Ya So Mutane
“Na yi murna saboda duniyar da ya halitta, amma na fi son ’yan Adam.”—MIS. 8:31, New World Translation.
1, 2. Mene ne ya nuna cewa Yesu yana ƙaunar ’yan Adam?
BABU wanda ya fi bayyana mana hikimar Jehobah kamar ɗansa na fari. Shi mai hikima ne sosai kuma shi “gwanin mai-aiki ne” tare da Ubansa. Hakika, ya yi farin ciki sosai sa’ad da Allah ya “shirya sammai” da “tussan duniya.” Amma a cikin dukan abubuwan da Allah ya halitta, ’yan Adam ne Yesu, wato Ɗan farko na Allah ya fi so. (Mis. 8:22-31) Yesu yana ƙaunar ’yan Adam tun kafin ya zo duniya.
2 Yesu yana da aminci kuma yana ƙaunar Ubansa da “’yan Adam” sosai. Shi ya sa ya “wofinta kansa” kuma ya zo duniya kamar ɗan Adam. Ya yi hakan don ya ba da kansa “abin fansar mutane da yawa.” (Filib. 2:5-8; Mat. 20:28) Hakika, yana ƙaunar ’yan Adam ƙwarai! Sa’ad da Yesu yake duniya, Allah ya ba shi ikon yin mu’ujizoji da suka nuna cewa yana ƙaunar mutane. Ta hakan, Yesu ya nuna abubuwa masu kyau da za su faru a duniya nan ba da daɗewa ba.
3. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?
Luk. 4:43) Yesu ya san cewa Mulkin zai tsarkake sunan Allah kuma zai magance dukan matsalolin ’yan Adam. Mu’ujizojin da Yesu ya yi sa’ad da yake duniya sun nuna cewa yana ƙaunar ’yan Adam. Me ya sa hakan yake da muhimmanci a gare mu? Don darussan da za mu koya za su sa ƙarfafa mu kuma su sa mu kasance da bege game da nan gaba. Bari mu tattauna mu’ujizojin Yesu guda huɗu.
3 Sa’ad da Yesu yake duniya, ya yi wa’azin “bishara ta mulkin Allah.” (YANA DA IKON “WARKARWA”
4. Mene ne ya faru sa’ad da Yesu ya haɗu da wani mutum mai kuturta?
4 Sa’ad da yake duniya Yesu ya yi wa’azi a yankin Galili. A wani gari da ke wurin ne Yesu ya ga wani abin tausayi. (Mar. 1:39, 40) Ya haɗu da wani mutum mai ciwon kuturta. Da yake Luka likita ne, ya ce mutumin yana “cike da kuturta” don ciwon ya ci jikinsa sosai. (Luk. 5:12) “Sa’ad da ya ga Yesu, ya faɗi bisa fuskarsa ya roƙe shi, ya ce, Ubangiji, idan ka yarda, kana da iko ka tsarkake ni.” Mutumin ya san cewa Yesu yana da ikon warkar da shi, amma Yesu zai so ya warkar da shi kuwa? Yaya Yesu ya bi da wannan mutum? Mene ne Yesu yake tunani sa’ad da ya ga wannan mutum da wataƙila ya ɓata kamaninsa? Shin Yesu zai yi watsi da shi kamar yadda Farisawa suke bi da mutanen da suke fama da kuturta ne? Da a ce kai ne, wane mataki ne za ka ɗauka?
5. Me ya sa Yesu ya ce “Na yarda” sa’ad da yake warkar da mai kuturta?
5 A bayyane yake cewa mutumin bai ta da murya ya ce “marar-tsarki, marar-tsarki” bisa ga dokar da aka ba da ta hannun Musa. Yesu bai yi fushi ba. Maimakon haka, ya mai da hankali ga mutumin da kuma abin da yake damunsa. (Lev. 13:43-46) Ba mu san ainihin abin da Yesu ya yi tunaninsa ba, amma mun san abin da ke zuciyarsa. Yesu ya ji tausayin mutumin kuma ya yi abin da ya ba mutane mamaki. Ya miƙa hannunsa ya taɓa kuturun kuma ya yi magana da tabbaci da kuma tausayi, ya ce: “Na yarda; ka tsarkaka. Nan da nan fa kuturta ta rabu da shi.” (Luk. 5:13) Hakika, Jehobah ya ba Yesu iko don ya yi wannan mu’ujizan kuma don ya nuna cewa yana ƙaunar mutane.—Luk. 5:17.
