ABIN DA KE SHAFIN FARKO | ZA KA IYA KUSANTAR ALLAH
Rayuwa Mafi Inganci Ke Nan
Me za ka iya yi don ka kusaci Allah? Mun riga mun tattauna waɗannan matakai da za ka iya ɗauka don ka ƙulla dangantaka ta kud-da-kud da Allah:
-
Ka san sunan Allah, wato Jehobah kuma ka riƙa amfani da shi.
-
Ka riƙa yin addu’a ga Allah kuma ka karanta Littafi Mai Tsarki a kai a kai.
-
Ka dāge wajen yin abubuwan da za su faranta wa Jehobah rai.
Yanzu da ka san waɗannan matakan, shin za ka iya cewa kana yin abin da zai sa ka kusaci Allah? Shin akwai inda kake bukatar ka daɗa ƙoƙari? Hakika, yin hakan ba zai zama da sauƙi ba, amma ba aikin banza ba ne.
Jennifer daga Amirka ta ce, “Idan mutum ya yi ƙoƙari ya ƙulla dangantakata da Allah, ba zai taɓa yin da-na-sani ba.” Ta daɗa da cewa, “Irin wannan dangantakar tana kawo albarka sosai. Tana sa mutum ya dogara ga Allah sosai, ya san shi sosai kuma ya ƙaunace shi sosai. Hakika, rayuwa mafi inganci ke nan!”
Idan kana so ka ƙulla dangantaka ta kud-da-kud da Allah, Shaidun Jehobah za su taimaka maka ka yi hakan ta wajen yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kai kyauta. Ƙari ga haka, za ka iya halartan taro a Majami’ar Mulki, wato inda suke taro a yankinku don su tattauna Littafi Mai Tsarki kuma za ka ji daɗin yin tarayya da waɗanda suke daraja dangantakarsu da Allah. * Yayin da kake hakan, za ka ji kamar wani marubucin zabura da ya ce: “Ya yi mani kyau in kusanci Allah.”—Zabura 73:28.
^ sakin layi na 9 Idan kana so a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da kai ko kana so ka san inda Majami’ar Mulki take a yankinku, don Allah ka sanar da wanda ya ba ka mujallar nan ko ka shiga dandalinmu na www.pr418.com/ha kuma ka duba ƙarshen shafin farko, inda aka rubuta KA TUNTUƁE MU.