Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Jehobah, Allah Ne Mai Ma’amala da Mutane

Jehobah, Allah Ne Mai Ma’amala da Mutane

“Kasa kunne, zan yi magana da kai.”—AYU. 42:4, Littafi Mai Tsarki.

WAƘOƘI: 113, 114

1-3. (a) Me ya sa tunanin Allah da kuma yadda yake sadarwa sun fi na ’yan Adam? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

JEHOBAH ya halicci abubuwa masu rai don yana so su ji daɗin rayuwa da yake shi Allah ne mai farin ciki. (Zab. 36:9; 1 Tim. 1:11) Manzo Yohanna ya ce wanda Allah ya fara halitta shi ne “Kalma” kuma shi ne “farkon halittar Allah.” (Yoh. 1:1; R. Yoh. 3:14) Jehobah ya bayyana ra’ayinsa da kuma yadda yake ji ga wannan Ɗa da ya fara halitta, wato Yesu. (Yoh. 1:14, 17; Kol. 1:15) Manzo Bulus ya ce mala’iku suna da nasu ‘harshe’ ko yare, kuma ya bambanta sosai da na ’yan Adam.—1 Kor. 13:1.

2 Jehobah ya san kome game da biliyoyin mala’iku da kuma ’yan Adam da ya halitta. Yana jin addu’o’in da mutane da yawa suke yi masa duk da cewa suna yin hakan a harsuna dabam-dabam. Ƙari ga haka, yana sadarwa da mala’iku kuma yana ba su ja-gora a lokaci ɗaya. Shin ta yaya Jehobah yake cim ma hakan? Yana cim ma hakan ne don tunaninsa da yarensa da kuma yadda yake sadarwa sun fi na ’yan Adam. (Karanta Ishaya 55:8, 9.) Hakan ya nuna cewa Jehobah yana sauƙaƙa yadda yake sadarwa da mutane don su fahimce shi.

3 Yanzu, za mu tattauna yadda Jehobah ya ɗauki matakai don ya sanar da saƙonsa dalla-dalla ga ’yan Adam. Ƙari ga haka, za mu tattauna yadda Jehobah yake amfani da hanyoyi dabam-dabam don ya yi sha’ani da mutane bisa ga yanayinsu.

ALLAH YANA MAGANA DA MUTANE

4. (a) Wane yare ne Jehobah ya yi amfani da shi wajen sanar da saƙonsa ga Musa da Sama’ila da kuma Dauda? (b) Wane saƙo ne ke cikin Littafi Mai Tsarki?

4 Jehobah ya yi amfani da yaren ’yan Adam sa’ad da yake magana da Adamu. Wataƙila Allah ya yi amfani da yaren Ibraniyawa na dā. Daga baya, Jehobah ya sanar da saƙonsa da kuma ra’ayinsa ga Ibraniyawa kamar su Musa da Sama’ila da kuma Dauda. Waɗannan marubuta sun bayyana ra’ayin Allah, amma sun yi amfani da kalamansu da kuma tsarin rubutunsu. Sun rubuta wasu abubuwan da Allah ya sanar musu kai tsaye da kuma yadda Allah ya yi sha’ani da Isra’ilawa. Wannan ya haɗa da yadda suka nuna bangaskiya da ƙaunarsu ga Allah da kuma kurakuransu da rashin bangaskiyarsu. Dukan bayanan nan suna da muhimmanci a gare mu a yau.—Rom. 15:4.

