Ka Guji Tarayyar Banza a Wadannan Kwanaki na Karshe
“Zama da miyagu ta kan ɓata halaye na kirki.”—1 KOR. 15:33.
WAƘOƘI: 73, 119
1. Wane zamani ne muke ciki a yanzu?
MUNA rayuwa a mawuyacin lokaci. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa an soma “kwanaki na ƙarshe” a shekara ta 1914. A waɗannan “miyagun zamanu,” yanayin duniya ya lalace sosai fiye da yadda yake kafin wannan shekara. (2 Tim. 3:1-5) Bugu da ƙari, duniya za ta ci-gaba da lalacewa domin Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa “miyagun mutane da masu-hila za su daɗa mugunta gaba gaba.”—2 Tim. 3:13.
2. Waɗanne irin nishaɗi ne mutane da yawa suke jin daɗinsa a yau? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)
2 Mutane da yawa suna kallo ko kuma yi abubuwa da Littafi Mai Tsarki ya haramta kamar su ayyukan mugunta ko lalata ko sihiri ko kuma wasu abubuwan da ba su dace ba. Alal misali, sau da yawa Intane da shirye-shiryen talabijin da fina-finai da littattafai da kuma talifofin mujallu suna ɗaukaka mugunta da kuma lalata. A dā, mutane suna ƙyamar waɗannan abubuwa amma yanzu a wasu wurare doka ta amince da su. Amma, Allah ba ya son waɗannan halayen.—Karanta Romawa 1:28-32.
3. Yaya ake ɗaukan waɗanda suke bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki?
1 Bit. 4:4) A yau, mutane suna yin mamaki game da irin rayuwa da waɗanda suke bin ƙa’idodin Allah suke yi. Ƙari ga haka, ‘dukan waɗanda suke so su yi rai mai-ibada [“rayuwa ta ibada,” New World Translation] cikin Kristi Yesu za su sha tsanani.’—2 Tim. 3:12.
3 Mabiyan Yesu a ƙarni na farko sun guji yin nishaɗin da bai dace ba. Kuma sun bi ƙa’idodin Allah. Saboda haka an zarge su kuma an tsananta musu. Manzo Bitrus ya ce: “Suna maishe shi abin mamaki da ba ku [Kiristoci] yi gudu tare da su zuwa cikin haukar lalata irin tasu, suna aibatanku.” (“ZAMA DA MIYAGU TAKAN ƁATA HALAYE NA KIRKI”
4. Wane gargaɗi ne Littafi Mai Tsarki ya ba mu game da wannan duniya?
4 Littafi Mai Tsarki ya gargaɗi waɗanda suke son su yi nufin Allah kada su so wannan duniya da kuma ayyukanta. (Karanta 1 Yohanna 2:15, 16.) Shaiɗan Iblis “allah na wannan zamani” ne yake ja-gorar ƙungiyoyin addini da siyasa da kasuwanci da kuma kofofin yaɗa labarai na wannan duniya. (2 Kor. 4:4; 1 Yoh. 5:19) Saboda haka, a matsayinmu na Kiristoci, muna bukatar mu guji tarayyar banza. Kalmar Allah ta ce: “Kada ku yaudaru: zama da miyagu ta kan ɓata halaye na kirki.”—1 Kor. 15:33.
5, 6. Da waɗanne irin mutane ne ya kamata mu guji yin tarayya da su, kuma me ya sa?
5 Idan ba ma son mu ɓata halinmu, wajibi ne mu guji yin tarayya da mutanen da ke yin abubuwan da ba su da kyau. Hakan ya haɗa da waɗanda suke da’awa cewa suna bauta wa Jehobah amma suna taka dokokin Allah da gangan. Ba za mu ci-gaba da yin tarayya da su ba idan sun yi zunubi mai tsanani kuma sun ƙi su tuba.—Rom. 16:17, 18.
6 Idan muna tarayya da waɗanda ba sa bin dokokin Allah, muna iya soma yin abubuwan da suke yi don su amince da mu. Alal misalin, idan muna tarayya da waɗanda suke lalatar jima’i, muna iya soma bin halinsu. Hakan ya faru da wasu Kiristoci, kuma an yi wa wasu a cikinsu yankan zumunci domin sun ƙi su tuba. (1 Kor. 5:11-13) Idan ba su komo ga Jehobah ba, yanayinsu zai zama kamar yadda Bitrus ya kwatanta a waɗannan ayoyin.—Karanta 2 Bitrus 2:20-22.
