Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Kana Rayuwa Bisa Addu’ar Misali Kuwa?​—⁠Sashe na II

Kana Rayuwa Bisa Addu’ar Misali Kuwa?​—⁠Sashe na II

Ubanku ya san abin da ku ke bukata.”MAT. 6:8.

1-3. Me ya sa wata ’yar’uwa ta tabbata cewa Jehobah ya san bukatunmu?

WATA ’yar’uwa mai suna Lana ba za ta taɓa manta da wani abin da ya faru wata rana a Jamus a shekara ta 2012 ba. Tana ganin cewa Jehobah ya amsa addu’o’i guda biyu da ta yi. Ta yi addu’a ta farko a cikin jirgin ƙasa sa’ad da take zuwa wani tashar jirgin sama. Ta roƙi Jehobah ya ba ta zarafi ta yi wa’azi. Ta yi addu’a ta biyu bayan da ta isa tashar jirgin sama kuma aka gaya mata cewa an ɗaga tafiyar sai washegari. Lana ta yi addu’a cewa Allah ya taimake ta don kuɗinta ya kusan ƙarewa kuma ba ta da masauki.

2 Lana ba ta gama addu’arta ba sa’ad da ta ji wani ya ce mata, “Ya Lana, me kike yi a nan?” Wani abokin makarantarsu ne a dā yake mata magana. Saurayin yana tare da mahaifiyarsa da kakarsa, suna masa rakiya zuwa tasha don zai yi tafiya zuwa Afirka ta kudu. Da Lana ta gaya musu yanayin da take ciki, sai mahaifiyarsa mai suna Elke ta ce su je gidansu don ta sami wurin kwana. Elke mahaifiyar saurayin da kakansa sun kula da ita sosai kuma suka yi mata tambayoyi game da imaninta da kuma hidimar cikakken lokaci da take yi.

3 Washegari bayan sun karya, Lana ta ci gaba da amsa tambayoyin Littafi Mai Tsarki da suka yi mata kuma ta karɓi adireshinsu don a ci gaba da tattaunawa da su. Lana ta koma gida lafiya kuma ta ci gaba da hidimarta ta majagaba na kullum. Tana ganin cewa Jehobah “mai jin addu’a” ne ya amsa addu’o’inta kuma ya taimaka mata.—Zab. 65:2.

4. Waɗanne bukatu ne za mu tattauna?

4 Sa’ad da muke cikin matsala, mukan yi addu’a ba tare da ɓata lokaci ba, kuma Jehobah yana farin cikin jin addu’o’in masu bauta masa da aminci. (Zab. 34:15; Mis. 15:8) Amma, idan muka yi bimbini a kan addu’ar misali, za mu ga cewa akwai wasu bukatu masu muhimmanci da muke bukata mu yi addu’a a kansu. Alal misali, ka yi la’akari da yadda aka bayyana mana yadda za mu ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah a cikin batutuwa uku da muka tattauna a talifin da ya gabata. Shin da abin da za mu yi don mu yi rayuwar da ta jitu da batu na huɗu da ya shafi abincinmu na yau?—Karanta Matta 6:11-13.

“KA BA MU YAU ABINCIN YINI”

5, 6. Ko da muna da isashen abin biyan bukatu, me ya sa roƙon abincinmu na yau yake da muhimmanci?

5 Ka lura cewa Yesu ya ce mu roƙi a ba “mu” abincin yini, ba a ba “ni” ba. Wani mai kula da da’ira a Afirka mai suna Victor ya ce: “Ina gode wa Jehobah sosai cewa ni da matata ba ma damuwa game da yadda za mu sami abinci da kuma kuɗin haya. ’Yan’uwa suna kula da mu kullum. Amma, ina wa waɗanda suke taimaka mana addu’a cewa Allah ya ba su basira don su sami biyan bukata duk da matsalolin kuɗi da suke fuskanta.”

6 Idan muna da isashen abinci na kwanaki da yawa, muna iya tuna da ’yan’uwa da suke cikin talauci ko kuma waɗanda bala’i ya addabe su. Ya kamata mu yi addu’a a madadinsu kuma mu ɗauki wasu matakai don mu taimaka musu. Alal misali, muna iya ba wa ’yan’uwanmu abubuwan da suke bukata. Muna iya ba da gudummawa a kai a kai ga aikinmu na dukan duniya don mun san cewa ana amfani da kuɗaɗen nan a hanyar da ta dace.—1 Yoh. 3:17.

