Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | JESUS SAVES—FROM WHAT?

Mutuwar Yesu da Kuma Tashinsa Daga Mutuwa—Yadda Za Su Iya Amfanar Ka

Mutuwar Yesu da Kuma Tashinsa Daga Mutuwa—Yadda Za Su Iya Amfanar Ka

“Ka ba da gaskiya ga Ubangiji Yesu, za ka tsira.”—Ayyukan Manzanni 16:31.

Bulus da Sila ne suka furta waɗannan sanannun kalmomin ga wani mai gādin fursuna a birnin Filibi a Makidoniya. Mene ne kalmomin nan suke nufi? Idan muna so mu san yadda yin imani da Yesu yake da alaƙa da ceto, wajibi ne mu fara sanin dalilin da ya sa muke mutuwa. Ka yi la’akari da abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki.

Ba a halicci mutum don ya mutu ba

Sai Ubangiji Allah ya ɗauki mutum, ya sanya shi cikin gonar Adnin domin shi aikace ta, shi tsare ta kuma. Ubangiji Allah kuma ya dokaci mutumin, yana cewa, an yarda maka ka ci daga kowane itacen gona a sāke: amma daga itace na sanin nagarta da mugunta ba za ka ɗiba ba ka ci: cikin rana da ka ci, mutuwa za ka yi lallai.”—Farawa 2:15-17.

Sa’ad da Allah ya halicci mutumi na farko, wato Adamu, ya saka shi cikin aljanna a duniya, wani wuri mai dabbobi da kuma itatuwa masu kyau. Adamu na iya cin ’ya’yan itatuwan a duk lokacin da yake so. Amma Jehobah ya nuna wa Adamu wani itace kuma ya gaya masa dalla-dalla cewa kada ya ci ’ya’yan itacen domin idan ya yi hakan, zai mutu.

Shin Adamu ya fahimci muhimmancin wannan dokar? Ya san me ake nufi da mutuwa domin ya ga yadda dabbobi suke mutuwa. Da a ce Allah ya halicci Adamu don ya mutu ne, da wannan gargaɗi ba ta kasance da wani muhimmanci ba. A maimakon hakan, Adamu ya fahimci cewa idan ya yi biyayya da Allah kuma ya ƙi ya ci ’ya’yan itacen, zai rayu har abada.

Wasu suna ganin itacen na wakiltar jima’i, amma hakan ba gaskiya ba ne. Jehobah ya so Adamu da matarsa Hawwa’u su “yalwata da ’ya’ya” kuma su ‘mamaye duniya, su mallake ta.’ (Farawa 1:28) Wannan gargaɗin game da itace na zahiri ne. Jehobah ya kira itacen “itace na sanin nagarta da mugunta” domin yana wakiltar ikonsa na kafa wa mutane dokoki. Da a ce Adamu bai ci ’ya’yan itacen ba, da ya nuna cewa yana yin biyayya da kuma godiya ga Allahn da ya halicce shi kuma ya ba shi abubuwa masu kyau.

Adamu ya mutu domin ya yi rashin biyayya ga Allah

[Allah] ya ce wa Adamu, don ka . . . ci kuma daga cikin itacen, wanda na dokace ka, . . . sai da jiɓi a fuskarka za ka ci abinci, har kuma ka koma ƙasa; gama daga cikinta aka ciro ka: gama turɓaya ne kai, ga turɓaya za ka koma.”—Farawa 3:17, 19.

Kamar yadda Jehobah ya faɗa, Adamu ya mutu. Allah ya halicci Adamu daga “turɓayar ƙasa” kuma ya gaya masa cewa zai koma “turɓaya.” Adamu bai koma wani wuri dabam don ya ci gaba da rayuwa ba kuma bai canja siffarsa ba. Amma sa’ad da ya mutu, ya zama turɓayar ƙasa.—Farawa 2:7; Mai-Wa’azi 9:5, 10.

Muna mutuwa don mu ’ya’yan Adamu ne

“Zunubi ya shigo cikin duniya ta wurin mutum ɗaya, mutuwa kuwa ta wurin zunubi; har fa mutuwa ta bi kan dukan mutane, da yake duka sun yi zunubi.”—Romawa 5:12.

Sakamakon rashin biyayya ko kuma zunubin da Adamu ya yi bai shafe shi kaɗai ba. Sa’ad da ya yi zunubi, ya hana kansa da kuma zuriyarsa damar yin rayuwa har abada. Ƙari ga haka, Adamu ya zama ajizi sa’ad da ya yi zunubi kuma ya jawo wa zuriyarsa wannan sakamakon ma.

Dukanmu ’ya’yan Adamu ne. Daga wurinsa ne muka gāji ajizanci da kuma mutuwa. Bulus ya kwatanta irin mummunan halin da muke ciki sa’ad da ya ce: “Ni kuwa mai halin mutuntaka ne, bautar zunubi kawai nake yi. Kaitona! Wa zai cece ni daga jikin nan wanda ke kai ni ga mutuwa?” Bulus ya ba da amsar tambayar da kansa kuma ya ce: “Godiya tā tabbata ga Allah, . . . ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu!”—Romawa 7:14, 24, 25, LMT.

