Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TARIHI

Na Sami Abin da Ya Fi Suna Daraja

Na Sami Abin da Ya Fi Suna Daraja

Sa’ad da nake matashiya a shekara ta 1984, an raɗa mini Sarauniyar Kyau na Birnin Hong Kong. An saka hotunana a bangon jaridu da kuma mujallu da yawa. Na yi waƙa, na yi rawa, na ba da jawabai, na yi shirye-shiryen talabijin, na saka tufafi masu kyau kuma na yi cuɗanya da manya-manyan mutane kamar su gwamnar Hong Kong.

Bayan shekara ɗaya, sai na soma yin fina-finai, sau da yawa ni ce tauraruwa a fim da muka yi. Maneman labarai suna son tarihina, masu ɗaukan hoto suna son hotunana, mutane da yawa kuma suna so in kasance a lokacin da ake yin lancin ko kuma in zo fatin da suka shirya. Hakan ya sa na zama sananniya sosai.

Lokacin da nake fim ɗin yaƙi

Da sannu-sannu, sai na fahimci cewa dukan waɗannan abubuwan ba sa burge ni kamar yadda nake tsammani. Ina yawan yin fim da ake faɗa kuma yin hakan na da haɗari sosai. Masu yin fina-finai a birnin Hong Kong ba sa hayan wani ya taimake su yin wani sashe na fim kamar yadda ’yan fina-finan Amirka suke yi. Saboda haka, ni ke yin waɗannan abubuwan da kaina kamar su tuka babur a kan mota. Fina-finai da yawa da na yi na lalata ne da kuma mugunta, wasu kuma na sihiri.

Na auri wani mai shirya fim a shekara ta 1995. Ina da abubuwan da ya kamata su sa ni farin ciki kamar su suna da wadata da kuma mijin da ke so na sosai, amma duk da haka, ba na farin ciki. Sai na daina yin fim.

ADDININ DA NA BI SA’AD DA NAKE ƘARAMA

Na soma tunani a kan addinin da na bi sa’ad da nake ƙarama. A lokacin, ni da yayata muna ziyartar wani iyalin Shaidun Jehobah kowace Asabar. Shugaban iyalin mai suna Joe McGrath yana nazarin Littafi Mai Tsarki da mu da kuma ’ya’yansa uku. Suna farin ciki sosai a iyalinsu kuma shugaban iyalin yana kyautata wa matarsa da kuma yaransa. Ina kuma jin daɗin halartan taron Kirista da su. A wasu lokuta ma, muna halartan manyan taro. Wannan lokaci ne da mutane suke farin ciki sosai. Hankalina ba ya tashi sa’ad da nake tare da Shaidun Jehobah.

Akasin haka, munanan abubuwa sun faru da ni a gidanmu. Salon rayuwar babana ya ta da hankalin mahaifiyata sosai, har ta soma baƙin ciki mai tsanani. Sa’ad da na kusan kai shekara goma, mahaifiyata ta daina cuɗanya da Shaidun Jehobah. Amma na ci gaba da yin tarayya da su ko da yake ba na yin hakan da dukan zuciyata. Na yi baftisma sa’ad da nake ’yar shekara 17. Jim kaɗan bayan haka, na yi abin da ya saɓa wa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kuma na daina tarayya da ikilisiya.

NA YANKE SHAWARAR DAWOWA

Jim kaɗan bayan bikin aurena, dattawa biyu daga ikilisiyar Shaidun Jehobah da ke unguwarmu sun ziyarce ni. Sun bayyana min abin da zan yi don in komo ga Jehobah, bayan haka, sai suka ce wata ’yar’uwa da take wa’azi a ƙasashen waje mai suna Cindy ta taimake ni. A wannan lokacin, bangaskiyata ta riga ta yi sanyi, don haka sai na ce ta tabbatar mini cewa Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah ce. Ta nuna mini wasu annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki da suka cika. Da sannu-sannu muka zama ƙawaye kuma ta ce mu yi nazari a kan wasu muhimman koyarwar Littafi Mai Tsarki. Na amince da hakan. Wannan ne ƙaro na farko da na koya cewa Jehobah, Allah ne mai ƙauna kuma yana son in yi farin ciki.

Sa’ad da na soma halartan taro, na fahimci cewa yin cuɗanya da Shaidu yana sa ni farin ciki fiye da kasancewa tare waɗanda muke yin fina-finai da su. Amma abin da na fuskanta sa’ad da nake ƙarama ya sa na tsani kaina kuma ba na yarda da mutane. Wata ’yar’uwa a ikilisiyarmu ta taimaka mini sa’ad da ta nuna mini daga cikin Littafin Mai Tsarki yadda zan magance matsalolina, kuma na koyi yadda zan nemi abokan kirki.

ABIN DA YA FI SUNA DARAJA

A shekara ta 1997, ni da maigidana mun ƙaura zuwa Hollywood a birnin Kalifoniya, Amirka. A wurin ne na taimaka wa mutane sosai su san Kalmar Allah. Na ji daɗin koyar da Littafi Mai Tsarki fiye da kasancewa da suna da kuma zama tauraruwa a fina-finai. Alal misali, a shekara ta 2002, na sami wata mai suna Cheri da muka taɓa yin aiki tare a birnin Hong Kong. Tarihina da nata kusan iri ɗaya ne. An raɗa mata Sarauniyar Kyau a birnin Hong Kong kafin ni. Ita ce ta saka mini rawanin a lokacin da aka ba ni wannan matsayin. Ta zama ’yar wasa da kuma mai shirya fina-finai, tana aiki da darektocin da suke tashe. Ita ma ta ƙaura zuwa Hollywood.

