Ka Shirya Yanzu don Yin Rayuwa a Sabuwar Duniya
‘Su yi alheri, . . . domin su ruski rai wanda yake hakikanin rai.’—1 TIM. 6:18, 19.
WAƘOƘI: 125, 40
1, 2. (a) Waɗanne abubuwa ne za ka so ka mora a Aljanna a duniya? (Ka duba hoton da ke shafin nan.) (b) Mene ne zai fi sa mu farin ciki a sabuwar duniya?
IDAN muka ji furucin nan “hakikanin rai,” mukan yi tunanin rai na har abada a Aljanna a duniya. Manzo Bulus ya kwatanta “rai na har abada” da “hakikanin rai.” (Karanta 1 Timotawus 6:17-19.) Muna sai rai cewa za mu ci-gaba da yin rayuwa har abada cikin gamsuwa da farin ciki. Ka yi tunanin yadda za mu ji sa’ad da muka tashi kowace rana cikin ƙoshin lafiya da kwanciyar hankali. (Isha. 35:5, 6) Ƙari ga haka, za mu yi farin cikin yin cuɗanya da ’yan’uwa da abokai, hakan ya haɗa da waɗanda aka ta da su daga mutuwa! (Yoh. 5:28, 29; A. M. 24:15) Za mu sami zarafin inganta gwanintarmu game da kimiyya da kaɗe-kaɗe da zane-zanen gini da makamantansu.
2 Ko da yake muna begen jin daɗin waɗannan abubuwa, amma bauta wa Jehobah ne zai fi sa mu farin ciki a sabuwar duniya. Za mu yi murnan sanin cewa an tsarkake sunan Jehobah kuma dukan mutane sun amince da sarautarsa. (Mat. 6:9, 10) Ka yi tunanin yadda za mu ji sa’ad da muka ga yadda nufin Allah ga ’yan Adam da duniya yake cika. Ƙari ga haka, yayin da muke zama kamilai da sannu a hankali, kusantar Jehobah ba zai kasance da wuya ba.—Zab. 73:28; Yaƙ. 4:8.
3. Waɗanne matakai ne ya kamata mu ɗauka yanzu?
3 Mun gaskata cewa Jehobah zai cika duka waɗannan alkawuran don Yesu ya tabbatar mana cewa ‘ga Allah dukan abu [zai] yiwu.’ (Mat. 19:25, 26) Amma, idan muna so mu yi rayuwa a sabuwar duniya, kuma mu ci-gaba da rayuwa bayan Sarautar Yesu na Shekara Dubu, wajibi ne mu ɗauki matakai yanzu don mu sami rai na har abada. Ƙari ga haka, ya kamata mu yi rayuwa da sanin cewa ƙarshen zamanin nan zai zo ba da daɗewa ba, kuma mu ɗauki matakai da suka dace yanzu don mu yi shirin yin rayuwa a sabuwar duniya. Ta yaya za mu yi hakan yayin da muke jiran ƙarshen wannan mugun zamani?
YADDA ZA KA YI SHIRI
4. Ka kwatanta yadda za mu iya yin shiri yanzu don zama a sabuwar duniya.
4 Ta yaya za mu yi shiri yanzu don yin rayuwa a sabuwar duniya ta Allah? Alal misali, a ce muna shirin ƙaura zuwa wata ƙasa. Ta yaya za mu yi shiri? Za mu iya soma koyan yaren mutanen ƙasar. Wataƙila za mu koyi wasu al’adunsu. Za mu iya gwada cin wasu abincin da ake ci a ƙasar. Hakika, za mu soma yin rayuwa kamar mun riga mu soma zama a ƙasar. Hakan ya dace don irin rayuwar da za mu yi ke nan idan muka je ƙasar. Hakazalika, za mu iya yin shiri yanzu don zama a sabuwar duniya ta wajen bin salon rayuwar da za mu yi a lokacin. Bari mu bincika wasu hanyoyin da za mu iya yin hakan.
5, 6. Ta yaya bin ja-gorar ƙungiyar Jehobah yanzu zai taimaka mana mu yi shiri don yin rayuwa a sabuwar duniya?