7. Ta yaya Yesu ya kwatanta shawarar da ya ba mu cewa “kada fa ku yi alhini a kan gobe”?

7 Mai yiwuwa, sa’ad da Yesu yake magana game da abincinmu na yau, yana nufin bukatunmu na yanzu ne. Saboda haka, ya bayyana cewa Allah yana suturtar da furannin jeji, sai ya ce: “Balle ku, ku masu-ƙanƙantar bangaskiya? Kada ku yi alhini fa, kuna cewa . . . da mene ne za mu yi sutura?” Ya kammala maganar da wannan shawara mai muhimmanci: “Kada fa ku yi alhini a kan gobe.” (Mat. 6:30-34) Hakan ya nuna cewa bai kamata mu so abin duniya ba, maimakon haka, mu kasance da wadar zuci game da bukatunmu na yau da kullum. Waɗannan bukatun sun ƙunshi samun gidan da ya dace, aiki don kula da iyalinmu, da kuma hikimar tsai da shawarwari masu kyau a batun jinya. Ba zai dace mu riƙa yin addu’a don waɗannan bukatu kawai ba. Bukatu da suka shafi dangantakarmu da Jehobah sun fi muhimmanci.

8. Wace bukata ce mai muhimmanci ya kamata kalamin Yesu game da abincinmu na yau ya tuna mana? (Ka duba hoton da ke shafi na 25.)

8 Ya kamata yadda Yesu ya ambata abincinmu na yau ya sa mu tuna da bukatunmu da suka shafi dangantakarmu da Jehobah. Yesu ya ce: “Ba da abinci kaɗai ba mutum za ya rayu, amma da kowace magana da ke fitowa daga bakin Allah.” (Mat. 4:4) Saboda haka, ya kamata mu ci gaba da yin addu’a cewa Jehobah ya ci gaba da yi mana tanadin abin da zai ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah.

“KA GAFARTA MANA LAIFOFINMU”

9. Me ya sa zunubanmu suke kama da ‘bashi’?

9 Me ya sa Yesu ya ce: “Ka yafe mana basusukanmu.” Amma kuma a wani lokaci, ya ce: “Ka gafarta mana zunubanmu”? (Mat. 6:12, New World Translation; Luk. 11:4) Yesu ya faɗi hakan ne don zunubanmu suna kama da bashi. Fiye da shekaru 60 da suka shige, wannan mujallar ta bayyana cewa: “Idan muka yi zunubi kuma muka taka dokar Allah, tamkar mun ci bashinsa. . . . Allah zai iya ɗau ranmu don zunubin da muka yi. . . . Zai iya hana mu salama da muke mora daga wurinsa. . . . Ƙaunarsa kamar bashi ne a gare mu kuma idan muka yi masa biyayya, tamkar mun biya bashin, yin zunubi yana hana mu biyan wannan bashi ta ƙauna don zunubi kishiyan ƙauna ne a gaban Allah.”—1 Yoh. 5:3.

10. Mene ne muke bukatar mu yi don Jehobah ya gafarta mana zunubanmu, kuma yaya ya kamata mu ji game da hakan?

10 Muna yin zunubi kullum kuma muna bukatar gafara kullum, hakan ya nuna cewa hadayar da Yesu ya bayar ne kaɗai Jehobah zai yi amfani da ita don ya kawar da zunubanmu. Ko da yake, an ba da wannan fansa kusan shekaru 2,000 da suka shige, ya kamata mu riƙa nuna godiya kuma mu ɗauka kamar yau ne a ka ba da kyautar fansar. Fansar da aka biya don ranmu tana da tamani sosai, kuma babu ɗan Adam ajizi da zai yi biyan irin wannan fansar. (Karanta Zabura 49:7-9; 1 Bitrus 1:18, 19.) Hakika, ya kamata mu ci gaba da yi wa Jehobah godiya don wannan kyauta mai tamani. Ƙari ga haka, ya kamata wannan kalmar “zunubanmu” ta tuna mana cewa dukan masu bauta wa Jehobah suna bukatar wannan fansar da Allah ya tanadar don yafe zunubai. Hakika, Jehobah yana son mu riƙa mai da hankali ga mutane da kuma dangantakarsu da shi, har da waɗanda suka yi mana laifi. Irin waɗannan kurakurai suna ba mu damar nuna cewa muna ƙaunar ’yan’uwanmu kuma muna so mu gafarta musu yadda Allah ya gafarta mana.—Kol. 3:13.

