Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki

Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki

Zai yiwu gwamnati guda ta mallaki dukan duniya?

Ta yaya gwamnati guda za ta haɗa kan dukan mutane? Ishaya 32:1, 17; 54:13

Ka yi tunani a kan yadda ’yan Adam za su amfana idan gwamnati guda ta mallaki dukan duniya. A yau, mutane da yawa suna shan wuya domin talauci, alhali kuma wasu suna da wadata sosai. Amma gwamnatin da ta san bukatun talakawanta za ta iya tabbata cewa sun sami biyan bukata. Kana ganin zai yiwu ’yan Adam su kafa irin wannan gwamnati kuwa?—Karanta Irmiya 10:23.

Tun lokacin da ’yan Adam suka soma sarauta, sun kasa biyan yawancin bukatun talakawansu musamman ma na mabukata. Wasu masu mulki suna wulaƙanta talakawansu. (Mai-Wa’azi 4:1; 8:9) Amma Allah Maɗaukaki ya yi alkawarin samar da gwamnatin da za ta sauya dukan gwamnatocin duniya. Sarkinta zai kula da talakawansa sosai.—Karanta Ishaya 11:4; Daniyel 2:44.

Mene ne Mulkin Allah zai cim ma?

Jehobah ya zaɓi Ɗansa ya yi sarauta bisa duniya kuma shi ne shugaban da ya fi dacewa. (Luka 1:31-33) Yesu ya taimaka wa mutane sosai sa’ad da yake duniya. A matsayinsa na Sarki, zai kawo haɗin kai tsakanin mutanen dukan ƙasashe kuma zai kawar da dukan wahala.—Karanta Zabura 72:8, 12-14.

Dukan mutane ne za su yarda Yesu ya zama Sarkinsu? A’a. Amma Jehobah mai haƙuri ne. (2 Bitrus 3:9) Yana ba mutane dama su amince da Yesu a matsayin sarkinsu. Nan ba da daɗewa ba, Yesu zai halaka dukan miyagu kuma zai sa salama da kwanciyar rai su kasance a dukan duniya.—Karanta Mikah 4:3, 4.