Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ku Tarbiyyatar da Matasanku don Su Bauta wa Jehobah

Ku Tarbiyyatar da Matasanku don Su Bauta wa Jehobah

“Yesu kuwa yana yin gaba a cikin hikima da girma, da kuma tagomashi wurin Allah da wurin mutane.”LUK. 2:52.

WAƘOƘI: 41, 89

1, 2. (a) Wane ƙalubale ne iyaye suke fuskanta sa’ad da yaransu suka kai ƙuruciya? (b) Mene ne Kiristoci matasa za su yi don su ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah?

WANI abin da ke sa iyaye farin ciki sosai shi ne ganin lokacin da ake yi wa ɗansu ko ’yarsu baftisma. Wata mahaifiya mai suna Berenice da yaranta guda huɗu sun yi baftisma kafin su kai shekara 14 ta ce: “Mun yi matuƙar farin ciki. Muna godiya cewa yaranmu sun yanke shawarar bauta wa Jehobah. . . . Amma mun san cewa za su fuskanci ƙalubale da yawa sa’ad da suka zama matasa.” Idan ɗanku ko ’yarku ta soma zama matashiya, za ku fahimci abin da Berenice take nufi.

2 Wani masani game da yanayin yara ya amince cewa yara suna fuskanta ƙalubale a lokacin ƙuruciya. Amma kuma ya ce: “Ƙuruciya ba lokacin ‘hauka’ ko ‘wawanci’ ba ne. Lokaci ne na bayyana ra’ayi da cuɗanya da kuma nuna azanci.” Sa’ad da yaranka suke matasa, za su iya ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah, su inganta yadda suke wa’azi, kuma su biɗi maƙasudai a bautar Jehobah. Za su iya jin daɗin ƙuruciyarsu idan suka inganta dangantakarsu da Jehobah a wannan lokacin kamar yadda Yesu ya yi sa’ad da yake matashi. (Karanta Luka 2:52.) Ta yaya iyaye za su iya taimaka wa yaransu a wannan lokaci mai muhimmanci? Za mu tattauna yadda Yesu ya nuna ƙauna da tawali’u da kuma basira. Iyaye za su iya koyan darasi daga yadda Yesu ya nuna waɗannan halayen kuma su tarbiyyartar da yaransu matasa don su bauta wa Jehobah?

KU NUNA WA YARANKU MATASA ƘAUNA

3. Me ya sa Yesu ya kira manzanninsa abokansa?

3 Yesu ya nuna ƙauna da aminci ga manzanninsa. (Karanta Yohanna 15:15.) A zamanin Yesu, iyayengiji ba sa cika bayyana ra’ayinsu da kuma damuwarsu ga bayinsu. Amma Yesu ya yi abota da manzanninsa masu aminci duk da cewa shi maigidansu ne. Ya kasance tare da su kuma ya saurare su sa’ad da suke bayyana masa ra’ayinsu. (Mar. 6:30-32) Irin wannan cuɗanya da Yesu ya yi da manzanninsa ya ƙarfafa dangantakarsu kuma ya shirya su don hidimar da suka yi daga baya.

4. Ta yaya za ku yi abota da yaranku ba tare da sun daina yi muku biyayya a matsayinku na iyaye ba? (Ka duba hoton da ke shafi na 8.)

