HASUMIYAR TSARO—NA NAZARI Nuwamba 2015

Wannan fitowar tana dauke da talifofin nazari da za a yi daga ranar 28 ga Disamba, 2015, zuwa 31 ga Janairu, 2016.

Ku Tarbiyyatar da Yaranku don Su Bauta wa Jehobah

Halaye uku da Yesu ya nuna yayin da yake wa’azi za su taimaka muku ku tarbiyyatar da yaranku da kyau.

Ku Tarbiyyatar da Matasanku don Su Bauta wa Jehobah

Ta yaya za ku taimaka wa yaranku matasa su karfafa dangantakarsu da Jehobah a lokacin da suke matasa?

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Mene ne ya nuna cewa ba a kewaye birnin Yariko na dogon lokaci kafin a halaka shi?

Ka Rika Godiya ga Jehobah, Allah Mai Karimci

Littafi Mai Tsarki ya nuna muradin da ya dace da wanda bai dace ba na ba da lokacinmu da kuzarinmu da kuma dukiyarmu.

Jehobah Allah Ne Mai Kauna

Ta yaya Jehobah ya nuna cewa yana kaunar ’yan adam?

Kana “Kaunar Makwabcinka Kamar Ranka” Kuwa?

Za ka iya bi umurnin Yesu a aurenka da ikilisiyarku da kuma sa’ad da kake wa’azin bishara.

Abubuwan da Mulkin Allah Ya Cim ma a Cikin Shekara Dari

A wadanne hanyoyi uku ne aka shirya mu don yin wa’azi game da Mulkin Allah?

DAGA TARIHINMU

“Kada Ku Yarda Wani Abu Ya Hana Ku!”

A shekara ta 1930 zuwa 1939, masu hidima ta cikakken lokaci a Faransa sun kafa misali mai kyau na kasancewa da kwazo da kuma jimiri.