Ku Tarbiyyatar da Yaranku don Su Bauta wa Jehobah
“Mutumin nan na Allah . . . shi koya mana abin da za mu yi da yaron da za a haifa.”—ALƘA. 13:8.
WAƘOƘI: 88, 120
1. Mene ne Manoah ya yi sa’ad da aka gaya masa cewa matarsa za ta haihu?
MANOAH da matarsa sun san cewa ba za su iya haifan ’ya’ya ba. Wata rana, Jehobah ya aika mala’ika ya gaya wa matar Manoah cewa za ta haifi ɗa. Hakan ya ba ta mamaki sosai. Sa’ad da ta gaya wa Manoah, babu shakka Manoah ya yi farin ciki sosai. Amma ya san cewa yana da aiki a gabansa. Shin ta yaya zai tarbiyyartar da ɗansu ya bauta wa Jehobah a cikin wannan al’ummar da mutane suke aikata mugunta? “Manoah ya roƙi Ubangiji” cewa: “Ka bar mutumin nan na Allah [mala’ikan] da ka aiko shi, shi sake zuwa garemu, shi koya mana abin da za mu yi da yaron da za a haifa.”—Alƙa. 13:1-8.
2. Mene ne iyaye suke bukata su koya wa yaransu kuma ta yaya za su cim ma hakan? (Ka duba akwatin nan “ Ɗalibanka na Littafi Mai Tsarki da Suka Fi Muhimmanci.”)
2 Idan kai mahaifi ne, wataƙila za ka fahimci dalilin da ya sa Manoah ya yi wannan roƙon. Kai ma kana da hakkin rainon ɗanka don ya san Jehobah kuma ya ƙaunace shi. (Mis. 1:8) Shi ya sa iyaye Kiristoci suke gudanar da Ibada ta Iyali mai ƙayatarwa a kai a kai. Amma wajibi ne ku taimaka wa ’ya’yanku su so Jehobah daga zuciyarsu. (Karanta Kubawar Shari’a 6:.) Ta yaya za ku iya cim ma hakan? Za mu tattauna yadda iyaye za su yi koyi da Yesu a wannan talifin da kuma na gaba. Ko da yake Yesu bai haifi ’ya’ya ba, amma ya nuna ƙauna da tawali’u da kuma basira sa’ad da yake koyar da almajiransa, kuma iyaye za su iya koyan darussa daga yadda ya yi hakan. Bari mu tattauna waɗannan halayen ɗaya bayan ɗaya. 6-9
KU ƘAUNACI ’YA’YANKU
3. Ta yaya Yesu ya nuna cewa yana ƙaunar almajiransa?
3 Yesu bai ji kunyar gaya wa almajiransa cewa yana ƙaunarsu ba. (Karanta Yohanna 15:9.) Kuma ya nuna hakan ta yin cuɗanya da su a kowane lokaci. (Mar. 6:31, 32; Yoh. 2:2; 21:12, 13) Yesu abokinsu ne ba malaminsu kawai ba. Saboda haka, sun tabbata cewa yana ƙaunar su da gaske. Wane darasi ne iyaye za su iya koya daga wurin Yesu?
4. Ta yaya za ku nuna wa yaranku cewa kuna ƙaunarsu? (Ka duba hoton da ke shafi na 3.)
4 Ku riƙa gaya wa yaranku cewa kuna ƙaunarsu kuma ku nuna musu cewa suna da daraja sosai a gare ku. (Mis. 4:3; Tit. 2:4) Wani ɗan’uwa da ke zama a Ostareliya mai suna Samuel ya ce: “Sa’ad da nake ƙarami, babana yakan karanta mini Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki kowace yamma. Yana amsa tambayoyina, ya rungume ni kuma ya sumbace ni sa’ad da zan yi barci. Na yi mamaki sosai, sa’ad da na gane cewa babana bai taso a gidan da iyaye suke nuna wa yaransu ƙauna a waɗannan hanyoyin ba! Duk da haka, ya yi iya ƙoƙarinsa don ya ƙaunace ni. Sakamakon haka, na ƙulla dangantaka ta kud da kud da shi.” Za ku iya taimaka wa yaranku su kusace ku idan kuna gaya musu cewa kuna ƙaunarsu. Ku riƙa kasancewa tare da ’ya’yanku. Ku riƙa tattaunawa da su, ku ci abinci tare kuma ku riƙa wasa da dariya da su.