Yesu ya sadaukar da ransa don mu rayu har abada

“Uba ya aike Ɗan ya zama Mai Ceton duniya.”—1 Yohanna 4:14.

Jehobah ya shirya mana yadda za mu shawo kan zunubi kuma mu sami ’yanci daga sakamakon mutuwa ta har abada. Ta yaya? Ya aiko Ɗansa da yake ƙauna sosai daga sama zuwa duniya don ya zama mutum. Amma Yesu bai “yi zunubi ba” kamar yadda Adamu ya yi. (1 Bitrus 2:22) Domin shi kamiltacce ne, sakamakon zunubi bai shafe shi ba, kuma da a ce ya ga dama, da ya ci gaba da rayuwa a duniya a matsayin mutum har abada.

A maimakon haka, Jehobah ya bar maƙiyan Yesu su kashe shi. Bayan kwana uku, Jehobah ya ta da shi daga mutuwa a matsayin ruhu domin ya iya komawa sama. Yesu yana da ’yanci ya ci gaba da rayuwa a duniya a matsayin mutum, amma yayin da ya koma sama, ya sadaukar da wannan ’yancin don Allah ya yi amfani da ’yancin ya fanshi ’yan Adam. Jehobah ya yarda da wannan sadaukarwar, kuma ya buɗe hanyar yin rayuwa har abada ga dukan mutanen da suka yi imani da Yesu.—Romawa 3:23, 24; 1 Yohanna 2:2.

Ta hakan, Yesu ya samo mana abin da Adamu ya yi watsi da shi. Ya mutu domin mu rayu har abada. Littafi Mai Tsarki ya ce Yesu ya mutu ne “domin bisa ga alherin Allah ya ɗanɗana mutuwa sabili da kowane mutum.”—Ibraniyawa 2:9.

Wannan shirin da Jehobah ya yi ya nuna mana halinsa. Domin shi Allah mai adalci ne, ’yan Adam ajizai ba su iya fanshi kansu daga mutuwa ba. Amma saboda ƙauna da kuma jin kai, Allah ya sadaukar da Ɗansa don ya fanshi ’yan Adam.—Romawa 5:6-8.

Za a ta da mutane daga mutuwa kamar yadda aka ta da Yesu

“An ta da Almasihu daga matattu, shi ne ma nunan fari na waɗanda suka yi barci. Tun da yake mutuwa ta wurin mutum ta faru, haka kuma tashin matattu ta wurin mutum yake. Kamar yadda duk ake mutuwa saboda Adamu, haka duk za a rayar da kowa saboda Almasihu.”—1 Korintiyawa 15:20-22, LMT.

Mun tabbata cewa Yesu ya zo duniya kuma ya mutu, amma akwai abin da ya tabbatar mana da cewa ya tashi daga mutuwa? Ɗaya daga cikin hujjoji masu ƙarfi da suke nuna cewa Yesu ya tashi daga mutuwa shi ne bayyanuwarsa ga mutane da yawa a wurare dabam-dabam. A wani lokaci, ya bayyana ga mutane fiye da 500. Manzo Bulus ya yi magana game da wannan bayyanuwar sa’ad da ya rubuta wasiƙa zuwa ga Korintiyawa kuma ya ce wasu cikin mutanen da Yesu ya bayyana wa suna raye har lokacin. Hakan ya nuna cewa mutanen nan za su iya ba da shaidar abin da suka gani da kuma ji.—1 Korintiyawa 15:3-8.

Bulus ya ce Yesu ne “nunan fari” na waɗanda suka tashi daga mutuwa, kuma hakan ya nuna cewa za a ta da wasu mutane daga mutuwa bayan an ta da Yesu. Yesu da kansa ma ya ce lokaci na zuwa da “dukan waɗanda suna cikin kabarbaru” za su “fito.”—Yohanna 5:28, 29.

Wajibi ne mu yi imani da Yesu idan muna so mu rayu har abada

“Saboda ƙaunar da Allah ya yi wa duniya har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya halaka, sai dai ya sami rai madawwami.”—Yohanna 3:16, LMT.

Shafuffuka na farko a cikin Littafi Mai Tsarki sun yi bayani a kan yadda mutuwa ta shigo duniya da kuma yadda aka yi hasarar Aljanna. Shafuffuka na ƙarshe sun yi bayani a kan lokacin da Allah zai kawar da mutuwa kuma ya mayar da duniyar nan Aljanna. A lokacin, mutane za su yi rayuwa mai ma’ana har abada. Ru’ya ta Yohanna 21:4 ta ce: ‘Mutuwa ba za ta ƙara kasancewa ba.’ Da yake Allah yana so ya tabbatar mana cewa alkawarin nan zai cika, ya faɗa a aya ta 5 cewa kalmomin “masu-aminci ne masu-gaskiya.” Jehobah yana cika dukan alkawuransa.

Shin ka gaskata cewa waɗannan kalmomin “masu-aminci ne masu-gaskiya”? Idan haka ne, ka ƙara koyo game da Yesu Kristi kuma ka yi imani da shi. Idan ka yi hakan, za ka sami amincewar Jehobah. Zai albarkace ka yanzu kuma za ka kasance da begen yin rayuwa a cikin Aljanna a duniya har abada, ba tare da mutuwa ko “baƙin ciki, ko kuka, ko azaba” ba.