Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DAGA TARIHINMU

“Kada Ku Yarda Wani Abu Ya Hana Ku!”

“Kada Ku Yarda Wani Abu Ya Hana Ku!”

A WATAN Mayu a shekara ta 1931, ɗimbin mutane daga ƙasashe 23 suna shigan wani sanannen gidan wasa na Pleyel a birnin Paris. Manyan motocin haya suna ta saukar da fasinjoji da suka yi shiga masu kyau a gaban gidan wasan, kuma ba daɗewa ba gidan ya cika maƙil da mutane kusan 3,000. Shin waɗannan mutanen sun zo kallon wasa ne? A’a. Sun zo ne su saurari jawabin Ɗan’uwa Joseph F. Rutherford, da ke ja-gorar wa’azin bishara a lokacin. An fassara jawabansa masu daɗi zuwa faransanci da jamusanci da kuma yaren ’yan Polan. Ana jin babbar muryar ɗan’uwan Rutherford ko’ina a gidan wasan.

Wannan taron da aka yi a Paris ya kawo canji na musamman a wa’azin bishara ta Mulki a ƙasar Faransa. Ɗan’uwa Rutherford ya ƙarfafa mutane da suka fito daga ƙasashe dabam-dabam, musamman matasa su soma hidimar majagaba a ƙasar Faransa. Wani matashi bature, mai suna John Cooke ba zai taɓa manta da gargaɗi mai ban ƙarfafa da Ɗan’uwa Rutherford ya bayar ba: “Matasa kada ku yarda wani abu ya hana ku soma yin hidimar majagaba!” *

Ban da John Cooke wanda ya zama mai wa’azi a ƙasar waje daga baya, ’yan’uwa da yawa sun soma hidimar majagaba. (A. M. 16:9, 10) Adadin majagaba a Faransa ya ƙaru daga 27 a shekara ta 1930 zuwa 104 a shekara ta 1931. Wannan ba ƙaramin ƙaruwa ba ce a cikin shekara ɗaya. Tun da yake yawancin waɗannan majagaba ba sa Faransanci, ta yaya za su bi da ƙalubalen yare da talauci da kuma kaɗaici?

FAMA DA ƘALUBALEN WANI YARE

Majagaba daga wasu ƙasashe sun dogara da katin wa’azi don su yi wa’azin bishara game da Mulkin. Wani ɗan’uwa daga Jamus da ya yi wa’azi gabansa gaɗi a Paris ya ce: “Mun san cewa Allahnmu mai iko ne. Idan muna fargaba sa’ad da muke wa’azi, ba wai muna jin tsoron mutane ba ne amma muna tsoro cewa za mu manta da wannan kalamin: ‘Voulez-vous lire cette carte, s’il vous plaît? [Don Allah ka karanta wannan katin]’ Muna da tabbaci cewa hidimarmu tana da muhimmanci sosai.”

Majagaba na dā sun yi amfani da kekuna da babura don su yi wa’azin bishara a ƙasar Faransa

Sa’ad da majagaban suke wa’azi a gidajen bene, sau da yawa masu kula da gidan sukan kore su. Wata rana wani mai kula da gida ya fusata da wasu ’yan’uwa mata biyu turawa da ba su iya faransanci ba kuma ya tambaye su wane ne suke nema. Ɗaya daga cikin matan ta lura da wata alama a jikin ƙofar da aka rubuta: “Tournez le bouton [Ka buga kararrawar],” kuma ta ɗauka cewa shi ne sunan masu gidan. Sai ta ce: Mun zo wurin Malama ‘Tournez le bouton.’” Waɗannan majagaba masu ƙwazo sun ji daɗin hidimarsu don irin waɗannan abubuwan ban dariya!

