Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

“Marar Wayo Yana Gaskata Kowace Magana”

“Marar Wayo Yana Gaskata Kowace Magana”

“Wanda ba ya karanta jarida wawa ne; amma wanda yake yarda da kome da ya karanta a cikin jarida ya fi wauta.” —In ji August von Schlözer (1735-1809), wani marubuci da masanin tarihi daga Jamus.

IDAN har ba a gaskata da dukan abin da aka rubuta a cikin jarida shekaru 200 da suka shige ba, bai kamata a gaskata da dukan bayanai da muke da su a Intane a zamaninmu ba. Ana samun tabbataccen bayanai masu kyau da inganci a Intane, kuma ana samun bayanan ƙarya, marasa amfani kuma masu cutarwa a Intane. Saboda haka, wajibi ne mu yi hattara sosai wajen zaɓan abubuwan da muke karantawa a shafuffukan dandalai da yawa da ake samu a Intane. Wasu za su iya ɗauka cewa duk wani bayani da ke Intane gaskiya ne ko da yana da ban mamaki. Ko kuma su gaskata da wani abu don abokansu sun aika musu ta imel ko ta waya, musamman idan ba su saba amfani da Intane ba. Littafi Mai Tsarki ya ba da gargaɗi cewa: “Marar wayo yana gaskata kowace magana: Amma mai hankali yakan lura da al’amuransa da kyau.”—Mis. 14:15.

Wani lokaci, labarai marasa amfani da za su iya cutar da mu sukan ɓullo mana sa’ad da muke amfani da Intane. Ta yaya za ka kasance ‘mai hankali’ kuma ka san irin waɗannan labaran? Da farko, ka tambayi kanka: ‘Shin wannan bayanin daga tabbataccen dandali ne, ko kuma wani shafin Intane ne da ba a san tushenta ba? Wani dandalin intane mai fallasa bayanan ƙarya ya taɓa ambata cewa bayanin jabu ne?’ * Ka nuna “fahimi” ko kuma basira wajen bi da irin wannan yanayin. (Mis. 7:7) Idan ba ka tabbata da labarin ba, da halama cewa labarin ƙarya ne. Ƙari ga haka, idan labarin zai ɓata sunayen wasu, mai yiwuwa wani ne yake so ya shafa musu kashin kaza kuma idan ka aika wa mutane saƙon, kana taimaka masa ne.

WAJIBI NE KA TURA SAƘON DA AKA TURA MAKA?

Wasu za su iya aika wa wasu saƙonnin imel da wani ya aika musu ba tare da sun bincika ba, kuma ba tare da sun yi la’akari da sakamakon ba. Wataƙila suna son mutane su san da su ne kuma suna son su zama waɗanda aka soma jin wani labari daga wurinsu. (2 Sam. 13:28-33) Amma “mai hankali” yakan yi tunani ko labarin zai iya ɓata sunan wani mutum ko kuma wata ƙungiya.

Kafin mutum ya tabbata cewa wani labari gaskiya ne, sai ya yi bincike da kyau kuma hakan yana ɗaukan lokaci. Shi ya sa wasu suke aika wa mutane saƙon imel kai tsaye don suna ganin cewa wanda aka tura masa saƙon zai yi binciken. Amma wataƙila ba za su sami lokacin yin haka ba don hidimomin da ke gaban su. (Afis. 5:15, 16) Bai kamata mu aika saƙo idan ba mu tabbata da shi ba. A maimakon haka, mu kawar da shi.

Ka tambayi kanka: ‘Shin ina yawan aika wa mutane saƙonnin da aka turo min? Na taɓa ba wa mutane haƙuri saboda wani saƙon da ba gaskiya ba da na aika musu? Wani ya taɓa gaya maka cewa ka daina tura masa saƙon da aka aika maka?’ Ka tuna cewa duk wanda yana cikin jerin sunayen lambobin mutane da ke na’urarka zai iya shiga Intane. Saboda haka, zai iya neman wani bayani daga Intane ba tare da taimakonka ba. Ba sa bukatar ka tura musu labarai ko bidiyon ban dariya da makamantansu. Ƙari ga haka, bai dace ka riƙa tura saƙonnin rubutaccen jawabin Littafi Mai Tsarki ko kuma wanda aka ɗauka da na’ura da aka tura maka ba. * Ban da haka, ka tuna cewa idan mutum ya yi binciken nassosin Littafi Mai Tsarki ko kuma abubuwan da za a tattauna a taro da kansa, zai amfana sosai daga taron. Saboda haka, bai dace ka riƙa tura wa mutane irin waɗannan bayanan ba.

