Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | YADDA ZA KA JI DAƊIN KARANTA LITTAFI MAI TSARKI

Amfanin Karanta Littafi Mai Tsarki

Amfanin Karanta Littafi Mai Tsarki

Wata mai suna Jovy ta ce: “Na ɗauka cewa Littafi Mai Tsarki yana da wuyan fahimta.”

Wata mai suna Queennie ta ce: “Ina ganin kamar Littafi Mai Tsarki ba shi da daɗin karantawa.”

Wani mai suna Ezekiel ya ce: “Yawan shafuffukan Littafi Mai Tsarki yana sa ni ƙyuyar karanta shi.”

Shin irin waɗannan dalilan da aka ambata sun taɓa sa ka ƙi karanta Littafi Mai Tsarki? Mutane da yawa ba sa son karanta Littafi Mai Tsarki. Amma me za ka yi idan ka koyi cewa Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka maka ka yi farin ciki da kuma rayuwa mai ma’ana? Ko kuma idan ka gano cewa da akwai abubuwa da yawa da za ka iya yi da za su sa ka ji daɗin karanta Littafi Mai Tsarki? Za ka so ka san yadda Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka maka?

Ka yi la’akari da abin da wasu suka ce game da albarkar da suka samu sa’ad da suka soma karanta Littafi Mai Tsarki.

Wani mai suna Ezekiel da ya ba shekara 20 baya ya ce: “A dā rayuwata tana kamar wani da ke tuƙa mota ba tare da sanin inda za shi ba. Amma karanta Littafi Mai Tsarki ya kyautata rayuwata sosai. Yana ɗauke da shawarwari masu kyau da zan iya amfani da su kowace rana.”

Wata mai suna Frieda da ta ba shekara 20 baya ta ce: “A dā ina saurin fushi. Amma sa’ad da na soma karanta Littafi Mai Tsarki, na koyi na riƙa kame kaina. Hakan ya sa mutane suna so su yi tarayya da ni sosai kuma yanzu ina da abokai da yawa.”

Wata mata mai suna Eunice da ta ba shekara 50 baya ta ce: “Littafi Mai Tsarki yana taimaka mini na zama mutumiyar kirki kuma na canja halayena marasa kyau.”

Karanta Littafi Mai Tsarki zai taimaka maka ka ji daɗin rayuwa kamar waɗannan mutanen da muka ambata da kuma miliyoyin mutane a duniya. (Ishaya 48:17, 18) Ƙari ga haka, zai taimaka maka ka (1) yanke shawarwari masu kyau, (2) ka samu abokan kirki, (3) ka shawo kan matsaloli (4) kuma mafi muhimmanci, ka koyi gaskiya game da Allah. Shawarwarin da ke cikin Littafi Mai Tsarki daga wurin Allah ne don haka, yana da muhimmanci ka bi su. Allah ba zai taɓa ba ka shawara marar kyau ba.

Abin da ya fi muhimmanci shi ne ka soma karatun. Waɗanne abubuwa ne za su sa ya yi maka sauƙi ka soma karatun kuma ka ji daɗinsa?