Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Jehobah Zai Kula da Kai

Jehobah Zai Kula da Kai

“Ubangiji za ya toƙara shi a bisa shimfiɗarsa ta rashin lafiya.”—ZAB. 41:3.

WAƘOƘI: 23, 138

1, 2. Ta yaya Allah ya taimaka wa waɗanda suke rashin lafiya a dā, kuma wane tunani ne mukan yi sa’ad da muke rashin lafiya?

IDAN ka taɓa yin rashin lafiya mai tsanani, wataƙila ka yi tunani ko za ka sami sauƙi. Mai yiwuwa ka taɓa yin wannan tunanin sa’ad da wani a iyalinku yake rashin lafiya. Mukan damu sa’ad da muke fuskantar yanayi na rashin lafiya mai tsanani. Wasu sarakuna biyu a zamanin Iliya da Elisha sun taɓa samun kansu a irin wannan yanayin. Sarki Ahaziah, ɗan Ahab da Jezebel ya yi mugun faɗiwa kuma ya aika a tambayo masa ko zai warke daga ciwon. Sarki Ben-hadad na Suriya ya taɓa yin rashin lafiya mai tsanani kuma ya yi wannan tambayar: “Zan warke daga wannan ciwota?”—2 Sar. 1:2; 8:7, 8.

2 Sa’ad da mu ko wasu da muke ƙauna suke rashin lafiya, fatarmu ita ce dukanmu mu sami sauƙi. Duk da haka, wasu suna tunani ko Allah yana taimaka wa waɗanda suke rashin lafiya. Allah ya yi mu’ujiza don ya warkar da mutane a zamanin waɗannan sarakunan da muka ambata ɗazu. Ƙari ga haka, Jehobah ya ta da waɗanda mutu suka ta wurin annabawansa. (1 Sar. 17:17-24; 2 Sar. 4:17-20, 32-35) Shin ya kamata mu sa rai cewa zai yi hakan a zamaninmu?

3-5. Allah da Yesu suna da ikon yin me, kuma waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?

3 Hakika, Allah yana da ikon addabar mutane da cuta ko kuma warkar da waɗanda suke rashin lafiya. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ya taɓa addabar wasu mutane da cuta. Alal misali, ya hukunta Fir’auna da rashin lafiya a zamanin Ibrahim, kuma shekaru da yawa bayan haka, ya addabi Maryamu ’yar’uwar Musa da cuta. (Far. 12:17; Lit. Lis. 12:9, 10; 2 Sam. 24:15) Allah ya ja kunnen Isra’ilawa cewa idan sun yi rashin biyayya zai addabe su da “kowace cuta, da kowace annoba.” (K. Sha. 28:58-61) A wasu lokatai kuma, Jehobah zai iya kawar da rashin lafiya kuma ya kāre mutanensa daga cuta. (Fit. 23:25; K. Sha. 7:15) Ƙari ga haka, zai iya warkar da mutane. Ayuba ya yi rashin lafiya mai tsanani har ma ya so ya mutu, amma Allah ya warkar da shi!—Ayu. 2:7; 3:11-13; 42:10, 16.

4 Muna da tabbaci cewa Allah zai iya warkar da wanda yake rashin lafiya. Yesu ma yana da iko ya warkar da mutane. Littafi Mai Tsarki ya ce Yesu ya warkar da kutare, masu farfaɗiya da makafi da kuma waɗanda jikinsu ya shanye. (Karanta Matta 4:23, 24; Yohanna 9:1-7) Waɗannan warkarwar suna tuna mana abubuwan da Yesu zai yi a sabuwar duniya. A lokacin, ba wanda zai ce: “Ina ciwo.”—Isha. 33:24.

5 Shin ya kamata mu sa rai cewa Allah ko kuma Yesu zai warkar da mu ta mu’ujiza a yau? Wane ra’ayi ne ya kamata mu kasance da shi game da cututtuka masu tsanani, kuma waɗanne matakai ne ya kamata mu ɗauka game da su?

KA DOGARA GA JEHOBAH SA’AD DA KAKE RASHIN LAFIYA

6. Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da “baiwar warkarwa” da aka ba wa wasu Kiristoci na farko?

6 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Allah ya ba wasu iko a ƙarni na farko su yi mu’ujiza. (A. M. 3:2-7; 9:36-42) Ya ba su “baiwa iri iri” kuma hakan ya haɗa da “baiwar warkarwa.” (1 Kor. 12:4-11, Littafi Mai Tsarki.) Amma Littafi Mai Tsarki ya ce jim kaɗan za a kawo ƙarshen waɗannan baiwar da kuma wasu kamar baiwar yin harsuna dabam-dabam. (1 Kor. 13:8) Ba a yin hakan a yau. Saboda haka, bai kamata mu riƙa sa rai cewa Allah zai warkar da mu ko ƙaunatattunmu da suke rashin lafiya ta hanyar mu’ujiza ba.

