KA YI KOYI DA BANGASKIYARSU | TIMOTAWUS
“Dana Cikin Ubangiji, Kaunatacce, Mai-Aminci.”
TIMOTAWUS ya fito daga gida yana takawa, kuma ya mai da hankalinsa ga abin da yake gab da shaidawa. Abokansa ne suke gaba yayin da suke bin hanyar da Timotawus ya sani sosai. A hankali, a hankali, sun fita daga birnin Listra da ke kan tudu. Timotawus ya yi murmushi yayin da yake tunani a kan mahaifiyarsa da kuma kakarsa domin suna alfahari da shi kuma ba sa so su nuna cewa suna kewarsa yayin da yake barin gida. Shin zai sake juyawa ya yi musu ban kwana?
Daga yanzu, manzo Bulus zai riƙa ƙarfafa Timotawus a kai a kai. Ya san cewa har ila, Timotawus yana jin kunya, amma yana farin ciki domin matashin yana da ƙwazo sosai. Timotawus matashi ne, wataƙila bai kai shekara ashirin ba tukun ko ya ɗan wuce, kuma yana daraja da kuma ƙaunar Bulus sosai. A yanzu haka, Timotawus yana bin wannan mutum mai aminci zuwa wuri mai nisa sosai. Za su yi tafiya da kafa da kuma jirgin ruwa, za su kuma fuskanci haɗari a kan hanya. Timotawus bai san ko zai sake dawowa gida ba.
Mene ne ya motsa wannan matashin ya biɗi irin wannan rayuwar? Wace albarka ce zai samu don wannan sadaukarwar da zai yi? Kuma wane darasi za mu koya daga bangaskiyar Timotawus?
‘TUN YANA JARIRI’
Bari mu ɗan tattauna abin da ya faru a birnin Listra shekaru biyu ko uku kafin abin da muka ambata ɗazun ya faru. Listra wani ƙaramin gari ne da ke kwari kuma akwai rafi a wurin. Wataƙila mutanen garin suna jin yaren Helas, amma ainihin yarensu Likoniyanci ne. Wata rana, sai hayaniya ta tashi a garin. Me ya jawo wannan hayaniyar? Wasu Kiristoci biyu, wato manzo Bulus da abokin tafiyarsa, Barnaba sun zo daga wani babban birni da ke kusa, wato Ikoniya. Sa’ad da suke wa’azi, sai Bulus ya hangi wani gurgu da ya nuna cewa yana da bangaskiya sosai. A sakamakon haka, Bulus ya warkar da shi ta hanyar mu’ujiza.—Ayyukan Manzanni 14:5-10.
Mutanen Listra sun gaskata cewa allolinsu suna yin shigan mutane a zamanin dā kuma su shigo cikin garin. Saboda haka, sun yi tsammanin cewa Bulus wani allahnsu ne mai suna Harmasa, Barnaba kuma Zafsa! Waɗannan Kiristoci masu tawali’u sun sha da ƙyar don su hana mutanen yi musu hadaya.—Ayyukan Manzanni 14:11-18.
Amma wasu mutane a Listra sun san cewa ba allahn ƙarya ba ne ya shigo cikin garinsu. Alal misali, wata Bayahudiya mai suna Afiniki wadda maigidanta wani Bahelane * ne da ba Kirista ba, da kuma mahaifiyarta Loyis, sun saurari Bulus da Barnaba sosai. Sun ji abin da kowane Bayahude zai so ya ji, wato cewa Almasihu ya zo kuma ya cika dukan annabcin da aka yi game da shi a cikin Nassosi.
Ka yi tunani a kan yadda ziyarar Bulus ta shafi Timotawus. An riga an koyar da Timotawus ‘tun yana jariri’ don ya so littattafai masu tsarki na 2 Timotawus 3:15) Timotawus ya bi misalin mahaifiyarsa da kuma kakarsa domin ya yi imani da abin da Bulus da kuma Barnaba suka koyar game da Almasihu. Ka yi la’akari kuma da gurgun da Bulus ya warkar. Babu shakka, tun Timotawus yana ƙarami, ya saba ganin wannan mutumin a kan titin Listra. Amma yanzu, Timotawus ya gan mutumin yana tafiya! Irin waɗannan abubuwan ne suka motsa Afiniki da Loyis da kuma Timotawus su zama Kiristoci. A yau ma, iyaye da kuma kakanni za su iya koyan darussa daga Loyis da Afiniki. Shin za ku iya kafa wa matasa misali mai kyau?
