokacin gwaji na ƙarshe, waɗanda suka yi wa Jehobah tawaye ma za su nuna irin mugun halin ‘Gog na Magog,’ wato ƙasashen da suka haɗa kai don kai wa mutanen Allah hari a gab da ƙarshen ƙunci mai girma. Za a halaka waɗannan ’yan tawayen kamar yadda za a halaka ‘Gog na Magog.’ (R. Yoh. 19:20, 21; 20:9) Saboda haka, sunan nan “Gog da Magog” ya dace da dukan waɗanda suka yi tawaye a ƙarshen Sarautar Almasihu na Shekara Dubu.

A matsayinmu na masu son bincika Kalmar Allah, muna marmarin ganin wanda zai zama “sarkin arewa.” Ba a san wanda zai ja-goranci wannan al’ummai da suka haɗa kai don kai hari ba, amma mun tabbata da abubuwa biyu: (1) Za a yi nasara a kan Gog na Magog da rundunarsa kuma za a halaka su; ƙari ga haka, (2) Sarkinmu Yesu Kristi, zai ceci mutanen Allah kuma zai bishe su zuwa cikin sabuwar duniya da za a yi zaman lafiya.—R. Yoh. 7:14-17.