Na ji tausayin Cheri sa’ad da na ji cewa saurayinta ya rasu sanadiyyar ciwon zuciya. Mabiyan addinin Buddha ba su iya ta’azantar da ita ba. Ta yi sunan da mutane da yawa suke nema ido a rufe, duk da haka, ba ta yi farin ciki ba kuma ba ta yarda da kowa. Sai na soma koya mata abin da na koya daga Littafi Mai Tsarki amma da yake ita mabiyar Buddha ce, ba ta ɗauki abin da muhimmanci sosai ba.

Ƙawata Cheri tana fim

Cheri ta kira ni wata rana a shekara ta 2003, daga birnin Vancouver, a ƙasar Kanada, inda ta je yin fim. Da fara’a ta gaya min cewa tana tuƙi kuma tana sha’awar abubuwan da take gani a karkarar sai farat ɗaya ta soma yin addu’a tana cewa: “Ka gaya mini, Kai ne Allah na gaskiya? Mene ne sunanka? Sai ga shi kawai ta wuce a gaban wata Majami’ar Mulki kuma ta ga sunan Jehobah. Ta ga cewa lallai Allah ne ya amsa addu’arta, don haka, ta so ta haɗu da Shaidun Jehobah nan da nan. Na taimake ta binciko wurin da ake taro na yaren Caina a birnin Vancouver kuma ta soma halartan taron bayan ’yan kwanaki.

Cheri ta gaya min cewa: “Mutanen da na haɗu da su a wurin suna ƙaunata sosai. Ina iya gaya musu yadda nake ji.” Na yi farin cikin jin hakan don a lokacin da take sana’ar fim, ba ta da abokai. Cheri ta ci gaba da halartan taro. Amma a shekara ta 2005, ta karɓi kwangilar yin wasu fina-finai biyu a ƙasar Caina kuma hakan ya sa ta koma birnin Hong Kong. Abin farin ciki shi ne, a shekara ta 2006, Cheri ta yi baftisma a babban taro na Shaidun Jehobah a birnin Hong Kong. Ko da yake ta so ta yi wa Jehobah ibada sosai amma sana’ar fim ta sa hakan ya zama da wuya, kuma don haka, tana baƙin ciki sosai.

FARIN CIKIN TAIMAKA WA MUTANE

Cheri ta canja salon rayuwarta gaba ɗaya a shekara ta 2009. Don haka, ta tsai da shawarar yin murabus a kamfanin fim don ta yi amfani da duk lokacinta a bautar Jehobah. Ta sami sabbin abokai a ikilisiyar Kirista. Ta soma hidima ta cikakken lokaci tana wa’azi don ta taimaka wa mutane su sami hanyar rai.—Matta 24:14.

Bayan haka, sai Cheri ta tsai da shawarar koyan yaren Nepal don ta taimaka wa wani rukunin Shaidun Jehobah da suke yaren a birnin Hong Kong. Ba a ɗaukan yawancin mutanen Nepal da ke Hong Kong da daraja don ba su iya Turanci ko yaren Caina ba sosai. Ƙari ga haka, ana rena su don al’adunsu dabam ne. Cheri ta gaya min cewa tana jin daɗin taimaka musu su san Littafi Mai Tsarki. Alal misali, ta ce wata rana da take wa’azi, ta haɗu da wata mata da ke yaren Nepal da aka taɓa gaya mata wasu abubuwa game da Yesu amma ba ta san Allah na gaskiya, wato Jehobah ba. Cheri ta yi amfani da Littafi Mai Tsarki don ta taimaka wa matar ta fahimci cewa Yesu ya yi addu’a ga Ubansa na sama. Sa’ad da matar ta fahimci cewa za ta iya yin addu’a ga Allah na gaskiya mai suna Jehobah, sai ta amince da bisharar. Bayan haka, maigidanta da ’yarta ma suka soma nazarin Littafi Mai Tsarki.—Zabura 83:18; Luka 22:41, 42.

Cheri a yau

Da na ga yadda Cheri take jin daɗin hidima ta cikakken lokaci, sai na tambayi kaina, ‘Me zai hana ni yin hakan?’ A lokacin, na riga na koma birnin Hong Kong. Sai na tsai da shawarar tsara ayyukana da kyau don in ƙara ƙwazo wajen koya wa mutane Littafi Mai Tsarki. Na fahimci cewa sauraron mutane da kuma taimaka musu su san Kalmar Allah ne ke sa ni farin ciki sosai.

Na fahimci cewa taimaka wa mutane su san Kalmar Allah ne ke sa ni farin ciki sosai

Alal misali, na taɓa nazarin Littafi Mai Tsarki da wata ’yar Vietnam da take yawan baƙin ciki da kuma kuka. Yanzu tana farin ciki kuma tana cuɗanya da ikilisiya.

Ni da Cheri mun sami wani abin da ya fi suna daraja. Ko da yake yin fina-finai yana da daɗi kuma yana sa a san da mu, amma koya wa mutane game da Jehobah ya fi kawo farin ciki don yana sa a daraja Jehobah. Hakika, mun ga cikawar furucin Yesu da ya ce: “Bayarwa ta fi karɓa albarka.”—Ayyukan Manzanni 20:35.