5 A sabuwar duniya, za mu ji daɗin rayuwa don Jehobah ne zai yi sarauta. Hakan ya bambanta da zaman ’yancin kai da ake yi a wannan duniyar da Shaiɗan yake mulki. Mutane da yawa ba sa son sarautar Allah kuma suna son yin abin da suka ga dama, amma mene ne sakamakon haka? Da yake ’yan Adam sun yi watsi da sarautar Allah, hakan ya haddasa wahala, baƙin ciki da kuma masifa. (Irm. 10:23) Babu shakka, muna ɗokin lokacin da dukan ’yan Adam za su amince da sarautar Jehobah!
6 Za mu yi farin cikin kasancewa a ƙarƙashin sarautar Allah a sabuwar duniya yayin da muke yin ayyuka don mu mai da duniya wuri mai kyau, muna koyar da waɗanda aka ta da su daga mutuwa da kuma yin nufin Allah. Amma idan masu ja-gora a lokacin suka ce mu yi wani aiki da ba ma so fa? Shin za mu amince da ja-gorarsu kuma mu yi iya ƙoƙarinmu mu yi aikin da farin ciki? Hakika! Idan haka ne, shin muna bin ja-gorar da Allah yake bayarwa ta ƙungiyarsa a yanzu? Yin hakan ya nuna cewa muna shiri don yin rayuwa har abada a sabuwar duniya.
7, 8. (a) Me ya sa ya kamata mu nuna haɗin kai? (b) Waɗanne canje-canje ne wasu Kiristoci suka fuskanta? (c) Wane tabbaci ne za mu kasance da shi game da rayuwa a sabuwar duniya?
7 Ƙari ga haka, za mu iya yin shiri don rayuwa a sabuwar duniya ta kasancewa da wadar zuci da haɗin kai. Idan muka ba da haɗin kai ga waɗanda suke ja-gora a yau, hakan zai taimaka mana mu nuna haɗin kai a sabuwar duniya. (Karanta Ibraniyawa 13:17.) A Ƙasar Alkawari, an rarraba gado bisa ga sunayen ƙabilu. (Lit. Lis. 26:52-56; Josh. 14:1, 2) Hakika, yanzu ba mu san inda za a saka kowannenmu a sabuwar duniya ba. Amma haɗin kai zai sa mu kasance da wadar zuci da kuma matuƙar farin ciki yayin da muke yin nufin Jehobah a duk inda aka ce mu zauna a sabuwar duniya.
8 Yin rayuwa a Mulkin Allah ba ƙaramin gata ba ne. Saboda haka, muna farin ciki yin duk wani abin da ake bukata don mu ba da haɗin kai ga ƙungiyar Jehobah kuma mu yi aikin da aka danƙa mana. Ko da yake, da shigewar lokaci, yanayinmu zai iya canjawa. Alal misali, an tura wasu da ke hidima a Bethel na Amirka su yi hidima a matsayin masu wa’azi a wasu yankuna kuma suna samun albarka a wannan sashe na hidima ta cikakken lokaci. Saboda tsufa ko kuma wasu dalilai, an mai da wasu masu kula masu ziyara majagaba na musamman. Idan muka kasance da wadar zuci, muka roƙi Allah ya taimake mu kuma muka yi iya ƙoƙarinmu a aikin da ya ba mu, za mu yi farin ciki kuma za mu sami albarka sosai a wannan kwanaki na ƙarshe. (Karanta Misalai 10:22.) Wataƙila, a sabuwar duniya, za mu so mu zauna a wani wurin da muke so, amma za a iya ce mana mu koma wani wuri dabam. A duk inda muka zauna da kuma aikin da muka yi a lokacin, muna da tabbaci cewa za mu yi godiya kuma za mu yi wadar zuci da farin ciki sosai.—Neh. 8:10.
9, 10. (a) A waɗanne ɓangarori ne za mu bukaci mu kasance masu haƙuri a sabuwar duniya? (b) Ta yaya za mu nuna cewa mu masu haƙuri ne?
