Kana Bukatar Jimiri
BAYAN Anita * ta yi baftisma a matsayin Mashaidiyar Jehobah, sai mijinta ya soma tsananta mata sosai. Ta ce: “Ya hana ni zuwa taro kuma ya ce kada in ambaci sunan Allah. Duk lokacin da na kira sunan Jehobah sai ya hasala.”
Wani ƙalubale da Anita take fuskanta ya ƙunshi koya wa yaranta game da Jehobah. Ta ce: “An hana bautar Jehobah a cikin gidana. Ba na iya yin nazari da ’ya’yana a fili kuma ban isa in kai su taro ba.”
Labarin Anita ya nuna cewa hamayya daga dangi ko iyali zai iya gwada amincinmu. Haka ma yake da rashin lafiya mai tsanani da kuma mutuwar wani a iyalinmu. Ko kuma idan wani a iyalinmu ya daina bauta wa Jehobah. Shin mene ne zai taimaka wa Kirista ya kasance da aminci a irin wannan yanayin?
Mene ne za ka yi a irin wannan yanayin? Manzo Bulus ya ce: Kana “bukatar haƙuri” ko kuma jimiri. (Ibran. 10:36) Shin me zai taimaka maka ka jure?
KA DOGARA GA JEHOBAH TA YIN ADDU’A
Wani abu da zai taimaka mana mu jure shi ne yin addu’a ga Allah. Alal misali, wani abu ya faru da iyalin wata ’yar’uwa mai suna Ana a wata ranar Litinin, mijinta da suka yi shekara 30 da aure ya mutu. Ana ta ce: “Ya je aiki kuma bai sake dawowa ba, shekararsa 52 ne kawai.”
Mene ne ya taimaka wa Ana? Ta koma aiki kuma hakan ya taimaka mata don aikinta yana bukatar natsuwa sosai amma hakan bai hana ta yin baƙin ciki ba. Ta ce: “Na gaya wa Jehobah abin da yake ci min tuwo a ƙwarya kuma na roƙe shi ya ba ni ƙarfin hali na jure wannan babban rashi.” Shin Jehobah ya amsa addu’arta ne? Ta tabbata cewa ya yi hakan. Ta ce: “Allah ya ba ni kwanciyar hankali da natsuwa. Na tabbata cewa Jehobah zai ta da mijina daga matattu.”—Filib. 4:6, 7.
Jehobah “mai jin addu’a” ne kuma ya yi alkawari cewa zai tanadar wa bayinsa duk wani abin da suke bukata don su kasance da aminci a gare shi. (Zab. 65:2) Hakika, sanin hakan zai ƙarfafa ka kuma zai iya taimaka maka ka jure, ko ba haka ba?
TARON IKILISIYA YANA TAIMAKA MANA
Jehobah ya taimaka wa mutanensa ta ikilisiyar Kirista. Alal misali, a lokacin da ikilisiyar da ke Tasalonika take fuskantar tsanantawa, manzo Bulus ya ƙarfafa su ‘yi ma junansu ta’aziya, su gina juna, kamar yadda suke yi.’ (1 Tas. 2:14; 5:11) Kiristoci da ke Tasalonika sun yi nasara a wannan lokacin gwaji sa’ad da suka kusaci da kuma taimaka wa juna. Sun kafa mana misali mai kyau a yadda suka nuna jimiri don hakan ya nuna mana abin da zai taimaka mana mu jimre.
Ƙulla abota ta kud da kud da ’yan’uwa a cikin ikilisiya zai iya taimaka mana mu yi “abubuwa waɗanda za mu gina junanmu da su.” (Rom. 14:19) Hakan yana da muhimmanci musamman ma a mawuyacin lokaci. Bulus da kansa ya fuskanci matsaloli da yawa kuma Jehobah ya taimaka masa ya jimre. A wani lokaci, Allah ya yi amfani da ’yan’uwa don ya ƙarfafa Bulus. Alal misali, sa’ad da Bulus yake aika saƙon gaisuwa wa ’yan ikilisiyar da ke Kolosi, ya ce su ne “waɗanda suka yi mini ta’aziyya.” (Kol. 4:10, 11) Hakika, sun ƙarfafa Bulus a lokacin da yake cikin matsala saboda yadda suke ƙaunarsa. Wataƙila, kai ma ka taɓa samun irin wannan ƙarfafa daga ’yan’uwa a cikin ikilisiyarku.