Nassosin Helenanci. (“TA WURIN WAHALA DA YAWA”
Babu shakka, mutanen da suka zama Kiristoci a Listra sun yi farin cikin sanin begen da mabiyan Kristi suke da shi. Amma sun kuma koyi cewa ba daɗi kaɗai za su riƙa ji ba. Yahudawa masu tsattsauran ra’ayin daga Ikoniya da kuma Listra sun shigo cikin gari kuma suka zuga mutanen don su yi wa Bulus da Barnaba dūka. Ba da daɗewa ba, sai mutanen suka zo suna jifan Bulus da duwatsu har ya faɗi a ƙasa. Da ganin haka, sai mutanen suka jawo shi zuwa bayan birnin suna tsammani cewa ya mutu.—Ayyukan Manzanni 14:19.
Amma, almajiran da ke Listra suka zo wurin Bulus kuma suka kewaye shi. Babu shakka, sun yi murna sa’ad da Bulus ya juya, ya tashi kuma ya sake koma birnin Listra da gaba gaɗi. Washegari, sai shi da Barnaba suka je Darba don su ci gaba da wa’azinsu. Bayan sun taimaka wa mutane da yawa su zama Kiristoci, sai suka sake komawa Listra. Wane sakamako suka samu? Littafi Mai Tsarki ya ce “suna ƙarfafa rayukan masu-bi, suna yi masu gargaɗi su lizima a cikin imani. Ka yi tunanin yadda Timotawus yake saurarawa yayin da Bulus da Barnaba suke koya wa Kiristocin cewa za su sami albarka sosai a nan gaba don zaɓin da suka yi. Suka ce: “Sai ta wurin wahala da yawa za mu shiga Mulkin Allah.”—Ayyukan Manzanni 14:20-22.
Timotawus ya ga yadda Bulus ya sha wahala sosai don ya yaɗa bishara ga wasu. Saboda haka, Timotawus ya san cewa idan ya bi misalin Bulus, mutanen Listra za su tsananta masa, wataƙila har da mahaifinsa ma. Duk da haka, Timotawus bai ƙyale hakan ya hana shi bauta wa Allah ba. Akwai matasa da yawa a yau da suke kamar Timotawus. Suna yin abokai da mutanen da suke da imani sosai da za su ƙarfafa su. Kuma ba sa ƙyale tsanantawa ta hana su bauta wa Allah na gaskiya ba!
‘ ’YAN’UWA NA YABONSA’ SOSAI
Kamar yadda muka ambata ɗazun, wataƙila Bulus ya kai wannan ziyarar bayan shekara biyu ko uku. Ka yi tunanin irin farin cikin da iyalin Timotawus suka yi sa’ad da Bulus da kuma Sila suka zo wurinsu. Babu shakka, Bulus ma ya yi farin ciki sosai. Ya ga sakamakon wa’azin da ya yi a Listra. Ya ga Loyis da Afiniki ‘yarta sun zama Kiristoci masu aminci, suna da “bangaskiya marar-riya,” kuma wannan hali ne da Bulus yake sha’awa sosai. (2 Timotawus 1:5) Timotawus kuma fa?
Bulus ya sami labari cewa tun ziyararsa ta farko, matashin ya daɗa manyanta. “’Yan’uwa da ke Listira” da kuma Ikoniya a arewa matso gabashin garin, wanda yake da nisan wajen mil 20 (kilomita 32) suna ‘yabon’ Timotawus. (Ayyukan Manzanni 16:2, Littafi Mai Tsarki) Yaya aka yi Timotawus ya yi suna haka?