5. Yaren Ibrananci ne kawai Jehobah ya yi amfani da shi wajen sadarwa da mutanensa? Ka bayyana.

5 Da shigewar lokaci, Allah ya ci gaba da sanar da saƙonsa ga ’yan Adam a wasu harsuna. Sa’ad da Isra’ilawa suka dawo daga bauta a Babila, sun yi amfani da harshen Aramaic a harkokinsu na yau da kullum. Wataƙila shi ya sa Jehobah ya ja-goranci annabawa kamar su Daniyel da Irmiya da kuma Ezra firist su rubuta wasu sassa na Littafi Mai Tsarki a harshen Aramaic. *

6. Ta yaya aka tanadar da Kalmar Allah a wasu harsuna ban da Ibrananci?

6 Sa’ad da Sarki Alexander the Great ya ci ƙasashe da yawa da yaƙi, yaren Girka, wato Koine ya zama yaren da ake yi a ƙasashe da yawa. Saboda haka, Yahudawa da yawa suka soma yin yaren Girka, kuma hakan ya sa aka fassara littattafan Farawa zuwa Malakai daga Ibrananci zuwa yaren Girka. Masana sun ce mafassara guda 72 ne suka yi wannan fassara, kuma ana kiranta Septuagint. Ita ce fassarar Littafi Mai Tsarki ta farko kuma ta zama mai muhimmanci sosai. * Wasu mafassaran sun fassara kalma bayan kalma, wasu kuma sun fassara ma’ana. Duk da haka, Yahudawa da ke yaren Girka da kuma Kiristoci sun gaskata cewa fassarar Septuagint Kalmar Allah ce.

7. Wane yare ne Yesu ya yi amfani da shi wajen koyar da almajiransa?

7 Sa’ad da Yesu ya zo duniya, wataƙila ya yi amfani da Ibrananci wajen koyar da almajiransa. (Yoh. 19:20; 20:16; A. M. 26:14) Mai yiwuwa Yesu ya yi amfani da wasu kalaman yaren Aramaic da yake an fassara wasu sassan Littafi Mai Tsarki a wannan yaren. Amma ya yi amfani da Ibrananci na dā da Musa da sauran annabawa suka yi amfani da shi, wanda ake karantawa kowane mako a cikin majalisa. (Luk. 4:17-19; 24:44, 45; A. M. 15:21) Ƙari ga haka, mutane sun yi amfani da harsunan Girka da kuma Helenanci. Amma Littafi Mai Tsarki bai ambata cewa Yesu ya yi waɗannan yarukan ba.

8, 9. Yayin da addinin Kirista yake yaɗuwa, me ya sa yaren Girka ya zama ainihin yaren da almajiran Yesu suke yi, kuma mene ne hakan ya nuna game da Jehobah?

8 Almajiran Yesu sun iya Ibrananci, amma bayan mutuwarsa, sun yi wasu yaruka. (Karanta Ayyukan Manzanni 6:1.) Yayin da addinin Kirista yake yaɗuwa, Kiristoci sun yi amfani da yaren Girka wajen sadarwa. Da yake yaren Girka ya zama yaren da ake yi a ko’ina a lokacin, an fassara kuma an rarraba Linjilar Matta da Markus da Luka da kuma Yohanna a yaren Girka. Saboda haka, za mu iya ce almajiran Yesu sun yi amfani da yaren Girka, ba Ibrananci ba. * Ƙari ga haka, an rubuta wasiƙun manzo Bulus da kuma wasu littattafan Littafi Mai Tsarki a yaren Girka.

9 Sa’ad da marubutan Nassosin Helenanci (Matta zuwa Ru’ya ta Yohanna) suke ƙaulin wasu ayoyi daga Attaura, wato Farawa zuwa Malakai, sun yi hakan ne daga fassarar Septuagint. Ko da yake waɗannan ayoyi sun ɗan bambanta da yadda kalmomin suke a Ibrananci, suna cikin Littafi Mai Tsarki da muke amfani da shi a yau. Saboda haka, aikin mafassara ajizai ya kasance cikin Kalmar Allah kuma hakan ya nuna cewa Allah ba ya ɗaukan wani yare da muhimmanci fiye da wani.—Karanta Ayyukan Manzanni 10:34.