9 A sabuwar duniya, za mu bukaci mu kasance da haƙuri a wasu lokatai. Alal misali, za mu iya jin cewa an ta da wasu mutane daga mutuwa kuma hakan zai sa danginsu da abokansu su yi murna sosai. Amma wataƙila za mu jira zuwa wani lokaci kafin a ta da ƙaunatattunmu. Idan haka ne, shin za mu taya su murna kuma mu kasance da haƙuri? (Rom. 12:15) Idan muka kasance da haƙuri yanzu da muke jiran cikar alkawuran da Jehobah ya yi mana, hakan zai taimaka mana mu kasance da haƙuri a lokacin.—M. Wa. 7:8.
10 Za mu iya yin shiri don yin rayuwa a sabuwar duniya ta wajen zama masu haƙuri game da ƙarin haske da ake samu a koyarwar gaskiya. Shin muna yin nazarin waɗannan koyarwar, kuma muna yin haƙuri idan ba mu fahimci koyarwar sosai ba? Idan haka ne, ba zai yi mana wuya mu zama masu haƙuri a sabuwar duniya yayin da Jehobah yake bayyana umurninsa ga ’yan Adam ba.—Mis. 4:18; Yoh. 16:12.
11. Me ya sa ya dace mu riƙa gafarta wa juna yanzu, kuma ta yaya hakan zai taimaka mana a sabuwar duniya?
11 Wani hali kuma da zai taimaka mana a sabuwar duniya shi ne yin gafara. A Sarautar Yesu na Shekara Dubu, wataƙila zai ɗauki lokaci kafin masu adalci da marasa adalci su kawar da halayen da ba su da kyau. (A. M. 24:15) Shin za mu iya bi da juna cikin ƙauna a lokacin? Idan muna gafarta wa juna kuma muka yi ƙoƙari mu kasance da dangantaka mai kyau da mutane, yin hakan a sabuwar duniya ba zai yi mana wuya ba.—Karanta Kolosiyawa 3:12-14.
12. Me ya sa ya kamata mu yi shirin yin rayuwa a sabuwar duniya tun yanzu?
12 Rayuwa a sabuwar duniya ba ta nufin cewa za mu sami duk wani abin da muke so a lokacin da muke son sa. Za mu bukaci mu kasance masu godiya da wadar zuci a kowane yanayi yayin da muke yin biyayya ga Jehobah da kuma jin daɗin sarautarsa. Hakan yana nufin cewa za mu nuna halaye masu kyau da muke koya yanzu. Saboda haka, nuna waɗannan halayen yanzu zai taimaka mana mu ci-gaba da yin haka har abada. Ƙari ga haka, yin hakan zai sa mu ƙara kasance da bangaskiya game da sabuwar “duniya mai-zuwa.” Ibran. 2:5; 11:1) Ban da haka, za mu nuna cewa muna son mu yi rayuwa a ƙarƙashin yanayi na adalci da Allah zai kawo a lokacin. Hakika, muna yin shiri don yin rayuwa har abada a aljanna a duniya.
(KA MAI DA HANKALI YANZU GA ABUBUWAN DA SUKA SHAFI BAUTAR JEHOBAH
13. Waɗanne ayyuka ne za su fi muhimmanci a sabuwar duniya?
13 Ka yi la’akari da wata hanyar da za mu iya yin shiri don yin rayuwa a sabuwar duniya. Jehobah zai tanadar mana da abinci mai yawa da kuma wasu bukatu a sabuwar duniya, amma abubuwan da za su ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah ne za su fi sa mu farin ciki. (Mat. 5:3) Ibadarmu ga Jehobah za ta fi muhimmanci a gare mu kuma za mu ji daɗin bauta wa Jehobah. (Zab. 37:4) Idan muka saka dangantakarmu da Jehobah kan gaba yanzu, hakan ya nuna cewa muna shirin yin rayuwa a sabuwar duniya.—Karanta Matta 6:19-21.
14. Waɗanne maƙasudai ne matasa za su iya kafawa da za su taimaka musu a sabuwar duniya?
14 Ta yaya za mu ƙara yin farin ciki a ayyukan da muke yi a bautarmu ga Jehobah? Hanya ɗaya ita ce ta kafa maƙasudai. Idan kai matashi ne kuma kana tunanin yin amfani da rayuwarka a bautar Jehobah, zai dace ka yi binciken akan wasu bayanai da aka wallafa game da sassa dabam-dabam na hidima ta cikakken lokaci kuma ka biɗi ɗaya daga cikin waɗannan hidimomin. * Za ka iya neman shawara daga wasu da suka yi shekaru da yawa suna hidima ta cikakken lokaci. Idan ka yi amfani da rayuwarka a yin hidima ta cikakken lokaci, kana shirya kanka don yin hidima ga Allah a sabuwar duniya da yake abubuwan da ka koya yanzu za su taimaka maka ka ci-gaba da hidima a sabuwar duniya.