7. Su waye ne ya kamata mu yi abota na kud da kud da su?
7 Ko da yake muna son mu yi wa waɗanda ba sa bin dokokin Allah alheri, bai kamata mu zama abokansu na kud da kud ba. Saboda haka, ba zai dace Shaidun Jehobah su riƙa fita zance da waɗanda ba su yi baftisma ba da kuma waɗanda ba sa bin ƙa’idodin Jehobah. Kasancewa da aminci yana da muhimmanci fiye da yin tarayya da waɗanda ba sa bin dokokin Jehobah. Ya kamata abokanmu su zama waɗanda suke yin nufin Allah. Yesu ya ce: “Iyakar wanda za ya aika nufin Allah, shi ne ɗan’uwana, da ’yar’uwata, da uwata.”—Mar. 3:35.
8. Ta yaya tarayyar banza ta shafi Isra’ilawa ta dā?
8 Isra’ilawa sun yi tarayyar banza kuma sun sha wahala saboda haka. Sa’ad da Jehobah ya cece su daga hannun mutanen Masar kuma ya ja-gorance su su shiga Ƙasar Alkawari, ya yi musu gargaɗi game da mazauna ƙasar, ya ce: ‘Ba za ku yi sujada ga allolinsu ba, ba kuwa za ku bauta masu ba, ba kuwa za ku yi bisa ga al’amuransu ba: amma za ku rushe su sarai, ku farfashe umudansu. Za ku bauta wa Ubangiji Allahnku.’ (Fit. 23:24, 25) Yawancin Isra’ilawa ba su bi umurnin Allah ba. (Zab. 106:35-39) Saboda haka, Yesu ya ce game da su: “Ga shi, an bar muku gidanku kango.” (Mat. 23:38) Jehobah ya yi watsi da Isra’ilawa, kuma ya zaɓi ikilisiyar Kirista a matsayin mutanensa.—A. M. 2:1-4.
KA YI HANKALI DA ABIN DA KAKE KALLO DA KUMA KARANTAWA
9. Me ya sa nishaɗi na wannan duniya yake da lahani?
9 Yawancin nishaɗi da ake tanadarwa a kofofin watsa labarai da shirye-shiryen talabijin da intane da littattafai na wannan duniya suna iya ɓata dangantakarmu da Jehobah. Irin waɗannan abubuwa ba sa taimaka mana mu kasance da bangaskiya ga Jehobah da kuma alkawuransa. Maimakon haka, suna ƙarfafa mutane su dogara ga wannan duniya ta Shaiɗan. Saboda haka, muna bukatar mu mai da hankali sosai don kada mu zaɓi nishaɗi da zai sa mu soma “sha’awoyi na duniya.”—Tit. 2:12.
10. Mene ne zai faru da mugun nishaɗi da ake ɗaukakawa a wannan duniya?
10 Ba da daɗewa ba, mugun nishaɗi da ake ɗaukakawa a wannan duniya ba zai ƙara kasancewa ba. Za a kawar da dukansu sa’ad da aka halaka duniyar Shaiɗan. Kalmar Allah ta ce: “Duniya ma tana wucewa, duk da sha’awatata: amma wanda ya aika nufin Allah ya zauna har abada.” (1 Yoh. 2:17) Hakazalika, marubucin zabura ya ce: “Za a datse masu-aika mugunta: amma waɗanda ke sauraro ga Ubangiji, su ne za su gāji duniya. Amma masu-tawali’u za su gāji ƙasan; za su faranta zuciyarsu kuma cikin yalwar salama.” Har zuwa wane lokaci? “Masu-adalci za su gāji ƙasan, su zauna a cikinta har abada.”—Zab. 37:9, 11, 29.