TALAUCI DA KAƊAICI BAI HANA SU YIN WA’AZI BA

A shekarun 1930 zuwa 1939, yawancin mutane a Faransa suna fama da talauci kuma hakan ya shafi majagaba da suka zo daga wasu ƙasashe. Wata majagaba Baturiya mai suna Mona Brzoska ta bayyana abin da ita da abokiyar hidimarta suka fuskanta, ta ce: “Masauƙinmu ba wani abin a zo a gani ba ne, kuma wata babbar matsalar da muka fuskanta ita ce, ɗuma ɗakin a lokacin sanyi. Mukan kwana a cikin wani ɗaki mai sanyin tsiya. Da safe, sai mun fasa ƙanƙara kafin mu sami ruwan wanke fuska.” Shin waɗannan majagaban sun karaya saboda wannan mawuyacin yanayi ne? Ko kaɗan! Ɗaya daga cikinsu ta bayyana yadda suka ji sa’ad da ta ce: “Ba mu da kome amma ba mu rasa kome ba.”—Mat. 6:33.

Majagaba turawa da suka halarci taron da aka yi a Paris a shekara ta 1931

Ƙari ga haka, waɗannan majagaba masu ƙarfin hali sun yi fama da kaɗaici. Tsakanin shekara ta 1931 da 1933, masu wa’azin bishara ba su wuce 700 ba kuma yawancinsu suna zama a wurare dabam-dabam a faɗin ƙasar. Shin me ya taimaka wa waɗannan majagaban su kasance da farin ciki? Mona da abokiyar hidimarta sun fuskanci wannan yanayin. Ta ce: “Mun sha kan wannan yanayin ta wajen yin nazarin littattafai da ƙungiyar Jehobah take wallafawa tare a kai a kai. Tun da yake a lokacin ba ma koma ziyara ko kuma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane, da yamma mukan rubuta wasiƙu ga iyalanmu da kuma wasu majagaba don mu gaya musu abin da muka shaida a hidima kuma mu ƙarfafa juna.”—1 Tas. 5:11.

Waɗannan majagaba masu ƙwazo sun kasance da ra’ayin da ya dace duk da ƙalubalen da suka fuskanta. Bayan sun yi shekaru da yawa suna wa’azi a Faransa, wasiƙun da suka rubuta zuwa ofishin Shaidun Jehobah da ke ƙasar sun nuna cewa sun kasance da ra’ayi mai kyau. Wata ’yar’uwa shafaffiya mai suna Annie Cregeen da mijinta sun yi hidima a wurare dabam-dabam a ƙasar Faransa daga shekara ta 1931 zuwa 1935. Ta ce: “Mun yi rayuwa mai ma’ana da kuma ban farin ciki! A matsayinmu na majagaba, mu abokan juna ne. Kamar yadda manzo Bulus ya ce, ‘Ni na dasa, Afollos ya yi ban ruwa; amma Allah ne ya ba da amfani.’ Wannan yana sa mu farin ciki da yake mun sami zarafin taimaka wa mutane shekaru da yawa da suka wuce.”—1 Kor. 3:6.

Waɗannan majagaba masu haƙuri da ƙwazo sun kafa misali mai kyau ga waɗanda suke so su faɗaɗa hidimarsu. A yau, a ƙasar Faransa, akwai majagaba na kullum guda 14,000. Da yawa daga cikinsu suna hidima a rukuni ko kuma ikilisiyoyi da ke wani yare. * Kamar waɗanda suka gabace su, ba su yarda wani abu ya hana su yin wa’azi ba!—Daga tarihinmu a Faransa.

^ sakin layi na 4 Za ka sami ƙarin bayani game da wa’azin bishara da ’yan Polan da ke Faransa suka yi a talifin nan “Jehobah Ya Kawo Ku Faransa don Ku Koyi Gaskiya,” a cikin fitowar Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Agusta, 2015.

^ sakin layi na 13 A shekara ta 2014, ofishin Shaidun Jehobah da ke Faransa yana kula da ikilisiyoyi da rukunoni fiye da 900 da ke wani yare. Waɗannan ikilisiyoyin da rukunonin suna taimaka wa mutane da ke son saƙonmu a harsuna 70.