“Littattafai masu-tsarki” da mahaifiyar Timotawus da kuma kakarsa suka koya masa ‘tun yana jariri’ sun ƙunshi shawarwari masu kyau don matasa. (2 Timotawus 3:15) Ga wani misali: “Ka tuna da Mahaliccinka kuma a cikin kwanakin ƙuruciyarka.” (Mai-Wa’azi 12:1) Waɗannan kalmomin sun taimaki Timotawus sosai sa’ad da ya zama Kirista. Ya lura cewa hanya mafi kyau na tuna da Mahaliccinsa ita ce yaɗa bishara game da Ɗan Allah, wato Kristi. Da sannu-sannu, Timotawus ya daina jin kunya kuma ya yi gaba gaɗi sosai wajen yaɗa bishara game da Yesu Kristi.
Mazan da ke ja-gora a cikin ikilisiyar sun lura cewa Timotawus yana samun ci gaba. Babu shakka, sun yi farin cikin ganin yadda yake ƙarfafa mutanen da yake haɗuwa da su. Amma abu mafi muhimmanci shi ne, Jehobah ya lura da Timotawus. Allah ya sa a yi wasu annabci game da shi, wataƙila game da irin hidimar da zai yi wa ikilisiyoyi da yawa. Sa’ad da Bulus ya kawo ziyarar, ya lura cewa Timotawus zai kasance da ban taimako a wa’azin da yake yi a ƙasashen waje. ‘Yan’uwan da ke Listra sun amince da hakan. Sun ɗibiya masa hannu, wato sun naɗa shi ya yi aiki na musamman a hidimarsa ga Jehobah.—1 Timotawus 1:18; 4:14.
Babu shakka, wannan aikin da aka ba Timotawus ya sa shi mamaki da kuma tawali’u sosai. Yanzu, ya yi shirin soma hidimarsa. * Amma yaya mahaifin Timotawus wanda ba mai-bi ba ne ya ji sa’ad da ya sami labari cewa ɗansa yana so ya yi wannan hidimar? Wataƙila ya so ɗansa ya biɗi wani maƙasudi dabam. Mahaifiyar Timotawus da kuma kakarsa fa? Shin sun yi alfahari da ɗansu ne duk da cewa sun ɗan damu don kada kome ya same shi? Da alama abin da ya faru ke nan.
Abin da muka sani shi ne, Timotawus ya yi wannan hidimar. A safiyar ranar da muka ambata ɗazun, Timotawus ya soma wa’azi a ƙasashen waje tare da manzo Bulus. Yayin da yake barin Listra, a duk lokacin da ya ɗaga kafa, yana daɗa nisa da garinsu zuwa wurin da bai sani ba. Bayan su uku sun yi kwanaki da yawa suna tafiya, sai suka isa birnin Ikoniya. Sai Timotawus ya soma lura da yadda Bulus da Sila suke gaya wa ‘yan’uwan umurnin hukumar da ke kula da ayyukan Kiristoci a lokacin kuma suna ƙarfafa ‘yan’unsu da ke Ikoniya. (Ayyukan Manzanni 16:4, 5) Amma wannan mafari ne kawai.
Bayan sun ziyarci ikilisiyoyin da ke Galatiya, sai suka bi ta Roma kuma suka yi tafiya mai nisa. Suka ratsa ta Firijiya kuma suka nufi arewa, bayan haka, sai suka yi yamma. Sun ma bi ja-gorar ruhu mai tsarki na Allah, sa’ad da suka je Taruwasa, suka shiga jirgin ruwa zuwa Makidoniya. (Ayyukan Manzanni 16:6-12) A lokacin, Bulus ya ga cewa Timotawus yana da amfani sosai har ya bar shi a Biriya tare da Sila. (Ayyukan Manzanni 17:14) Ya ma aika Timotawus kaɗai zuwa Tasalonika. A nan, Timotawus ya yi koyi da abin da ya lura kuma ya ƙarfafa Kiristoci masu aminci da ke wurin.—1 Tasalonikawa 3:1-3.