7. Ta yaya Zabura 41:3 za ta iya ƙarfafa mu?

7 Ko da cewa Allah ba ya warkar da mutane ta hanyar mu’ujiza a yau, zai iya ƙarfafa mu, ya ba mu hikima kuma ya tallafa mana kamar yadda ya yi wa bayinsa a dā. Sarki Dauda ya ce: “Mai-albarka ne shi wanda ya kula da matalauta: Ubangiji za ya cece shi cikin baƙar ranar. Ubangiji za ya kiyaye shi, ya rayar da shi.” (Zab. 41:1, 2) Dauda ba ya nufin cewa wanda ya kula da matalauta zai ci gaba da rayuwa har abada ta hanyar mu’ujiza. Amma Allah zai taimaka wa wannan mai aminci. Ta yaya? Dauda ya ƙara cewa: “Ubangiji za ya toƙara shi a bisa shimfiɗarsa ta rashin lafiya: kana gyarta masa shimfiɗa cikin cutarsa.” (Zab. 41:3) Hakika, wanda ya kula da matalauta yana da tabbaci cewa Allah zai tuna da shi da kuma alherin da ya yi. Ƙari ga haka, Allah ya halicce mu a yadda za mu iya warkewa daga ciwo. Saboda haka, wannan mutumin ya tabbata cewa Jehobah zai taimaka masa ya sami sauƙi.

8. Bisa ga Zabura 41:4, mene ne Dauda ya roƙi Jehobah ya yi masa?

8 Dauda ya yi wannan maganar saboda abin da ya faru da shi. Ya ce: “Ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai: Ka warkar da raina; gama na yi maka zunubi.” (Zab. 41:4) Wataƙila Dauda ya rubuta wannan ayar ne a lokacin da Absalom ya so ya yi masa juyin mulki kuma Dauda ya rasa abin da zai yi don yana rashin lafiya a lokacin. Dauda bai manta da zunubin da ya yi da Bath-sheba ba duk da cewa Allah ya gafarta masa. (2 Sam. 12:7-14) Duk da haka, ya tabbata cewa Allah zai kula da shi sa’ad da yake rashin lafiya. Shin Dauda yana roƙo Allah ya warkar da shi ta mu’ujiza kuma ya ƙara masa dogon kwana ne?

9. (a) Ta yaya yanayin Dauda ya bambanta da na Sarki Hezekiah? (b) Mene ne Dauda ya sa rai cewa Jehobah zai yi masa?

9 Shekaru da yawa bayan haka, Allah ya warkar da Sarki Hezekiah da “ya yi ciwo har bakin mutuwa.” Wannan yanayin ya bambanta da na Dauda. Hezekiah ya sami sauƙi har ya ƙara yin rayuwa na shekaru 15. (2 Sar. 20:1-6) Amma, Dauda bai yi addu’a cewa Allah ya warkar da shi ta hanyar mu’ujiza ba. A maimakon haka, Dauda ya roƙi Jehobah ya taimaka masa kamar yadda yake taimaka wa duk wani mai aminci. Ya tabbata cewa Allah zai kula da shi sa’ad da yake rashin lafiya. Dauda yana da dangantaka mai kyau da Jehobah shi ya sa ya roƙi Allah ya ƙarfafa shi kuma ya tallafa masa don ya sami sauƙi. (Zab. 103:3) Mu ma za mu iya roƙan Allah ya kula da mu sa’ad da muke rashin lafiya.

10. Mene ne za mu iya koya daga abubuwan da suka faru da Turofimus da kuma Abafroditus?

10 Ko da yake manzo Bulus da wasu sun warkar da mutane a ƙarni na farko, ba dukan Kiristoci ba ne aka warkar da su ta hanyar mu’ujiza ba. (Karanta Ayyukan Manzanni 14:8-10.) Bulus ya warkar da “uban Bubliyus” wanda “ciwon zazzaɓi da atuni” ya kwantar da shi. (A. M. 28:8) Wani ɗan’uwa mai suna Turofimus ya bi Bulus zuwa wa’azi a ƙasar waje. (A. M. 20:3-5, 22; 21:29) Amma sa’ad da ya yi rashin lafiya kuma ya kasa tafiya tare da Bulus, manzon bai warkar da shi ba. A maimakon haka, ya bar shi a Militus don ya sami sauƙi. (2 Tim. 4:20) Wani abokin tafiyar Bulus mai suna Abafroditus ya yi “ciwo, saura kaɗan ya mutu.” Littafi Mai Tsarki bai ce Bulus ya warkar da shi ba.—Filib. 2:25-27, 30.

