“Tun da Kingsley Ya Yi, Ni Ma Zan Iya!”
KINGSLEY ya soma karanta Littafi Mai Tsarki sa’ad da aka taɓa shi a kafaɗa. Wannan shi ne jawabinsa na farko a Makarantar Hidima ta Allah a ikilisiyar. Yana furta kowace kalma ba tare da kuskure ba. Amma, ba ya kallon Littafi Mai Tsarki yayin da yake karatun. Me ya sa?
Kingsley wani makaho ne da ke zama a ƙasar Siri Lanka. Ƙari ga haka, ba ya jin magana sosai kuma shi gurgu ne da ke yawo da keken guragu. Shin ta yaya wannan mutum ya san Jehobah kuma ya zama ɗalibi a Makarantar Hidima ta Allah? Barin in ba ka labari.
Lokacin da na haɗu da Kingsley, na yi mamakin yadda yake son koyon gaskiya da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Shaidun Jehobah da dama sun riga sun yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Littafinsa na Sanin Da ke Bishe Zuwa Rai na Har Abada na makafi ya riga ya tsufa. * Ya amince in yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi, amma mun fuskanci wasu matsaloli biyu.
Na farko, Kingsley yana zama a wani gidan kula da tsofaffi da waɗanda suka naƙasa. Da yake ba ya ji sosai kuma saboda yanayin wurin, nakan ɗaga muryata sosai sa’ad da nake nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Saboda haka, kowa a wurin
yana jinmu sa’ad da muke nazari kowane mako.Na biyu, Kingsley ba ya fahimtar abubuwa da yawa a lokaci guda sa’ad da na yi nazari da shi. Saboda haka, yana yin shiri da kyau don ya amfana daga nazarin. Yakan karanta inda za mu yi nazarinsa sau da yawa kuma ya duba nassosin da aka ambata daga nasa Littafi Mai Tsarki na makafi kafin lokacin nazarin. Ƙari ga haka, yakan shirya amsoshin kafin mu soma nazari. Irin wannan tsarin ya taimaka sosai. Sa’ad da muke nazari sai ya harɗe a kan dadduma yana bayyana abin da ya koya da farin ciki kuma da babbar murya. Da shigewar lokaci, sai muka soma nazari sau biyu a mako, kuma muna nazari mai tsawon awa biyu kowane lokaci.
HALARTAN TARO DA YIN KALAMI
Kingsley ya yi marmarin halartan taro a Majami’ar Mulki, amma yin hakan bai kasance da sauƙi ba. Yana bukatar taimako sa’ad da yake hawa da kuma sauka daga kekensa na guragu da mota da kuma sa’ad da yake shiga cikin Majami’ar Mulki. Amma ’yan’uwa da yawa sun taimaka masa bi da bi kuma sun yi farin ciki yin haka. Sa’ad da ake taro, Kingsley yakan sa kunnensa kusa da lasifika kuma ya saurari jawabai cikin natsuwa, har ma ya yi kalami!
Bayan na yi nazari da Kingsley na ɗan lokaci, sai ya yi rajista a Makarantar Hidima ta Allah. Makonni biyu kafin ya yi aikin da aka ba shi, wato karanta Littafi Mai Tsarki, sai na tambaye shi ko yana shiri. Ya ce, “E, Ɗan’uwa, na karanta wajen sau 30.” Sai na yaba masa kuma na ce ya karanta in ji. Ya buɗe Littafi Mai Tsarki na makafi kuma ya soma karatu. Amma sai na lura cewa ba ya saka yatsunsa a inda yake karantawa kamar yadda ya saba. Ashe, ya haddace karatun gaba ɗaya!
Abin ya ba ni mamaki kuma hawaye sun soma fita daga idanuna. Na tambaye Kingsley ta yaya ya iya haddace karatun gaba ɗaya bayan ya karanta sau 30 kawai. Ya ce: “A’a, a kowace rana, ina karantawa sau 30.” Kingsley yakan zauna a kan daddumarsa kuma ya karanta jawabin har ya haddace shi. Ya yi sama da wata ɗaya yana yin hakan.
Sai ranar da zai yi karatun a Majami’ar Mulki ya yi. Sa’ad da ya gama karatun, ’yan’uwa a ikilisiya suka yi masa tafi sosai, mutane da yawa sun yi kuka don irin ƙoƙarin da Kingsley ya yi. Wata mai shela da ta daina ba da jawabi a makarantar hidima saboda tsoro ta ce za ta sake shiga makarantar. Me ya sa? Ta ce, “Tun da Kingsley ya yi, ni ma zan iya!”
A ranar 6 ga Satumba ta shekara ta 2008 ne Kingsley ya yi baftisma, bayan na yi shekara uku ina nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Ya kasance da aminci har mutuwarsa a ranar 13 ga Mayu, 2014, Kingsley ya ba da gaskiya cewa a aljanna a duniya, zai ci gaba da bauta wa Jehobah da ƙarfi da kuma ƙoshin lafiya. (Isha. 35:5, 6)—Paul McManus ne ya ba da labarin.
^ sakin layi na 4 An wallafa shi a shekara ta 1995; yanzu an daina bugawa.