6. Me ya sa mu’ujizojin Yesu suke da ban sha’awa, kuma mene ne suka nuna?
6 Allah ya ba Yesu Kristi ikon yin mu’ujizoji masu ban al’ajabi da yawa. Ya warkar da kuturta da kuma kowace irin cuta da mutane suke fama da ita. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Taro suka yi mamaki, da suka ga bebaye suna magana, masu-dungu suka yi sarai, guragu suna tafiya, makafi suna gani.” (Mat. 15:31) A wani lokaci, idan gaɓan mutum yana ciwo, akan ɗauki gaɓan jikin wani kuma a dasa masa. Amma Yesu bai yi hakan ba, ya warkar da waɗannan gaɓaɓuwan da suke ciwo. Ƙari ga haka, ya warkar da mutane ba tare da ɓata lokaci ba, a wani lokaci ma, ya yi hakan daga nesa. (Yoh. 4:46-54) Mene ne waɗannan abubuwan al’ajabi suka nuna? Da yake an naɗa Yesu Sarki a sama, yana da ikon da kuma niyyar warkar da dukan cututtuka har abada. Sanin yadda Yesu ya bi da mutane zai sa mu kasance da tabbaci cewa wannan annabcin Littafi Mai Tsarki zai cika a sabuwar duniya: “Za ya nuna tausayi ga matalauci da mai-rashi.” (Zab. 72:13) Hakika, a lokacin, Yesu zai yi marmarin taimaka wa waɗanda suke sha wahala.
“KA TASHI, KA ƊAUKI SHIMFIƊARKA, KA YI TAFIYA”
7, 8. Wane yanayi ne ya sa Yesu ya haɗu da wani mutumin da ya naƙasa a tafkin Baitasda.
7 ’Yan watanni bayan Yesu ya warkar da kuturun a Galili, sai ya je Yahudiya don ya yi wa’azin bishara ta Mulkin Allah. Babu shakka, Yesu ya motsa dubban mutane da saƙonsa da kuma yadda ya bi da su. Burinsa ne ya yi shelar bishara ga matalauta, ya yi shelar saki ga ɗaurarru da kuma ƙarfafa waɗanda suke baƙin ciki.—Isha. 61:1, 2; Luk. 4:18-21.
8 A watan Nisan, Yesu ya je Urushalima don ya yi abin da Ubansa ya umurta, wato Idin Ƙetarewa. Birnin ya cika da mutanen da suka zo don wannan biki mai muhimmanci. A lokacin ne Yesu ya haɗu da wani mutumin da ya naƙasa a arewacin haikalin, kusa da wani tafki da ake kira Baitasda.
9, 10. (a) Me ya sa mutane suke zuwa tafkin Baitasda? (b) Mene ne Yesu ya yi a tafkin, kuma wane darasi ne muka koya? (Ka duba hoton da ke shafi na 8.)
9 Mutane da yawa da suke rashin lafiya suna zuwa tafkin Baitasda. Mene ne yake kai su wannan wurin? Sun gaskata cewa idan mai rashin lafiya ya shiga cikin ruwan sa’ad da ruwan yake motsi, zai warke. Ka yi tunanin irin yanayin da ake ciki don yadda mutane masu fama da cututtuka dabam-dabam suka taru kuma sun ƙosa su warke! Shin mene ne ya kawo Yesu da bai taɓa rashin lafiya ba a wannan wurin? Don yana ƙaunar mutane. A nan ne Yesu ya haɗu da wani mutum da yake rashin lafiya tun kafin a haifi Yesu.—Karanta Yohanna 5:5-9.