KA YANKE SHAWARWARI MASU KYAU

11, 12. Me ya sa Luka ya taimaka wa Bulus, kuma ta yaya muka san cewa shi likitan ƙwarai ne?

11 Luka “ƙaunataccen likita,” ne ya rubuta littafin Ayyukan Manzanni kuma ya yi tafiya tare da Bulus. (Kol. 4:14; A. M. 16:10-12; 20:5, 6) Mai yiwuwa, Luka ya ba wa Bulus shawarwari game da magani kuma ya kula da shi da kuma wasu da suke tafiya tare. Me ya sa Luka ya yi hakan? Don Bulus ma da kansa ya yi rashin lafiya sa’ad da suke tafiye-tafiye don wa’azi. (Gal. 4:13) Yesu ya ce: “Masu-lafiya ba su da bukatar mai-magani; sai dai masu-cuta.” Saboda haka, wataƙila Luka ya ba wa Bulus da kuma wasu magunguna.—Luk. 5:31.

12 Littafi Mai Tsarki bai ambaci wuri ko lokacin da Luka ya je makarantar likita ba. Amma ya ce Bulus ya aika saƙon gaisuwa ta hannun Luka zuwa ga ’yan’uwa da ke Kolosi. Saboda haka, zai iya yiwuwa cewa Luka ya yi makaranta a Lawudikiya, wani birni da ke kusa da Kolosi. Luka ba jabun likita ba ne da ke yawan ba wa mutane maganin da bai san kome a kai ba. Mun san cewa shi likitan ƙwarai ne don yadda ya yi amfani da wasu kalmomin da likitoci suke amfani da su sa’ad da yake rubuta littafin Luka da Ayyukan Manzanni, da kuma yadda ya mai da hankali ga warkarwa da Yesu ya yi.

13. Wane irin ra’ayin ne ya kamata mu kasance da shi sa’ad da wani ya ba mu shawara game da jinya?

13 A yau, ba wani ɗan’uwa da zai iya warkar da mu ta mu’ujiza. Amma akwai ’yan’uwan da suke son mu sami sauƙi. Saboda haka, sukan ba mu shawarwari a kan wasu magunguna. Hakika, wasu shawarwarin sukan kasance mai kyau. Alal misali, manzo Bulus ya ƙarfafa Timotawus ya sha ruwan inabi. Ya faɗi hakan saboda Timotawus yana ciwon ciki wataƙila don ruwa marar kyau da yake sha. * (Karanta 1 Timotawus 5:23.) Amma ya kamata mu mai da hankali. Wani ɗan’uwa zai iya nacewa mu sha wani irin magani ko mu ci ko mu guji wani abinci. Suna iya gaya mana cewa: ‘Wani dangina yana da irin wannan ciwo kuma ya sha . . . sai ya warke.’ Amma hakan ba ya nufin cewa maganin zai warkar da mu. Ya kamata mu tuna cewa duk wata shawara da wani ya ba mu game da wani magani, zai iya kawo kasada ko da maganin da mutane suka sani ne sosai.—Karanta Misalai 27:12.

KA YI TUNANI DA KYAU

14, 15. (a) Wasu suna ɗaukan rashin lafiya zarafin yin mene ne? (b) Ta yaya Misalai 14:15 za ta taimaka mana sa’ad da wani yake ba mu shawara game da jinya?

14 A matsayin mu na Kiristoci, muna son mu kasance da ƙoshin lafiya don mu ji daɗin rayuwa yayin da muke bauta wa Allah. Amma muna rashin lafiya saboda mu ajizai ne. Akwai abubuwa da yawa da za mu iya yi don mu sami sauƙi sa’ad da muke rashin lafiya. Kowane mutum yana da ’yanci ya zaɓi maganin da yake so. Abin baƙin ciki, wasu a duniyar nan sun ɗauki wannan zarafin a matsayin hanyar neman kuɗi. Wasu suna sayar da “magunguna” kuma suna cewa wani ya sha ya warke. Wasu mutane ko kuma kamfanoni suna nace wa mutane su saya wasu magunguna masu tsada don su ci riba sosai. Wanda yake rashin lafiya zai iya yarda da abin da suka ce domin yana son ya sami sauƙi. Amma Littafi Mai Tsarki ya ce: “Marar wayo yana gaskata kowace magana: Amma mai hankali yakan lura da al’amuransa da kyau.”—Mis. 14:15.