4 Wani mahaifi mai suna Michael yana da ’ya’ya biyu. Ya ce: “Ko da yake ba za mu iya zama tsarar yaranmu ba, amma za mu iya zama abokansu.” Abokai suna kasancewa tare da juna. Ku yi addu’a kuma ku duba ko kuna bukata ku ɗan rage yawan aikin da kuke yi don ku riƙa kasancewa tare da ’ya’yanku. Abokai suna sha’awar yin wasu abubuwa tare. Saboda haka, ku yi ƙoƙari ku so abubuwan da yaranku matasa suke jin daɗinsa kamar kiɗa da fina-finai ko kuma wasanni. Wata ’yar’uwa mai suna Ilaria da ke zama a Italiya ta ce: “Iyayena sun so irin kiɗan da nake ji. Har ma mahaifina ya zama abokina na kud da kud. Ina sake jiki sa’ad da nake tare da shi kuma ba na ɓoye masa kome.” Idan kuka yi abota da yaranku matasa, za ku taimaka musu su kasance da dangantaka ta kud da kud da Jehobah. Hakan ba ya nufi cewa ba za ku iya ba su umurni a matsayinku na iyaye ba. (Zab. 25:14) Akasin haka, yana nuna cewa kuna ƙaunarsu kuma kuna daraja su. Ƙari ga haka, hakan zai nuna cewa kun damu da su. A sakamako, za su riƙa sake jiki kuma su riƙa bayyana muku ra’ayinsu.

5. Ta yaya Yesu ya taimaka wa almajiransa su kasance da farin ciki a yin hidimar Jehobah da ƙwazo?

5 Yesu ya so almajiransa da abokansa su kasance masu farin ciki yayin da suke yi hidima da ƙwazo a bautar Jehobah. Shi ya sa ya ƙarfafa su su riƙa yin hidimomi da dama a bautar Jehobah. Burin Yesu shi ne su taimaka wa mutane su zama almajiransa. Ya gaya musu cewa zai tallafa musu don su yi nasara a wannan aikin.—Mat. 28:19, 20.

6, 7. Ta yaya nacewa wajen yin ayyuka na ibada zai nuna cewa iyaye suna ƙaunar ’ya’yansu?

6 Burin iyaye shi ne yaransu su ci gaba da kasancewa da dangantaka ta kud da kud da Jehobah. Kuma Allah yana so ku tarbiyyartar da yaranku bisa ga “horon Ubangiji da gargaɗinsa.” (Afis. 6:4) A matsayinku na iyaye, ku tabbata cewa kuna nacewa a yin ayyukan da suka shafi ibada. Alal misali: Burinku ne yaranku su je makaranta don kun san cewa karatu yana da amfani. Saboda haka, kuna taimaka musu su kasance da sha’awar yin karatu. Hakazalika, iyaye masu ƙauna suna nacewa don ’ya’yansu su amfana daga “horon Ubangiji” da muke samu a taron ikilisiya da kuma wasu abubuwa da ke ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah. Da yake kun san cewa koyarwar gaskiya tana da muhimmanci, kuna ƙoƙarin taimaka wa yaranku su so koyarwar nan kuma su kasance da hikima. (Mis. 24:14) Kamar yadda Yesu ya taimaka wa almajiransa, kuna bukata ku taimaka wa yaranku matasa su yi nasara a hidimarsu kuma su kasance da sha’awar koyar da Kalmar Allah da kuma yin wa’azi da ƙwazo.

7 Ta yaya yin ayyukan ibada zai shafi yaranka matasa? Wata ’yar’uwa mai suna Erin da ke Afirka ta Kudu ta ce: “Sa’ad da muke yara, mukan yi gunaguni game da nazarin iyali, zuwa taro da kuma fita wa’azi. A wani lokaci, sai mu katse nazarin iyali da gangan don a ce mu bar wajen. Amma iyayenmu ba su karaya ba.” Ta daɗa cewa: “Wannan horon ya taimaka min in kasance da naciya. Idan wani abu ya katse min wasu ayyukan ibada da nake yi, ina sha’awa sake ci gaba da yin abin ba tare da ɓata lokaci ba. Ba na zaton zan kasance da irin wannan sha’awar da a ce iyayenmu ba su nace wajen tabbatar da cewa muna ayyuka na ibada babu fashi ba. Da a ce sun karaya, na tabbata cewa hakan zai sa ina sanyin jiki wajen halartan taro da kuma saka hannu a wasu ayyukan ibada.”