5, 6. (a) Mene ne Yesu ya yi wa almajiransa don yana ƙaunarsu? (b) Ka bayyana yadda yi wa yara horon da ya dace zai tabbatar musu cewa iyayensu suna ƙaunarsu.
* (R. Yoh. 3:19) Ko da yake almajiran Yesu sun sha yin jayayya a kan wanda ya fi girma a cikinsu, Yesu bai yi watsi da su ba. Amma kuma bai yi jinkirin yi musu horo sa’ad da suka ƙi bin shawararsa ba. Yesu ya yi musu gyara cikin ƙauna da kuma hankali. Ƙari ga haka, ya yi hakan a wuri da kuma lokacin da ya kamata.—Mar. 9:33-37.
5 Yesu ya ce: “Iyakar waɗanda nake ƙauna, ina tsauta su ina masu horo.”6 Ku riƙa yi wa yaranku horo, hakan zai nuna cewa kuna ƙaunar su. Hakika, kuna iya bayyana wa yaranku cewa yin wani abu yana da kyau ko kuma ba shi da kyau. Amma, a wani lokaci, ɗanku ko ’yarku za ta iya yin watsi da umurninku. (Mis. 22:15) Idan hakan ya faru, ku bi gurbin Yesu. Ku yi wa yaranku horo cikin ƙauna da hankali. Za ku iya yin hakan ta yi musu ja-gora, ta koyar da su ko kuma ta yi musu gyara. Wata ’yar’uwa a Afirka ta Kudu mai suna Elaine ta ce: “Iyayena ba sa fasa yi min horo a duk lokacin da ya kamata. Idan suka yi min gargaɗi kuma na ƙi jin maganarsu, suna yi min horo. Amma ba sa yi mini gyara cikin fushi kuma ba tare da sun bayyana mini dalilin ba. Hakan ya tabbatar mini cewa suna ƙauna ta. Ƙari ga haka, na san abubuwan da suke so in yi da kuma waɗanda bai kamata in yi ba.”
KU KASANCE DA TAWALI’U
7, 8. (a) Ta yaya Yesu ya nuna cewa shi mai tawali’u ne sa’ad da yake addu’a? (b) Ta yaya addu’arku zai taimaka wa yaranku su dogara ga Jehobah?
7 A darensa na ƙarshe a duniya, Yesu ya yi addu’a cewa: ‘Abba, Uba, abu duka ya yiwu a gareka; ka kawar mani da wannan ƙoƙo: amma dai ba yadda ni ni ke so ba, yadda kai kake so.’ * (Mar. 14:36) Shin yaya kake ganin almajiransa suka ji sa’ad da suka san da wannan addu’ar? Yesu ya nuna cewa yana bukata taimakon Allah duk da cewa shi kamili ne. Saboda haka, ya nuna tawali’u kuma ya roƙi Allah ya taimake shi. Almajiransa sun fahimci cewa su ma suna bukatar su nemi taimakon Jehobah tun da har ɗan Allah ya yi hakan.
8 Yaranku suna iya koyan abubuwa da yawa daga yadda kuke yin addu’a. Ko da yake, ba wai kuna addu’a kawai don ku koya wa yaranku yadda ake yin addu’a ba. Duk da haka, idan kuna nuna cewa kun dogara ga Jehobah sa’ad da kuke addu’a tare da su, su ma za su dogara ga Jehobah. Wata ’yar’uwa mai suna Ana da ke zama a Brazil ta ce: “Sa’ad da muke fuskantar matsaloli kamar a lokacin da kakannina suke rashin lafiya, iyayena sukan roƙi Jehobah ya ba su ƙarfin jurewa da kuma hikima don su bi da yanayin yadda ya dace. Suna dogara ga Jehobah ko da suna fuskantar matsaloli masu tsanani. Hakan ya sa na soma dogara ga Jehobah.” Sa’ad da kuke addu’a tare da yaranku, kada ku riƙa addu’a a madadinsu kawai. Ku roƙi Jehobah ya taimake ku, ku iyaye. Za ku iya yin addu’a a kan yadda za ku nemi izini a wajen aiki don a ba ku damar halartan babban taro, ko yadda za ku sami ƙarfin zuciya ku yi wa maƙwabtanku wa’azi da kuma yadda zai taimaka muku a wasu hanyoyi dabam. Idan kuna dogara ga Jehobah cikin tawali’u, yaranku za su bi misalinku.
