Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Fassarar Littafi Mai Tsarki Mai Saukin Fahimta

Fassarar Littafi Mai Tsarki Mai Saukin Fahimta

“Maganar Allah mai-rai ce.”—IBRAN. 4:12.

WAƘOƘI: 37, 116

1. (a) Wane irin aiki ne Allah ya ba Adamu? (b) Tun daga lokacin, ta yaya mutanen Allah suke yin amfani da yare?

JEHOBAH ALLAH ya ba ’yan Adam baiwar iya yin yare. A lambun Adnin, Allah ya ba Adamu aikin ba wa dukan dabbobi sunaye. Adamu ya ba kowace dabba suna mai ma’ana. (Far. 2:19, 20) Tun daga lokacin, mutanen Allah sun ci gaba da yin amfani da yare don su yabi Jehobah kuma su sanar da nufinsa ga mutane. A kwanan nan, mutanen Allah sun ɗaukaka bauta ta gaskiya ta wajen fassara Littafi Mai Tsarki don mutane da yawa su ƙara koya game da Jehobah.

2. (a) Waɗanne ƙa’idodi ne Kwamitin Fassara Littafi Mai Tsarki na New World Translation suka bi sa’ad da suke aikinsu? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

2 Ko da yake akwai dubban fassarar Littafi Mai Tsarki, amma sun bambanta a yadda suka bayyana saƙon da ke cikin rubuce-rubucen Littafi Mai Tsarki na asali. A shekara ta 1940 zuwa 1949, Kwamitin Fassara Littafi Mai Tsarki na New World Translation sun kafa ƙa’idodin fassara da mafassara suke bi a yaruka fiye da 130. Waɗannan ƙa’idodin su ne: (1) A tsarkake sunan Allah kuma a yi amfani da sunan a cikin Littafi Mai Tsarki yadda aka yi a fassara na asali. (Karanta Matta 6:9.) (2) Idan zai yiwu, a fassara hurarren saƙo na asali kalma bayan kalma, amma idan hakan ba zai yiwu ba, sai a fassara ainihin ma’anar. (3) An yi amfani da yare mai sauƙin fahimta da zai sa mutane su karanta Littafi Mai Tsarki. * (Karanta Nehemiya 8:8, 12.) Bari mu ga yadda aka bi waɗannan ƙa’idodin a juyin New World Translation na 2013 da yadda mafassara na wasu yaruka suka yi amfani da ƙa’idodin.

FASSARAR DA KE ƊAUKAKA SUNAN ALLAH

3, 4. (a) Waɗanne rubuce-rubucen Littafi Mai Tsarki na dā suke ɗauke da baƙaƙe huɗu wato, YHWH? (b) Mene ne mafassaran Littafi Mai Tsarki da yawa suka yi game da sunan Allah?

3 Masanan rubuce-rubucen Littafi Mai Tsarki na Ibrananci na dā, kamar Littattafai na Tekun Gishiri sun yi mamakin ganin cewa baƙaƙen nan huɗu, wato YHWH, da suke wakiltar sunan Allah sun bayyana a wurare da yawa a cikin littattafan. An gano sunan Allah a waɗannan rubuce-rubuce na Ibrananci na dā da kuma wasu littattafai na Septuagint a yaren Girka daga ƙarni na biyu kafin haihuwar Yesu zuwa ƙarni na farko bayan haihuwar Yesu.

4 Ko da yake akwai ƙwaƙƙwarar shaida da ta nuna cewa akwai sunan Allah a cikin Littafi Mai Tsarki, masu fassara da yawa sun cire sunan Allah gabaki ɗaya daga fassararsu. Alal misali, bayan shekara biyu da aka fito da juyin New World Translation of the Christian Greek Scriptures a shekara ta 1950, an wallafa juyin Revised Standard Version. Amma mafassaran sun cire sunan Allah. Ƙari ga haka, sun canja dokar mawallafan juyin American Standard Version na 1901. Me ya sa? A gabatarwar sun ce: “Bai dace ko kaɗan mutane su riƙa kiran sunan Allah makaɗaici a coci ba.” Kuma hakan ya sa mafassara da yawa a Turanci da kuma wasu yaruka suka cire sunan Allah daga fassararsu.