10. Wane darasi ne muka koya game da yadda Jehobah ya tanadar da Littafi Mai Tsarki wa mutane?

10 Waɗannan abubuwan da muka tattauna game da yadda Allah yake sadarwa da mutane ya koya mana cewa Jehobah yana yin hakan bisa ga bukata da kuma yanayin mutanensa. Bai nace sai mun yi amfani da wani yare na musamman kafin mu san shi da kuma nufinsa ba. (Karanta Zakariya 8:23; Ru’ya ta Yohanna 7:9, 10.) Ko da yake Jehobah ne ya ja-goranci mutane su rubuta Littafi Mai Tsarki, duk da haka, ya amince mutane su rubuta shi a harsuna dabam-dabam.

YADDA ALLAH YA KĀRE KALMARSA

11. Me ya sa yawan yaruka bai hana Allah sha’ani da mutane ba?

11 Shin yawan yaruka da kuma ɗan bambancin da aka samu a fassara ya hana Allah sadarwa da mutane? A’a. Alal misali, ainihin kalaman da Yesu ya yi amfani da su a yaren Ibrananci kaɗan ne kawai suke cikin Littafi Mai Tsarki da muke amfani da shi a yau. (Mat. 27:46; Mar. 5:41; 7:34; 14:36) Amma Jehobah ya tabbata cewa an fassara koyarwar Yesu a Girkanci da kuma wasu yaruka. Daga baya, Yahudawa da Kiristoci sun kofi Littafi Mai Tsarki sau da sau kuma hakan ya sa aka adana waɗannan rubuce-rubuce da aka hure da ruhu mai tsarki. Wajen shekaru 400 bayan haihuwar Yesu, wani marubuci mai suna John Chrysostom ya ce a zamaninsa, an fassara koyarwar Yesu zuwa yarukan Suriyawa da Masarawa da Farisawa da Habashawa da kuma wasu yaruka da dama.

12. Ta yaya mutane suka yi ƙoƙarin hana yaɗuwar Littafi Mai Tsarki?

12 Fassara Littafi Mai Tsarki a harsuna da yawa ya sa magabta sun kasa hana yaɗuwar Littafi Mai Tsarki. Alal misali, a shekara ta 303 bayan haihuwar Yesu, Sarkin Roma mai suna Diocletian ya ba da umurni cewa a halaka dukan fassarar Littafi Mai Tsarki. Ƙari ga haka, an kai hari wa mutanen da suka fassara da kuma rarraba Littafi Mai Tsarki. A ƙarni na 16, wani mafassari mai suna William Tyndale ya ɗauki matakin fassara Littafi Mai Tsarki daga Ibrananci da kuma Girkanci zuwa Turanci. Ya gaya wa wani malamin addini cewa: “Idan Allah ya yarda, zan sa yaron da ke huɗa a gona ya san Littafi Mai Tsarki fiye da kai.” Tyndale ya tsere daga Ingila zuwa Turai don ya fassara kuma ya buga Littafi Mai Tsarki. Duk da cewa malaman addini sun yi ƙoƙarin ƙona dukan fassarar Littafi Mai Tsarki da suka tattara a lokacin, ba a daina rarraba Littafi Mai Tsarki ba. Daga baya, an ci amanar Tyndale, aka maƙure shi kuma aka ƙone shi a kan gungume. Amma fassarar Littafi Mai Tsarki da ya yi, ya ci gaba da yaɗuwa. An yi amfani da shi sosai wajen shirya da kuma fassara juyin Littafi Mai Tsarki na King James.Karanta 2 Timotawus 2:9.

