Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Tarihi

Ya Tsai da Shawara Mai Kyau Sa’ad da Yake Matashi

Ya Tsai da Shawara Mai Kyau Sa’ad da Yake Matashi

BABBAN kawuna Nikolai Dubovinsky ya rubuta tarihinsa game da ibadarsa ga Jehobah, wato yanayi na farin ciki da wahala da ya fuskanta a lokacin mulkin tarayyar Soviet ta dā, sa’ad da aka hana aikin Shaidun Jehobah da kuma bayan haka. Ya rubuta wannan labarin ne a shekarunsa na ƙarshe a rayuwa. Ya kasance da aminci da ƙwazo kuma duk da cewa ya fuskanci ƙalubale da kuma matsaloli, ya ji daɗin rayuwa. Nikolai yana son matasa su ji labarinsa. Saboda haka, zan bayyana wasu abubuwa masu muhimmanci da suka faru da shi. An haife shi a shekara ta 1926 kuma iyalinsu manoma ne a ƙauyen Podvirivka da ke yankin Chernivtsi Oblast a ƙasar Yukiren.

NIKOLAI YA BAYYANA YADDA YA KOYI GASKIYA

Kawu Nikolai ya fara da cewa: “Wata rana a shekara ta 1941, yayana Ivan ya kawo wasu mujallun Hasumiyar Tsaro da littattafan nan The Harp of God da The Divine Plan of the Ages da ƙasidu da dama. Na karanta su duka kuma na koyi cewa Shaiɗan ne sanadin dukan wahalolin da muke sha a duniya, ba Allah ba. Hakan ya ba ni mamaki. Na karanta linjila tare da mujallun kuma hakan ya sa na san gaskiyar da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa. Na yi farin cikin gaya wa mutane abin da na koya game da Mulkin Allah da ƙwazo. Yayin da na karanta waɗannan mujallu, sai na ƙara fahimtar gaskiyar kuma hakan ya sa na kasance da burin zama mai bauta wa Jehobah.

“Na san cewa zan sha wahala saboda imanina. A lokacin ana yaƙi kuma ba na son in yi kisa. Sai na fara haddace ayoyin Littafi Mai Tsarki kamar Matta 10:28 da 26:52 don na shirya kaina saboda gwaji da ke tafe. Na yanke shawara cewa zan kasance da aminci ga Jehobah ko da za a kashe ni!

“Sa’ad da na kai ɗan shekara sha takwas, wato a shekara ta 1944, doka ta bukace ni in shiga aikin soja. Saboda haka, sai aka kai ni inda ake ɗaukan mutane a aikin soja. A nan ne na fara haɗuwa da wasu Shaidun Jehobah, matasa kamar ni. Mun gaya wa hukuma cewa ba za mu saka hannu a yaƙi ba. Saboda haka, hafsan da hukumar ta aika ya ji haushi kuma ya ce zai hana mu abinci, ya tilasta mana mu haƙa ramuka ko kuma ya harbe mu. Ba mu ji soro ba kuma muka ce: ‘Muna hannunka. Ka yi mana abin da ka ga dama amma ba za mu karya dokar Allah da ta ce: “Ba za ka yi kisankai ba.”’—Fit. 20:13.

“An tura ni da wasu ’yan’uwa biyu zuwa ƙasar Belarus don mu je mu yi aiki a gonaki kuma mu gyara gidajen da suka lalace. Ba zan taɓa manta da ɓarnan da yaƙi ta yi a bayan garin Minsk ba. Bishiyoyi da suka ƙone suna kwance a kan hanya. Gawawwakin mutane da kuma na dawaki da suka kumbura suna ko’ina a cikin ramuka da kuma jeji. Na ga taragwai da kayan yaƙi har da tarkacen jirgin da ya faɗi. Hakika, na ga sakamako karya dokokin Allah.