KU KAFA MISALI MAI KYAU A NUNA TAWALI’U

8. (a) Ta yaya Yesu ya nuna cewa yana bukatar taimako? (b) Ta yaya tawali’un da Yesu ya nuna ya shafi almajiransa?

8 Yesu kamili ne duk da haka ya kasance da tawali’u kuma ya gaya wa almajiransa cewa yana bukatar taimako daga wurin Jehobah. (Karanta Yohanna 5:19.) Shin tawali’un da Yesu ya nuna ya sa almajiransa sun daina ba shi daraja ne? A’a. A maimakon haka, almajiransa sun ƙara amincewa da shi sa’ad da ya dogara ga Jehobah sosai. Daga baya, sun kasance da tawali’u kamar yadda Yesu ya yi.—A. M. 3:12, 13, 16.

9. Sa’ad da kuka amince da laifinku da kuma kasawarku, ta yaya hakan zai shafi yaranku matasa?

9 Yesu kamili ne amma muna yin kurakurai da yawa don mu ajizai ne. Idan muka yi laifi, ya kamata mu amince da laifin. (1 Yoh. 1:8) Alal misali, za mu daraja maigida da yake amincewa da laifinsa maimakon wanda ba ya son amincewa da laifinsa. Idan yaranku matasa sun ji kuna amincewa da laifinku, hakan zai sa su ƙara daraja ku. Ƙari ga haka, su ma za su riƙa amincewa da kurakuransu. Wata ’yar’uwa mai suna Rosemary da ke da yara uku ta ce: “Muna amincewa da laifinmu, kuma hakan ya sa yaranmu ba sa ɓoye mana kome sa’ad da suke da wata damuwa. Sa’ad da suke bukatar taimako, mukan gaya musu su nemi amsar daga littattafanmu da aka wallafa bisa Littafi Mai Tsarki.”

10. Ta yaya Yesu ya nuna tawali’u sa’ad da yake ba mabiyansa umurni?

10 Yesu yana da iko ya ba wa mabiyansa umurni. Amma ya nuna tawali’u wajen bayyana dalilan da suka sa ya ba da wasu umurnai. Alal misali, ya gaya wa mabiyansa cewa su biɗi Mulkin Allah da adalcinsa farko a rayuwarsu, amma ya ba da dalili, ya ce: “Waɗannan abubuwa duka fa za a ƙara maku su.” Sa’ad da Yesu ya gaya wa mutane cewa: “Kada ku zartar,” ya bayyana abin da sa yin hakan bai dace ba. Ya ce: “Domin kada a zartar muku. Gama da irin shari’a da kuke shar’antawa, da ita za a shar’anta muku.”—Mat. 6:31–7:2.

11. Me ya sa yake da kyau ku bayyana dalilan da suka sa kuka yanke wasu shawarwari a matsayinku na iyaye?

11 A duk lokacin da ya dace, ku iyaye ku riƙa bayyana dalilin da ya sa kuka tsai da wata shawara. Idan yaranku matasa sun fahimci abin da kuke nufi, za su so su yi biyayya daga zuciyarsu. Wani ɗan’uwa mai suna Barry da ya tarbiyyatar da yaransa huɗu ya ce: “Idan kuka ba da hujjar da ta sa kuka tsai da wata shawara, hakan zai taimaka wa yaranku matasa su ga cewa kuna da ƙwaƙƙwaran hujja na yanke shawarwari kuma ba ku yi hakan bisa ra’ayinku ba.” Ƙari ga haka, yayin da matashi yake girma, yana kyautata tunaninsa ko kuma ‘hankalinsa.’ (Mis. 3:21) Barry ya ce: “Matasa suna bukata su yanke shawarwari da ke bisa tabbataccen dalili, ba haka kawai ba.” (Zab. 119:34) Idan kuka nuna tawali’u kuma kuka bayyana dalilan da suka sa ku tsai da wasu shawarwari, yaranku matasa za su gane cewa kun san suna girma kuma wata rana za su zama babba. Saboda haka, suna bukata su yi amfani da ‘hankalinsu.’

