Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | YESU YANA CETONMU—FROM WHAT?

Dalilin da Ya Sa Muke Bukatar Ceto

Dalilin da Ya Sa Muke Bukatar Ceto

‘Mutum duka kwanakin ransa gajere ne, kwanakin wahala kuwa. Yakan yi girma ya bushe nan da nan kamar furanni.’—Ayuba 14:1, 2, Littafi Mai Tsarki.

Mutane sun daɗe suna sha’awar yin rayuwa har abada, ba tare da tsufa ba. Amma, abin baƙin cikin shi ne: Muna mutuwa. Wannan furucin da Ayuba ya yi fiye da shekaru dubu uku da suka shige suna faruwa har yau.

A ko’ina a faɗin duniya, mutane suna sha’awar yin rayuwa har abada. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa Allah ya halicce mu da sha’awar yin rayuwa har abada da kuma sha’awar sanin abin da hakan yake nufi. (Mai-Wa’azi 3:11) Saboda wannan, kana ganin Allah da yake ƙaunarmu zai sa mu yi sha’awar abin da ba za mu iya cim ma ba? Idan amsarka a’a ce, to ka yi daidai. A cikin Kalmar Allah, an kira mutuwa maƙiyiya kuma an yi alkawari cewa ‘za a kawar da mutuwa.’—1 Korintiyawa 15:26.

Babu shakka, mutuwa maƙiyiya ce. Babu wani a cikin hankalinsa da zai so ya mutu. A duk lokacin da muka ga cewa mummunar abu za ta auko mana, mukan nemi hanyoyin guje ta. Idan muka yi ciwo, mukan nemi magani. Muna iyakacin ƙoƙari mu ga cewa mun guji duk wani abin da zai kashe mu.

Shin akwai abubuwa da za su iya tabbatar mana cewa za a kawar da wannan maƙiyiyar? Ƙwarai kuwa. Jehobah, wanda shi ne Mahalicci, bai yi mutane don su yi rayuwa na ’yan shekaru kawai sa’an nan su mutu ba. Ba nufin Allah ba ne mutane su riƙa mutuwa. Asali dai, ya nufe su da rayuwa har abada, kuma yana cim ma dukan nufe-nufensa.—Ishaya 55:11.

To, ta yaya za a kawar da mutuwa? A duk tarihin ’yan Adam, mutane sun ƙoƙarta su kawar da mutuwa, amma ba su yi nasara ba, kuma har yanzu suna kan neman hanyar kawar da ita. Masana kimiyya sun fitar da rigakafi da kuma magunguna da dama don shawo kan wasu cututtuka. Sun kuma yi nazarin tsarin ƙwayoyin halittu na abubuwa masu rai. A wurare da yawa, mutane suna da tsawon rai yanzu fiye da yadda yake shekaru 100 da suka shige. Duk da haka, ba a kawar da mutuwa ba tukun. Hakan ya yi daidai da abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa cewa: ‘Turɓaya za mu koma.’—Mai-Wa’azi 3:20.

Abin farin ciki shi ne, ba ma bukatar mu dogara da hikimar ’yan Adam don kawar da wannan matsalar. Jehobah ya riga ya shirya yadda zai cece mu daga mutuwa kuma zai yi amfani da Yesu Kristi wajen cim ma hakan.