Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Sani?

Ka Sani?

Yaya ake ba da gudummawa a haikali a zamanin Yesu?

A zamanin Yesu, asusun haikalin suna cikin Farfajiyar Mata. Littafin nan The Temple—Its Ministry and Services ya ce: “A tsakanin ginshiƙai da suka kewaye farfajiyar, an jera asusu ko kuma ‘kakaki’ goma sha uku a jikin bango, [inda] ake saka gudummawa.”

An kira waɗannan asusun kakaki domin suna da siririn baki da kuma gindi mai faɗi. An manna alama a jikin kowane asusu don a nuna irin gudummawar da ya kamata a saka a ciki, kuma ana tara kuɗin da aka samu a cikin asusun don a yi wasu takamammun ayyuka da su. Yesu yana cikin Farfajiyar Mata ne a lokacin da ya ga mutane da yawa suna ba da gudummawa, har da wata gwauruwa matalauciya.—Luka 21:1, 2.

An keɓe asusu biyu don saka harajin haikali, ɗaya don harajin bara, ɗaya kuma don harajin bana. An keɓe asusu na 3 don gudummawar sayan kurciyoyi, na 4 don tantabaru, na 5 don itace, na 6 don turare, kuma na 7 don sayan tandayen zinari. Idan mutum ya kawo gudummawa fiye da wadda aka ayyana, zai iya saka abin da ya rage a cikin ɗaya daga cikin asusun da suka rage. Ana saka kuɗin da ya rage bayan an ba da gudummawa na hadayun zunubai a asusu na 8, a na 9 kuma hadayun laifi, a na 10 hadayun tsuntsaye, a na 11 hadayun masu hidimar Naziri kuma a na 12 hadayun kutaren da suka warke. An keɓe asusu na 13 ne don gudummawa ta son rai.

Shin Luka marubucin Littafi Mai Tsarki sahihin masanin tarihi ne?

Luka ya rubuta littafin Ayyukan Manzanni da kuma Linjilar da ake kira Luka. Luka ya ce ya “bi diddigin kowane abu daidai tun farko,” amma wasu masana sun yi sūkar abubuwan da Luka ya rubuta. (Luka 1:3) Shin abubuwan da ya rubuta sun yi daidai kuwa?

A rubutunsa, Luka ya ambata abubuwan da za a iya tabbatar da aukuwarsu. Alal misali, ya ambata laƙabin wasu ma’aikatan gwamnatin Roma da ba a san da su sosai ba. A yau, an sauya waɗannan laƙabin da mahukunta a Tasalonika; manyan hakimai na Asiya da dai sauransu. (Ayyukan Manzanni 16:20; 17:6; 19:31) Luka ya kira Hiridus Antibas da laƙabin nan muƙaddas, kuma ya kira Sarjiyus Bulus muƙaddashin Ƙubrus.—Ayyukan Manzanni 13:1, 7.

Yadda Luka ya yi amfani da laƙabin da suka dace yana da muhimmanci sosai domin a duk lokacin da aka canja matsayin wani yanki a ƙarƙashin mulkin Roma, laƙabin mai sarautar yankin ma zai canja. Duk da haka, wani manazarcin Littafi Mai Tsarki mai suna Bruce Metzger ya ce: “Kowane laƙabin da aka yi amfani da shi a Ayyukan Manzanni ya dace da yankin da kuma zamanin.” Shi ya sa wani masani mai suna William Ramsay ya kira Luka “ƙwararren masanin tarihi.”