15 Idan muna da wayo, ba za mu gaskata da duk wani abu da mutane suka ce game da magunguna ba. “Mai hankali” yakan yi tunani cewa: ‘Wannan mutumin ya ce bitamin ko maganin ya taimaki wani amma shin da akwai tabbacin da ya nuna cewa hakan gaskiya ne? Tun da jikinmu ya bambanta, shin wannan maganin zai warkar da ni kuwa? Shin ya kamata in yi bincike ko kuma in je in tuntuɓi wani da na san ya ƙware a wannan aikin?’—K. Sha. 17:6.

16. Waɗanne tambayoyi ne za su taimaka mana mu yi “hankali” game da magani ko jinya da mutane suke ɗaukakawa?

16 Kalmar Allah ta ba mu shawara cewa mu yi rayuwa da “hankali . . . cikin wannan zamani.” (Tit. 2:12) Ya kamata mu yi “hankali” musamman sa’ad da wani ya gaya mana cewa wani irin magani ko kuma jinya mai ban mamaki yana da amfani. Shin mai maganin ko kuma mai bayanin zai iya nuna dalla-dalla yadda maganin yake aiki? Shin likitoci da yawa sun amince cewa maganin yana warkar da mutane? (Mis. 22:29) Ko kuma ana ƙoƙari a rinjayi mai rashin lafiyar don ya sayi maganin ne? Wataƙila an gaya mana cewa sabon magani ne kuma likitoci ba su san da maganin ba tukuna. Mene ne ya nuna cewa maganin yana aiki da gaske? Wasu za su iya ce ba za a iya bayyana yadda maganin yake aiki ba. Hakan zai iya kasancewa da haɗari sosai don Allah ya ce mu guji yin sihiri ko sha’ani da boka.—Isha.1:13; K. Sha. 18:10-12.

“KU ZAUNA LAFIYA”

17. Wane muradi ne muke da shi?

17 Hukumar da ke Kula da Ayyukan Kiristoci na ƙarni na farko ta aika wata wasiƙa mai muhimmanci zuwa ga ikilisiyoyi. A cikin wasiƙar, ta ambaci abubuwan da ya wajaba Kiristoci su guje wa kuma ta kammala wasiƙar da cewa: “Idan kun tsare kanku daga waɗannan, kun kyauta ke nan. Ku zauna lafiya.” (A. M. 15:29) Hukumar ta yi amfani da wannan furucin “ku zauna lafiya” don ta yi wa ’yan’uwa fatan alheri ne, amma hakan zai iya nufin cewa tana yi musu fatan kasancewa da ƙoshin lafiya. Hakika, muna so mu kasance cikin ƙoshin lafiya don mu bauta wa Jehobah.

Muna so mu kasance da ƙoshin lafiya don mu bauta wa Jehobah (Ka duba sakin layi na 17)

18, 19. Mene ne muke sa rai cewa zai faru a sabuwar duniya?

18 Da yake mu ajizai ne, za mu iya yin rashin lafiya a wannan zamanin. Kuma idan muna fama da wani ciwo, kada mu sa rai cewa za mu sami sauƙi ta hanyar mu’ujiza. Amma, Ru’ya ta Yohanna 22:1, 2 sun ambaci lokacin da za a warkar da mu daga dukan cututtuka. Manzo Yohanna ya ga wahayin “kogin ruwa na rai” da ‘itatuwa na rai,’ da kuma ganyayen “domin warkarwar al’ummai.” Wannan ba ya nufin maganin gargajiya na yanzu ko a nan gaba. A maimakon haka, yana nufin tanadin da Jehobah ya yi ta wurin Yesu don dukan masu biyayya su sami rai na har abada. Babu shakka, wannan alkawari ne da muke sa rai cewa zai faru da gaske.—Isha. 35:5, 6.

19 Yayin da muke jiran wannan lokacin, ya kamata mu kasance da tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunarmu, ko da muna rashin lafiya. Mu dogara ga Allah kamar yadda Dauda ya dogara gare shi a lokacin da yake rashin lafiya. Kamar Dauda, za mu iya ce: “Ni dai kana riƙe da ni cikin adalcina, kana sa ni a idonka har abada.”—Zab. 41:12.

^ sakin layi na 13 Littafin nan The Origins and Ancient History of Wine ya ce: “Masana sun gano cewa cutar typhoid da kuma wasu ƙwayoyin cuta suna mutuwa idan aka saka su ciki ruwan inabi.”