5. Me ya sa yake da muhimmanci a yi amfani da sunan Allah a cikin Littafi Mai Tsarki?

5 Shin yana da muhimmanci ne mafassara su yi amfani da sunan Allah a fassararsu? Hakika! Jehobah Mawallafin Littafi Mai Tsarki yana son mutane su san sunansa. Ya kamata mafassari da ya ƙware ya san abin da mawallafi yake so ya sanar wa masu karatu kuma ya dace hakan ya shafi kalmomin da zai yi amfani da su a fassararsa. Ƙari ga haka, ayoyi da dama a cikin Littafi Mai Tsarki sun nuna cewa yana da muhimmanci a yi amfani da sunan Allah kuma a tsarkake shi. (Fit. 3:15; Zab. 83:18; 148:13; Isha. 42:8; 43:10; Yoh. 17:6, 26; A. M. 15:14) Ƙari ga haka, a rubuce-rubuce na dā, Jehobah ya hure marubutan Littafi Mai Tsarki su yi amfani da sunansa fiye da sau dubu bakwai. (Karanta Ezekiyel 38:23.) Saboda haka, mafassara ba sa daraja Jehobah idan suka cire sunansa daga fassarar da suka yi.

6. Me ya sa aka ƙara sunan Allah a wurare shida a sabon juyi na New World Translation?

6 A yau, muna da tabbacin da ya nuna cewa ya kamata mu yi amfani da sunan Allah. A juyin New World Translation na 2013, an yi amfani da sunan Allah sau 7,216, wanda ya ƙunshi ƙarin wurare 6 da aka yi amfani da sunan fiye da yadda ya bayyana a juyi na shekara ta 1984. Guda biyar a cikinsu suna waɗannan ayoyi da ke 1 Sama’ila 2:25; 6:3; 10:26; 23:14, 16. An yi hakan domin an gano sunan Allah a Littattafai na Tekun Gishiri da aka wallafa ba da daɗewa ba, kuma waɗannan littattafan sun yi sama da shekara 1,000 kafin a sami juyin Ibrananci. Bayan ƙarin bincike da aka yi a rubuce-rubuce na dā, an ƙara sunan Allah a Alƙalawa 19:18. Wannan shi ne ƙari na shida da aka yi.

7, 8. Mene ne ma’anar sunan nan Jehobah?

7 Kiristoci na gaskiya suna ɗaukan sunan Allah da muhimmanci. Rataye na juyin New World Translation na 2013 yana ɗauke da ƙarin bayani a kan wannan batun. Kwamitin Fassara Littafi Mai Tsarki na New World Translation sun fahimci cewa an samo sunan daga kalmar Ibrananci nan ha·wah, da take nufin “Yana Sa Ya Kasance.” * A dā, mun bayyana ma’anar sunan Allah ta wajen yin amfani da Fitowa 3:14 da ta ce: “Zan Zama Abin da Nake Son In Zama.” Shi ya sa a juyi na shekara ta 1984 aka bayyana cewa sunan yana nufin “yana sa kansa shi zama Mai Cika alkawura.” * “Amma an yi bayani a Appendix A4 na juyin New World Translation na 2013 cewa: ‘Ƙari ga wannan ma’anar, sunan yana nufin cewa Allah yana sa halittunsa su zama duk abin da ake bukata don ya cika nufinsa.’ (Don ƙarin bincike, ka duba ƙasidar nan Taimako don Nazarin Kalmar Allah, sakin layi na 3, shafi na 5).”

8 Jehobah yana sa halittunsa su zama duk abin da ake bukata. Daidai da ma’anar sunansa, Allah ya sa Nuhu ya gina jirgi. Ƙari ga haka, Jehobah ya sa Bezalel ya zama gwanin maƙeri, ya sa Gideon ya zama mayaƙi mai nasara kuma ya sa Bulus ya zama manzo ga al’ummai. Hakika, sunan Allah yana da ma’ana sosai ga mutanensa, shi ya sa Kwamitin Fassara Littafi Mai Tsarki na New World Translation suka yi amfani da sunansa a wannan fassarar.

9. Me ya sa aka mai da hankali ga tanadar da juyin New World Translation a wasu harsuna?

9 An mayar da sunan Allah a cikin juyin New World Translation da aka fassara a harsuna fiye da 130 kamar yadda yake a ainihin rubuce-rubuce na dā. (Karanta Malakai 3:16.) * Amma wasu mafassaran Littafi Mai Tsarki na zamani suna canja sunan Allah da laƙabi kamar “Ubangiji” ko kuma sunan wani allan gargajiya a fassarar da suke yi. Wannan shi ne babban dalilin da ya sa Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta mai da hankali ga tanadar da Littafi Mai Tsarki da ke ɗauke da sunan Allah ga mutane da yawa a yarensu.

