Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shin Allah ne yake jawo wahala a duniya?

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

Allah yana jawo wahala kuwa?

Me za ka ce?

  • E

  • A’a

  • Wataƙila

Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce

“Sam, Allah ba mai aikata mugunta ba ne, a wurin Mai Iko Duka ba kuskure.” (Ayuba 34:10, Littafi Mai Tsarki) Ba Allah ba ne yake jawo mugunta da wahalar da ke duniyar nan ba.

Me kuma za mu iya koya daga Littafi Mai Tsarki?

  • “Sarkin duniya,” wato Shaiɗan Iblis ne yake jawo wahala.Yohanna 14:30.

  • Ƙari ga haka, wahala da mugunta suna faruwa sanadiyyar zaɓi marar kyau da mutane suke yi.Yaƙub 1:14, 15.

Wahala za ta taɓa ƙarewa kuwa?

Wasu sun yi imani cewa ’yan Adam za su iya cire wahala idan sun haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen yin hakan. Wasu kuma sun ce da kyar duniyar nan ta gyaru. Mene ne ra’ayinka?

Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce

Allah zai cire shan wahala. “Mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin ciki, ko kuka, ko azaba.”Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4.

Me kuma za mu iya koya daga Littafi Mai Tsarki?

  • Allah zai yi amfani da Yesu wajen cire wahalar da Shaiɗan ya jawo.1 Yohanna 3:8.

  • Masu adalci za su rayu a duniya cikin salama har abada.Zabura 37:9-11, 29.