Shin in aika wa wani saƙo mai ban mamaki da aka aika min?

Shin wane mataki ne ya kamata ka ɗauka idan ka yi karo da wani mugun labari game da ƙungiyar Jehobah? Ka yi watsi da shi nan da nan. Wasu suna gani cewa ya kamata su sanar da wasu don su ji ra’ayinsu, amma idan ka yi hakan, kana ƙara yaɗa mugun labarin ne. Idan muka ga wani bayani a Intane kuma abin ya dame mu, ya kamata mu roƙi Jehobah ya sa mu kasance masu hikima. Ƙari ga haka, mu bayyana yadda muke ji wa ’yan’uwan da suka manyanta. (Yaƙ. 1:5, 6; Yahu. 22, 23) An yi wa Yesu sharri kuma ya gaya wa mabiyansa cewa maƙiyansu za su tsananta musu kuma su ‘ƙaga musu kowace irin mugunta’ don su ƙaryata su. (Mat. 5:11, Littafi Mai Tsarki; 11:19; Yoh. 10:19-21) Saboda haka, wajibi ne mu kasance masu “hankali” da “fahimi,” don hakan zai taimaka mana mu guji “mutane masu-maganar tsokana” da kuma waɗanda suke “shiririta cikin hanyoyinsu.”—Mis. 2:10-16.

KA RIƘA DARAJA MUTANE

Wajibi ne mu mai da hankali game da labaran ’yan’uwanmu da muka ji. Ba kowane labari ne ya kamata mu riƙa faɗa wa mutane ba, ko da gaskiya ne. A wasu lokatai, bai dace mu riƙa yaɗa labarai ba don hakan ba zai nuna cewa muna ƙaunarsu ba. (Mat. 7:12) Alal misali, ba zai dace mu yi gulman mutane ba, ko da gulman gaskiya ne. (2 Tas. 3:11; 1 Tim. 5:13) Wasu labaran sirri ne, kuma za a sanar wa waɗanda labarin ya shafa a lokacin da ya dace kuma ta hanyar da ta dace. Muna nuna cewa muna ƙaunarsu idan ba mu yaɗa labarin tun da wuri ba. Amma idan muka yaɗa labarin kafin lokacin, yin hakan yana da illa sosai.

A yau, labari zai iya yaɗuwa cikin ƙanƙanin lokaci, ko da labarin gaskiya ne ko ƙarya ne, ko mai kyau ko marar kyau, ko mai illa ko marar illa. Ya kamata mu tuna cewa idan muka aika saƙon imel ko ta waya, saƙon zai iya zagaya duniya a cikin kyaftar ido ko da ba da sonmu ba. Saboda haka, ya kamata mu guji aika wa mutane saƙon da aka aika mana ba tare da mun yi nazarinsa ba. Sa’ad da muka karanta wasu labarai masu jan hankali, mu tuna cewa ’yan’uwa sun yarda da mu don suna ƙaunarmu kuma ƙauna ba wauta ba ce. Mafi muhimmanci, ƙauna ba ta gaskata da labaran ƙarya da ake yi game da ƙungiyar Jehobah ko kuma game da ’yan’uwanmu. Waɗanda suke yaɗa irin waɗannan labaran bayin Shaiɗan ne don shi ne “uban ƙarya.” (Yoh. 8:44; 1 Kor. 13:7) Kasancewa da hankali da kuma fahimi zai taimaka mana mu zama masu wayo kuma mu bi da bayanai da muke samu yau da kullum cikin sanin yakamata. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Marasa-wayo su kan gāji wauta: Amma ana yi ma masu-hankali ƙambi da ilimi.”—Mis. 14:18.

^ sakin layi na 4 Ka san cewa ana iya canja wani labarin ƙarya don mutane su ɗauka cewa gaskiya ne.

^ sakin layi na 8 Ka duba “Akwatin Tambaya” da ke Hidimarmu ta Mulki ta Afrilu 2010.