11. Ta yaya Allah yake tanadar wa mutanensa abubuwan da ke ƙarfafa dangantakarsu da shi?
11 Abubuwan da ƙungiyar Jehobah take wallafawa sun bambanta da na duniyar nan domin suna sa mutane su koyi halin da zai sa sami rai na har abada. Sa’ad da Yesu yake addu’a ga Jehobah, ya ce: “Rai na har abada ke nan, su san ka, Allah makaɗaici mai-gaskiya, da shi kuma wanda ka aiko, Yesu Kristi.” (Yoh. 17:3) Ta wurin ƙungiyarsa, Ubanmu da ke sama yana tanadar mana da abubuwa da za su ƙarfafa dangantakarmu da shi. Alal misali, muna da mujallu da ƙasidu da littattafai da bidiyo da bayanai a dandalinmu na intane da ke taimaka mana mu ci-gaba da bauta wa Allah. Ƙari ga haka, ƙungiyar Allah ta shirya a riƙa yin taro a kai a kai a cikin ikilisiyoyi fiye da 110,000 a faɗin duniya. A wuraren taron nan da manyan taro, muna nazarin littattafai da ke sa mu kasance da bangaskiya ga Allah da kuma alkawuransa.—Ibran. 10:24, 25.
KA AURI MAI BIN UBANGIJI KAƊAI
12. Ka bayyana abin da ake nufi da auren “mai bin Ubangiji” kaɗai.
12 Kiristoci da suke neman aure suna bukatar su mai da hankali game da waɗanda suke tarayya da su. Kalmar Allah ta ce: “Kada ku yi karkiya marar-dacewa tare da marasa-bangaskiya: gama wace zumunta ke tsakanin adalci da zunubi? ko kuwa wace tarayya haske ya ke da duhu?” (2 Kor. 6:14) Littafi Mai Tsarki ya gargaɗi bayin Allah su auri “mai bin Ubangiji” kaɗai, wato wanda ya yi baftisma a matsayinsa na Mashaidin Jehobah kuma yana bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. (1 Kor. 7:39, Littafi Mai Tsarki) Idan Kirista ya auri mai bi, abokiyar aurensa za ta taimaka masa ya kasance da aminci ga Jehobah.
13. Wane umurni ne game da aure Allah ya ba Isra’ilawa?
13 Jehobah ya san abin da ya dace da bayinsa, kuma bai canja umurninsa game da aure ba. Ka yi la’akari da umurnin da Jehobah ya ba Isra’ilawa ta hannun Musa game da mutanen al’ummai da ke kusa da su, ya ce: ‘Ba za ka yi surukuta da su ba; ɗiyarka ba za ka ba ɗansa ba, ba kuwa za ka ɗauka ma ɗanka ɗiyatasa ba. Gama za shi juyar da ɗanka ga barin bina, domin su bauta wa waɗansu alloli: hakanan fushin Ubangiji za ya yi ƙuna a kanka, ya hallaka ka farat ɗaya.’—K. Sha. 7:3, 4.
14, 15. Ta yaya yin watsi da gargaɗin Jehobah ya shafi Sulemanu?
14 Lokacin da Sulemanu ɗan Dauda ya zama sarkin Isra’ila, ya yi addu’a ga Jehobah ya ba shi hikima kuma Allah ya sa ya zama mai hikima sosai. Sarki Sulemanu ya zama sanannen sarki mai hikima da ke sarautar al’umma mai ni’ima. Sa’ad da sarauniyar Sheba ta ziyarci Sulemanu, ta ce: “Ban gaskanta zantattukan ba, sai lokacin da na zo, idanuna sun gani kuma; ga shi kuwa, ko rabi ba a faɗa mani ba: da hikimarka, da ni’imarka sun wuce gaban mashahurin sunan da na ji.” (1 Sar. 10:7) Amma, rayuwar Sulemanu ta nuna mana abin da zai iya faruwa da mutumin da ya ƙi bin umurnin Allah kuma ya auri wadda ba ta bauta wa Jehobah.—M. Wa. 4:13.
15 Duk da cewa Jehobah ya albarkaci Sulemanu sosai, ya yi watsi da umurnin Allah kuma ya auri matan da ba sa bauta wa Jehobah daga al’ummai da ke kusa da su. Sulemanu ya ‘ƙaunaci mata baƙi da yawa’ kuma ya auri mata 700 da ƙwaraƙwarai guda 300. Mene ne sakamakon? Lokacin da Sulemanu ya tsufa, matansa “suka juyar da zuciyarsa zuwa bin waɗansu alloli” kuma saboda haka, Sulemanu ya yi abin da ke mugu a idanun Ubangiji.” (1 Sar. 11:1-6) Tarayyar banza ya sa Sulemanu ya yi ɓatan basira kuma ya daina bauta wa Jehobah. Idan hakan ya faru da Sulemanu, zai iya faruwa da kowa. Shi ya sa ya dace Kirista ya guji yin tunanin auren wadda ba ta bauta wa Jehobah!
