Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | ZA KA IYA KUSANTAR ALLAH

Kana Addu’a ga Allah Kuma Kana Sauraronsa?

Kana Addu’a ga Allah Kuma Kana Sauraronsa?

Abokai na kud-da-kud suna magana da juna a kai a kai ko ta wayar salula ko ta imel ko ta wasiƙa ko kuma ta na’urar bidiyo, dangane da yanayinsu. Hakazalika, idan muna so mu kusaci Allah, muna bukatar mu riƙa yin magana da shi a kai a kai. Amma a wace hanya ce za mu yi hakan?

Muna magana da Jehobah ta hanyar addu’a. Amma yin addu’a ba ɗaya yake da irin taɗin da muke yi da tsaranmu ba. Sa’ad da muke yin addu’a, zai dace mu tuna cewa muna magana ne da Mahaliccinmu da kuma Maɗaukakin sama da ƙasa. Saboda haka, ya kamata mu yi addu’a da ban girma da kuma ladabi. Idan muna so Allah ya ji addu’armu, zai dace mu bi ƙa’idodi uku da ke gaba.

Na ɗaya, mu yi addu’a ga Jehobah Allah kaɗai, ba ga Yesu ko kuma wani tsarkakke ko siffa ba. (Fitowa 20:4, 5) Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Cikin kowane abu, ta wurin addu’a da roƙo tare da godiya, ku bar roƙe roƙenku su sanu ga Allah.’ (Filibiyawa 4:6) Na biyu, wajibi ne mu yi addu’a a cikin sunan Ɗan Allah, Yesu Kristi. Yesu ya ce: ‘Ba mai zuwa wurin Uban sai ta wurina.’ (Yohanna 14:6) Na uku, wajibi ne addu’o’inmu su jitu da nufin Allah. Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Idan mun roƙi kome daidai da nufinsa, yana jinmu.’ *1 Yohanna 5:14.

Abokai na kud-da-kud suna magana da juna a kai a kai

Hakika, abokantaka ba za ta wayi gari ba idan mutum ɗaya ne kawai yake yin magana a kowane lokaci. Kamar yadda ba mutum ɗaya ne kawai yake magana idan yana da aboki ba, mu ma ya kamata mu bar Allah ya yi magana da mu kuma mu riƙa sauraronsa. Ka san yadda Allah yake magana da mu?

A yau, Jehobah yana magana da mu ta wajen Kalmarsa, wato Littafi Mai Tsarki. (2 Timotawus 3:16, 17) Me ya sa muka faɗi hakan? Ga wani misali: A ce wani amininka ya rubuto maka wasiƙa. Bayan ka karanta wasiƙar, za ka iya gaya wa mutane cewa, “Ai yanzun nan na ji daga wurin abokina!” Hakika, kun yi magana, ko da yake ta wasiƙa ne. Haka nan ma, ta wajen karanta Littafi Mai Tsarki, za mu bar Jehobah ya yi magana da mu. Shi ya sa Gina, wadda aka ambata ɗazu ta ce, “A ganina, idan ina so Allah ya ɗauke ni a matsayin amininsa, wajibi ne in karanta ‘wasiƙar’ da ya aiko mana, wato Littafi Mai Tsarki.” Gina ta daɗa cewa, “Karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana ya sa na daɗa kusantar Allah.” Shin kana barin Jehobah ya yi magana da kai kullum ta wajen karanta Kalmarsa Littafi Mai Tsarki kowace rana? Yin hakan zai taimaka maka ka kusaci Allah sosai.

^ sakin layi na 5 Don ƙarin bayani a kan yadda addu’a za ta taimaka mana mu kusaci Allah, ka duba babi na 17 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.