FASSARAR DA AKA YI DAIDAI WA DAIDA

10, 11. Waɗanne matsaloli ne mafassaran suka fuskanta sa’ad da suke fassara New World Translation zuwa wasu harsuna?

10 Mafassaran sun fuskanci matsaloli da dama yayin da suke fassara juyin New World Translation na Turanci zuwa wasu harsuna. Alal misali, a dā, mafassaran sun bi tsarin wasu mafassaran Littafi Mai Tsarki kuma sun yi amfani da kalmar Ibrananci, wato “Sheol” a Mai-Wa’azi 9:10. Amma yawancin mutane da ke waɗannan harsuna ba su san abin da “Sheol” yake nufi ba. Ba su da wannan kalmar a cikin ƙamus na yarensu. Ƙari ga haka, wasu sun ɗauka cewa sunan wani wuri ne. Saboda haka, aka ba da izini a fassara “Sheol” da kuma kalmar Helenanci, wato “Hades” zuwa “Kabari.”

11 Fassara kalmar Ibrananci nan neʹphesh da kuma na Helenanci, wato psy·kheʹ zuwa wadda ta yi daidai da na Turanci yana da wuya a wasu yaruka. Me ya sa? Domin kalmar tana nufin fatalwa ko kuma kurwa a waɗannan yarukan. Saboda haka, idan suka yi amfani da kalmar a yarensu, za a ɗauka cewa ana nufin wani abu ne da ke barin jikin mutum bayan mutuwa. Don a magance wannan matsalar, an ba wa mafassara izini su fassara kalmar bisa ga mahallin da kuma ma’anar da an riga an bayyana a rataye na New World Translation of the Holy Scriptures—With References. An mai da hankali ga fassara kalmomin a yadda za su kasance da sauƙin fahimta kuma aka ba da ƙarin bayani a ƙasan shafuffukan.

12. Waɗanne gyare-gyare ne aka yi a juyin New World Translation na 2013? (Za ka sami ƙarin bayani a talifin nan “Juyin 2013 na New World Translation,” da ke cikin wannan fitowar.)

12 Tambayoyin da mafassara suka yi sun sa an gano wasu abubuwa da za su iya sa juyin New World Translation na Turanci ya yi wuyar fahimta. Saboda haka, a watan Satumba na shekara ta 2007, Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta ba da izini a kyautata fassarar. Sa’ad da ake yin bitar juyin, an bincika dubban tambayoyin da mafassaran Littafi Mai Tsarki suka aika. Aka sauya kalmomin Turanci da aka daina amfani da su, kuma aka mai da hankali sosai wajen sa fassarar ta kasance da sauƙin fahimta. Ƙari ga haka, an tabbata cewa fassarar ta kasance daidai wa daida kuma an bi shawarwarin da mafassaran juyin New World Translation zuwa wasu harsuna suka ba da don kyautata wannan sabon juyi na Turanci.—Mis. 27:17.

AN NUNA GODIYA DON WANNAN FASSARAR

13. Mene ne ’yan’uwa suka ce game da juyin New World Translation na 2013?

13 Mene ne ’yan’uwa suka ce game da sabon juyin New World Translation na Turanci? ’Yan’uwa maza da mata da yawa sun tura dubban wasiƙu zuwa hedkwatar Shaidun Jehobah da ke Brooklyn don nuna godiyarsu. Wata ’yar’uwa ta bayyana yadda mutane da yawa suka ji game da sabon juyin sa’ad da ta ce: “Littafi Mai Tsarki yana nan kamar akwati da ke cike da gwala-gwalai. Karanta kalmomin Jehobah daga juyi na 2013, yana kamar bincika kowane gwal yayin da kake mai da hankali ga haskensa da tsarinsa da kuma kyaunsa. Yadda juyin Littafi Mai Tsarki ya kasance da sauƙin fahimta ya sa na ƙara sanin Jehobah. Ƙari ga haka, Jehobah ya zama kamar Uba da ya ɗora hannunsa a kafaɗata yayin da yake gaya mini labarai masu daɗi.”