13. Mene ne nazarin rubuce-rubucen Littafi Mai Tsarki na dā ya nuna?

13 Hakika, akwai ƙananan kura-kurai da kuma bambanci a cikin rubuce-rubucen Littafi Mai Tsarki na dā. Amma masanan Littafi Mai Tsarki sun yi nazarin waɗannan littattafai cikin natsuwa kuma suka gano cewa wasu ayoyi kaɗan ne kawai aka sami bambanci kuma hakan bai shafi ainihin saƙon da ke cikin Littafi Mai Tsarki ba. Wannan nazarin Littafi Mai Tsarki da aka yi ya tabbatar wa masu son gaskiya cewa Littafi Mai Tsarki da muke da shi a yau Kalmar Allah ce.—Isha. 40:8. *

14. Ka bayyana yadda aka rarraba Littafi Mai Tsarki a yau.

14 Jehobah ya tabbata cewa an fassara Kalmarsa gaba ɗaya ko kuma sashenta zuwa harsuna fiye da 2,800 duk da hamayya da magabta suka yi. Littafi Mai Tsarki shi ne littafin da aka fi rarrabawa a tarihi, har ma a lokacin da mutane da yawa ba su yi imani da Allah ba. Ko da yake wasu fassarar Littafi Mai Tsarki sun fi wasu sauƙin fahimta, duk da haka, dukansu suna ɗauke da koyarwa da ke sa mutane su kasance da begen samun rai na har abada.

AN BUKACI SABUWAR FASSARAR LITTAFI MAI TSARKI

15. (a) Ta yaya aka sha kan matsalar yare? (b) Ta yaya Turanci ya zama harshen da ake amfani da shi wajen tanadar da littattafan da ke bayyana Littafi Mai Tsarki?

15 A shekara ta 1919 ne aka naɗa wani ƙaramin rukunin ɗaliban Littafi Mai Tsarki a matsayin “bawan nan mai-aminci, mai-hikima.” A yawancin lokaci suna sadarwa da mutanen Jehobah a harshen Turanci. (Mat. 24:45) Wannan ‘bawa,’ wato ɗaliban nan sun yi aiki sosai wajen tanadar da littattafan da ke bayyana Littafi Mai Tsarki a harsuna da yawa. Yanzu harsunan sun ƙaru zuwa fiye da 700. Kamar yaren Girka, wato Koine a ƙarni na farko, Turanci ya zama yare da ake amfani da shi wajen ilimantarwa da kuma kasuwanci. Saboda haka, ana tanadar da littattafanmu a Turanci don a fassara su zuwa wasu harsuna.

16, 17. (a) Wace bukata ce mutanen Allah suka kasance da ita? (b) Ta yaya aka biya wannan bukatar? (c) Mene ne burin Ɗan’uwa Knorr a shekara ta 1950?

16 Ana ɗauko batutuwan da aka tattauna a cikin littattafanmu daga Littafi Mai Tsarki. Shi ya sa da farko, mutanen Allah sun yi amfani da juyin King James Version na 1611 don shi ne Littafi Mai Tsarki da aka fi amfani da shi a lokacin. Amma, an fassara shi da Turanci na dā. Ƙari ga haka, a wasu wurare kaɗan ne kawai aka ambata sunan Allah, amma asalin rubuce-rubucen Littafi Mai Tsarki na dā suna ɗauke da sunan Allah a wurare da yawa. Wannan fassarar King James tana da kura-kurai da mafassara suka yi da kuma ayoyin da ba sa cikin ainihin rubuce-rubuce na dā. Wasu fassarar Littafi Mai Tsarki na Turanci suna da irin waɗannan kura-kuran.

