Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Yana da Muhimmanci a San da Aikinka Ne?

Yana da Muhimmanci a San da Aikinka Ne?

BEZALEL da Oholiab ƙwararrun masu sana’a ne. Mai yiwuwa sun yi aiki tuƙuru a gina bulo a ƙasar Masar sa’ad da suke zaman bayi. Amma shekaru da yawa sun wuce bayan haka. Yanzu sun zama ƙwararrun maƙera don an ba su aikin ƙera mazauni. (Fit. 31:1-11) Mutane da yawa ba su ga abubuwa masu kyau da suka ƙera ba. Shin sun karaya ne da yake mutane kaɗan ne suka san da aikinsu? Yana da muhimmanci a san cewa su ne suka yi aikin? Yana da muhimmanci a san da aikinka ne?

AYYUKA MASU BAN SHA’AWA DA MUTANE KAƊAN NE SUKA GANI

Wasu abubuwan ado da aka ƙera don mazaunin suna da gwanin kyau. Alal misali, ka yi la’akari da kerubobin zinariya da aka ƙera a kan sandukin alkawari. Manzo Bulus ya ce suna da “daraja.” (Ibran. 9:5) Babu shakka, waɗannan ƙere-ƙere da aka yi da zinariya za su kasance da ban sha’awa sosai.—Fit. 37:7-9.

Idan aka sami waɗannan kayayyakin da Bezalel da Oholiab suka ƙera a yau, za su cancanci a adana su a manyan gidajen ajiye kayan tarihi don jama’a su gani. Amma a lokacin da aka ƙera waɗannan kayayyakin masu matuƙar kyau, mutane ƙalilan ne suka sami zarafin ganinsu. Babban firist ne kawai yake samun zarafin ganin waɗannan kayayyakin sa’ad da ya shiga cikin wuri mafi tsarki sau ɗaya a shekara, wato a Ranar Kafara. (Ibran. 9:6, 7) Saboda haka, ba mutane da yawa ba ne suka ga waɗannan ƙere-ƙere masu kyau ba.

SAMUN GAMSUWA DAGA AIKINKA YA DANGANA GA MENE NE?

In da a ce kai ne Bezalel ko Oholiab kuma ka yi aiki tuƙuru don ka ƙera waɗannan kayayyaki masu kyau, yaya za ka ji idan ka san cewa mutane kaɗan ne suka san da aikinka? A yau mutane suna gamsuwa da aikinsu idan tsaransu suka yabe su. Suna gani cewa ta hakan ne za su san cewa aikinsu yana da daraja. Amma bayin Jehobah dabam suke. Suna jin daɗin yin nufin Jehobah don sun san cewa ya amince da aikinsu.

A zamanin Yesu, shugabannin addini sukan yi addu’a don su burge mutane. Amma Yesu ya ba da wata shawara dabam, ya ce mu yi addu’a daga zuciyarmu kuma kada mu riƙa yin haka don mutane su yabe mu. Idan muka yi hakan, ‘Ubanmu kuwa wanda yake gani daga cikin ɓoye za ya sāka mana.’ (Mat. 6:5, 6) Hakan ya nuna cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne yadda Jehobah ya ɗauki addu’armu, ba yadda mutane suka ɗauka ba. Idan muka yi la’akari da ra’ayin Jehobah, addu’armu za ta kasance da ma’ana. Haka ma yake da duk wani abin da muka cim ma a hidimarmu ga Jehobah. Mun san cewa ko da mutane ba su san da aikinmu ba, yana da muhimmanci a gaban Jehobah “wanda yake gani daga cikin ɓoye” kuma yana faranta masa rai.

Sa’ad da aka gama ƙera mazaunin sai “girgijen ya rufe tent na taruwa, darajar Ubangiji kuma ta cika mazaunin.” (Fit. 40:34) Hakan ya nuna cewa Jehobah ya amince da aikin. Yaya kake ganin Bezalel da Oholiab suka ji a lokacin? Babu shakka sun yi farin cikin sanin cewa Allah ya albarkaci aikinsu ko da ba a rubuta sunayensu a kan abubuwan da suka ƙera ba. (Mis. 10:22) Hakika, sun yi farin cikin shaida yadda aka ci gaba da yin amfani da kayayyakin da suka ƙera a bautar Jehobah a shekarun da suka biyo baya. Idan aka ta da Bezalel da Oholiab daga matattu a sabuwar duniya, za su yi farin ciki sosai idan aka gaya musu cewa an yi wajen shekaru 500 ana amfani da mazaunin don ɗaukaka bauta ta gaskiya.

Ko da ba wanda yake ganin aikin da kake yi, Jehobah yana gani!

A ƙungiyar Jehobah a yau, masu tsara bidiyon katoon na zamani da masu fasaha da masu ɗaukan hoto da masu fassara da masu rubuce-rubuce suna aikinsu a bayan fage, wato mutane da yawa ba sa ganin aikin da suke yi. Haka ma yake da ayyukan da ake yi a ikilisiyoyi fiye da 110,000 da ke faɗin duniya. Mutane ba sa ganin aikin da bawa mai-kula da lissafin kuɗi yake yi a ƙarshen wata. Hakan nan ma, ba wanda yake ganin aikin da sakatare yake yi sa’ad da yake shirya rahotannin wa’azi. Ƙari ga haka, wane ne yake lura da ɗan’uwan da yake gyare-gyare a Majami’ar Mulki?

Bezalel da Oholiab ba su sami wata lambar yabo ko kofi ko garkuwa saboda ayyuka masu gwanin kyau da suka yi ba. Amma sun sami abin da ya fi hakan daraja, wato Jehobah ya amince da aikinsu. Muna da tabbaci cewa Jehobah ya lura da ayyukansu. Bari mu yi koyi da su a yadda suka kasance da tawali’u kuma suka yi aiki da son rai.