16. Wace shawara ce Littafi Mai Tsarki ya ba wanda ya riga ya yi aure kafin ya soma bauta wa Jehobah?
16 Mene ne mutum zai yi idan ya riga ya yi aure kafin ya soma bauta wa Jehobah? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku mataye kuma, ku yi zaman biyayya ga mazaje naku; domin ko da akwai waɗansu da ba su yin biyayya da magana, su rinjayu ban da magana saboda halayen matansu.” (1 Bit. 3:1) Ko da yake mata Kiristoci ne aka ba wannan umurnin, ƙa’idar ta shafi na miji da ya riga ya yi aure kafin ya soma bauta wa Jehobah. Wane darasi ne muka koya daga wannan ayar? Ka zama miji ko mace tagari kuma mai bin ƙa’idodin Allah game da aure. Idan mijinki ko matarka ta lura cewa kana bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki, shi ko ita tana iya soma bauta wa Jehobah.
KA YI CUƊANYA DA WAƊANDA SUKE ƘAUNAR JEHOBAH
17, 18. Me ya sa Nuhu da kuma Kiristocin ƙarni na farko suka tsira a lokacin da aka kawo ƙarshen zamaninsu?
17 Tarayyar banza takan ɓata halin kirki, amma cuɗanya mai kyau takan kawo sakamako mai kyau. Ka yi la’akari da Nuhu wanda ya yi rayuwa a muguwar duniya amma bai yi abota na kud da kud da mutanen ba. A lokacin, “Ubangiji ya ga muguntar mutum ta yi yawa cikin duniya, kuma kowacce shawara ta Far. 6:5) Saboda haka, Allah ya tsai da shawara ya halaka mugayen mutane na zamanin Nuhu ta yin amfani da rigyawa. Amma, “Nuhu mutum mai-adalci ne, marar-aibi ne cikin tsararakinsa: Nuhu yana tafiya tare da Allah.”—Far. 6:7-9.
tunanin zuciyarsa mugunta ce kaɗai kullayaumi.” (18 Hakika, Nuhu bai yi tarayya da mutanen da ba sa bauta wa Jehobah ba. Nuhu da matarsa da ’ya’yansu maza uku da matansu sun mai da hankali ga yin aikin da Allah ya ba su, kuma hakan ya ƙunshi gina jirgi. Ƙari ga haka, Nuhu “mai-shelan adalci” ne. (2 Bit. 2:5) Wa’azin da Nuhu ya yi da aikin gina jirgi da kuma cuɗanyarsa da iyalinsa sun sa ya shagala ga yin nagargarun ayyuka da suka faranta wa Allah rai. A sakamako, Nuhu da iyalinsa sun tsira a lokacin da aka yi Rigyawa. Dukanmu a yau zuriyarsu ne, saboda haka, ya kamata mu riƙa godiya don Nuhu da iyalinsa sun yi biyayya ga Jehobah kuma suka guji yin tarayyar banza. Hakazalika, Kiristoci na ƙarni na farko masu aminci ga Allah ba su yi tarayya da mugayen mutane na zamaninsu ba. A sakamako, sun tsira a lokacin da aka halaka Urushalima a shekara ta 70 bayan haihuwar Yesu.—Luk. 21:20-22.
19. Mene ne za mu yi don Allah ya amince da mu?
19 A matsayinmu na masu bauta wa Jehobah, ya kamata mu yi koyi da Nuhu da iyalinsa da kuma Kiristoci a ƙarni na farko masu aminci. Wajibi ne mu guji tarayya da mutanen wannan mugun zamani amma mu nemi abokai tsakanin ’yan’uwanmu da ke faɗin duniya. Yin tarayya da waɗanda Allah yake musu ja-gora zai taimaka mana mu “tsaya da ƙarfi cikin imani” a wannan mawuyacin lokaci. (1 Kor. 16:13; Mis. 13:20) Ka yi tunanin bege mai kyau da muke da shi! Idan muka guji tarayyar banza a waɗannan kwanaki na ƙarshe, muna iya yin rayuwa zuwa ƙarshen wannan mugun zamani kuma mu shiga sabuwar duniya ta Jehobah da ke nan tafe!