17 Saboda haka, an bukaci Littafi Mai Tsarki da zai bayyana ainihin saƙon da ke cikin rubuce-rubuce na asali daidai kuma a harshen Turanci na zamani. Don a cim ma hakan, sai aka naɗa Kwamitin Fassara Littafi Mai Tsarki na New World Translation. Wannan kwamitin ya fitar da sassan fassarar Littafi Mai Tsarki guda shida a cikin shekara 10, wato daga 1950 zuwa 1960. Sa’ad da Ɗan’uwa N. H. Knorr yake fitar da sashe na farko a wani babban taro a ranar 2 ga Agusta, 1950, ya gaya wa masu sauraro cewa: “Ana bukatar fassarar Littafi Mai Tsarki a yaren zamani, fassarar da ta jitu da koyarwar gaskiya da za ta taimaka mana mu ƙara fahimtar gaskiya ta wajen fassara ainihin rubuce-rubuce na dā daidai kuma wadda mutanen zamani za su fahimta kamar yadda talakawa na zamanin dā suka fahimci koyarwar almajiran Kristi.” Burin Ɗan’uwa Knorr shi ne wannan fassarar ta taimaka wa miliyoyin mutane su ƙulla dangantaka ta kud da kud da Jehobah.

18. Wane mataki ne ya taimaka wajen fassara Littafi Mai Tsarki?

18 An cim ma wannan burin a shekara ta 1963, sa’ad da aka fitar da New World Translation of the Christian Greek Scriptures, kuma an fassara shi zuwa wasu harsuna shida, wato Faransanci da Jamusanci da Sfanisanci da yarukan mutanen Holland da Italiya da kuma Portugal. A shekara ta 1989, Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta kafa wani sashe a hedkwatarmu don a hanzarta fassarar Littafi Mai Tsarki. Bayan haka, a shekara ta 2005, aka soma mai da hankali ga fassara Littafi Mai Tsarki gaba ɗaya ko sashensa a harsunan da ake buga Hasumiyar Tsaro a ciki. A sakamakon haka, an fassara New World Translation gaba ɗaya ko kuma sashensa a fiye da harsuna 130.

19. Wane taro mai muhimmanci ne aka yi a shekara ta 2013, kuma mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

19 Da shigewar lokaci, ya zama wajibi a sabonta fassarar New World Translation na Turanci don a daidaita shi da Turanci na zamani. Saboda haka, ba ƙaramin farin ciki ba ne mahalartan taron shekara-shekara na 129 na Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania suka yi a ranakun 5 da 6 ga Oktoba, 2013, sa’ad da wani memban Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ya fitar da juyin New World Translation na Turanci. Mutane 1,413,676 a ƙasashe 31 ne suka shaida wannan aukuwar kai tsaye da kuma ta hanyar sadarwa ta bidiyo. Ƙari ga haka, da yawa daga cikinsu sun yi hawaye sa’ad da ake rarraba musu wannan juyin Littafi Mai Tsarki. Masu sauraro sun yi farin ciki sosai yayin da masu ba da jawabi a wannan taron suka karanta wannan fassarar Littafi Mai Tsarki don fassarar tana da sauƙin fahimta. A talifi na gaba, za mu tattauna wasu abubuwa game da wannan fassarar da kuma yadda ake amfani da ita wajen fassara Littafi Mai Tsarki zuwa wasu harsuna.

^ sakin layi na 5 Tun asali an rubuta Ezra 4:8–6:18, 7:12-26 da Irmiya 10:11; da kuma Daniyel 2:4b–7:28 a yaren Aramaic.

^ sakin layi na 6 Septuagint yana nufin “Saba’in.” An ce an soma fassarar ne a Masar wajen shekaru 300 kafin haihuwar Yesu kuma an kammala fassarar wajen shekaru 150 bayan haka. Wannan fassarar tana da muhimmanci har ila don tana taimaka wa masana su san ma’anar wasu kalmomin Ibrananci da kuma ayoyi da suke da wuyan fahimta.

^ sakin layi na 8 Wasu sun ce Matta ya rubuta Lingilar Matta a Ibrananci. Daga baya, wataƙila Matta da kansa ne ya fassara Linjilar zuwa yaren Girka.

^ sakin layi na 13 Ka duba rataye na A3 na fassarar New World Translation; da kuma ƙasidar nan, Littafi Don Dukan Mutane “Ina Yadda Littafin Ya Tsira?” shafuffuka na 7-9.