14, 15. Yaya mutane suka ji sa’ad da suka sami juyin New World Translation a yarensu?

14 Mutane sun yi godiya saboda juyin New World Translation da aka fassara zuwa yarensu. Wani tsoho daga birnin Sofia, a ƙasar Bulgariya ya nuna farin cikinsa sa’ad da ya sami juyin a yarensu, ya ce: “Na yi shekaru da yawa ina karanta Littafi Mai Tsarki, amma ban taɓa karanta fassara mai sauƙin fahimta kuma mai ratsa zuciya kamar wannan ba.” Wata ’yar’uwa da ta sami juyin New World Translation a yaren Albaniya ta ce: “Kalmar Allah ta fi daɗi a yaren Albaniya! Samun damar sauraron abin da Jehobah yake faɗa a yarenmu ba ƙaramin gata ba ne!”

15 Littafi Mai Tsarki yana da tsada a ƙasashe da yawa kuma ba a yawan samunsa. Saboda haka, samun Littafi Mai Tsarki ba ƙaramin albarka ba ne. An ba da wani rahoto daga ƙasar Ruwanda cewa: “A cikin shekaru da yawa, mutanen da ’yan’uwa suke nazarin Littafi Mai Tsarki da su, ba sa samun ci gaba don ba su da Littafi Mai Tsarki. Ba za su iya sayan wanda ake amfani da shi a coci ba don yana da tsada. Ƙari ga haka, ba sa fahimtar ma’anar wasu ayoyi sosai kuma hakan yana hana su ci gaba.” Amma abubuwa sun canja sa’ad da aka fitar da juyin New World Translation a yarensu. Wani iyali a Ruwanda da ke da matasa huɗu sun ce: “Mun gode wa Jehobah da kuma bawan nan mai aminci mai hikima saboda wannan Littafi Mai Tsarki. Mu talakawa ne kuma ba mu da kuɗin saya wa kowa a cikin iyalin Littafi Mai Tsarki. Amma yanzu kowannenmu yana da Littafi Mai Tsarki. Muna karanta Littafi Mai Tsarki kullum don mu nuna godiya ga Jehobah.”

16, 17. (a) Mene ne Jehobah yake wa mutanensa? (b) Mene ne ka kuɗiri niyyar yi?

16 Da shigewar lokaci, za a ƙara tanadar da New World Translation a wasu harsuna. Shaiɗan yana ƙoƙari ya hana wannan aikin, amma mun tabbata cewa Jehobah yana so dukan mutane su saurare shi yayin da yake yi musu magana a yaren da za su fahimta da sauƙi. (Karanta Ishaya 30:21.) Lokaci yana zuwa da “duniya za ta cika da sanin Ubangiji, kamar yadda ruwaye suke rufe teku.”—Isha. 11:9.

17 Bari mu kuɗiri niyyar yin amfani da kowace kyauta daga wurin Jehobah. Hakan ya haɗa da wannan juyin Littafi Mai Tsarki da ke ɗaukaka sunansa. Mu riƙa sauraronsa yayin da yake yi mana magana ta Kalmarsa. Yana sauraron dukan addu’o’inmu. Irin wannan sadarwa za ta taimaka mana mu ƙara sanin Jehobah kuma mu ƙaunace shi sosai.—Yoh. 17:3.

“Samun damar sauraron abin da Jehobah yake faɗa a yarenmu ba ƙaramin gata ba ne!”

^ sakin layi na 2 Ka duba Appendix A1 na sabon juyin New World Translation da kuma talifin nan “How Can You Choose a Good Bible Translation?” a Hasumiyar Tsaro na 1 ga Mayu, 2008 na Turanci.

^ sakin layi na 7 Wasu littattafai sun ba da wannan bayani, amma ba dukan masana ne suka yarda da hakan ba.

^ sakin layi na 7 Ka duba The New World Translation of the Holy Scriptures—With References, Appendix 1A “The Divine Name in the Hebrew Scriptures,” shafi na 1561.

^ sakin layi na 9 A lokacin, waɗanda suke tsoron Jehobah sun yi magana da juna, kowanne da ɗan’uwansa, kuma Jehobah ya yi ta saurarawa. Aka rubuta littafin tunawa a gabansa, domin waɗanda ke tsoron Jehobah da kuma bimbini a kan sunansa.—Mal. 3:16, New World Translation.