9. (a) Ta yaya Yesu ya koya wa almajiransa cewa su riƙa taimaka wa mutane? (b) Idan kuna ba da kanku don taimaka wa mutane, ta yaya hakan zai shafi yaranku?
Luka 22:27.) Ya koya wa manzanninsa cewa su riƙa sadaukarwa a bautar Jehobah da kuma yadda suke bi da ’yan’uwa. Idan kuna sadaukarwa, yaranku za su bi misalinku. Wata mahaifiya mai suna Debbie tana da ’ya’ya biyu. Ta ce: “Ba na kishi cewa mijina yana amfani da lokacinsa don taimaka wa wasu a matsayinsa na dattijo. Na san cewa zai kasance tare da mu a duk lokacin da muke bukatarsa.” (1 Tim. 3:4, 5) Mijinta mai suna Pranas ya ce: “Daga baya, yaranmu sun yi sha’awar taimakawa a manyan taro da kuma wasu ayyuka na ƙungiyar Jehobah. Hakan ya sa sun kasance da farin ciki kuma sun yi abota da ’yan’uwa maza da mata!” Yanzu kowa a cikin iyalin yana bauta wa Jehobah ta yin hidima ta cikakken lokaci. Idan kun kasance da tawali’u kuma kuna ba da kanku don taimaka wa mutane, yaranku za su so su riƙa taimaka wa wasu.
9 Yesu ya gaya wa almajiransa cewa su kasance da tawali’u kuma ya kafa misali mai kyau a yin hakan. (KarantaKU KASANCE DA BASIRA
10. Ta yaya Yesu ya nuna basira sa’ad da wasu masu sauraronsa suka yi marmarin binsa?
10 Yesu ya nuna basira ta wajen lura da abubuwan da mutane suke yi da kuma dalilin da ya sa suke yin hakan. Akwai lokacin da wasu daga cikin masu sauraronsa a Galili suka so su bi shi. (Yoh. 6:22-24) Da yake Yesu ya san abin da ke cikin zuciyarsu, ya gane cewa suna son su bi shi don abincin da suke samu ne, ba don suna son su bi koyarwarsa ba. (Yoh. 2:25) Ya gane matsalarsu sai ya daidaita tunaninsu cikin sanin yakamata, kuma ya bayyana musu abin da suke bukata su yi don su canja halayensu.—Karanta Yohanna 6:25-27.
11. (a) Ku ba da misali da suka nuna yadda basira za ta taimaka muku ku san yadda yaranku suke ji game da wa’azi. (b) Ta yaya za ku taimaka wa yaranku su ji daɗin wa’azi?
11 Ko da yake ba za ku iya sanin abin da ke cikin zuciyar mutum ba, za ku iya nuna basira idan kun yi ƙoƙarin sanin yadda yaranku suke ji game da wa’azi. Sa’ad
da aka fita wa’azi, iyaye da yawa sukan ɗan huta kuma su ɗan ci abinci ko kuma su sha lemu. Za ku iya tambayar kanku, ‘Yarana suna jin daɗin wa’azi kuwa, ko kuma hutun ne yake sa su fita wa’azi?’ Idan kun lura cewa yaranku ba sa jin daɗin wa’azi sosai, ku taimaka musu su yi hakan. Ku koya musu wasu abubuwan da za su yi don su yi wa’azi kuma hakan zai sa su ji daɗin wa’azi.12. (a) Ta yaya Yesu ya nuna basira sa’ad da ya yi wa mabiyansa gargaɗi game da lalata? (b) Me ya sa almajiran Yesu suka bukaci wannan gargaɗin?