Ka riƙa gafarta wa mutane idan kana son Allah ya gafarce ka (Ka duba sakin layi na 11)

11. Me ya sa yake da muhimmanci mu riƙa gafarta wa mutane?

11 Abin baƙin ciki shi ne, a wani lokaci mukan riƙe ’yan’uwanmu a zuciya, da yake mu ajizai ne. (Lev. 19:18) Idan muka gaya wa wasu batun, za su iya goyon bayanmu kuma hakan zai jawo matsala a cikin ikilisiya. Idan muka bar irin wannan yanayin ya ci gaba, hakan zai nuna cewa ba ma nuna godiya don jin kan Allah da kuma fansar. Idan ba ma gafarta wa ’yan’uwanmu, ba za mu amfana daga fansar da Ubanmu ya tanadar ba. (Mat. 18:35) Yesu ya ba da ƙarin haske a kan wannan bayan ya koyar da addu’ar misali. (Karanta Matta 6:14, 15.) Wajibi ne mu yi ƙoƙari mu guji yin zunubi mai tsanani idan muna son Allah ya gafarta mana. Da yake burinmu ne mu guji yin zunubi, Yesu ya yi roƙo na gaba.—1 Yoh. 3:4, 6.

“KADA KA KAI MU CIKIN JARABA”

12, 13. (a) Mene ne ya faru da Yesu jim kaɗan bayan ya yi baftisma? (b) Idan muka faɗa wa jaraba, me ya sa bai kamata mu ɗora wa wasu laifi ba? (c) Mene ne Yesu ya cim ma ta wajen kasancewa da aminci har mutuwarsa?

12 Yin la’akari da abin da ya faru da Yesu jim kaɗan bayan ya yi baftisma zai taimaka mana mu fahimci abin da ya sa muke bukatar mu yi wannan roƙon: “Kada ka kai mu cikin jaraba.” Yesu ya bi ja-gorar Ruhun Allah zuwa cikin jeji. Me ya sa? “Domin Shaiɗan shi yi masa jaraba.” (Mat. 4:1; 6:13) Hakan ba zai sa mu mamaki ba idan muka fahimci dalilin da ya sa Allah ya turo Ɗansa duniya. Ya zo ne don ya warware batun da aka ta da sa’ad da Adamu da Hawwa’u suka ƙi sarautar Allah. Ana bukatar lokaci don a warware wannan batun. Shin Allah ya halicci mutum da wani aibi ne? Shin zai yiwu ɗan Adam ajizi ya goyi bayan sarautar Allah idan “mugun” ya tsananta masa? Kuma kamar yadda Shaiɗan ya faɗa, shin ’yan Adam za su iya jin daɗin rayuwa idan Allah ba ya sarautarsu? (Far. 3:4, 5) Amsa waɗannan tambayoyin zai ɗauki lokaci amma zai nuna wa dukan mala’iku da ’yan Adam cewa Jehobah yana sarauta a hanyar da ta dace.

13 Jehobah mai tsarki ne kuma saboda haka ba ya jarabtar kowa da mugunta. Maimakon haka, Iblis ne “mai-jaraba.” (Mat. 4:3) Iblis yana iya jarabtar mu a hanyoyi dabam-dabam. Kowanenmu yana iya tsai da shawara ko zai faɗa wa jarabar ko a’a. (Karanta Yaƙub 1:13-15.) Yesu ya yi tsayayya da kowane gwaji ta wajen yin ƙaulin Kalmar Allah ba tare da ɓata lokaci ba. Ta hakan, Yesu ya kasance da aminci, amma Shaiɗan bai daina jarabtarsa ba, sai ya ‘jira wani zarafin da zai kuma dawo ya sake jarabtarsa.’ (Luk. 4:13) Yesu ya ci gaba da yin tsayayya ga dukan ƙoƙarin da Shaiɗan ya yi don ya ɓata dangantakarsa da Allah. Kristi ya ɗaukaka sarautar Jehobah kuma ya nuna cewa ɗan Adam zai iya kasancewa da aminci duk da mawuyacin gwaji da zai fuskanta. Amma, Shaiɗan yana ƙoƙari ya jarabci mabiyan Yesu, har da kai.