10 Sa’ad da Yesu ya tambaye shi ko yana so ya warke. Ya ce yana so ya warke amma ba wanda zai shigar da shi cikin tafkin. Sai Yesu ya ce wa mutum ya yi abin da marar lafiyar ya ɗauka ba zai taɓa yiwuwa ba, wato ya tashi ya ɗauki shimfiɗarsa kuma ya yi tafiyarsa. Mutumin ya gaskata da abin da Yesu ya faɗa kuma ya tashi ya ɗauki shimfiɗarsa ya soma tafiya. Wannan mu’ujizan ta tabbatar mana da abubuwa masu ban al’ajabi da Yesu zai yi a sabuwar duniya. Ƙari ga haka, mu’ujizan ya nuna cewa Yesu yana tausayin mutane. Yana neman mabukata. Ya kamata mu yi koyi da Yesu wajen neman mutane a yankinmu da ke baƙin ciki saboda abubuwan da ke faruwa a wannan duniya.
“WANE NE YA TAƁA TUFAFINA?”
11. Ta yaya labarin da ke Markus 5:25-34 ya nuna cewa Yesu yana tausayin waɗanda suke rashin lafiya?
11 Karanta Markus 5:25-34. Wannan matar ta yi shekara 12 tana fama da wata muguwa cutar. Cutar ta shafi kome a rayuwarta, har ma ba za iya zuwa cikin haikali ta yi ibada ba. Duk da cewa “ta sha wahala da yawa kuwa ga hannuwan masu-magani dayawa, ta ɓatar da dukan abin da ke wurinta,” amma duk da haka, yanayinta sai ƙara muni yake yi. Amma da yake ta so ta warke, sai ta kasance a wurin da za ta iya taɓa da Yesu. Ta shiga cikin jama’a ta taɓa tufafin Yesu. (Lev. 15:19, 25) Yesu ya ji cewa iko ya bar jikinsa, sai ya yi tambaya cewa wane ne ya taɓa shi. Matar ta ‘ji tsoro’ kuma ta soma “rawan jiki” sai ta “fāɗi a gabansa, ta faɗa masa gaskiya duka.” Da Yesu ya gane cewa Ubansa, Jehobah ne ya warkar da matar, sai ya yi mata magana a hankali ya ce: “Ɗiya, bangaskiyarki ta warkar da ke; ki tafi lafiya, ki rabu da azabarki.”
12. (a) Daga abubuwan da muka koya yanzu, yaya za ka kwatanta Yesu? (b) Wane misali ne Yesu ya kafa mana?
12 Yesu mai kirki ne sosai. Waɗannan labaran sun nuna cewa yana tausayin waɗanda suke wahala saboda rashin lafiya. Shaiɗan yana so mu ɗauka cewa ba a ƙaunarmu kuma ba mu da amfani. Amma mu’ujizan sun tabbatar mana cewa Yesu ya damu da mu da matsalolinmu. Hakika, Yesu Sarki ne da kuma Babbar Firist mai tausayi! (Ibran. 4:15) Ba za mu iya fahimtar yanayin waɗanda suke fama da cuta masu tsanani ba, musamman ma idan ba mu taɓa yin irin rashin lafiyar ba. Duk da haka, za mu iya sanin cewa Yesu ya fahimci yanayin marasa lafiya ko da bai taɓa yin rashin lafiya ba. Bari mu yi iya ƙoƙarinmu wajen yin koyi da Yesu.—1 Bit. 3:8.
“YESU YA YI KUKA”
13. Mene ne muka koya game da Yesu sa’ad da ya ta da Li’azaru daga mutuwa?
13 Wahalar da mutane suke sha ya motsa Yesu sosai. Yesu ya damu sosai sa’ad da abokinsa Li’azaru ya mutu, har ya “ji haushi cikin ruhunsa” kuma ya ji “zafi a ransa.” Ya damu sosai ko da ya san cewa zai ta da Li’azaru daga mutuwa ba da daɗewa ba. (Yohanna 11:33-36.) Yesu bai ji kunyar yin kuka a gaban mutane ba. Mutane sun ga yadda yake ƙaunar Li’azaru da iyalinsa. Yesu ya so Li’azaru sosai kuma shi ya sa ya ta da shi daga mutuwa.—Yoh. 11:43, 44.