Daga baya, Bulus ya yi wannan furuci game da Timotawus: “Ba ni da kowa wanda hankalinsa ya Filibiyawa 2:20) Ba a dare ɗaya Timotawus ya yi irin wannan sunan ba. Ya sami wannan sunan ta wajen yin aiki tuƙuru da nuna tawali’u da kuma jimre wa yanayi masu wuya. Babu shakka, Timotawus misali ne mai kyau sosai ga matasa a yau! Kada ka manta cewa za ka iya yin suna. Kana da zarafin yi wa kanka suna sa’ad da kake matashi ta wajen saka hidimar Jehobah a kan gaba da mutunta mutane da kuma daraja su.
yi daidai da nasa ba, wanda zai yi tattalin zamanku da gaskiya.” (“KA YI HANZARI KA ZO WURINA”
Timotawus ya yi sama da shekara 14 yana aiki tare da amininsa, manzo Bulus. Su biyu sun fuskanci haɗarurruka kuma sun yi farin ciki a hidimarsu. (2 Korintiyawa 11:24-27) Akwai ma lokacin da aka saka Timotawus a fursuna domin imaninsa. (Ibraniyawa 13:23) Shi ma yana ƙaunar ‘yan’uwansa Kiristoci sosai kamar Bulus. Shi ya sa Bulus ya ce masa: “Ina tunawa da hawayenka.” (2 Timotawus 1:4) Wataƙila Timotawus ya koyi yin “kuka tare da masu-kuka” daga Bulus. Ya yi hakan domin ya sami damar ƙarfafa da kuma ta’azantar da su sosai. (Romawa 12:15) Bari kowanenmu ya koyi yin hakan!
Shi ya sa ba da daɗewa ba, Timotawus ya zama ƙwararren dattijo Kirista. Bulus ya ba shi gatan ziyartar ikilisiyoyi don ya ƙarfafa su da kuma gatan naɗa mazan da suka ƙware a waɗannan ikilisiyoyin su zama dattawa da kuma bayi masu hidima.—1 Timotawus 5:22.
Manzo Bulus yana ƙaunar Timotawus sosai, kuma ya ba shi shawarwari masu kyau kamar yadda uba zai yi ga ɗansa matashi. Ya ƙarfafa Timotawus ya riƙe gatan da yake da shi hannu bibbiyu kuma ya sa kowa ya ga yadda yake samun ci gaba a hidimar Allah. (1 Timotawus 4:15, 16) Ya kuma ce kada Timotawus ya ƙyale ƙuruciyarsa da kuma wataƙila wasu kasawarsa su hana shi yin tsayin daka a kan abin da ya dace. (1 Timotawus 1:3; 4:6, 7, 11, 12) Bulus ya ma ba shi shawara a kan yadda zai magance ciwon da yake yawan yi.—1 Timotawus 5:23.
Yanzu Bulus ya san cewa an kusan kashe shi. Sai ya aika wa Timotawus wani hurarren wasiƙa. A wasiƙar ya ce: “Ka yi matuƙar ƙoƙari ka zo wurina da hanzari.” (2 Timotawus 4:9, LMT) Bulus yana ƙaunar Timotawus sosai har ya kira shi “ɗana cikin Ubangiji, ƙaunatacce, mai-aminci.” (1 Korintiyawa 4:17) Shi ya sa yake son amininsa ya kasance tare da shi yanzu da ya kusan mutuwa. Ya kamata kowanenmu ya tambayi kansa, ‘Shin mutane suna neman taimakona sa’ad da suke cikin yanayi mai wuya?’
Shin Timotawus ya zo wurin Bulus da sauri kuwa? Ba mu san amsar ba. Amma mun san cewa yana ƙoƙartawa wajen ƙarfafa Bulus da kuma wasu mutane da yawa. Timotawus ya cika sunansa da ke nufin, “Mutumin da Ke Daraja Allah.” Ya kafa wa dukanmu, yara da manya misali mai kyau na bangaskiya kuma ya kamata mu yi koyi da shi.
^ sakin layi na 9 Ka duba talifin nan “Ka Sani?” a shafi na 11
^ sakin layi na 20 Timotawus ya ma yarda a yi masa kaciya sa’ad da Bulus ya ce ya yi hakan. Ba domin an bukaci Kiristoci su yi hakan ba, amma domin Bulus ba ya so Yahudawan da zai yi musu wa’azi su ƙi sauraronsu domin mahaifin Timotawus Baheleni ne.—Ayyukan Manzanni 16:3.