14. Mene ne muke bukatar mu yi don kada mu faɗa cikin jaraba?

14 Domin batun da ya shafi sarauta, Jehobah ya ƙyale mai jaraba ya jarabce mu da abubuwan da ke cikin duniya. Allah ba ya kai mu cikin jaraba, amma ya tabbata cewa za mu kasance da aminci kuma yana son ya taimaka mana. Amma, da yake Jehobah ya ba mu ’yancin zaɓan yin abin da muke son mu yi, ba ya hana mu faɗawa cikin jaraba. Wajibi ne mu yi abubuwa biyu, wato mu kusaci Jehobah kuma mu ci gaba da addu’a don ya taimaka mana. Ta yaya Jehobah yake amsa addu’o’inmu?

Ka ci gaba da ƙarfafa dangantakarka da Jehobah kuma ka kasance da ƙwazo a hidima (Ka duba sakin layi na 15)

15, 16. (a) Waɗanne jarabobi ne muke bukata mu gujewa? (b) Idan mutum ya faɗa cikin jaraba, laifin wane ne?

15 Jehobah yana tanadar mana da ruhunsa mai tsarki don ya ƙarfafa mu kuma ya taimaka mana kada mu faɗa wa jaraba. Allah yana yin amfani da Kalmarsa da kuma ƙungiyarsa don ya gargaɗe mu game da abubuwan da ya kamata mu guje wa, kamar ɓata lokaci da kuɗi da kuma kuzarinmu a kan abin duniya da ba su da muhimmanci. Espen da matarsa Janne suna zama a wata ƙasa mai arziki a Turai. Sun yi shekaru da yawa suna hidimar majagaba na kullum a wani ɓangaren ƙasar da ake bukatar masu shela sosai. Sun daina hidimar majagaba sa’ad da suka haifi ɗansu na fari, kuma yanzu suna da yara biyu. Maigidan ya ce: “Mukan yi wa Jehobah addu’a cewa ya taimake mu kada mu faɗa a cikin jaraba yanzu da ba ma samun damar yin hidima kamar dā. Mukan roƙi Jehobah ya taimake mu mu ci gaba da ƙarfafa dangantakarmu da shi kuma mu kasance da ƙwazo a hidimarsa.”

16 Wata jaraba da muke bukatar mu guje wa ita ce kallon batsa. Kada mu ɗora wa Shaiɗan laifi idan muka faɗa wa irin wannan jaraba. Me ya sa? Domin Shaiɗan da duniyarsa ba za su iya tilasta mu mu yi zunubi ba. Wasu sun faɗa wa jarabar kallon batsa saboda tunanin banza da suke yi. Amma za mu iya yin tsayayya, kamar yadda ’yan’uwanmu da yawa suka yi.—1 Kor. 10:12, 13.

“KA CECE MU DAGA MUGUN”

17. (a) Ta yaya za mu yi rayuwar da ta jitu da roƙon nan a cece mu daga mugun? (b) Wane abin farin ciki ne zai faru nan ba da daɗewa ba?

17 Don mu yi rayuwar da ta jitu da roƙonmu “ka cece mu daga mugun,” wajibi ne mu yi ƙoƙari mu kasance ‘ba na duniyar [Shaiɗan] ba.’ Ƙari ga haka, ‘kada mu yi ƙaunar duniyar [Shaiɗan], ko abubuwan da ke cikin duniya.” (Yoh. 15:19; 1 Yoh. 2:15-17) Wajibi ne mu ci gaba da wannan gwagwarmaya. Amma, za mu yi farin ciki sa’ad da Jehobah ya amsa wannan addu’a kuma ya kawar da Shaiɗan da duniyarsa! Ƙari ga haka, ya kamata mu tuna cewa sa’ad da aka jefo da Shaiɗan daga sama, ya san cewa lokacinsa kaɗan ya rage. Saboda haka, yana hasala sosai kuma yana iya ƙoƙarinsa don ya sa mu daina bauta wa Jehobah. Shi ya sa ya dace mu ci gaba da roƙon Allah ya cece mu daga wannan mugun.—R. Yoh. 12:12, 17.

18. Mene ne za mu riƙa yi don mu tsira daga duniyar Shaiɗan?

18 Shin kana son ka yi rayuwa a duniyar da Shaiɗan ba zai kasance ba? Idan haka ne, ka ci gaba da yin addu’a Mulkin Allah ya tsarkake sunan Allah kuma ya sa a yi nufinsa a duniya. Ka dogara ga Jehobah don ya kula da kai kuma ya yi maka tanadin dukan abubuwan da kake bukata don ka kasance da aminci a gare shi. Hakika, ka ƙuduri niyyar yin rayuwa bisa addu’ar misali.