KU BI DA YARANKU MATASA CIKIN BASIRA DA FAHIMI

12. Ta yaya Yesu ya taimaka wa Bitrus cikin basira?

12 Yesu ya nuna basira kuma ya fahimci inda almajiransa suke bukatar taimako. Alal misali, sa’ad da Yesu ya gaya wa almajiransa cewa za a kashe shi, manzo Bitrus ya ce Allah ya sawwaƙa masa. Yesu ya san cewa Bitrus yana ƙaunarsa, amma ya san cewa tunanin Bitrus a wannan karon ba daidai ba ne. Saboda haka, ya tsauta wa Bitrus don ya taimaka masa da sauran almajirai ta wajen bayyana abin da zai iya faruwa da waɗanda suka ƙi yin nufin Jehobah don yana da wuya. Ƙari ga haka, ya faɗi albarkar da waɗanda suka yi nufin Jehobah za su samu. (Mat. 16:21-27) Babu shakka, Bitrus ya koyi darasi.—1 Bit. 2:20, 21.

13, 14. (a) Mene ne zai iya nuna cewa ɗanku ko ’yarku ta soma shakka? (b) Ta yaya basira za ta taimaka muku ku fahimci yanayin kuma ku taimaki ɗanku ko ’yarku?

13 Ku yi addu’a ga Jehobah don ku kasance da basira kuma ku gane inda yaranku matasa suke bukatar taimako. (Zab. 32:8) Alal misali, mene ne zai iya nuna cewa ɗanku ko ’yarku ta soma shakka? Wataƙila ba sa farin ciki, ko sun soma sūkar ’yan’uwa ko kuma sun soma yin wasu abubuwa a ɓoye. Kada ku yi hanzarin tunani cewa ɗanku ko ’yarku tana yin zunubi a ɓoye kuma ba ta so a sani. * Amma kada ku yi watsi da waɗannan alamun ko kuma ku ɗauka cewa ba wani abu ba ne idan ɗanku ko ’yarku ba ta son yin cuɗanya da ’yan’uwa.

Ku nemi zarafin taimaka wa yaranku su yi abota da ’yan’uwa a cikin ikilisiya (Ka duba sakin layi na 14)

14 Ku yi koyi da Yesu ta wajen yin tambaya a hankali kuma cikin sanin yakamata. Alal misali, idan kun yi hanzari kuma kuka tilasta wa yaronku matashi ya faɗi abin da yake zuciyarsa, za ku ɓata lokacinku kuma ba za ku san ainihin abin da yake damunsa ba. (Karanta Misalai 20:5.) Ilaria da aka ambata ɗazu ta ce: “Sa’ad da nake matashiya, hankalina ya rabu don ina yawan tarayya da ’yan ajina, saboda haka ba na jin daɗin kasancewa da ’yan’uwa a cikin ikilisiya. Hakan ya shafe ni sosai kuma iyayena suka gane cewa ba na farin ciki. Wata rana da yamma, suka ce sun lura cewa ba na farin ciki, kuma suka tambaye ni mene ne yake damuna. Sai na fashe da kuka, na gaya musu kome kuma na ce su taimake ni. Sai suka rungume ni suka ce sun fahimci yanayina kuma suka ce za su taimake ni.” Ba tare da ɓata lokaci ba, iyayen Ilaria suka soma taimakon ta ta soma yin abota da ’yan’uwa a cikin ikilisiya.