“An daina yaƙin a shekara ta 1945. Duk da haka, kotu ta yanke mana hukuncin shekara goma a gidan yari don mun ƙi shiga aikin soja. Mun yi shekara uku ba ma yin taro kuma ba ma samun littattafai. Amma mun tuntuɓi wasu ’yan’uwa mata ta wasiƙa. Daga baya, aka kama su kuma aka yanke musu hukuncin shekara 25 a sansanin aiki.

“Bayan haka, an sake mu a shekara ta 1950 kuma muka koma gida. Mahaifiyata da ƙanwata Maria sun zama Shaidun Jehobah a lokacin da nake gidan yari, amma yayuna suna kan nazarin Littafi Mai Tsarki! Hukumar tsaro ta Soviet ta so ta sake tura ni gidan yari saboda na ci gaba da yin wa’azi da ƙwazo. Sa’ad da na kai shekara 24 wani ɗan’uwa da yake shugabantar aikinmu ya ce in taimaka wajen buga littattafanmu a wani gidan ƙasa.”

BUGA LITTATTAFAI

“Shaidun Jehobah su sha faɗa cewa, ‘Idan an hana aikin bishara ta Mulki, za a ci gaba da yin sa a ɓoye.’ (Mis. 28:28) A wannan lokacin, yawancin aikin buga littattafanmu ana yin su ne a ɓoye a gidan ƙasa. Na fara yin aikin buga littattafai a gidan ƙasa da ke inda yayana Dmitry yake. A wani lokacin, ba na barin ɗaki har na sati biyu. Idan fitilar ta mutu saboda rashin iska, sai in kwanta kuma in jira har sai ɗakin ya sake cika da iska.

Zanen gidan ƙasa a ƙarƙashin gidan da Nikolai yake buga littattafai

“Wata rana, ɗan’uwa da nake aiki da shi ya tambaye ni ‘Nikolai, ka yi baftisma kuwa?’ Ko da shi ke na yi hidima na shekara 11 a bautar Jehobah amma ban yi baftisma ba. Saboda haka, ya tattauna batun da ni kuma aka yi min baftisma a daddare a wani tafki. A lokacin ina ɗan shekara 26. Bayan shekara uku na sami ƙarin ayyuka, na zama memban Kwamitin na Ƙasa. A lokacin ana naɗa ’yan’uwa don su maye gurbin ’yan’uwa da aka kama su. Saboda haka, aikin bishara ta Mulki ta ci gaba.”

MATSALOLIN YIN AIKI A GIDAN ƘASA

“Aikin buga littattafai a gidan ƙasa yana da wuya fiye da zama a gidan yari! Da yake ba na so ’yan sandan ciki su kama ni, na yi shekara bakwai ban halarci taro ba. Saboda haka, na ƙarfafa dangantakata da Jehobah da kaina. Ba na yawan ganin ’yan gidanmu sai in na ziyarce su. Amma sun fahimci yanayin da nake ciki kuma sun ƙarfafa ni. Yawan damuwa da kuma ƙoƙarin guje wa ’yan sanda ya gajiyar da ni sosai. Muna bukatar mu kasance a shirye don ba mu san abin da zai faru ba. Alal misali, wata rana da yamma ’yan sanda guda biyu sun zo gidan da nake. Na yi tsalle na fita ta tagar gidan kuma na shiga cikin daji a guje. Ina jin wani irin ƙara yayin da nake gudu. Sa’ad da na ji harbin bindiga, sai na gane cewa ƙarar da na ji na harsashi ne! Ɗaya daga cikin waɗanda suka bi ni ya hau kan doki kuma ya riƙa harbi har harsashin suka ƙare. Amma ya harbe ni a hannu. A ƙarshe na tsira sa’ad da na ɓuya a wani jeji bayan na yi kilomita 5 ina gudu. Daga baya, sa’ad da ake shari’a a kotu sai aka gaya mini cewa sun yi harbi har so 32 amma bai same ni ba.