15. Waɗanne maƙasudai ne masu shelar Mulki za su iya kafawa?
15 A matsayinmu na masu shelar Mulki, waɗanne maƙasudai ne za mu iya kafa wa kanmu? Muna iya kafa maƙasudin koyon wata hanyar yin wa’azi. Ko kuma mu yi ƙoƙarin ƙara fahimtar ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da yadda za mu yi amfani da su a rayuwarmu. Ƙari ga haka, muna iya kyautata yadda muke karatu da ba da jawabi da kuma yadda muke kalami a taro. Kana iya yin tunanin wasu wurare da za
ka iya yin hakan. A taƙaice, idan mun kafa maƙasudai a ibadarmu ga Jehobah zai taimaka mana mu ƙara himma kuma ya shirya mu don yin rayuwa a sabuwar duniya.RAYUWA MAFI KYAU A YANZU!
16. Me ya sa bauta wa Jehobah ce hanyar rayuwa mafi kyau?
16 Shin idan muna yin shiri yanzu don shiga sabuwar duniya ta Allah, muna ɓata lokacinmu ne? A’a! Bauta wa Jehobah ita ce hanyar yin rayuwa mafi kyau. Ba wai muna bauta wa Jehobah domin ya sa mu dole ko kuma don muna so mu tsira a lokacin ƙunci mai girma ba. Jehobah ya halicce mu don mu bauta masa kuma sa’ad muka yi hakan, muna yin farin ciki sosai. Yin rayuwa bisa ja-gorar Jehobah da kuma ƙaunarsa ya fi kome. (Karanta Zabura 63:1-3.) Ko a yanzu ma, za mu yi farin ciki idan muka bauta wa Jehobah da dukan zuciyarmu. Hakika, wasu a cikinmu da suka yi shekaru da yawa suna bauta wa Jehobah sun san cewa hakan ita ce rayuwa da ta fi kyau.—Zab. 1:1-3; Isha. 58:13, 14.
17. Ta yaya za mu fi jin daɗin shaƙatawa da yin abubuwan da muke so a Aljanna?
17 A sabuwar duniya ta Allah, za mu ji daɗin yin abubuwan da muke so kuma za mu shaƙata. Jehobah zai biya mana wannan bukata don ya halicce mu da sha’awar yin abubuwan da muke so da kuma jin daɗin rayuwa. (M. Wa. 2:24) Ta hakan, Jehobah zai “biya wa kowane mai-rai muradinsa.” (Zab. 145:16) Muna bukatar shaƙatawa da kuma hutu, amma za mu fi jin daɗinsu idan muka sa bautarmu ga Jehobah farko a rayuwa. Hakan ne zai kasance a sabuwar duniya. Saboda haka, yana da muhimmanci mu saka al’amura na Mulki kan gaba kuma mu mai da hankali ga albarka da muke samu don muna bauta wa Jehobah.—Mat. 6:33.
18. Ta yaya za mu nuna cewa muna shirin yadda za mu yi rayuwa a sabuwar duniya?
18 Za mu ji daɗin rayuwa a sabuwar duniya sosai. Bari mu riƙa yin shiri yanzu don mu cim ma muradinmu na yin rayuwa har abada. Saboda haka, mu ci-gaba da koyan halaye masu kyau kuma mu yi wa’azin bishara da himma. Za mu yi farin ciki idan muka saka bautar Jehobah a kan gaba a rayuwarmu. Muna da tabbaci cewa a sabuwar duniya, Jehobah zai cika dukan alkawuransa. Saboda haka, bari mu yi shiri yanzu yadda za mu yi rayuwa a sabuwar duniya!
^ sakin layi na 14 Ka duba warƙar nan, Matasa—Me Za Ku Yi da Rayuwarku?