15. Ka bayyana yadda Yesu ya nuna basira sa’ad da yake sha’ani da mutane.

15 Yesu ya nuna basira ta wajen mai da hankali da inda almajiransa suke ƙoƙari. Alal misali, sa’ad da wani mutum mai suna Natanayilu ya ji cewa Yesu ya fito daga Nazarat, sai ya ce: “Ya yiwu wani abu mai-kyau shi fito Nazarat?” (Yoh. 1:46) Da a ce kai ne, yaya za ka ɗauki Natanayilu? Mai sūka? Mai wariya? Ko marar bangaskiya? Yesu ya nuna basira kuma ya mai da hankali ga hali mai kyau na Natanayilu. Yesu ya ce da shi: “Mutumin Isra’ila na gaske, wanda ba shi da algus!” (Yoh. 1:47) Yesu ya san abin da ke zuciyar mutane, kuma ya mai da hankali ga halaye masu kyau da mutane suke da shi.

16. Ta yaya za ka iya taimaka wa ɗanka ko ’yarka matashiya ta kasance da halaye masu kyau?

16 Iyaye, ba za ku iya sanin abin da ke cikin zuciyar yaranku ba, amma Allah zai taimaka muku ku kasance da basira. Ku yi amfani da basira wajen mai da hankali ga halaye masu kyau da yaranku matasa suke da shi. Babu wanda yake so a kira shi “fitinanne.” Saboda haka, kada ku kira ɗanku ko ’yarku “marar jin gari” ko kuma “mai rigima.” Ko da ɗanku ko ’yarku matashiya tana fama, ku sa ta san cewa tana da halaye masu kyau kuma tana son yin abin da ya dace. Ku mai da hankali ga inda ɗanku matashi yake ƙoƙari kuma ku yaba masa. Ku taimaka masa ya kyautata halayensa masu kyau ta wajen ba shi ayyuka a kai a kai idan hakan zai yiwu. Abin da Yesu ya yi ke nan. Shekara ɗaya da rabi bayan sun haɗu da Natanayilu (ana kuma kiransa Bartalamawus), Yesu ya zaɓe shi ya zama manzonsa, kuma Natanayilu ya yi hidimar da aka ba shi da aminci. (Luk. 6:13, 14; A. M. 1:13, 14) Idan kuna yabon yaranku matasa kuma kuna ƙarfafa su, hakan zai sa su su ga cewa suna da amfani a matsayinsu na Kiristoci kuma Jehobah zai iya ba su aiki.

TABIYYARTAR DA YARANKU MATASA ZAI SA KU FARIN CIKI SOSAI

17, 18. Wace albarka ce za ku iya samu idan kuka yi aiki tuƙuru wajen tarbiyyartar da yaranku matasa don su bauta wa Jehobah?

17 Yayin da kuke tarbiyyartar da yaranku, za ku iya ji kamar yadda manzo Bulus ya ji don ya zama kamar mahaifi ga ’yan’uwa da yawa. Ya yi fama da “ƙunci mai-yawa da raɗaɗin zuciya” saboda “ƙauna” da yake da shi a gare su. (2 Kor. 2:4; 1 Kor. 4:15) Wani mahaifi mai suna Victor da ya yi rainon ’ya’ya maza biyu da mace ɗaya ya ce: “Ƙuruciya ba ta da sauƙi. Duk da haka, albarkar da muka samu ta fi ƙalubalen da muka fuskanta. Jehobah ya taimaka mana mu ƙulla dangantaka ta kud da kud da yaranmu.”

18 Ku ci gaba da yin aiki tuƙuru yayin da kuke tarbiyyartar da yaranku don su bauta wa Jehobah. Idan kuka yi hakan cikin ƙauna, hakan zai sa yaranku su iya yanke shawarar kasancewa cikin waɗanda suke “tafiya cikin gaskiya.” Hakika, hakan abin farin ciki ne sosai.—3 Yoh. 4.

^ sakin layi na 13 Iyaye za su iya duba wannan littafin Questions Young People Ask—Answers That Work, Vol. 1, shafi na 317, da kuma Questions Young People Ask—Answers That Work, Vol. 2, shafuffuka na 136-141.