KA NEMI TAIMAKO DAGA DATTAWA
Akwai wata hanya kuma da Allah yake tanadar da taimako a cikin ikilisiya, wato ta wurin Isha. 32:2) Babu shakka, hakan yana da ban ƙarfafa. Shin kana neman taimako daga wurin dattawa kuwa? Taimako da kuma ƙarfafa da suke bayarwa za su iya taimaka maka ka jimre.
dattawa. Waɗannan ’yan’uwa maza da suka manyanta suna “kamar maɓoya daga iska, makāri kuma daga hadarin ruwa; kamar koguna cikin ƙeƙasashiyar ƙasa, kamar inuwar babban dutse cikin ƙasa mai-agazari.” (Ko da yake, dattawa ba za su iya magance duka matsalolinka ba. Ƙari ga haka, su ajizai ne kamar kai, wato ‘mutane ne da ɗabi’a kamar tamu.’ (A. M. 14:15) Duk da haka, idan suka yi addu’a a madadinmu, za mu sami kwanciyar hankali. (Yaƙ. 5:14, 15) Wani ɗan’uwa a ƙasar Italiya da ya yi shekaru da yawa yana fama da wata muguwar cuta ya ce: “Yadda ’yan’uwan suka so ni da kuma yadda suke kawo min ziyara a kowane lokaci ya sa na jimre.” Idan kana fama da wata matsala, za ka iya gaya wa dattawa su taimaka maka.
KA CI GABA DA ƘARFAFA DANGANTAKARKA DA JEHOBAH
Har ila, akwai wasu abubuwa da za su iya taimaka mana mu jimre. Na ɗaya shi ne ka ci gaba da ƙarfafa dangantakarka da Jehobah. Ka yi la’akari da misalin wani ɗan’uwa mai shekara 39 mai suna John da likita ya ce yana da cutar kansa. Ya ce: “Ban ji daɗi ba ko kaɗan don ban tsufa ba.” A lokacin, ɗan John, yana da shekara uku kawai. Ya ci gaba da cewa: “Hakan yana nufin cewa matata za ta kula da ɗanmu kuma za ta yi jinyata. Ƙari ga haka, za ta riƙa taimaka mini zuwa asibiti.” Jinyar cutar kansar tana sa John gajiya da kuma ciwon ciki. Ban da haka, mahaifin John ya soma ciwon ajali kuma ya bukaci a kula da shi.
Mene ne John da kuma iyalinsa suka yi a wannan mawuyacin yanayi? Ya ce: “Duk da gajiyar da nake ji, na tabbata cewa muna yin abubuwan da ke ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah. Muna halartan duka taro, muna fita wa’azi kowane mako kuma muna yin ibada ta iyali, ko da yin hakan bai da sauƙi a wani lokaci. Hakika, John ya shaida cewa ci gaba da ƙarfafa dangantaka da Jehobah, yana da taimaka wa sosai wajen jure kowace irin matsala. John ya ba da wannan shawara ga waɗanda suke fuskantar mawuyacin yanayi: “Ko da yake abin ya jijjiga ni, amma daga baya, na sami kwanciyar hankali don na shaida cewa Jehobah yana ƙaunata kuma yana ƙarfafa ni. Saboda haka, na daina yawan tunani. Jehobah zai ƙarfafa ka, kamar yadda ya ƙarfafa ni.”
Hakika, da taimakon Jehobah, za mu iya jimre mawuyacin yanayi da muke fuskanta yanzu ko kuma za mu fuskanta a nan gaba. Bari mu ci gaba da dogara ga Jehobah ta yin addu’a, mu kusaci ’yan’uwa da ke ikilisiyarmu, mu riƙa neman taimako daga wurin dattawa kuma mu ci gaba da ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah. Idan muka yi hakan, muna bin shawarar manzo Bulus sa’ad da ya ce: “Kuna . . . bukatar [jimiri].”
^ sakin layi na 2 An canja wasu sunaye.