14, 15. (a) Me ya nuna cewa Jehobah yana da burin kawar da wahala da ’yan Adam suke sha? (b) Mene ne kalmar Helenanci da aka fassara kabari ta ƙunsa?
14 Littafi Mai Tsarki ya ce Yesu shi ne ‘surar’ Mahalicci. (Ibran. 1:3) Yesu ya nuna ta mu’ujizojinsa cewa shi da Ubansa suna da burin kawar da rashin lafiya da mutuwa. Nan ba da daɗewa ba za su ta da mutane daga matattu. Yesu ya ce: “Sa’a tana zuwa, inda dukan waɗanda suna cikin kabarbaru za su . . . fito.”—Yoh. 5:28, 29.
15 An samo Kalmar Helenanci da aka fassara zuwa kabari daga wata kalma da ke nufin tunawa. Hakan yana nufin cewa Allah zai tuna da dukan waɗanda yake so ya ta da daga matattu. Allah Maɗaukakin Sarki ne ya halicci duniya da taurari, kuma zai iya tuna da kome game da ’yan’uwanmu ƙaunatattu da suka mutu, hakan ya haɗa da halayensu. (Isha. 40:26) Ba wai zai iya tuna da su kawai ba, amma shi da Ɗansa suna da burin yin hakan. Ta da Li’azaru daga matattu da kuma wasu tashin matattu da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki suna nuni ga abubuwan da za su faru a sabuwar duniya.
ABIN DA MUKA KOYA DAGA MU’UJIZOJIN YESU
16. Wace dama ce amintattun Kiristoci da suke raye yanzu za su samu?
16 Idan muka kasance da aminci, za mu sami damar shaida wata mu’ujiza mai ban mamaki sosai, wato za mu tsira daga ƙunci mai girma. Bayan yaƙin Armageddon, za mu ƙara shaida mu’ujizoji da dama, kowane ɗan Adam zai kasance da ƙoshin lafiya. (Isha. 33:24; 35:5, 6; R. Yoh. 21:4) Ka yi la’akari da yadda mutane za su yar da tabarau da sanduna da kekunan guragu da makamancinsu. Jehobah ya san cewa waɗanda za su tsira a Armageddon suna bukata su kasance da ƙoshin lafiya don suna da ayyuka da yawa da za su yi. Hakan zai sa su kasance da himma yayin da suke mai da wannan duniyar da Allah ya ba mu aljanna.—Zab. 115:16.
17, 18. (a) Mene ne ya sa Yesu ya yi mu’ujizai sa’ad da yake duniya? (b) Me ya sa ya kamata ka yi iya ƙoƙarinka don ka shiga sabuwar duniya?
17 “Taro mai-girma” suna samun ƙarfafa sa’ad da suka karanta labarin yadda Yesu ya warkar da marasa lafiya. (R. Yoh. 7:9) Waɗannan mu’ujizojin sun tabbatar mana cewa Yesu, Ɗan fari na Allah yana ƙaunar ’yan Adam sosai. (Yoh. 10:11; 15:12, 13) Ƙari ga haka, tausayin da Yesu ya nuna yana tabbatar mana cewa Jehobah ya damu da kowane bawansa.—Yoh. 5:19.
18 ’Yan Adam suna fama da cututtuka da kuma mutuwa. (Rom. 8:22) Shi ya sa muke bukatar sabuwar duniyar da Allah ya yi alkawari cewa za a kawar da dukan cututtuka. Littafin Malakai 4:2, ta ce za mu yi “tsalle tsalle kamar ’yan maruƙa” don ƙoshin lafiya. Za mu yi farin ciki don mun sami ’yanci daga ajizanci. Bari mu kasance masu godiya da kuma bangaskiya ga alkawuran da Allah ya yi kuma mu ci gaba da yin iya ƙoƙarinmu yanzu don mu cancanci waɗanda za su shiga sabuwar duniya. Hakika, muna farin ciki cewa mu’ujizojin da Yesu ya yi sa’ad da yake duniya suna nuni ga abubuwan da za mu ji daɗinsu a sarautarsa na shekara dubu.