12 Yesu ya nuna basira ta bayyana abubuwan da za su iya sa mutum ya yi zunubi. Alal misali, mabiyansa sun san cewa zina ba ta kyau. Yesu ya ja musu kunne kan yin abubuwan da za su iya sa mutum ya yi zina sa’ad da ya ce: “Dukan wanda ya dubi mace har ya yi sha’awarta, ya rigaya ya yi zina da ita cikin zuciyatasa. Kuma idan idonka na dama yana sa ka yi tuntuɓe, ka cire shi, ka yar.” (Mat. 5:27-29) Wannan gargaɗin ya taimaka wa Kiristoci da suka yi rayuwa a ƙarƙashin mulkin Roma don ana wasannin da ke cike da lalata da kuma ashar a lokacin. Saboda haka, gargaɗin da Yesu ya bayar yana da kyau kuma hakan ya taimaka wa almajiran su guji duk wani abin da zai sa su yi lalata.
13, 14. Ta yaya za ka kāre yaranka daga nishaɗin da ba shi da kyau?
13 Basira za ta taimake ku ku kāre yaranku daga duk wani abin da zai ɓata dangantakarsu da Jehobah. A zamaninmu, yara suna iya kallon hotunan batsa da kuma wasu abubuwan lalata ba da son su ba. Hakika, ya kamata iyaye Kiristoci su gaya wa yaransu cewa fina-finai da ke ɗaukaka lalata ba su da kyau. Amma, basira za ta iya taimaka muku ku gane cewa yaranku za su so su san ko mene ne hotunan batsa. Ku tambayi kanku: ‘Mene ne zai iya sa ɗanmu ya kalli hotunan batsa? Shin ya san cewa yin hakan yana tattare da haɗari kuwa? Ina sake masa fuska kuwa, don ya nemi taimakona a duk lokacin da ya kalli hotunan batsa?’ Za ku iya gaya wa yaranku tun suna ƙanana cewa: “Duk lokacin da kuka ga hotunan batsa kuma kuka kalla, kada ku yi jinkirin gaya min. Kada ku ji kunya. Zan taimake ku.”
14 Basira za ta taimaka muku ku yi nishaɗin da ya dace. Ɗan’uwa Pranas da aka ambata ɗazu ya ce: “Irin waƙoƙin da iyaye suke sauraro da littattafai da suke karantawa da fina-finai da suke kallo suna shafan kowa a cikin iyalin. . . . Idan kun ga dama, ku riƙa magana daga safe har dare, misalin da kuka kafa ne yaranku za su bi.” Idan yaranku sun lura cewa kuna yin nishaɗin da ya dace, su ma za su yi koyi da ku.—Rom. 2:21-24.
JEHOBAH ZAI TAIMAKE KU
15, 16. (a) Me ya sa kuke da tabbaci cewa Allah zai taimaka muku ku tarbiyyartar da yaranku? (b) Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?
15 Mene ne ya faru sa’ad da Manoah ya roƙi Jehobah ya taimaka masa don ya tarbiyyartar da yaronsa da kyau? “Allah ya ji muryar Manoah,” wato ya ji addu’arsa. (Alƙa. 13:9) Hakazalika, Jehobah zai ji addu’ar iyaye kuma zai taimake ku ku tarbiyyartar da yaranku. Idan kuka nuna ƙauna da tawali’u da kuma basira sa’ad kuke taimaka wa yaranku, za ku yi nasara.
16 Hakika, Jehobah yana taimaka wa iyaye su tarbiyyartar da yaransu. Yayin da yaran suke girma, Jehobah zai ci gaba da taimaka wa iyaye tarbiyyatar da su. A talifi na gaba, za mu bincika yadda iyaye za su nuna ƙauna da tawali’u da kuma basira sa’ad da suke taimaka wa yaransu matasa su bauta wa Jehobah.
^ sakin layi na 5 A cikin Littafi Mai Tsarki, tarbiyyartar da yaro ya ƙunshi yi masa ja-gora cikin ƙauna, koyar da shi, yi masa gyara, a wani lokaci har da horo, amma ba cikin fushi ba.
^ sakin layi na 7 Wani ƙamus na Littafi Mai Tsarki ya ce: “A zamanin Yesu, yara suna kiran mahaifinsu da kalmar nan, ʼabbā.ʼ Yin hakan ya nuna cewa suna ƙaunar mahaifinsu kuma suna daraja shi.”