“Da yake ina yawan zama a gidan ƙasa, na yi fari kamar wanda ba shi da jini a jiki. Hakan ya sa mutane sun san abin da nake yi. Saboda haka, sai na soma zama a cikin rana. Zama a gidan ƙasa ya shafi lafiyar jikina har ila. A wani lokaci ban iya halartan wani taro mai muhimmanci da ’yan’uwa ba don jini na fita daga hancina da kuma bakina.”

AN KAMA NIKOLAI

A sansanin aiki a ƙasar Mordvinia a shekara ta 1963

“An kama ni a ranar 26 ga Janairu a shekara ta 1957. Bayan wata 6, sai Kotun Ƙoli na ƙasar Yukiren ta yanke mini hukuncin kisa kuma aka ce za a harbe ni. Amma tun da doka ta kawar da irin wannan hukuncin a ƙasar, sai kotu ta canja zuwa ɗaurin shekara 25 a gidan yari. Mu takwas ne aka tura a sansanin aiki. An tura mu aiki a ƙasar Mordvinia, kuma Shaidun Jehobah da ke ƙasar sun yi kusan 500. Muna haɗuwa a asirce kuma a ƙananan rukunoni don mu yi nazarin Hasumiyar Tsaro. Bayan da wani ma’aikacin tsaro ya bincika wasu tsofaffin mujallunmu, sai ya ce: ‘Idan kuka ci gaba da karanta waɗannan mujallu, ba za a iya canja ra’ayin ku ba!’ Kowace rana muna aiki da ƙwazo, a wani lokaci ma muna yin aiki fiye da wanda aka ba mu. Duk da haka, shugaban sansanin ya ce: ‘Aikin da kuke yi a nan bai da muhimmanci a gare mu. Abin da muke bukata kawai a gare ku shi ne ku ba da haɗin kai kuma ku yi biyayya ga gwamnatin ƙasar.’”

“Kowace rana muna aiki da ƙwazo, a wani lokaci ma muna yin aiki fiye da wanda aka ba mu”

YA CI GABA DA KASANCEWA DA AMINCI

Wata Majami’ar Mulki a garin Velikiye Luki

Bayan da aka fito da shi daga sansanin a shekara ta 1967, Kawu Nikolai ya taimaka wajen shirya ikilisiyoyi a ƙasar Estonia da kuma birnin St. Petersburg a ƙasar Rasha. A shekara ta 1991 ne, aka sauke hukuncin da aka yi masa shekaru 34 kafin wannan lokacin saboda babu hujja da ta nuna ya aikata laifi. A wannan lokacin ne aka sake Shaidun Jehobah da yawa da suka sha wahala a ƙarƙashin hukumomi. A shekara ta 1996, Nikolai ya koma birnin Velikiye Luki a yankin Pskov Oblast da ke da nisan kilomita 500 daga St. Petersburg. Ya sayi wani ƙaramin gida, kuma aka gina Majami’ar Mulki a wajen a shekara ta 2003. A yau ikilisiyoyi biyu ne suke amfani da Majami’ar Mulkin.

Ni da mijina muna hidima a ofishin Shaidun Jehobah na ƙasar Rasha. ’Yan watanni kafin mutuwarsa, Kawu Nikolai ya yi mana ziyara ta ƙarshe a watan Maris na shekara ta 2011. Abin da ya faɗa ya ratsa zuciyarmu yayin da yake fara’a kuma ya ce: “Daga dukan alamu, an soma zagaye ta bakwai don kewaye Jericho.” (Josh. 6:15) Yana nufin ƙarshen duniya tana nan tafe. A lokacin shekararsa 85 ne. Ko da shike rayuwarsa ba ta kasance da sauƙi ba, amma ya kwatanta hakan ta cewa: “Ina farin cikin cewa sa’ad da nake matashi, na yanke shawarar bauta wa Jehobah kuma ban yi nadamar yin haka ba!”